Skip to content
Part 16 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Uchenna Pov.

Yau kwanansa uku da fara aiki a Hanam Fashion House, kuma aiki a wajen na masa daɗi, shi da Hanam suke zana ɗinkin da za’ayi, amma kullum tana faɗin nasa yafi kyau, kuma a kullum zai yi ɗinki cikin yabawa take.

Amma kuma ya lura da wasu sabbabin ɗabi’u da take da su, bata sakarwa kowa fuska, duk da dama can haka take, amma kuma na yanzu yafi na da ɗin, kuma a yadda ya lura bata da aure, hakan yasa ya tambayi wani Aminu a wurin, wanda yake kawo masa kayan aiki idan ya buƙata.

Kuma Aminu ya faɗa masa cewa, suma haka suka ganta da ɗan, daga tafiya USA na shekara biyu sai gata ta dawo da da, kuma har yau iƙirari take kan cewar itace uban ɗan, abun yaso ya ɗaure masa kai, dan haka yayi niyyar tambayar Abba.

Yana zaune a office ɗin da aka bashi domin ɗinki, bayan ya gama dinka wata riga sai ya ɗauki break yana shan coffee, kawai sai yace bari ya kira Abba ya tambayeshi, tunda basa samu su hadu.

“Abbana”

Cewar Uche bayan Abba ya ɗaga kiran kuma sun gaisa.

“Na’am ɗana”

“Tambayarka na ke sanyi”

Ya faɗi yana kallon windown daya buɗe, hannunsa na dama rike da mug.

“Faɗi ɗan Abbansa, ina jinka”

“Abba…”

Sai kuma yayi shiru, shi sam bai iya ƙunbiya-ƙunbiya ba, idan yana so ya faɗi abu kansa tsaye ya ke faɗarsa, amma yanzu sai ya ji nauyin Abban, sai ya tattaro ƙarfinsa ya furta abinda zai zama sanadiyyar sauyawar ƙaddararsa.

“Abba ni Hanam ta tab’a aure ne ?”

Abba bai yi mamakin tambayar ba, dan tun a ranar da Uche ya fara zuwa HANAM FASHION HOUSE ɗin ya faɗa masa cewa ai ya san Hanam sun tab’a yin aji ɗaya a secondary.

“A’a Haris, bata tab’a aure ba”

Uche yayi wata b’oyayyar ajiyar zuciya, amma duk da haka saida Abba ya ji, Abba yayi murmushi

“Haris”

“Na’am Abba”

“Next week zanje Hakuɗau, kuma tare nake so muje”

Hakuɗau shine mahaifar Alhaji Muhammad.

“Zuwa lokacin na gama aiki a nan, ba matsala zamu iya zuwa”

“Eh nasan zuwa lokacin ka gamawa Hanam aikinta, kawai na faɗa maka ne dan ka shirya”

“To Abbana, Allah ya kaimu”

“Ameen ɗan albarka na”

Kuma daga haka wayar ta ƙare, Uche ya aje mug ɗin hannunsa akan wani table, sannan ya dawo ya ɗauki measuring tape, ya shiga auna wani yadi, zuciyarsa fal tunane-tunane iri-iri.

Kuka yaji, kuma yasan cewa babu me kukan bayan Arya, dan ɗakin da ake renonsa kusa da office ɗin sa ne, Allah ya sani tun daga ranar da yaron ya riƙe ƙafarsa ya shiga ransa, dan haka da sauri ya aje yadin da measuring tape ɗin duka ya fice da sauri ya faɗa ɗakin.

Ya iske Naani ɗin nasa ta na rarrashinsa shi kuma sai kuka yake, gabaɗaya ya rikita Naani ɗin nasa.

“Kinga kawo shi”

Ya faɗi yana miƙa mata hannu, miƙa masa shi tayi, shi kuma ya karb’eshi ya fice daga ɗakin.

Office ɗin nasa ya koma da shi, ya shiga rarrashinsa, amma yaƙi shiru, sai kawai Uche ya ɗauki wani zanin atamfa daya yanka ya goyeshi, yana jijjiga shi.

Tunda Aryaan yazo duniya ba’a tab’a masa goyo irin wannan ba, dan Hanam bata goyonsa sai dai ta saka shi a baby carrier, nan da nan yayi bacci.

