Skip to content
Part 38 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

TAFIDA POV.

“Eshaan sauƙo daga kan wurin mana”

Muryar Roshni ta faɗi tana duban Ehsaan dake tsaye a kan coffee table, ya saka lap cort ɗin babansa, ga stethoscope ya rataya a wuyansa, har da saka wani glasses, shi a dole ga likita.

“Nahi Maa(No Maa), baki ganni ba ne?, nine likita”

Roshni ta yi dariya tana girgiza kai.

 “Kana so ka zama likita ?”

Ya gyaɗa mata kai.

 “To ka dena ƙin jin magana, kullum da safe idan Maa ta baka madara ka shanye cup ɗin duka, ka riƙa zuwa makaranta, kuma kana yin homeworks ɗinka, banda yawam guje-gije ko hawa sama”

Daga ita har shi suka waiga dan kallon Auwal dake masa wannan bayani, Eshaan ya sauƙo da ga kan coffee table, sannan ya yi wurin Auwal da gudu, ga lap cort ɗin jikinsa sai sharar ƙasa take, sbd yawan da ta masa.

Yana zuwa dab da Auwal ya yi tsalle ya faɗa jikinsa. Auwal ya yi dariya yana ɗago shi.

“Idan na yi haka zan zama likita?”

 “Ɗari bisa ɗari”

Eshaan ya yiwa Auwal peck a kumatu, sannan ya maƙalƙale masa wuya.

“I love you Appa”

Auwal ma ya yi masa peck ɗin a ka.

 “I love you too son”

 “Ni kuma fa ?”

Auwal na dariya ya ƙarasa inda Roshni take, sannan ya haɗesu su duka ya rungume. “I love you all…”

Sai suka yi dariya, wannan sautin dariyar ya shiga maimaita kansa cikin kunnen Tafida.

A hankali ya shiga buɗe idonsa, kafin ya buɗe shi gaba ɗaya, ya bi ɗakin da kallo, yanda ya hargitsa komai na ciki, dama kuma ya saba, hakan tasa baya san cika tarkace a ɗakinsa.

Da ƙyar ya iya miƙewa zaune, Abun mamaki yanzu ake kiran sallar asuba, miƙewa ya yi tsaye, a lokacin kuma ya yi arba da wutar hannunsa na ci.

Ya dunƙule hannun sannan ya buɗe, kasancewar babu curtains a ɗakin shi yasa ya fahimci cewa har yanzu a duhun asuba ake.

Hannayensa biyu duka ya ɗaga, sannan ya shiga meda kayan da suka faɗi ba tare da ya tab’a koda ɗayansu ba.

Kafin ya shiga banɗaki, ya yi wanka ya fito ya sauya kaya, kana ya wuce masallaci. Bai dawo ba sai shida.

Kuma yana dawowa kaitsaye ya wuce ɗakin Maryam, yasan cewa dole ta ji abinda ya faru jiya, wata ƙilama ya hanata bacci, dan haka zai je ya dubata.

Karatun ƙur’ani ne ya fara shiga kunnewansa yana buɗe ƙofar.

Daga can cikin wani rami kuma, wani abu da aka ƙulle a cikin kwalba ya girgiza, baƙin hayaƙin da ke ciki ya shiga yawo a cikin kwalbar.

Kan Tafida ya sara, dan haka ya dafe shi, yana tura ƙofar ɗakin, ji yake kamar ana raba kan nasa gida biyu, kamar guduma aka ɗauka ake buga masa a kan.

Cak ya tsaya yana kallonta, zaune take a kan darduma, bayanta jingine da jikin gado, idonta a lumshe, kamar me jin bacci, yanda muryarta ta ke fita cikin karatun kaɗai zai nuna maka cewar bacci take ji.

Duk da yana cikin wani hali na azaba, amma sai da tausayinta ya kama shi, baiwar Allah yanzu haka bata samu bacci ba.

Yaci gaba da takawa zuwa cikin ɗakin, amma hannunsa riƙe a kansa.

Dif!, ya ji karatun nata ya tsaya, numfashinta ya yi nauyi, alamun dai bacci ta fara.

A lokacin kuma wannan bajin hayaƙin da ke cikin kwalba ya dena motsi, kwalbar ma ta dena jijjiga.

Tsayawar karatun nata ya tsaya tare da sarawar da kansa ke yi. A hankali ya zauna a kusa da ita, kuma har lokacin bata farka ba, kanta ya kama tare da ɗorashi a kan kirjinsa, ya rungumeta a jikinsa tsam.

Cikin bacci Maryam ta ji kamshinsa a hancinta, sai kuma ta ji kamar an riƙeta, hakan yasa a wahalce ta buɗe idonta, ai ko ta yi kyakyawan gani, dan ƙur suka haɗa ido da shi, da ƙwayar idonsa wadda take ja.

Maryam ta razana zata fice daga jikinsa, amma yaƙi ya saketa.

