Skip to content
Part 8 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Da karfi na ce mishi “Ha’a ba ance muku ku sakar min mara ba?”

Ya ce “Ai yanzu kika ce duk maganar da aka yi ana dariya ko murmushi wasa ake yi.”

Ya dan saki fuska ya ce” Wuce muje can falon Umma ki shirya mana abin karyawa kafin ta fito.”

Na ce “A’a yau baba kadai zan yiwa abin karyawa.”

Ya ce “To muje ki yi mishin in taya ki.”

Na waiwaya na kalleshi nayi murmushi na ce

“Ka taya ni fa ka ce?”

Ya ce  “To menene don na taya ki kinyi wa Umma da Baba abinda za su ci?

Muna kitchen din Umma ina aiki na shi kuma yana zaune kan kujera mai tsayi yana gaya min ya kamata ki rinka gane kin girma Rabi, ki rinka barin Umma tana morewa rayuwarta amma ba kowane lokaci kina manne da ita ba tana daki kina daki manne da ita ba tana daki kina daki tana waje kina waje wai Babama inya zo sai kin je kin zauna musu ba zaki barta ita kadai tare da shi ba kamar yanda kowacce a cikinsu take yi.

Na bata fuska na ce “To meye? “

Ya ce “Ba komai bane tunda ta kyaleki kina yi mata shima Baba ya sa muku ido amma ni da wanda ya isa ya shiga tsakani na da mata ta ne?

Ranar farko da naji yaya Almu ya yi min maganar da ta shafi matarshi nayi murmushi na ce mishi “Ka ce in na zo gidanku kai da anti Aina’u in bi a hankali.”

Ya kalleni yayi murmushi ya ce “Wai me yasa ki ke zaban min Aina’u ne a cikin duka ‘yan matan?”

Na ce mishi “Nafi ganin kyau kwalliyarta in ka lura kwalliyarta daban take da ta sauran ba kowacce irin sutura take sanyawa ba bata kuma dauri ta wani karka toshi, amma kuma kana kallonta ka san yar gaye ce.” Na ce “Kuma ta kasa boye son da take yi maka.”

Yayi maza ya tsuke fuska ya ce “Kar ki yi mata sharri to gaya min wacece mai hankalin cikinsu?”

Da sauri na ce mishi “Anti Rahma ai ta fisu  natsuwa ma ko sallah akan lokaci ta fisu ni nama fison ta saboda mun fi shiri da ita, ita ba ruwanta ma da tadin samari.”

Ya ce “To me yasa baki yi tunanin ki zabamin ita ba tunda gashi ma kuna shiri ko da yake ban tabbatar ba don kuwa kakan yi shin ne da mutumin halaiyar ta dan zo zaya ke kuwa baki da irin halayen nan nata da ki ka lissafa natsuwa, hankali da sallah akan lokaci.”

Na ce “Uhm, ina aikina shi kuwa hiran yake so mu yi don haka sai ya sake shigo da wani zancen amma ai ina ganin rabi in aka kwashe ‘yan matan gidan nan aka yi aurensu aka barki daga ke sai yan yara aiki zai miki yawa.

Da sauri na kalleshi na kyalkyale da Dariya na ce “Ai ni a dadina babu wani aikin da zai dameni wa za rinka sani? dama kai da yaya Juanidu ne wadannan samarin da za’a barni da su kuwa kwanta-kwata shekara biyu zuwa uku suka bani ba wani takura min da zasu yi don bazan yarda ba shi ya sama tun bara na dena sake musu fuska ko gaishesu zan yi sai na bata rai don karsu ga alamar wasa suce zasu kawo min raini.”

Sai da na kawo nan naji gaba na ya fadi nayi maza na waiwaya na kalli fuskarshi don in gani ko yau ma nayi subutar bakin nawa dana saba banga alamar hakan ba don haka na cigaba da yi mishi bayani.

Kuna bari gidan nan ko kwana bakwai bazaku yi ba zan fara hawa mota.”

Ya ce “A’a haba Hajiya zumuzi ai kya bari ki koya.”

Na yi maza na ce “Ni na dade da iya tuki wurin Jul… Nayi maza nayi gum ban karasa ambaton sunan ba, shima sai ya nuna bai gane wanda nayi -niyyar ambaton ba.

“Abin karyawan na mutum nawa zaki yi ne?”

Na ce “Da Baba da Umma da Umma amarya dani.”

Ya ce “To ki hada da Umma karama ko kuma ki kai mata na wajenki ki zo mu karya ana gida.” Ya tashi ya fita ya barni ina fadin hu’un.

Kwanaki biyun baba sun cka ya kuma dauki amaryarshi sun tafi sun barmu da kewa shi kam yaya Almu ko a jikinshi har mamakinshi nake yi, bai taba nuna ya damu da Umma amarya ba balle ka ga alamar wata shakuwa a tsakanin su.

Ranar monday na isa wurin TP na a makare saboda a safiyar na muka yi sallama da Baba shima yaya Almu sauke ni ya yi ckin sauri ya wuce don yana da case a kot yau.

Cikin ladabi na gaida yallaba ya amsa tare da bina da kallo in ce ko yau daga wurin party ku ke ne ke da yayan naki?

