Skip to content
Part 3 of 18 in the Series Warwara by Haiman Raees

Birnin Wakanda

Mu baƙaƙen fata ne,

Mu ‘yan Afirka ne,

Mu ma mutane ne,

Mu ne ‘yan Wakanda.

2.

Muna fahari da tarihinmu,

Muna ji da al’adunmu,

Muna ji da ƙasarmu,

Mu ne ‘yan Wakanda.

3.

A Wakanda babu wariya,

A Wakanda babu sanya,

A Wakanda babu karaya,

Mu ne ‘yan Wakanda.

4.

Mu ke da Black Panther,

Mu ke da Dora Milaje,

Mu ke da Vibranium,

Mu ne ‘yan Wakanda.

5.

Ba mu damu da kowa ba,

Ba mu da rage wa kowa ba,

In ka taɓa mu ba sauƙi,

Mu ne ‘yan Wakanda.

6.

Wakanda tamu ce,

Mu ne da ita,

Ita ce da mu,

Mu ne ‘yan Wakanda.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Warwara 2Warwara 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×