Skip to content
Part 13 of 32 in the Series Waye Zabin Munibat? by Husaina B. Abubakar

 Daya  ɗaga cikin doctor ne ya samu damar yi mata bayani da cewa” ya samu barci ne sakamakon jinin sa da diba, so yana buƙatar hutu Hajiya..” yana rufe bakin sa ya cigaba da tura shi abin sa…

” Ubawa ya baku damar ɗibar min jinin yaro na, akan wannan dalili za’a ƙwashe wa yaro na jinin? shi yace ta hau kan tittin da za’a ɗibe mai jinin..” ta faɗa cikin tsananin masifa da kumfar baki…

Doctor ko waigo baiyi ba bare ta sa ran zai saurare ta, su Hajiya kuwa tun lokacin da aka fito da MUNIBBAT suka bi bayan ta, dan ganin ɗakin da za’a sanya ta, so basu san abinda ke faruwa ba…

AN’NUWAR ya taso da sauri ganin mutane sun fara tsayawa, yace” haba Mommy kiyi ƙasa da muryar ki mana, bakya ganin mutane sun fara taruwa…

Kayi min shiru!! duk wa yajawo? da kayi tuƙi irin na masu hankali ta Yaya zaka bigeta? haka kawai bamu san ko ita wacece kun wani ƙwaso mana ita, ta iya yiwa ma irin yaran nan ne marasa jin magana, duk da ban kalle fuskar yarinyar ba amma naji sam bana ƙaunar ta, da ta farka KU salame ta ta kama gaban ta kana jina?..” ta faɗa mai ido cikin ido haɗi da ware su akan shi…

Tunda yake da Mommy na shi bata taɓa mai haka irin na yau ba, lallai ko ranta ba ƙaramin baci yayi ba, sai yasa a ranshi ko bata farka ba muddin ya bar wajen nan ya tafi kenan…

Mommy ta koma ma zaunin ta ranta a mutuƙar ɓace sai cika take tana batsiwa, a hankali ya zauna kusa da ita cikin ladabi yace” sorry Mommy bazan kara ba, wannan din ma tsutsayi ne, domin sam hankali na baya gaba na ne a lokacin muna magana da Mama ne, amma zan kiyayye gaba insha Allahu…”

 Bata ce mai komai ba ila hannun ta da ta ɗaura kan kumtun sa tana shafa a hankali, kan ta na kallon gefe domin har yanzu bata dawo ɗai-ɗai ba, jira kawai take yaron ta ya tashi ta haɗa kan su su wuce gida…

*****

Yana fito gidan su Aysha ya wuce hankalin sa tashe, ɗaga bakin ƙofar gidan ya tsaya yana ta raɗa salama, Ummace ta amsa mai ɗaga ciki kana ta turo Yaya yazo ya dubo wanda ke salama…

Cikin mutuntawa suka gaisa da Yaya, Kawu yace” am MUNIBBAT ta shigo ne yanzu?..”

” A’a bata zo ba gaskiya, domin tun safe ina gida banga shigowar ta ba…”

Ok na gode, yana gama faɗa ya wuce abin sa, Yayan Aysha ya tsaya zuciyar sa cike da tunnanin…

Abu kamar wasa, neman duniya Kawu yayi min bai gani ba, iyaka tunanin sa da ƙwarewar sa duk inda yaje sai ace ba’a ganin ba, hankalin sa bai gama tashi ba sai da yaga magariba ta ƙuno kai, babu ni babu alamata gida ya dawo cikin tsananin kiɗima,  gaba ɗaya jikin sa yayi laushi a haka yayi sallah yana salamewa, ya sake fita nema nan ma dai shiru, sai a lokacin yake samun labarin hatsarin da aka taffka yau a babban titti, da yake an saya labarin sai gaba ɗaya tunanin sa bai bashi nice ba…..

