Skip to content
Part 48 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Ya sake kallona ya ce ai a gidan za’a bani auren Baba ne zai kara min nayi maza na ce kawu a gida kuma? Ya ce eh mana Adawiyya ga kyawawan yanmata a gida yaushe zanje ina neman a waje? Na yi murmushi na ce ai fa anyi kyawawan yanmata a gidan ga kwalliya sai dai akwai wata da ta fisu kyau kawu iyaka dai bata isa auren bane kawai ya ce wacece? Na ce mishi takwarar Umma Amarya ya sake kallona ya ce yanzu nan Maryam bata isa aure ba? Na ce bata isa ba kawu sha shida ne shekarunta ya çe haka ne.

Washegari muka nufi Legos ni da yaya Almu wurin Anti Rahma naje don in dan tausata anyi sa’a bata dauki auren da wani tsanani ba tunda ya gaya mata cewar Baba ne ya ce zai ba shi ba shi ne ya ce yana so ba, sabanin yanda ni kuma ya ce min shi ya ce yana so lokacin ne na tuna lokacin auren Lailatu nima cewa aka yi min ba yaya Almun ne yake so ba ba şhi kawai aka yi.

Daukar auren yaya Junaidu da sauki da Anti Rahma tayi sai yasa al’amura suka yi matukar yin dadi ta kowane bangare mu’amalla mai dadi ake yi.

Shirin biki sosai akayi gabadayanmu mun rufe gidanmu muka yi a Kaduna muka nufi gida cikin shirin buki sosai.

Baba zai sake bikin wasu ‘ya’yan biki na uku kenan tun bayan aurar damu da yayi sai dai tun daga wancan lokacin bai sake bukin yara masu yawa ba, kamar na wannan karon a yanzu zai yi auren ‘yanmata bakwai ne samari kuma biyar in aka hada da yaya Junaidu mai yin kari shida zai ba da daya kuma a waje.

Mun isa gida duk da ba wannan ne zuwan Lailatu gidan na farko ba nayi matukar kokarina wajen ganin na maida ita ‘yar gida a gidan komai zanyi zan neme ta muyi tare ko da yake ita bata yarda ta zauna a inda nake wai ita ‘yar dakin Umma karama ce don haka can take zuwa tana na mikawa, da daddare na dauki Rabi’atu naje falon  Baba don in kai mishi ita sai na kira Lailatu muka tafi tare muka samu Umma amarya yaya Junaidu da kuma yaya Almu a ciki Baba yana zaune a kasa yayin da Abdulhakam yake kan cinyarshi yayi matukar yin girma sai rigima yake yi mishi yana ta kokarin cire mishi madubin idonshi muka gaishe shi ni da Lailatu na kuma matsa kusa da shi na tura Rabi’atu na ce mata je ki ki gaida Baba ya mika mata hannu ya dauke ta yana cewa ke mai gashin doki wannan gashin dai ba naki ba ne kari uwarki tayi miki don kiyi barazana na ce a’a Baba nata ne ai gashi ne da ita don ma ina yankewa, ban san Ummana ta shigo ba sai ji nayi tana cewa uh ka ji ashana sau daya nefa ta yanke matà gashin amma ka ji ta ce wai tana yankewa gaba daya aka kwashe da dariya.

Umma ta dauki Abdulhakam ta gama ba shi kunnunshi ta ajiye a kasa ya ci gaba da wasanninshi yayin da baba yake tattanbayan Lailatu wasu abubuwa don dai ya nuna mata itama yarshi ce ni kuwa ina kusa da Umma amarya wata magana nake yi mata sai dai ba a ji muna cikın zancen sai naji Baba yana cewa uwata ce dai ban san dalili ba kullum ka ganta a rame dubi yanda ta koma dakin gwanin kyau amma yau dube ta, wai maimakon Ummana ta fadi wata magana ko kuma taja bakin ta tayi shiru sai kawai naji ta ce mishi Adawiyyah ai kishi ne da ita mai tsanani kishi kuwa hana mutum kyan gani yake yi sai kullum ayi ta rama in ba haka ba me ke damunta ba ga ‘yar uwarta nan ba gwanin sha’awa da ita tayi mul-mul.

