Skip to content
Part 11 of 18 in the Series Warwara by Haiman Raees

Na Gode

Godiya ga Allah,

Godiya ga manzo.

Godiya ga iyaye,

Godiya ga ƙawaye.

Godiya ga waɗanda ke hawaye,

Godiya ga masu kewaye.

Na gode da soyayya,

Na yaba da ƙauna.

Na yaba da zumunci,

Na yaba da kara.

Na ga kawaici,

Na ga karamci.

Na ga halacci,

Na ga butulci.

Na ga abinda ƙauna ke iya yi,

Na ga abinda kuɗi bai iya yi.

Na gode wa dukkanku abokai,

Na yaba wa manzo.

Na gode wa maƙiya,

Na yaba wa mabiya.

Allah Ne kaɗai mai duniya,

Kai nake roƙo yafiya.

Ka bani juriya da danniya,

Akan dukkanin mai murɗiya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Warwara 10Warwara 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×