بسم الله الرحمن الرحيم
(والسارق والسارقة فاقطعو أيديهما جزاء بما كسبا نكالا من الله،والله عزيز حكيم).{سورة المائدة} أية ٣٧.
Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a cikin alƙura'ani mai girma* *cikin suratul MA'IDA aya ta 37
(Da Ɓarawo namiji da Ɓarauniya mace idan kun Kamasu ku yanke musu hannayen su guda ɗaya gwargwadon abun da suka aikata na game da sata, Allah mai girma ne kuma mai hikima)
*****
RAMLAT ba ita ta tashi komawa gida ba sai ƙarfe sha ɗaya na dare kamar ba matar aure ba,a falo ta tarar da MUBARAK a zaune akan sallaya da alamu salla ya idar,ya ɗaura kanshi a kan kujera kamar mai bacci,amma kuma ba. . .