Sai ya gyaɗa mata kai yana takawa ya soma barin wurin.
“Min bit kun ?”
(waye kai ?)
Ba tare da ya juyo ba ya amsa ta da.
“Ana bi kun zauja (Ni mijinta ne)”
Su Mero da ‘ya’yanta sai kukan nadama suke, Hakama Hajjo, duk da ita bata wani ƙuntatawa Hanam ɗin sosai ba.
Haris ya tsaya a gaban Rashidat yana ƙoƙarin karb’ar Arya, sai ta girgiza masa kai
“No, you go, and take care of your wife, ka barmin shi, zan kula da shi”
“Kin tabbata ?”
Rashidat ta gyaɗa masa kai, shima sai ya gyaɗa mata kan.
“Idan kin shirya tafiya kimin magana, sai nazo na ɗauke ki”
“Kada ka damu, a gidan Hajiya zan kwana ai, fatan de yaron yana cin abinci ?”
Kansa kawai ya gyaɗa mata, dan tsabar damuwa ya rasa ina zai saka kansa ma, motarsa ya koma sannan ya tuƙa motar zuwa Cosgrove estate.
Yana zuwa ya shimfiɗe Hanam a ɗakinsa, sannan ya kira Dr. Hasina, dan tazo ta dubata.
Yana zaune a wurin har tazo ta dubanta, sannan ta sanar masa cewa ba wata babbar matsala bace, amma duk da haka hankalinsa bai kwanta ba.
Har zuwa bayan isha yana zaune a wurin, kafin ya yanke shawarar zuwa ya watsa ruwa a jikinsa, wata ƙila ko zuciyarsa zata huce.
Sai dai me? Yana shiga bandlɗakin beko cire kayansa ba ya tsaya akan shower tana zuba akansa, ya rasa tunani me kyau akansa. Tunanin Abba ya dawo cikin kansa, ba shiri yaji wani kuka na neman kufce masa, kukan da ya yi ta riƙe shi tun jiya, kukan da ya hana shi fita tun jiya har zuwa yau ɗin nan.
Kasa riƙe kukan ya yi, dan haka ya ƙyaleshi ya fito, ya shiga rera kunsa amma mara sauti, jikinsa na karkarwa sbd kukan da yake ɗin, ya juya yana kallon bango, tare da dafe bangwan da hannunsa.
Can kuma da takaici ya ishe shi sai ya naushi bangwan, wani abu na suya a zuciyarsa, ba ‘ya’yan Abba ne kaɗai suka yi rashin sa ba, shima ya yi rashin Abba, a hankali memories ɗin Abban suka shiga dawo masa. Yaci gaba da kunsa yanzu harda shessheƙa.
Hannu yaji ya dafa shi daga baya, hakan ke nuna masa cewar Hanam. ta farka, ya yi sauran kai hannu ya share hawayen sannan ya juyo ya kalleta, tsaye take a bayan nasa itama ruwan na zuba a kanta, gashin kanta dake a hargitse ɗazu zuwa yanzu ya kwanta a bayanta sbd ruwan.
Yaga itama hawaye take, abinda yaga a fuskarta ne yasa ya kasa riƙe kukansa sai kawai ya rungumeta ya shiga rera sabon kuka, itama ta riƙeshi gam tana nata kukan, still ruwan yana zubowa a kansu.
An rasa waye zai rarrashi wani, domin babu wanda be yi rashi a cikinsu ba, shine ya fara ƙoƙarin seta kansa sannan ya saketa, ita har yanzu tana hawaye, wanda ya kasa banbance shi sbd ruwan dake zuba akan fuskarta.
Hannu ya kai ya tallafo fuskarta yana kallonta, kafin a hankali ya kai bakinsa kan nata, a karo na farko ya yi abinda bai tab’a ba, bai tab’a sumbatar mace ba koda wasa, kusan a tare suka lumshe ido.
Hanam bata tab’a tsintar kanta cikin irin yanayin ba, this was the first time ever da hakan ya faru da ita, a hankali Haris ya janye bakinsa daga kan nata, amma goshinsa a kan nata, tana jin yanda yake meda numfashi, hannayensa biyu ya saka ya kamo kugunta, sannan ya shiga raɗa mata kalaman ban haƙurin da bai samu ya mata ba.