Hanam taji kukan Arya hakan yasa itama ta fito domin taga abinda yake faruwa, sai Naani ɗin ta faɗa mata cewar ai wannan na ɗayan office ɗin yazo ya karb’eshi, dan haka Hanam ta fita, ta shiga office ɗin Uche.

Samunsa tayi yana kai kawo da Aryaan ɗin a bayansa, kuma gashi ya goye shi, wani abu ya motsa a kirjinta, wanda rabonsa da ya motsa tun shekaru biyu baya, sai ta kawar da tunanin, dan a ganinta abun ba mai yiwuwa bane, ita sai abun ma yaso ya bata dariya, namiji da goyo, kuma ya iya goyon ko dan igbo ne oho.

“Yanzu Uche da atamfar dubbunan kuɗin ka goyi yaro ?”

Ta faɗi tana shigowa ciki, shi sam ma bai kalleta ba.

“Me zai hana idan dai boy zai yi shiru, idan yana kuka bazan iya aiki cikin kwanciyar hankali ba”

Hanam taji wanna abun ya ci gaba da motsawa, kuma wannan irin wanda ta ji ne lokacin da ta haifi Arya ɗin.

“Naga ya yi bacci kawo shi, kar ya hanaka aiki”

“Ba dole yayi bacci ba, yaji goyo, nasan yanzu haka ba goyonsa kike ba”

Ya faɗi yana ƙoƙarin since zanin goyon.

“Na miye zan wani zo ina goyonsa, ai baby carrier ɗin shine dai-dai shi”

Ta faɗi a lokacin da ya miƙa mata shi, daga haka kuma ta fice daga wajen, Uchenna ya bi su da kallo su duka, yana murmushi ya dawo ya ci gaba da aikinsa.

ALARO CITY, BLOCK 3, HOUSE NO 122.

Da misalin karfe 06:00pm.

Maryam ce tsaye a cikin kitchen ɗin gidan, meat pie take haɗawa, dan yau da safe Tafida ya faɗa mata cewar an gama komai na makarantar ta dan haka gobe za suje tare a ƙarasa sauran abubuwan.

Yanayin murnar da take ciki sam ba mai kwatantuwa bane, lokacin da aka ɗaura musu aure kowa faɗi yake cewa tayi sa a duk ba taga sa’ar da tayi ba sai yanzu, a yadda ta fahimta shima sam baisan da auren ba, amma kuma haka ya haƙura ya karb’i auren nasu hannu biyu.

Kuma babu abunda ya rageta da shi, komai yana mata, bata da wani abunyi sai godewa Allah da kuma shi Tafidan, data fusakanci baya san tana gode masa sai ta samo wata hanya ta gode masa da ban, Ta lura da yana da san cin abinci, kuma yana san abincin da take girkawa dan haka sai ta ke gode masa ta hanyar abinci.

Kullum da safe sai ta tsantsara masa girki na gani na faɗa, da yamma ma haka, dama na rana baya ci a gidan, duk girkin da take dashi a wayarta shi take masa, kuma dama ita gwanace wajen girki, kuma ta lura da yana jin daɗin girkin nata.

Saboda zata fara zuwa makaranta yasa yau ta yanke shawarar musu meat pie da cake, saboda koda zata makara da safe wata rana, sai su samu su rage hanya.

Kuma shekaran jiya yace mata taje su gaisa da matar maƙocinsu, kuma taje ɗin dan harma ta ɗan jima a gidan dan matar tana da kirki, duk da ta girme mata a shekaru, dan zata iya fin Anti Fati ma.

So take tayi ta gama soya meat pie ɗin kafin magariba tayi, dan cake kam tuni ta riga ta gama shi, shima meat pie ɗin kaɗan ne ya rage.

Kuma kafin maghribar ta gama soya shi tas, ta juye a wasu containers masu kyau, ta zuba cake biyar meat pie shida a wani ƙaramin kwano me murfi, wanda zata miƙawa Maman Ilham, kamar yanda matar tace mata shine sunan ƴarta ta farko.

Ta zuba gabaɗaya kayan data b’ata a dish washer, dan bata wani wanke-wanke, komai cikin sauƙi take yinsa, ta goge duk inda ta b’ata, sannan ta ɗebi warmers ɗin data zuba abincin data girki, ta fita daga kitchen ɗin.