Jawabin na Umma ya firgita ni a gaban kowa zata ce wai kishi ne yake hana ni yin kiba ban san lokacin da na soma yi mata kuka ba ina cewa ba kishi ba ne Baba, yayi maza ya ce yi shiru uwata ba kishi ba ne amma menene damuwarki?

Na ce mishi kurarrajin baki sun dame ni bana iya cin abinci da yunwa nake wuni da na gaji da hakan nema na ce gara kawai in rinka yin niyya ina yin azumi har kafin su warke. Umma Amarya ta ce to an taba yin haka kullum ana azumi? Ba za a dauki matakin daya dace ba’? Yaya Almu ya ce ai Rabi taurin kai ne da ita umma gata da musu nayi mata magana tun farkon abin ta ce ba haka ba ne kurarraji ne kawa kuma Sun warke, ta ce amma ai kai lalurar da ta kawo kurarrajin aka yi ba ganewan da na yi tonawa kaina asiri kawai na yi a gaban kowa da kowa maimakon in kare kaina daga zargin kishi da Ummana ta yi min sai kawai na sulale na fita daga wurin na bar Baba yana yiwa yaya Almu fada har yana yi mishi barazanar sake rike ni har sai na haihu na yaye kafin ya bar ni in koma dakina tunda dai shi ba zai iya taimakona kan lalurata ba.

Ni kam dakin Umma Amarya naje nayi kwanciyata saboda nasan wurin Ummana a cike yake da jama’a, Umma Amarya ta shigo ta same ni yanzu yau da kike yi Azumin da me kika yi buda baki? Na gaya mata ta kama yi min fada ke yarinya ce karama ba za ki taimaki kanki ba tunda kin san ga yanda kike in dai kowane ciki sai anyi wadannan kurarrajin ai ya zama dole ke da mijinki ku dauki matakin da ya dace, shiru nayi ban ce mata komai ba.

Muna nan dakin muna hirarmu ni da Umma Amarya sai ga yaya Almu ya shigo, na daga ido na kalli agogo sha daya da rabi ne na dare, ya nemi wuri ya zauna cikin natsuwa ya kalli Umma ya ce mata in ranki ba zai baci ba Umma zan hakura da zama da Lailatu in yaso na natsa sai sai in kara wani auren don bana sha’awar zama da mace guda daya.

A hankali Umman ta tambaye shi me tayi maka? Ya ce mata yanzun nan a daki, Junaidu ne ya banbare hannunta daga jikina yana bata hakuri, Umma ta ce a’a me yayi zafi haka? ya ce ta ce wai muna munafurtarta ni da Rabi bamu gaya mata Rabin tana da ciki ba sai anan a cikin mutane akaci mata fuska, na ce mata nima yanzu ne na tabbatar don a gida da na tambaye ta musu tayi min, amma bata yarda ba ta tada rigima wai sai na sake ta da na tashi zan fita kuma ta rike ni in ban da anan gidan nanne Umma ba zan yarda da hakan ba ta ce mishi to kayi hakuri amma ai babu wani abin bacin rai itama ba tuntuni ake cewa tana da nata cikin ba wa yayi tashin hankali? Duk da kiran da Umma Amarya ta yiwa Lailatu tayi mata maganganu na kwantar da hankali ta kuma yiwa yaya Almu fada a gabanta bai hanata barin gidan ba da sassafe ta tafi gidansu, don haka bata nan aka yi sakun lalle aka shiga hidimar bikin, ni kam ko wurin Ummana bana zuwa balle in ji ko ta san abin da ake ciki a sashin Umma Amarya nake zaune wacce duk da hidimar Jama’ar da take fama dasu bai hanata tarairayata ba sai wani ji dani take yi tana kuma nuna min cewar in yi iyakacin kokarina wajen ganin mijina ya zauna lafiya a gidanshi, gashi Allah ya baku haihuwar nan da aka dade ana nema.

Ranar Asabar wajen karfe goma sha biyun rana aka soma hidimar daurin aure abin mamaki wai har da mai sunan Umma Amarya a cikin yanmatan da aka daura wa auren kuma wai ita aka baiwa yaya Junaidu.