Ku yi haƙuri da wannan wallahi barci nake ji…

Kawu na ya shiga cikin tsananin tashin hankali, lokacin da ya fahimci cewa bana cikin anguwar gaba d’aya, domin duk inda yake sa ran gani na yaje bana nan, bai gama birkicewa ba sai da yaga k’arfe goman dare yayi, bashi da yanda zanyi dole ya juyo gida hankalin sa a tashe…

Anty na kenan, ita ko a jikin ta domin tun taran dare tayi barcin abun ta, tana tsaka da barci abun ta taji saukar duka akan cinyar ta, ran shi a had’e yace mata” dalla can tashi!  ki kore yarinyar mutane ki neme waje kin wani shantake..”

Cikin yanayin barci ta mik’e zaune had’i da yamutsa fuska tace” na kore ta dai mallan, dama can ta gaji da zama da mu tunda ta tafi menene abun damuwa, ni wallahi lamarin ka yana bani mamaki, akan yar k’aramar yarinyar nan ka d’auki damuwar duniya ka daurawa kan ka, to wallahi babu ruwa na in wani ciwo ya kama ka tunda kai kajawo kan ka ace yarinyar kamar wata Yar gwal…

Ai bai bari ta ida ba ya zaffga mata wani ingarman mari, gaba d’aya k’uncin ta sai da ya d’auki dumi, cikin mutu’kar b’acin rai yace” wallahi kinji na rantse ko zaki fita a saceki sai kin fita a gidan nan kin nemo min y’ata, in ba haka ki bar gidan nan bari na har abada…”

Tsananin kad’uwa ya sa ta mike tsaye, jikin ta ya dauki rawa bakin ta a karkarwa tace” kayi wa Allah da manza tsira kayi hakuri, ko da ace zanje neman ta mu bar wa safiya..”

” Wallahi kinji na rantse? banga wanda ya isa ya hanani aikata abunda na ga dama ba a cikin gidan nan, dole ne kiyi abinda nace ko kuma ki kama gabanki..”

Babban tashin hankali ya rufe a lokacin, ji tayi wani kashi ya matse ta, sabida tsabar tsoro ta sake marairaice fuska tace” Abban Hanna, ka dube dajarar yayan dake tsakanin na dakai kayi min sausauci, wallahi zanje amma da safe..”

” Ok zaki tsaya ja inja dani kenan, yanzu ko zan nuna miki hauka na yafi naki..” ya fad’a yanayi kan tabaryar dake yashe a tsakar gida…

Ai kafin ya dawo ta zira haijabin ta, da Yar k’aramar fittilar ta, ta fito waje…

Yana kallon ta ta fice hankali a tashe da tunanin ina zata nufa yanzu kuma?…

Sai a lokaci wani hawayen ladama yazo mai,  alwala ya daura ya tada sallah, zuciyar sa cike da tunanin halin da take ciki a yanzu domin a jikin sa yaji duk inda take yanzu to babu lafiya…

******

” Ya aike ciki doctor?…” Cewar Hajiya Daddah..

Murmushi yayi cikin yarda da kan shi yace” to Alhamdulillahi zamu ce Hajiya, domin munyi nasarar ceto rayuwar ta, yanzu haka ina me miki albushir da cewa zata iya tashi a ko wanne lokaci…”

Murna ya cika zuciyar su Hajiya cikin jin dadi tace” mun gode doctor, Nusaiba kina ji ko?..” ta fad’a cikin murna had’i da duban Nusaiba dake tsaya a gefen ta…

Doctor yayi murmushin takaici kana yace”

 sai da akwai wata matsala guda daya, zaiyi  wuya in ta farka ta tashi kalau, domin bincike ya nuna mana ta samu matsalar a cikin bring dinta, sanadiyar buguwar da tayi ta samu rauni sosai gaskiya, kuma bazai yiwa muyi mata aika a halin da take ciki a yanzu ba ….”

Take an’nuri fuskar sa ya dauke, damuwa da tashin hankalin ya shige su a lokaci d’aya, Hajiya Daddah tace” to yanzu doctor ya za’ayi? ko akwai wata dabara da za’ayi mata?..”