Ta jerewa Tafida nasa akan danning table, sannan tayi sama. Sallar magariba ta gabatar, sannan ta ƙara sauƙowa ƙasa ta ɗauki wayarta dake chargy a parlo, ta ɗauki wannan kwanon data zubawa Maman Ilham meat pie ɗin, ta janyo ƙofar parlon ta fito compound ɗin gidan.

Sai da ta kalli parking lot ɗin gidan, motocin Tafida ne guda biyu kawai, dan ya fita da guda ɗaya, ta buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ta fito.

Bata damu da ta kulle gidan ba, dan a ganinta babu wanda zai iya shiga gidan bare har yayi sata, ta tsaya tana kallon kyakyawar unguwar tasu, yadda take da kyau da daddare, bata tab’a fitowa da daddare ba sai yau, dan last time data fito har ta shiga gidan Maman Ilham ɗin da rana ne, kuma shine fitarta na farko, sai kuma yau a gabaɗaya zamanta a unguwar wurin kwana shida, sai dai ta ganta ta saman balcony.

A hankali ta shiga takawa har zuwa ƙofar gidan dake jikin nasu, wanda yake shima sak nasun yake, ita ranar data shiga gidan ma tayi zaton zata ga komai na ciki irin nasu ne, amma sai taga hatta da ginin cikinma irin nasun ne amma banda kayan cikin.

Kanta tsaye ta tura ƙaramar ƙofar ta shiga, dan ta lura da gaba ɗaya gidajen unguwar basu da masu gadi.

Sai da ta ƙwanƙwasa ƙofar parlon gidan, sannan aka buɗe, Ilham ɗin ce ta buɗe mata ana gaisheta, itama Maryam ɗin ta amsa mata da fara’a

“Ilham waye ne ?”

Muryar Maman Ilham ɗin ta tambaya daga cikin parlon, Ilham ɗin ta buɗe kofar gaba ɗaya tana faɗin.

“Anti Maryam ce”

“To ta shigo mana, sai ta tsaya a waje?”

Maryam ta shigo tana murmushi, Maman Ilham ɗince a parlon ita da sauran yaran nata biyu, Aliyu da Abdul, ta zauna a sanda suma suke gaishe ta, sannan suka gaisa da Maman Ilham ɗin.

“Maman Ilham meat pie ne nayi, shine nace bari na kawo miki a bawa yara”

“A’a to an gode”

Maman Ilham ta faɗi tana karb’ar bowl ɗin

“Gobe zan fara zuwa makaranta”

“Ta na Alaro zaki fara zuwa ?”

“Eh”

Maryam ta amsata kanta a ƙasa kamar yadda ta saba.

“To Allah ya taimaka, Allah ya bada sa’a Maryam.”

“Ameen, ni zan koma”

Take ta miƙe.

“Har za ki koma?”

“Eh magariba ta yi, nasan ya kusa dawowo”

“Hakane kam, Ilham tashi ki rife mana ƙofar”

Ta ƙarashe tana kallon ilham ɗin, lokacin Maryam har ta kai bakin ƙofa.

Tun daga fitar ta daga gidan su Ilham ɗin ta hangi motar Tafida sai kawai ta tsaya a ƙofar gidan har ya ƙaraso, ya buɗe gate ɗin da wayarsa sanna ya shiga da motar.

Amma bai kulle gate ɗin ba dan ya ganta shima, fitowa yayi daga motar ya dawo ƙofar gidan inda take, kuma tun kafin ya ƙarasa inda take ya fara sabbaben nasa, wato sauraren bugun zuciyarta, wani abu da ya zame masa farilla a kwanakin nan, abun na mugun bashi mamaki, dan yanzu abun ya zame maza jiki.

Idan baya gidan har Allah-Allah yake ya dawo, dan yazo yaci daddaɗan girkinta, ga kuma daddaɗan sautin bugun zuciyarta, wanda yake saka masa nutsuwa a kodayaushe, a da daga asibiti sai gida sai kuma filin wasan cricket, bashi da wani abu na nishadi bayan cricket ɗin.

Amma yanzu an samu sauyi, zuwan Maryam rayuwarsa ya sauya abubuwa da dama, ya koma wani Tafidan da ban da na da, yanzu ya koyi yawan cin abinci, sab’anin da, da ba sosai ya cika cin abincin ba, saboda shi bai cika san cin abincin waje ba, yafi so ya girka da kansa, wani lokacin a makare yake tashi baya samun damar yin girkin.