A wurin liyafar cin abincin dare da Baba ya saba shiryawa ‘yan uwa da abokan arziki a duk lokacin da yayi irin wannan hidimar ina zaune tare da yaya Almu yayin da Rabia’tu ke kan cinyata na waiwaya na kalli yaya Almun bayan na gama kallon yaya Junaidu da yar yarinyar da ya aura sai da nayi tsaki kafin na ce mishi gaskiya ban san yaya Junaidu budurwar zuciya ce dashi ba sai yau, don Allah dubi yar yarinyar da ya ce yana so kuma wai Baba ya bashi ita, ita kuma da yake sokuwa ce dubi yanda take ta faman murmushi ko me yake gaya mata? Oho, Ita bata san tsoho ta aura ba.

Yaya Almu yayi murmushi ya ce ba za ki gane abin da yayin ba komai ba ne sai nima na ce Baba ya bani wacce naga tana tasowa yanzu, nayi maza na galla mishi harara na ce ai sai kuyi tayi ku rinka auren sa’o’in ‘ya’yan cikinku yayi dariya ya ce ba komai ba ne Rabi an riga an yardar mana yin hakan sai dai kuma kin san ko yar sila zan aura son da nake yi miki dabanne da wanda zan yiwa kowacce da haka na danji sanyi cikin zuciyata.

To an tashi biki gaba daya amare da angwaye sun nufi gidajensu, don haka baki ma watsewa suke tayi, ina zaune tare da Baba a falonshi hira muke yi ni dashi da yaya Almu Abdulhakam yana bacci a gefenshi, hakan ya kara tabbatar min da maganar da Ummana ta gaya min cewar duk inda yake bai rabuwa dashi duk matar da take tare dashi kuma ita ce mai kula mishi dashi ko da kuwa wacece.

Na kalli Baba cikin ladabi na ce mishi Baba ashe dama zaka iya ba da kari? Yayi murmushi ya ce zan bayar mana uwata ba hudu aka ce ayi ba? Na ce haka ne, yaya Almu ya kwashe abin da na fada akan yaya junaidu da amaryarshi ya fada mishi baba yayi murmushi ya ce bai mata tsufa ba uwata, Junaidu ai yaro ne, yaya Almu ya ce ai nima nan gaba gida zan zo a kara min Baba cikin yankananan masu tasowa, nayi maza na ce a’a baba shi yaya Almu ai dama mata biyu ya ce min zai yi to ga riga kuma ya yi sai dai kawai ayi mana addu’ar zaman lafiya baba da yaya Almu suka kyalkyale da dariya, baba ya kalli yaya Almu ya ce to ka ji Lamido uwata ta ce ya isheka haka.

Mun koma gida bayan an kammala biki iyayen Lailatu kuma sun dawo da ita saboda ganewan da suka yi Yaya Amu dai bai shirya binta ba, sai dai ta dawo dinne kawai amma bata shirya a zauna lafiya da ita ba, tunda ta gane ciki ne dani ta tsire neman fitina mai tsanani bata zauna lafiya da mijinta ba balle kuma dani hatta su Baba Talatu da Azumi da ita da kanta ta kawo ta ta ce wai itama munafuka ce ta koma wurina.

Kullum burinta tayi danbe dani ne ban san me take nufi ba watakila gani take tunda ina da lalura zata iya dukana, rannan na fito daga dakina zan shiga kicin ita kuma daga kicin din take zata nufi nata wurin, ban yi aune ba sai kawai naji ta bangaje ni, ni kuma sai nayi wuf na sharara mata mari mai tsananin karti nan take ta juyo ta rarumame ni da karfi, abin da ya zama danbe mai tsanani a tsakaninmu daga Baba Talatu har Azumi baba abin da ba su yi ba don su raba mu Lailatu bata yarda ba kokarin ta kawai shi ne nata samu damar da ta buge ni a ciki ko kuma ta kai ni kasa, shi ne kuma abin da bata samu ikon yi ba saboda shigowan mutumin da ke kulawa yaya Almu da tsabtar gida abin da ya shafi share-share da gyaran furanni.