Yayi gyaran murya yace” eh yanzu zamu daura ta akan magani ne, da ta samu sauki wannan raunin dake kanta, sai muyi mata aiki nan da wata sheda masu zuwa insha Allahu…”

” Doctor kamar wanne aiki kenan.. cewar Nusaiba dake shirin fashewa da kuka…

” Yauwa abinda nake nufi a nan shine….

to sabida haka tana mutu’kar buk’atar kulawar ku, zata nayi wasu abubuwan tamkar k’aramar yarinya, tunda ta manta komai nata nan ma tana buk’atar kulawa, abun ma zaizo mata da sauki sabida maguguna da zamu rubuta mata yanzu…”

Gaba d’ayan su hawaye suke sharewa, cikin jarumta Hajiya Daddah ta kama hannun Nusaiba tace”  kwantar da hankalin ki yata, babu abinda zan faru da yarda Allah, zata samu lafiya insha Allah wata sheda akace ai ba shekara ba, ki nutsu kinji?..”

” Hajiyar mu yanzu ya zanyi da hakkin yarinyar nan ne? da ban mai magana ba da bai make musu yarinya ba…”

” Shittt bana son irin wannan maganar kinji, kiyi mata addu’a domin ita take buk’ata a yanzu, Allah ya bata lafiya okay..”

*****

Duk inda take sa ran ganin ta taje, a cikin daran nan amma babu wani ci gaba, kamala d’aya ce ake maimaita mata,  hata gidajan da take bi sai da taje, wasu har sun kulle gida wasu kuma ko tayi magana babu amsa, sai wajejen Sha biyu da rabi na dare ta nufo gida, zuciyar ta nayi mata rad’ad’i musamma in ta tuna wai yau akan MUNIIBAT mijin ta uban yayata ya wanka mata mari har da kiran ta wawuya, ta dalilin ta igiyar auren ta ke rawa, tsikashi aiko muddin yarinyar nan ta dawo sai nayi mata mugun dukan da sai ta gwamace kida da karatu wallahi…

Iya masifa da bala’i duk inda take, a ranar yau Anty ta shige ta, domin da tayi wasa sai da Kawu yayi mata mugun duka, wanda tunda ya aure ta ku zagi bai tab’a shiga tsakanin su ba, sai yau ya had’a mata har da duka, tayi kuka kamar ranta zai fita sai yanzu ta hango katuwar wautar da tayi, tabbas ta aikata babban k’usk’ure da ta saka aka kori MUNIBBAT…

******

Bayan kwanan biyar, duk wannan badakalar da ake ban saniba Ina kwance akan gado tamkar gawa, ban san komai bana jin komai kuma.

Bayan k’wana biyar, duk wannan badak’alar da ake ina k’wance tamkar gawa, domin ko motsin kirki bana iyawa, ruwa kam na shashi sosai..

Allah sarki bayin Allah nan mutanen kirki ne, domin daddah da Nusaiba suke min wanka in buk’atar hakan ta taso,  suna kulawa dani tamkar d’iyar cikin su, mommy kuwa tun daga ranar da abun ya faru bata sake zuwa, inda nake ba…

Cikin rantsatsiyar shiga ta alfharma, tana zauna a tsakiyar falon ta ta hakkimce, cikin isa da gaddara ta d’ago idanun ta da kyar ta motsa bakin ta kamar bata so tace” My son! baza ka tab’a gane abinda nake so da kai ba, yanzu banda abinka me zai daga maka hankali akan abinda nayi itafaki ko takata kayi ta mutu, duk cikin garin nan babu wanda ya isa yaja damu, bare kuma dan ta bugo shine ka d’auki damuwar duniya ka d’aura wa kan ka, haba My son me kake san zama ne yanzu?  Ita baka duba babbar sadaukar war da Big Man yayi mata ba? Jinin shi ya bata, har abada bata da abinda zata saka mai dashi KO ta tashi, no bana son damuwa kaji ka saki jikin ka kayi rayuwar ka kamar dah, ina so ka manta da ita ko asibitin daga yau na soke maka zuwan shi…”