Da yamma kuma ya dawo a gajiye wataran sai dai ya ci bread kawai ya sha ruwa, amma yanzu a kullum so yake tace masa ga abinci, dan ya samu yaci daddaɗan girkinta, shi yana mamakin yadda kanta yake a waye, ga yanda ta iya girki, har tunani yake ma wataƙila tayi makarantar koyon girki ne.

Ga kuma yawan sauraren waƙa da yake a da, amma banda yanzu, sam sauraren waƙarma baya gabansa, wannan bugun zuciyar tata, shine ya zame masa kamar waƙar, wani lokacin sai ya raba dare yana saurarensa, koda tana ɗakinta yana iya jiyoshi.

Sai dai idan tana ƙasa ne, amma middin tana ɗaki to zaiji yanda zuciyarta ke bugawa, kuma har yanzu idan yana tsaye a gabanta zuciyarta na bugawa cikin tsoro.

Sai kuma wani abu dake faruwa da shi, rabon da baƙin ruhinsa ya tashi tun yana Haɗejia, kuma hakan ya bashi mamaki, duk da a wasu lokutan idonsa na sauya kala, duk da a da can baƙin ruhin baya tashi sai idan an b’ata masa rai.

Shi kuma abu mawuyacine ke b’ata masa rai, a kwanakin nan ne abun yayi ƙamari, amma kuma yanzu gashi ya tafi, Sannan har cikin ransa yake fatan Allah yasa ya tafi har abada. Sai dai kuma shi da kansa yawan cewa yana nan, babu inda ya tafi, Dan akwai wannan super natural ɗin a jikinsa.

Ko kaɗan baya fatan wani abu da zai cutar da Maryam, musamman ma ace daga gareshi ne. Gaskiya Muktar ya faɗa, tabbas yayi dace, dan Maryam ɗayace tamkar da dubu, samun irinta a wannan zamanin sai an tona.

“Sannu da zuwa”.

Muryarta ta fito cikin sanyinta, kuma yaji sanda zuciyarta ta buga, ya samu kansa cikin irin yanayin da yake tsintar kansa a duk lokacin da ya saurari bugun zuciyar tata cikin tsoro ko nishadi koma murna.

“Sannu Daaso, gidan Mustapha kika je?”

Daaso? Da shekaran jiya ya fara kiranta da sunan, wataƙila dan nishaɗi yake kiran sunan, Mustapha kuma ta san sunan mijin Maman Ilham ne, dan haka ya faɗa mata ranar da yace mata taje gidan.

“Eh, nan naje, banma jima ba yanzu na shiga kuma na fito”

Ya ɗan cije lips dinsa kaɗan, sannan ya gyaɗa kansa a hankali.

“Hira kika je ku kayi?”

“Ko kaɗan, nayi meat pie ne, shine na kai mata nace a bawa yara”

Yanzu ma kansa ya gyaɗa sannan yace.

“Muje ko?”

A hankali ta fara takawa zuwa cikin gidan, ya tsaya a wajen yana kallonta, sannan ya rufe gate ɗin, ya shigo gidan shima.

Bai sameta a parlo ba dan haka yayi saman shima, wanka kawai yayi dan yayi Sallah a hanya, ya saka wasu jogger set farare, ya rufe kansa da hular hoodie ɗin kayan, ya sauƙo ƙasa, cike da farin cikin zai ci girkin Maryam.

Kuma kamar yadda ya zata ɗin ne, ta aje masa komai akan danning, ruwan shansa da abincinsa yaga yau harda juice a wani jug na glass.

Bai san sanda murmushi ya sub’uce masa ba, to shi kuwa miye ba zai yiwa wannan innocent soul ɗin ba?

Kujera ya ja ya zauna, sannan ya buɗe plate ɗin da ta aje, ya buɗe warmer ɗin farko, wadda yake da tabbacin miyace a ciki, kamshin spices ne suka fara shiga hancinsa, kafin yayi arba da cabbege sauce, kalar cabejin daya hadu da attaruhu da tattase sune suka fi ɗaukar hankalinsa.

Harda haɗiyar yawunsa, sannan ya aje murfin a gefe, ya janyo ɗayar ya buɗe ita kuma farar shinkafa ce a ciki, wadda ta dafata da carrots da kuma green beans.