Washegarin faruwar abin su Umma suka iso saboda kiran da Yaya Almu ya yi musu, Umma na ce tazo ita da Hajiya Hauwa sai Abdulhakam da tazo dashi.

Gaba dayansu ni suka dorawa laifi a cewar wai da Lailatu ta bangaje ni sai in rabu da ita in yaso in yaya Almu ya dawo in gaya mishi tunda nasan bani kadai ba ce, Yaya Almu ya nuna musu bacin rai mai yawa kan abin da nayin suma kumna suka taya shi jin haushina, Umma kuma ta sani na bashi hakuri, kafin ta kalle shi ta ce mishi to ko Adawiyyah zata je gida ne a’a Umma ba zai yiwu ace duk lokacin da take da ciki sai taje gida ba ta zauna nan ba. Hajiya Hauwa ta ce gaskiya ne Lamido to Allah ya raba su lafiya ya ce mata amin.

Bayan tafiyarsu na yi fama da rashin lafiya mai tsanani ga ciwon jiki ga kumburin da kafafuwana suka yi tayi amma ban gaya wa yaya Almu ba saboda duk da ba wani dadi muke yi ni dashi ba a dalilin fushin da yake yi dani dana lura da kyau kuma sai na gane rashin dadin da suke yi da Lailatu ya fi haka yawa don ya dage kan cewar kisan kai take so tayi mishi a gida in ban da haka me zai sa tayi danbe da mace mai ciki wata bakwai? Ko so kike itama tayi barinshi kamar yadda kika ce kinyi naki? Don shi a lokacin gani yake tanfar cikin wata bakwai ne dani.

Kwana biyar bayan danben namu na tashi da daddare cikin matsanancin rashin lafiya mai tsanani ciwon baya da ciki mai gigitarwa na kira Baba Talatu dake taya ni kwana tayi maza ta farka tana tambayata yaya dai uwardakina ruwa zan baki ko me? Don tasan ina da dabi’ar yawan shan ruwa na ce Baba yau kam ina jin haihuwa zan yi don wannan ciwo ya tsananta nan take ta kama salati tana kuka wai zai haihu loka ci bai kai ba na ce mata kiyi fatan mu rabu lafiya kawai, tsawon daren idonmu biyu bamu runtsa ba tayi juyin duniya wai zata je ta taso yaya Almu ta ce mata ban yarda ba Baba mutumin da baya magana da kowa kyale shi kawai zata fara yi min fa da nayi maza na kama yi mata kuka dama kuma wahala ta ishe ni gashi babu Ummana a kusa babu kuma umma amarya nan da nan ta shiga bani hakuri sai ni ce nake ce mata shafa min baya Baba shafa min nan shafa man can cikin zuciyata nace kai Umma amarya dai ta iya tarairayar mai nakuda.

A haka muka yi ta fama har sai wajen asuba sannan na haifi wani dan kankanin yaro bai ko kusa da girman Abdulhakam ba, Baba Talatu ta dauke shi cikin murna da godiyar Ubangiji tana fadin ikon Allah bakwaini ne amma kuma lafiyaiye na ce mata ba bakwaini ba ne Baba ke dai kawai karami ne nayi mishi addu’o’i na kuma diga mishi ruwan dabino, a baki, kamar yanda naga Umma Amarya ta yi wa dan uwanshi, ina zaune ina jiran biyowan mahaifa addu’o’i iri-iri nake ta karantowa ina kuma neman sauki wurin Ubangiji yayin da Baba Talatu keto son in barta ta jijjiga ni wai mahaifa ta fado ni kuwa naki saboda tsananin da jikinnawa yayı zuwa can sai kawai na sake jin wani yunkurin kankace meye wannan sai ga wani yaron ya fito har kuma da mahaifar gabadaya shima yana fitowa hakan ya kama kamar yanda dan’uwanshi yayi da gudu Baba Talatu ta yi waje har tana sulewa kofar yaya Almu taje tana  duka tana fadin fito Babangida fito yau kaga alherin da ya sauka a gidanmu.