Da yasan yanda kalaman nasa ke ƙona mata zuciya da bai fara ba, ita fa ta’aziyya ƙara tada mata miki take, shima kuma ya gane hakan, jin yanda teke shirin yin kuka, ya lalubo kunnenta sannan ya furta mata.
“I have falling for you Hanam, I am sorry”.
Sautin maganar tasa yasa jikin Hanam rawa, tsigar jikinta ta tashi, ba shiri hannayenta suka kewayo bayansa, sannan ta riƙe rigarsa ta baya, ta riƙeshi gam, kamar hakan ne zai sa ta dena jin abinda take ji.
Hannu ya kai ya kashe shower ɗin, sannan ya dawo da fuskarsa baya kaɗan, yana kallon fuskarta, idonta a rufe yake ruf, ruwan daya sauƙa a jikinta yasa fuskar tata jiƙewa, hakama kanta.
Kafin a hankali ya ƙara meda bakinsa kan nata, ya shiga kissing ɗinta a hankali, Hanam ta ƙara ƙanƙame rigar tasa, yayinda numfashinta ya shiga kai kawo a maƙoshinta.
*****
West Pavilion, Tafawa balewa square TBS complex, Victoria Island, Lagos.
Heleen ce zaune a kan ɗaya daga cikin kujerun dake falon gidan, codeine take shaƙa, dan kanta ya ɗau zafi, bata ganewa komai, babu abinda yake ƙona mata rai irin yanda taga matar Tafida, Tafida ?, ta yi imani cewa san Tafida shine ajalinta.
Ta ɗaga kanta sama bayan ta shaƙo hodar ibilis ɗin, a hankali kuma ta sauƙe kan nata, ta dishi-dishin da take gani taga siffar Tafida tsaye a bakin ƙofar falon, tunaninta shaye-shayen da ta yi yau ne yasa har take ganin siffar Tafidan, dan haka ta jingin da jikin kujerar, hawaye na sauƙo mata a ido, kalabar kanta ta sauƙo mata kan fuska.
Idonta ta rintse ko wannan siffar ta gabanta zata b’ace, amma sai taga tana nan bata b’ace ba, hakan yasa ta tabuɗe idonta da kyau, ta yanda zata samu tagan shi da kyau, wata iriyar wutar bala’i da masifa ta gani a idonsa, duk da a bige take ta ga yanda yake mata wani irin kallo, babu abinda ya ƙara kaɗa hanjin cikinta irin yanda kalar idonsa ta rikiɗe mata zuwa ja. Ta kafeshi da ido har ya ƙaraso gabanta.
A yau Tafida ya yi wa kansa alƙawarin kawo ƙarshen iskanci Heleen, he will make sure that he crash her fucking life.
Babban kuskuren da ta tafka shi ne tab’a masa Maryam da ta yi, ya tabbatar da wannan shi ne babban kuskuren da ta tab’a tafka irinsa a gaba ɗayan rayuwarta.
Yana ƙarasa inda take be yi wata-wata ba, ya damƙi wuyanta ya ɗagata sama, ya shiga naushin fuskarta da ɗayan hannun nasa.
Heleen ta shiga bubbuge hannunsa cikin neman ɗauki, kafin da ƙyar ta samo miryarta ta ƙwalawa yaranta kira a wahalce.
Babu b’ata lokaci suka fito daga ɗakunansu, kuma suna ganin yanda aka shaƙe ogar tasu sai suka yi kan Tafida, suka shiga dukansa amma ko gezau be yi ba, ji ya yi suna takura masa dan haka ya saketa ya komo kansu, ya shiga dukansu kamar da aka aiko shi, bai barsu ba saida ya kai kowannen su masa.
Sannan ya dawo kan bakar she**yar dake yashe a ƙasa, da ƙyar ta samu ta iya miƙewa a kan ƙafafunta, ganin kamar idan ta ƙyale Tafida kushewa zai kaita yasa ta kai masa naushi, kasan cewar a bige take, babu wani kuzari a jikinta, gashi kuma shi na miji ne, marfin ba ɗaya ba, kuma ga ba shi kaɗai ba ne, akwai baƙin ruhinsa tare da shi.