Nayi maza na dago ido na kalleshi ya ce “Eh, ai wannan yayan naki yayan zamani ne babu abinda da bazai ya ba ai na ganku shekaran jiya can ranar juma’a da yamma ke da shi saboda haka ban sake karbar wani uzuri ni da shi duk so muke yi don haka babu wani mai haramtawa wani”

Nayi shiru ina sauraronshi sai da naji ya yi shiru sai na ce mishi “To ba shi bane shekaran jiya ba muje ko’ina ba ni da shi da yaya Junaidu muka fita.”

Ya ce “Afto ke ki ce mun duk gidan naku samarin kine to koma dai menene banga laifinsu ba kina da kyau don haka na guji da zaman zurawa juna ido da muke yi in baki sani ba ni a takure nake yau, muyi mu’amallar hadin kai kawai ki amfane ni ni ma in amfancki in bak sani ba ita mu’amulla mai dadi in anyi ta babu wanda bata amfani in bazan miki karyar kudi da gold ba tunda ki na dasu ai kuma takardunki zasu biyo ta hannuna knga kenan ina da wani abin yi akanki.”

Shiru kawai nayi ina sauraronshi dana ji yayi shiru sai kawai na sunkuyar kàn ai kina sha biyu tuna ciki ya mike ya ce “To lokacin break ne yanzu tashi muje mu dawo da sauri kan ya zo daukan naki, na daga ido na kallesh jikina sai faman rawa yake yi saboda ganin da nayi mishi a tsaye a kaina, ai sai kin tashi min tafi yau na gaji da cintar da ki ke yi min ya miko hannu zai taba min jikina nayi maza na shige karkashin teburin na mukure ina ta faman bashi hakuri.

“Ai sai kin fito abin da bai wuce in ture teburin ba.”

Sai kawai ga yaya Almu a office din ya yi rin shigowar shi da ya saba ta rashin ne izini.

Yallabai yana ganinshi ya saki hannuna da ya riga ya kamo yana kokarin jawoni in fito daga karkashin teburin yana fadin fito kawai ba komai a hankali ma za’a gani na fito daga karkashin teburin jiki na sai faman bari ya ke yi kam in gama fitowa tuni yaya Almu ya yi waje na mike ina kuka na biyo bayanshi zan fita shi kuma yallabai yana tambayata wai kukan na menene ko so nake in kulla mai irin janhurun da yan mata suka saba kullawa mutane shi da nan da nake ganinshi babu abin da zai firgita shi don babu Irin mutumin da bai gani ba ban tanka mishi ba, na share hawaye nakwai na fita na taho wurin yaya Almu ina tunania irin tuhumar da zai minkan abin da tarar yana faruwa tsakanina da yallabai.

Ina zama a cikin motar ya tasheta cikin sauri ya fada kan hanya bai ce min komai ba ni ma bance mishi ba har muka iso shatatalen unguwar mu yana gama shi yayaya tsaya bai kallen ba, ya ce min sauka ki shiga gida sauri nake yi, na dan kalleni cikin damuwa na ce mishi daga nan zan karasa zuwa cikin gida da.. kan in karasa ya daka min tsawa sauka ki bani wuri nace da sauri na fita na bar mishi motarshi na kama hanya ina tafiya a hankali cikin zuciyata ina tunanin to ni da ba tashi muka yi ba me ya dawo dani gida wannan tafiyar da nake yi ma ai kafin in gama ta an koma break din.

Ina shiga falin Umma nayi sa’a na sameta a ciki ita da baba talatu kwanciya nayi a jikinta ina kuka ina gaya mata “Umma bana son 1.T ya isheni a takure nake zama a wurin ki taimake ni ki yiwa yaya Almu magana ni a barin haka bana son karatun bokon wahla yake bani yanzu ma kafafuwana ciwo suke yi min.”

Baba Talatu tayi maza ta shiga matsaminsu tana fadin “Sannu da kokari uwar dakina.”

Ina na wurin akwance jikin Umma har yaya Almu ya shigo “Tashi mu je in mai da ke.” Na daure fuska na ce.

“Ni abarni kawai in huta a gida.”

Ya ce “Yi hakuri rabin Umma.”

Umma ta yi dariya ta ce “Haba Babangida Adawiyya ai takace tashi ku je tashi tashi maza kina ji yayanki yana baki hakuri kina wani minmike.”

Na mike na tashi naje na samu motar a sashin Umma don haka ban yi tafiya mai yawa ba na bude ta na shiga sai dai zuciyata cike take da  tsoro saboda ban san me zai faru ba, tsakanin a da yallabai ni zu manar ba don nasan halin yaya Almu cewa zai yi sharri zan yi mishi nice nake sonshi, haka dai na daure na koma office bayan ya sauke ni gabana yana faduwa na shiga office din yallabai yana zaune kan kujerarshi kirjina yana bugawa na ce mishi “Barka da aiki yallabai.”