Ina jin shigowarsu na shige cikin toilet nasa key na kulle nayi wanka na zuba ruwan zafi da detol na shiga ciki na zauna nayi ta matse cikina lokaci mai tsawo kafin na kintsa kaina na fito na zauna ina shafa mai na amsa gaisuwar Lailatu na kuma ce mata hada min tea ki bani ta ce to ta hado min, na karba na sha na gyara kwanciyata lokacin ne yaya Almu ya shigo bayan ya gama da yaranshi sannu Rabi na ce mishi yauwa, babu dai mas’ala ko? Na ce mishi eh, Baba dasu Umma suna gaishe ki na ce to ina amsawa ya zauna anan yana yi mun magana kan haihuwar da nayi a gida na.ce ai ba komai gida da asibiti duk Allah ke rabawa.

Washe gari da sassafe sai ga Umma karama ita Baba ya turo tazo tayi min zaman biki na yiwa Baban tudu waya na ce mishi a turo mun wata daga katagun, nan da nan ya turo min Baba Marka suka hadu da Baba Talatu su suka tsare min komai suka tafiyar dashi yanda ya kamata, Umma karama kuwa tan far ba zaman jego tazo mun ba bini-bini tana wurin Lailatu ko me suke kulluwa oho, ni dai cikin zuciyata cewa nake yi kuje kuyi tayi yanda Ummana tafi karfinki haka nan nasan nafi karfin Lailatu cikin yardar Allah don haka ba kwa ga bana ban iya cewa ga irin cincirindon jama’ar da suka rinka zuwa da irin hidimar yaya Almu da suka rinka cikin yaya Almu bai kwatantuwa kan wannan haihuwar yini yake yi yana kaiwa abokanshi masu zuwa yi mishi murna yara suna gani su kuma sai su rinka cewa a’a Adawiyyah kuma haihuwa ta samu ni wancan babban ya ma shekara kuwa? Shi kuma yana dariya yana fadin a’a haba ya shekara mana wannan watan ne ya cika shekara guda sai kuma su kwashe da dariya suna fadin to ga biyu kuma hidima sosai yaya Almu yayi don a wannan haihuwar ne Baba ya sakan mishi lamarin gidanshi sauran duk abubuwan da ake yi a baya Baba ne mai bada kudin yin komai ko kuma yayiwa yaya Junaidu umarnin ya bayar.

Yadda Baba ya tura sunan Abdulhakam katagun ya bar wa Baban tudu zabin sunan da za’a sanyawa jarirai haka shima yaya Almu ya tura radin sunan katagun sai dai shi yaya Junaidu ya bar wa zabin sunan da za’a sanyawa jariran don haka ranar suna da sassafe bayan anyi kiran suna a can sai yayi waya ya fadi sunan yaran Jabir da Jibrin, muka yi sunan ma a Kaduna suma su Umma suka yi nasu sunan a gida anyi suna da kwana biyar Umma karama tafi tana barin gidan kuwa na tsukewa yaya Almu fuska ya tasani a gaba yana son sanin dalili na ce mishi to dama muna magana da juna ne yaya Almu? Ai gaba kake yi dani ba sai muci gaba ba kawai ya ce amma bai wuce ba? Na ce da aka yi me ya wuce? Ina halin rashin lafiya baka ji tausayina ba kana fushi dani sai na samu lafiyar ka ce ya wuce? Ai muyi tayi kawai, ya kalle ni ya ce baki da hankali Rabi nayi maza na ce mishi da sannu ai zanyi.

Muna cikin wannan zaman ni dashi sai kuma Lailatu ta fito da wata ka’ida wai bata yarda da shigowan da yake yi wurina ba tunda ba ni da girki zaman jego nake yi ya ce mata haka ake yi Lailatu ke da kika yi naki jegon haka tayi miki, rikicin yayi tsanani a tsakaninsu har takai karar shi gidansu aka musu shari’a ban san me aka ce mishi ba ni dai naga ya shigo dakina yazo ya zauna ya ce min Rabi taimake ni ki karbi girkinki yau ban ce mishi don me ba? Ban kuma ce mishi ba zanyi ba don ba zai yiwu ace ta ko ina ba zai ji yadda yake so ba don haka sai kawai na ce mishi to, yayi matukar jin dadin hakan da nayi yayi min addu’a ya kuma tashi ya fita ya shiga wurin Lailatu.