Hannun nata ya murɗe, jI kake ƙass!,ƙass!, ƙashin hannun na karyewa, ƙarar karyewar ƙashin ta fito tare da ƙarar Heleen ɗin, ta kai ɗayan hannun nata ta dafe wurin tsabar azaba, duk wahalar da ta sha a rayuwa bata tab’a shan makamanciyar wannan ba, bata tab’a sanin cewa haka Tafida yake ba sai yau.
Ɗayan hannun nata ya kama shima ya karya, yanzu kam saida ta cika gidan da ihu, be ƙyaleta haka na seda ya mata kara uku.
Kafin ya saketa ta faɗi ƙasa, sai kukan azaba take, a hankali ta dube shi, taga kalar ƙwayar idonsa, ga fiƙar da ke bakinsa data sauƙo, nan take wani tsoro ya ƙara mamayeta, rabonta da ta ji tsoro a rayuwarta tun sanda ta shiga kungiyar su, amma yau gata tana jin tsoron wani abun da ta so a baya.
“Idan kika ƙara kusantar koda inuwar matata ne, da ranki zan rabaki, fatan kin gane ?”
Kuma bai jira cewarta ba ya miƙe ya fita, Heleen ta ƙarawa kukanta volume, bata tab’a sanin cewa aljani take so ba sai yau, ashe dama Tafida aljanine ? To me yasa ita bata tab’a ganin hakan ba ? Kawai kyansa ne ya ruɗeta yasa ta fara sansa, yanzu azabar da ƙasusuwan jikinta ke mata itace ta dameta, ko sanda aka harbeta bata ji azaba irin wannan ba.
Da ƙyar muryarta ke fita wajen kiran sunan ɗaya daga cikin yaranta, shima da ƙyar ya miƙe kan ƙafafunsa, ya dafe ƙafarsa dake masa zugin azaba.
“Ka kira min doctor”
“A’a oga, asibiti ya kamata ace an kaiki”
“Ka kiramin likita nace, bana buƙatar ƙara zuwa asibit, ka kiramin wani likitan!!”
Ba zata ƙara wannan gangancin ba, dole ne ta kaucewa hanyar da zata ƙara haɗata da wannan aljanin, ba zata ƙara zuwa asibiti bama, balle taje ta ga wani aljanin shi ma ta fara sansa. Ita da Tafida kuma wata ƙila se a wata rayuwar, babu ita babu shi, ba zata ƙara bin hanyarsa ba ma.
*****
“Ka shiga ta farfaɗo”
Cewar Dr. Ola yana kallon Tafida, wanda bayan ya bar gidan Heleen gidansa ya koma, ya yi wanka sannan ya sauya kaya, ya ɗebarwa Maryam wasu kayan da zata saka gobe idan zasu dawo gida, dan ya riga ya yanke cewar daga yau bazata ƙara kwanan asibiti ba. Bayan ya fito shi ne ya shiga gidansu Ilham, ya faɗawa babanta sannan ya dawo asibitin.
Ya ɗago da idanuwansa da suka koma blue bayan ya sauƙe fishinsa ya kalli Dr. Ola.
“Me ya sameta ?”
Dr. Ola ya ɗan tab’e baki cikin faɗin.
“Kada ka damu fa, she is alright, babu wata damuwa yanz…”
“Me ya…sameta ?”
Ya maimaita tambayar cikin wata murya da shi kansa zai iya cewa ba tasa bace. Dr. Ola ya haɗiye wani abu sannan yace.
“Akwai rauni a gefen fuskarta, da alama dukan wurin a kayi, sannan an buga mata kai da bango, sai kuma wunyanta da aka saka ƙafa a ka taka, shi ne kawai”
Tafida ya ɗaga kansa sama yana hasaso yanda abun ya kasance, ina!, gaskiya hukuncin da ya yiwa Heleen ya yi kaɗan, bai kamata ace ya barta haka ba, tana buƙatar ƙari, saide kuma lokaci ya ƙure, dan zuwa yanzu yasan wata ƙila tana asibiti, domin karaya uku ya mata a kowani hannu, ga kuma yanda ya daki gefen fuskarta.