Bai daga ido ya kallen ba, ya masa kanshi a sunkuye. “Yauwa, baiwar Allah.” na wuce sum-sum na je na zauna ina aikina ina kuma sauraron abin da zai ce min har aka tashi bai kalli inda nake ba balle ya yi min wata magana nayi mishi sallama sai gobe ba tare da ya kallo ni ya ce min yauwa mu kwana lafiya.

Na fito ina mamaki tare da tunanin abin da ya hana yaya Amu zuwa daukana sai da na fito kofar ma’aikatarmu na ganshi a zaune a bayan motarmu yana Kallon masu wuce wa, na shiga na zauna muka dawo gida.

Tun daga ran nan yaya Almu bai sake leka office dinmu ba in ya zo a waje yake jira na in fito in same shi da na tambaye shi dalili sai ya ce wai ya lura ne bana son shigan nashi dan haka ya daina.

Shima Yallabai bai sake kallona ba, balle a ci gaba da ambaton suna ko har a samu damar yin Magana.

Na yi IT na na gama cikin kwanciyar hankali muka yi sallamar arziki sabanin yadda ya yi ta rantsuwar zai rike min takardu na.

Kullum na dauko zancen don in yiwa yaya Almu hirar yallabai da mamakin canzawar shi, sai ya tsuke fuska ya ce wai ba wani nan kawai don naga na dawo gida bai biyo ni ba, ni kuma gashi ina mutuwar son shi, a dole na dena kawo mishi hirar yallabai.

Ina gama hutun gama I.T. da nayi na sati guda na koma zuwa makaranta karatun da ba wani dadin shi nake ji ba dama dai inyi za’a in maye gurbin carry over da nake da shi a jarrabawa ta ta second semester gashi na ce wa yaya Almu ya je ya ga malamin tun kafin su kai makon ya fito saboda ni ma nasan ban kulla wani abin kirki ba a cikinshi ya ce wai abinda ba zai taba zuwa ya yi ba kenan ya bada wani abu don aba ni cin jarrabawa in bazan yi ba, to inje inyi ta cin carry over ni ta saba shima yaya Junaidu da nayi mishi maganar sai ya ce mun haba Adawiyyah kamar ki kuma sai anje ana neman wani malami don ya baki ci to me zaki yi da wannan sakamakon tunda kin san ba na guminki ba ne? Ai kije ki yi jarrabawarki kawai tas zaki cinye sai dai in baki tsaya kin duba note din ki ba.

Haka dole na hakura na yi jarrabawar tunda babu halin in gaya musu cewar ba sosai nake  hallatar lectures ba.

Ana cikin wannan lokacin ne tafiyar Umma ta zo, saboda dawowar Umma Amarya dan kiris ya rage mini in roki Ummana ta bar tafiyar in ya so ita Umma Karama ta je sai na tunan maganar Yaya Almu ta cewar in daina shiga lamarin jin dadin ta da mijinta, don haka na ja bakina na yi shiru muka yi musu rakiya muka dawo na shiga falon ta na zauna cikin kewa da tunanin kwanakin da za ta yi kafin ta dawo.

Duk da hirar da su Yaya Zubairu suka zo suka yi mini bai hana ni kewar Umma ba, da sassafe na kama goge hotunta da ke ajiye a falonta da ke ajiye a falonta, duk wanda na goge kuwa sai na zuba mishi ido ina kallonta a jiki tanfar dai na shekara rabona da ita.

Sai da na gama wannan aikin na tsabtace ko’ina, sannan na shiga kicin don shirya abin karyawa. Yaya Almu ya shigo ya same ni.

“Wa kike yi wa abin karyawa haka bayan Ummana ba ta nan?”

Na kalle shi na dan yi murmushi, don na san cewar da ya yi Umman shi ya yi amfani da yanda nake kiranta ne na ce, ‘Umma anmarya? Ni fa na ce kai ma za ka iya samu, don na mutum hudu zuwa biyar na nke shiryawa.

Ya ce, “To bari in je in dawo.”

Sai da na gama komai sannan na dauki abin karyawar na je na kai mata, daga nan na zauna mata muka dan yi hira kafin na dawo saboda na san Yaya Almu zai zo nemana.

Na shigo kenan ina shan kunun gyadar da na taho da shi daga wurinta sai ga shi shi ma ya dawo na je na kawo mishi yana karyawa ina gaya mishi.

“Umma amarya ta ce in rufe ko’ina in koma can wurin ta.”

Yaya Almu ya yi maza ya ce, ‘A’a Rabi sai dai in so kike duk ki takura mana yanzu nan mu biyu ba za mu iya rike dakin uwar mu ba? Sai kuma kawai don ba ta nan mu rufe wurinta gaba daya mu koma wani wuri? Kenan har yanzu mu din yara ne kanana? Ai kawai mu yi zaman mu anan su Junaidu ne za su rinka zuwa mana hira, kin ga kamar tana nan kenan ko kuwa?”

Na ce, “To bari in anjima in na je kai mata abincin rana sai in gaya mata inta yarda shi

kenan.” Ya cc, “To rokonta za ki yi sai ki gaya mata cewar za ki iya zaman ba, ba cewa za ki yi wan zai taya ki ba.”

Na ce mishi, “To.”

<< Wace Ce Ni? 7Wace Ce Ni? 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×