Duk da sati uku ne kawai da haihuwata Baba Talatu tana gama abincin gidan dana sata tayi sai na fito ina sanye da kayan sanyi na suturta jikina na shiga kicin na shirya mishi abincin shi da lokacin kwanciya yayi kuwa shigowa yayi ya sallami Marka da Baba Talatu dake taya ni kwana da yaran ya ce musu su tafi wurinsu sai da safe shi zai taya ni duba yara suna cikin gadajensu muma muna namu, na kalli yaya Almu na ce mishi kai yaya Almu jego fa nake yi, ya ce nafi kowa sani tunda ga yan tagwaye biyu can ina kallo wadanda Ubangiji ya azurtani dasu amma hakan ba zai hana ni in yi abin da naga zan iya ba, jego mai dadi nayi ran girkina ina manne jikin mijina a haka muke kwana in yara sun motsa kan in tashi ya riga ni zai yi musu komai sai dai ya miko min su ina daga kwance in ba su nono in sunsha sun koshi ya maida su wurin kwanciyar su, sannan ya dawo mu kwanta maimakon in takura sai kuma naga ni gata ma tayi min in bani ce da girki ba kuwa bana jiran sai yazo ganinsu ana gama musu wanka da gyara in na basu nono suka koshi sai in ce akai mishi su nima in kintsa in yi kwanciyata in yi ta baccina mai dadi, kafin in yi wata guda daga ni har su munyi gwanin sha’awa.

Rannan na karbi girki, rannan kuwa kwanan mu talatin da bakwai ne, kwalliya sosai na yiwa mijina da zamu kwanta kuma na sanya wata shu’umar rigar barci da ban taba amfani da ita ba, ni ina ki ka samu irin rigunan baccinnan ne Rabi?

Na dan kalle shi kadan kafin na maida hankalina kan yaron da nake baiwa nono don yaya Almu ya matsa in sa su suyi bacci na ce mishi tun rannan fa na gaya maka na ce maka set din akwati biyu Umma tayi min na rigunan bacci kawai, ya mika hannu yana wasa da igiyoyin rigar tare da fadin riga ce mai kyau Rabi na ce mishi eh.

Kwalliya nayi don in burge yaya Almu in kuma faranta mishi rai amma ba don wani abu ba sai kuma ya ki yarda da tsayawa kan wasannin da muka saba yi, ya ce fafur shi yayi kokari kwanaki talatin da bakwai din da akayi ai tun ban fi sati biyu ba yake ganina ina sallah, to ina laifinshi? Da dai lura kin yarda na zai kawo bacin rai mai yawa sai kawai na sallama iyaka dai nayi tunanin matakin da zan dauka wanda zan taimaki kaina dashi.

Randa muka yi arba’in ranar na tafi Legos ni dasu da Rabi’atu tare da Baba Marka da Baba Talatu muka je na kaiwa Baba su ya gansu Baba yayi murna, murna kuwa mai tsanani ya kalleni ya ce ikon Allah yau ga uwata da haihuwa har da ta yantagwaye, ni kam murmushi kawai nayi Umma karama ce a wurinshi itama ina aka saka damu tayi, nayi kwana daya anan daya kuwa a gidan yaya junaidu zamanshi da matanshi gwanin sha’awa komai zasu yi tare suke yi shi kuma yana tsakaninsu, anti Rahma kuma ta yaba mun da adalcin yaya Junaidu, daga Legos gida muka wuce in da muka samu Ummana da Umma amarya muka fara bakunta mai dadi kwananmu uku da zuwa sai ga Yaya Almu yazo wai zuwa yayi mu tafi ni kuwa na tubure na ce ai ba haka muka yi da shi ba, Umma cewa nayi zanyi kwana biyu a Legos in zo nan in yi bakwai in  tafi katagun in yi biyar sai kuma kawai ko bakwai din farko ba ayi ba ya biyo mu ya ce bakuntar ta isa haka? Umma ta ce haka kuka yi Babangida?  Ya ce ch amma ai ta kwashe mutanen gidan ta tafi dasu don haka na fara bakuntar ta ishe ni haka tazo kawai mu tafi gida, Umma ta ce a’a ba zai yiwu ba sai taje katagun ta kaiwa su Alhajin tudu yara sun gansu don haka washegari muka nufi katagun har da yaya Aimu muka je mukayi kwana biyu muka wucc gida.