Duka ya juye shinkafar a plate ɗin, sannan ya zuba miyar, ya hauci yana ta lumshe ido, da ace yana da yawan magana da wataƙila santi zai yi, dan abincin nata ya kai a masa santi.

Yana ci yana haɗawa da strawberry juice ɗin da ta aje masa, har ya cinye tas, dan dama bata tab’a zuba masa abinci ya rage ba. Tashi yayi ya shiga kitchen ɗin, ya buɗe dish washer sannan ya jere mata kayan a ciki.

Har ya juya zai fita kamshin wani abu ya bigi hancinsa, ya waiga ya waiga sai hango wasu containers guda biyu kusa da stove, bai yi tunanin komai ba ya nufi wajen.

Ta farko ya buɗe yaci karo da meat pie, hannu ya kai ya ɗauki guda ɗaya ya kai bakinsa, ya cinye shi tas, sai kuma ya rufe mata.

Ya buɗe ɗayar ita kuma cup cakes ne a ciki shi kam guda biyu ya ɗiba ya cinye shi duka, a ransa yake faɗin, Maryam na so ta maida shi acici.

Rufewa yayi ya maida mata ya aje sannan ya fito, a parlo ya zauna, ya kunna wata tashar da ake nuna wasan cricket, ya kishingiɗa yana kallo, harda ture hular hoodie ɗin, ya shiga shafa sumarsa data fara taruwa, saboda alƙawarin da ya yiwa Daadi, hatta wajen fade ɗin ma ya tara gashi.

Ko me ya tuna sai ya miƙe tsaye ya nufi ɗakinsa ya ɗauko wani abu ya dawo ƙasan, yana daga inda yake ya ƙwala kiran Maryam.

Maryam na zaune a ɗaki tana sauraren ƙira’a qur’ani, taji kamar Tafida na kiranta, kasan cewar kunne ɗaya ta saka.

Sai ta cire ear piece ɗin, ta shiga ƙoƙarin danna pause amma sam wayar taƙi bata haɗin kai, haka take mata kwana biyu, ta ɗan ja gajeren tsaki, sai ta tsayar ta jikin ear piece ɗin, ta miƙe hannunta riƙe da wayar ta saka hijjabinta ta fita.

A parlo ta sameshi, sai ta zauna a ƙasa.

“No seat here”

Maryam ta kalli inda yake nuna mata, gefen kujerar da yake zaune a kai ne, kasan cewar kujerar nada tsayi ita kuma sai ta zauna a can ƙarshen kujerar.

Kanta a ƙasa kamar kullum idan tana gabasa, gyaran murya yayi, bayan ya gama saurarar abinda ya saba.

“Kamar yadda na faɗa miki, an gama komai da kamai na makarantar ki, so gobe zamu je tare zamu ƙarasa abinda ya rage. Nasan za ki buƙaci wani abun na amfanin makaranta, so ni bansan me kike so ba, dan haka na yanke shawarar kawai na baki kuɗin ki siyi kome kike so, dan akwai super market nan kusa da block ɗin mu, zaki iya zuwa ki siyi abunda kike da buƙata”

Ya ƙarashe yana mika mata kuɗin da Maryam bata san adadinsu ba, hannunta cikin hijabinta ta karb’a, kuma hannu biyu

“Nagode sosai, Allah ji ƙan mahaifa”

Bai amsa a fili ba sai yaci gaba da cewa

“Kina da waya ne?”

A hankali ta gyaɗa masa kai, tana fito da wayar tata daga hijabi ta nuna masa, sai da Tafida ya kusa yin dariya, amma yasan idan yayi zata ji babu daɗi, amma wayar tata ta bashi dariya, like for real matar Tafifa da wannan wayar.

“Daaso wanna ai ba waya bace”

Dama tasan za’a rina, taya za’ayi Tafida ya kalli wayarta da kima, yana riƙe waya biyu, kuma duk da ba sanin kuɗin wayoyin ta yi ba tasan masu tsadane.

Barinma iPhone ɗinsa, dan wayar ta burgeta ita kanta, musamman ma gefen wayar wani abune aka kewaye wayar dashi kamar gold

“Karb’i wannan, akwai numbers ɗima akai, idan na shirya zan karb’e su”

Ya miƙa mata Samsung ɗinsa, ƙirar S22 ultra, Maryam ta kalli wayar, sai kuma a hankali ta ɗago ta kalleshi, shima ɗin ita yake kallo, kafin ta kai hannunta ta karb’i wayar, za tai masa godiya ya katseta da faɗin.