Cikin sauri ya kai duban shi zuwa gare ta, hankalin sa a tashe yace” mommy  bakya ganin in nayi mata haka ba rashin adallaci nayi ba? domin koma wannan irin hali take a yanzu na kaddara iyayen ta a yanxu suna cikin babbar damuwa da rudani, Mommy NA CUCE TA  sosai, na rabata da iyayen ta dangin ta, kannen ta, na fara tunanin naje gida rediyo ko BBC na saka cikiyar iyayen ta KO Allah sai sa a dace, tunda abin nan ya  faru bana jin wani nata yazo,  wallahi mommy ina cikin wani hali ina ji a jiki na kamar…”

” kai! kai! kana jin me!?? me kake san mayar da kan ka ne? wai shin ka manta ko kai din d’an waye? ka manta matsayin ka da ikon ka, yanzu dama akan wata yar tsintuwa kake son daurwa kan ka damuwa? kar ka manta ko ita yar waye a cikin garin nan kana da ikon da za kayi banza da rayuwar ta ma ba wai damuwa da ita ba,bana san shirme An’nuwar! ko da wasa muddin kana bin umarni na karka sake zuwa inda take, bare ma ta dame ka! ba shawara nake baka ba umarni na ne kaji ko?…”” ta fad’a cikin masifa, amma  muryar ta cikin salama take maganar…

” OK mommy ya wuce Allah ya bata lafiya..””

” Ameen yaro na, zanyi ma daddyn ku magana zuwa jibi ma zaka bar kasar nan, ko hakan zai sa kasamu nutsuwa…”

Baice komai ila wasa da yatsun hannun shi da yake, zuciyar sa cike da tunanin yarinyar da yake mata kallon sani a yanzu, gefe d’aya kuma tausayin ta yake ji, gani ba wanda ya neme ta, sam baiyi farin ciki da wannan maganar da mommy tayi masa ba, amma dole ne ya kasance me biyayya…

 ******

A tsaye yake akan ta, ranshi a mutuk’ar b’ace yake duban ta, cikin k’ak’ausar  murya yace” wallahi tunda har yanzu sanyin idaniya ta bata dawo cikin gidan nan  ba, daga rana irin ta yau kema kinyi bankwana da farin ciki! dama ba’a kan shi bane kika kore ta? ki sa a ranki kamar yanda ya tafi kema wani bangarenki ya tafi, karki manta har yanzu ina nan akan bakata muddin na gano gaskiya to zaki fuskaci hukunci me tsanani…”

in da sabo yaci ace zuwa yanzu Anty ta saba da halin Kawu na yanzu, amma ba’a sabo da cikin mutunci ko kad’an….

Ta share kwallar dake bin  kunci ta, cikin shashek’a da sauke ajiyar zuciya tace” yanzu dama nan gaba banda wannan cin mutuncin da kake min akwai wani wanda ka tanadar mini  da har yafi na yanzu? karfa ka manta ni matar kace uwar y’ay’anka, dan Allah dan girman Allah dan sanka da fiyayya halinta, ka rangon ta min ko yaya ne…?””

Wani banzan kallo ya aika mata dashi, wanda ya rud’a mata yan hanjin ta, cikin halin ko in kula yace” ki fara neman rangwame a wajen mallicin mu, ba’a waje na ba, karkiga na tsaya ina magana dake a yanzu, kamawa tayi ki wuce kije ki nemo min  yarinya ta…”

Jiki a sanyaye ta fice a gidan kafaffun ta ko sai ciwo suke mata, tana fita ya neme waje ya zauna zuciyar sa na zafi, a hankali ya dafe sitting zuciyar sa game da numshe idanun sa, ” ina kike shiga ne yar amana ta? yanxu me kike a wanne hali kike ciki yanzu? me yasa zakiyi min haka? dama zaki iya tafiyar ki bar Kawun ki?…” Sai kuma k’walla ta biyo baya…

<< Waye Zabin Munibat? 12Waye Zabin Munibat? 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×