Wata na shida da haihuwa su Jabir suna ta zamansu har suna nema suyi rarrafe sunyi matukar yin girma gasu da lafiya gasu kullum kamanninsu sai karuwa yake yi yaya Almu sai ji dasu yake yi in suna wurinshi barin komai yake yi yayi hidimarsu, na shiga dakinshi na same shi tare dasu na ce mishi yaya ko zan je asibitin ne? Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce me kuma ya faru? Na ce mishi yauma al’ada nake yi kuma ba ka ga yanda take zuba ba kamar ba kwana bakwai ba ne kawai da daukewar wancan ya ce min to har na kama hannun Rabi’atu zamu tafi sai naji ya ce min tsaya Rabi, bari in zo mu tafi tare na gaji da  wannan al’adar taki tunda muka fito daga asibitin yaya Almu bai ce min komai ba ga dukkan alamu dai ranshi a bace yake ban san mne Likitan ya gaya mishi ba don ya kira shi sun kebe can cikin Zuciyata cewa nake yi Allah dai yasa ba wani abu ya gaya mishi ba.

Muna shiga gida naji ya kira Marka da Baba Talatu ya basu yara ya ce su kula dasu, shi kuwa ya biyo ni daki ya nemi wuri ya zauna ya daga ido ya kalle ni ya’ce min Rabi ai kin dade kina burin yin nesa dani ko? Ban iya amsa mishi tambayar ba saboda mamakin da ta bani kan in yi tunanin amsar da zan bashi sai naji ya ce za ki iya yin hakan a yanzu dama kina da gidan da kika sai wa kanki don hakan to ki koma ciki ki zauna ba zan  zo inda kike ba, na kalle shi na ce me ya faru? Ya ce babu komai ganinki ne kawai bana so na kuma baki minti talatin ne ki fita ki bani wuri, na ce ba ma sai an kai haka ba na mike na dauki jakata na fita na tsaya ina kiran Baba Talatu ta kawo min yara ya biyo ni da sauri ya ce bar su a inda kika same su.

Tsananin mamaki da kaduwa ne ya same ni don haka ban je inda ya ce din ba gida na wuce kai tsaye don nasan Umma tana can na gama mayar mata da bayanin yanda aka yi duka mamaki ya kamata ta ce me kika yi mishi haka?

Na ce nima ban sani ba sai tà ce to bari yazo mu ji tunda na kira shi, sai dare yaya Almu ya iso na kuma yi sa’a yazo da yaran har da Rabi’atu, yana shigowa ya ganni ya ce me ya kawo ki gaban Umma Rabi? Me yasa in wulakancin ki ya motsa ba kya barin abin ya tsaya tsakanina dake sai kinzo gabanta don kiyi sana din bacin ranta? Ba gidanki na ce ki tafi ba?

Umma ta ce haba nifa nasan haka kawai ba za ka yi irin wannan hukuncin ba, ina kuka yaya Almu ya kalle ni cikin takaicin ya ce ban san me zance miki ba Umma iyaka dai kin san mas’alar data samu Rabi ta yawan al’ada har tana ta zirga-zirgar asibiti Umma ta yi maza ta ce mishi eh, ya ce to allurar da take yi ta hutun haihuwa da tsarin iyali ne ta jawo mata abinda Likita ya gaya min kenan.