Kansa ya sauƙe yana karb’ar file ɗin Maryam daga hannun Dr. Ola, sannan cikin dakiya yace.
“Ka ba mu takardar sallama zuwa gobe, dan bazata ƙara kwana a nan ba”
Da mamaki Dr. Ola yake kallonsa, can kuma sai ya tab’e baki, tunawa da ya yi ashe shima likita ne. Sai kawai ya gyaɗa masa kai.Daga haka ya yi gaba ya bar ƙofar ɗakin.
Saida Tafida ya haɗiye wata busasshiyar iska a maƙogwaron sa, sannan ya murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, tun daga inda yake ya fara jiyo sahibin nasa, wato bugun zuciyarta, saide ba a tsorace yake bugawa ba, ba kuma cikin nishaɗi ba, ba cikin farin ciki ba, haka kuma ba cikin ƙunci ko damuwa ba, yana bugawa ne cikin rauni da gazawa.
Saida ya ɗanyi jimm, yana kallonta a kan gadon, kafin ya iya daurewa kansa ya ƙarasa jikin gadon, a lokacin da itama ta kai dubanta kansa, wuyanta naɗe da bandage ga iskar oxygen da aka saka mata, dan bata iya jan numfashi me kyau, sai kanta da aka naɗe da bandage.
Tana ganinsa ƙwalla ta taru a idonta, kuma a hankali ta silalo, sai yanzu ta shiga tuna yanda ta ji raɗaɗi da azaba bayan matar nan ta take mata wuya da ƙafarta, cike da rashin imani take mitsika mata wuyan nata, kuma har yanzu ji take kamar ma ta karya mata ƙashin wuyan ne.
Tafida na ganin ta fara hawaye, ya yi saurin ake jakar dake hannunsa sannan ya danna wani switch a jiki gadon, gadon ya ɗan ɗago sama daga wurin kanta, ya zama kamar a zaune take, zama ya yi a gefen gadon, yana dubanta cike da tausayawa.
So take ta yi kuka me sauti, amma ta rasa sautin nata, ko yawu bata jin zata iya haɗiyewa, Ita da Allah ne kaɗai suka san yanda take ji, hatta da numfashin ta da ƙyar take iya kamoshi.
Tafida ya riƙo hannayenta ya kai setin bakinsa ya sumbata, bisa ga mamakin Maryam sai ta ga yana hawaye, ta ji zuciyarta ta karye, ashe har akwai abinda zai saka Tafida kuka ?, bata tab’a ɗaukarsa a irin wannan mutanen ba, hawaye yake sosai kuma yana kallonta, itama nata hawayen suka ƙara gudu tana ci gaba da kallonsa, yayin da take jan iska da ƙyar.
“I am so sorry, Miriam, duk abinda ya same ki nine sila, ni naja miki Maryam, kullum bani da addu’a da ta wuce kada Allah yasa na zama sanadiyyar cutuwarki Miriam, amma na makara, ki yafeni Miriam, ki yafeni”
Muryartasa har wani rawa take sbd hawayen da yake, wani abu da ba sabonsa ba, bai cika yin kuka ba koda lokacin da yake tasowa, kome za’a masa zai jure, amma yau akan Miriam ɗinsa ya koma me rauni, ya ji bazai iya jurewa ba, dole ne ya zubar da hawaye, wata ƙila ta ji tausayinsa ta yafe masa.
Duk da Maryam na cikin halin raɗaɗin azaba saida ta ɗago da hannunta ta kai kan fuskarsa tana share masa hawaye da ƙyar, ya kama hannun nata yana sumbata, sannan yace.
“Kina jin zafi ko ?”
Ba za ta iya gyaɗa masa kai ba, bare ta bashi amsa, kuma shima yasan amsar tata, dan haka ya saki hannyenta, ya kai nasa hannyen duka biyu setin wuyanta, sannan ya lumshe idonsa.
Maryam tana ganin yanda tafukan hannunsa ke zama jajawur, kamar garwashi, kuma tana ganin yanda yake ciccije baki, kamar yana zuƙe ciwon jikin nata zuwa nasa jikin.
Kuma a hankali, a hankali raɗaɗin yake raguwa daga wuyanta, taji kamar ana zare mata ciwon.