“No Miriam, you don’t need to be”

Miriam ? Ita kuma haka za ta yi ta samun sauyin sunaye?

Ranar haka ta kusan raba dare tana ta shige da fice a cikin wayar, ita wayar ta ma fi burgeta akan kuɗin da bata ma samu ta ƙirga ba.

Duk da shima kuɗin ta ji daɗinsa, domin bata tab:a riƙe kudi kamar haka ba, ƙololuwar yawan kuɗin da take riƙewa a hannunta shine na registration ɗinta.

Amma ita wayar tafi yin gaba da ita, kuma taga babu sim a kai, saide wasu numbers da basu da yawa, kuma a ciki akwai ta Daadi, Neha, Chaacu Imran (Wato kawu Imran), Chaacu Irfan (Kawu Irfan).

Choti Gulzar (Sieger Gulzar), Ramesh, Arjit, Mahesh, da dai sauranau, yawancin number ɗin na india ne, hakan ke nuna mata cewar da yan uwansa na india Yake waya.

Sai kuma gallery data duba, tarin hotunansa ne birjit, abun har ya bata mamaki, ganin namiji da yawan hoto, ita da take mace ma bata da wasu hotuna na azo a gani, amma nasa kam sai baki take kamawa dan mamaki.

Kuma ciki taga na wadda take kyautata zaton itace Neha da kayan sojoji an musi shi da ita, abun mamakin shine kayan sojijin nigeria ne a jikinta, kuma gata ba india, hotuna dai sai wanda ya manta baiyi ba.

A ciki ma taga wani nasa wanda ya tara gashi a kansa har yayi parking ɗinsa, harda dariyarta, dan style ɗin hoton ya bata dariya.

“Eshaan Tafiida”

Ta furta muryarta ɗauke da wani irin nishadi da bata san daga ina yake fitowa ba, a cikin daren gaba ɗaya ta ɗebe kayan wayarta ta maida kan wayar, amma bata tab’a masa hotonsa ba ko ƙwara ɗaya, dan wataƙila ya buƙaci kayansa, amma taji daɗin samun wayar sosai ba kaɗan ba.

Hanam Pov.

Cikin sati ɗayan da Uchenna Franklin yayi a ƙarƙashinta sun ƙara samun kusanci, duk da bata fatan ya haura harkar kasuwanci kawai, dan ita dan shi tasa aka kawo shi, bayan nan kuma bata fatan wata alaƙa daban, saboda kamar yadda ta faɗa masa ne a wancan lokacin suna da banbanci sosai.

Kuma cikin sati ɗayan ya gama mata aikin da zai mata, sannan taji daɗin aiki dashi sosai ba kadan ba, dan ya iya ɗinki sosai, kuma bayan sun gama aiki saida ta sake masa tayin karb’ar kuɗi kamar tun sanda suka fara aikin amma yaƙi, kamar de da farkon.

Yace ita ƙanwarsa ce, ba zai karb’i kuɗinta ba, yayi mata ne matsayinta na ƙanwarsa.

An ce komai yayi farko yanada karshe, gashi har yau Uchenna zai bar fashion house ɗin, ya shigo office ɗinta tana bawa Arya custard dan yau Naani ɗinsa bata zo ba, ta miƙe da Arya ɗin a hannunts, tana masa murmushin da ma’aikatan wurin suka faɗa masa shi kaɗai takewa irinsa, amma su dai kam basa samunsa.

“Har ka gama ?”

Ta yi maganar tana kallon jakar hannunsa

“Eh wallahi na gama haɗa komai, zan kuma koma bakin aiki na”

“To Mr. Uchenna, Nagode, nagode sosai, thanks a ton”

“ you got it, my friend baƙo zai yi halinsa”

Ya faɗi yana ƙoƙarin karb’ar Arya daga hannunta ta sakar masa shi, ya karb’eshi.

“Muje na taka maka to”

Haka ta raka shi har parking lot, inda ya aje motarsa, ya bata Aryaan sannan yayi musu sallama ya tafi.

Mafarin komai kenan

<< Yadda Kaddara Ta So 15Yadda Kaddara Ta So 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×