Umma tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta yana ganin haka ya mike zai fita wai zai je gaida Umma amarya Umma ta ce mishi debi su Jabir ka kai mata, ya ce to yana barin dakin Umma ta soma zagıina wani irin zagin da bata taba yi min ba har tana kirana butulu, haihuwar da muka nema kamar yaya? Muka hadiyi bakin cikin da bai misaltuwa akanta ita ce a yau kika je neman tsari da ita saboda ke butulu ce maimakon ki zauna kiyi tayi wa Ubangiji godiya kan ni’imar da yayi mana, to ni ba su ishen ba jeki ki haifo su a jaka Adawiyyah ki kawo mun su, ba Lamido kike so kiyiwa tsiya ba, ni da dan ‘uwana kike so kiyiwa don mune bamu da wata hanya ta yaduwar zuriyarmu sai ta dalilinki, Lamido ai in ya kara aure zai samu ya’ya a tare da matar, yanzu ma kuma kina tare da wata na kuma ji karama tana cewa ciki ne da ita, har yaya Almu ya dawo Umma bata hakura ta bar fadan da take yi min ba cikin sanyin jiki ya nemi wuri ya zauna ya shiga bata hakuri har yana ce mata wai ba butulci ne yasa nayi hakan ba wahalar kurarrajin bakin dake hana min sukuni ne dalili amma nan gaba zai dauki matakin da ya kamata.

Da aka natsa yaya Almu ya ce in tashi mu tafi gida sai na ce mishi a’a ya barni kawai ya yi tafiyarshi ai tunda ya ce in fita in bar mishi gida ba zan sake komawa wannan gidan ba, ya soma yim in magana kiyi hakuri Rabi raina ne ya baci kema kin san…..Umma tayi maza ta katse shi ta ce kar ka baiwa Adawiyyah hakuri Babangida, kyaleta tayi abin da taga ya yi mata daidai ba dai burinta ta bata min rai ta sanya ni bakin ciki ba?

To ta yi ta ji dadi ni kuma na yafe mata, na yafe miki Adawiyya na yafe miki kiyi min duk abin da kike so ba zan ji zafin ki ba, zanyi ta yafe miki, tana maganar tana kuka, hankalin yaya Almu yayi matukar tashi ya shiga bata hakuri yana fadin laifinane Umma da na zartar da irin wannan hukuncin na dauka zata bi umarnin da na bata nata koma wurinta ban san zata kawo maganar gabanku ba amma kuyi hakuri, ke Rabi jeki ki dauko su Jibrin sai kizo mu tafi, Umma tayi maza ta ce a’a abar wa Maryam su bata da kowa a dakinta zasu yi mata dadi.

Zubewa nayi a kasa ina kuka a gaban Umma bata kula ba, yaya Almu ya soma bata hakuri cikin sanyin jiki don shima bai son rabuwa da yaran ta ce mishi kul ka ce zaka yi min wata magana ai na bar muku su sune ina jiran ku samu wani kar ayi ta barinku cikin kewa tunda kuwa basu dame ta ba to taje.

Haka muka fito daga gidan daga ni sai yaya Almu itama Rabin Umma ta ce a barta a gidan ni kam nayi kuka har na gaji a gida kuwa ga kewar Rabi’a da yara ga ciwon nono gashi yaya Almu ya tasa ni a gaba duk wanda ya tambayi yana sai ya gaya mishi abin da nayi wanda yasa Umma ta kwace su duka wai har da yaya Junaidu ya gayawa shi kuma tunda ya gaya mishi ya daina maganna dani ko gaishe shi nake yi a dake yake amsawa wai bai taba ganin mai rashin hankali irina ba gaba daya na tsargu babu abin da nake so irin in sake jin kurarrsjin baki sun sake feso min shiru babu su babu dalilin su, hankalina yakai matuka wajen tashi kar dai na daina haihuwar kenan?

Kullum tambayar da nake yiwa kaina kenan a duk lokacin da na tuna abin da nayin da irin wahalolin da muka sha a baya da bakin ciki da gorin haihuwar da akayi tayi sai inga to in ban da butulcin da Umma ta ce ina dashi me zai sa in je neman hutun haihuwa? Ina yin irin wannan tunanin sai in yi maza inyi ta istigifari ina neman gafarar Ubangiji, yaya Almu kuwa kusan kullum sai ya gaya min cewar shi fa ya riga ya saba da mu’amalla da yara tunda ni da Lailatu mun sake zama juyoyi to shi gaskiya zai nemi auren badurwa mai sha biyar ko sha shida wacce kafin ta gaji da haihuwar zata haifar mishi ko guda goma, in ce yana kyau haka din gara ka himmatu.

<< Wace Ce Ni? 47Wace Ce Ni? 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×