“Ki yi baccin ki kawai ”

“A… abinci zanje na yi, yau ak…akwai aiki…”

“Ki kwanta nace ko ?”

Maryam ta yi shiru, amma kuma baccin ya gudu da ga idonta, kuma bata jin zai dawo, dan bazata iya bacci a haka ba, a cikin hannayensa ? Cabɗijam!!.

UCHENNA POV.

Yana dawowa gidan ya shiga neman Hanam, ɗakinta ya fara zuwa bai ganta ba, dan haka ya shiga ɗakin Arya, yasan cewa baza ta wuce nan ba.

Tsaye ya sameta a jikin baby cradle ɗin Arya, ta bashi baya, be san me take ba.

Da alama ma bata san cewa ya dawo ba, zuciyarta ta cilla cikin kogi tunanin, ji take kamar za’a rabata da Aryaan ne.

Bata ankara ba ta ji an kewaye ƙugunta ta baya, saida ta ɗan ja iska a maƙogwaronta sannan ta gane cewa shi ne.

“Nagode Hanam, ban tab’a tunanin cewa mafarkin da nake zai zama gaskiya ba, ban tab’a tunanin cewa zan shiga studio na yi waƙa ba, a koda yaushe mafarkina a nesa nake hangoshi, can nesa sosai, amma sanadiyyar ki, yau ya zo kusa, na ganshi a kusa”

Hanam ta yi ajiyar zuciya, Tun bayan rasuwar Abba ta yanke cewa za ta yi magana da Falaƙ, a kan fara waƙar Haris ɗin, yana san waƙa, kuma yana da talent ɗin waƙar. Kuma tasan cewa tun da yanzu ba Abba aikin a ƙarƙashin Kamal ba ze iyu ba.

A hankali ta juyo ta kalle shi, ba tare da ta ce masa komai ba.

Ta shiga ƙoƙarin fita daga hannunsa, amma yaƙi ya saketa.

“Waye Gabriel ?”

Tambayar ta doka wani abu me sauti kamar ganga a kan Hanam, duk da tasan cewa zai buƙaci sanin hakan, yana buƙatar sanin waye Gabriel!!.

*Room 330, Presbyterian hospital, New york*

Hanam ce kwance a kan gadon marasa lafiya, gefen fuskarta rufe da bandage, yayinda idanuwanta suka kumbura har bata iya buɗe su da kyau, a hankali siriryar ƙwalla ke zubowa ta gefen idonta.

A jiya kawai rayuwarta ta yi wani irin sauyi, sauyin da ba zai tab’a gogewa ba, a jiyan kawai Gabriel ya ɗan-ɗana mata azabar da tun da uwarta ta kawota duniya bata tab’a shan makamanciyar ta ba, a jiya Gebriel ya haike mata, ya haike mata cikin rashin imani da rashin tausayi.

Ta yi zaton cewa bayan rashin uwa da ta yi shikenan wahalarta ta yanke, ashe ba haka ba ne, ashe akwai wata wahala da azaba dake jiranta a gaba.

Ta tabbatar da yanzu rayuwarta ta gama wargajewa, babu na mijin da zai iya aurenta a haka, kimarta ta gama zubewa a idon kowa.

Ƙofar ɗakince ta buɗe, maƙociyarta Banedita ta shigo, wadda itace ta temaketa ta kawota a aibitin a jiya.

Kuma itace ta sanar da ‘yan sanda, hannuta riƙe da leda ta shigo cikin ɗakin. Cike da tausayawa take kallon Hanam, dan likitan da ya karb’eta jiya yace ba ƙaramin azaba aka bata ba, ta wahala sosai.

“Sannu kinji, sunce zaki iya cin wani abu tashi na baki”

Hanam ta kawar da kanta gefe, alamun bata so, kuma itama Beneditan ta faɗa ne kawai, dan tasan wannan abun akwai ciwo ga ‘ya mace, bayan haka kuma ita harda raunika a jikinta.

Haka Hanam ta yi jinya kusan sati uku a asibitin, amma bata faɗawa Abba ba, kuma yansanda sunyi bincike a kan bayanan da ta basu sunce basu samo wanda ta faɗa ba.

Kuma itama sai ta share komai ta karb’i sauyin da rayuwa ta zo mata da shi, inde har Allah zai ci gaba da ɗora mata ƙaddararo kala-kala ta shirya karb’ar su, kuma tana fatan Allah yasa ta iya jurewa.

Kuma bayan sati ukun ne ta koma aikinta, saide ta rage abubuwa da yawa, ta dena kwalliya, ta dena yawan fara’a da surutu, duk da dama can ba wani sosai take hakan ba, amma na yanzu ya ragu sosai. Kullum idan ka ganta kamar mara kafiya.

Bayan wata biyu ta soma jinya, tana laulayi irin na masu ciki, kuma tun kafin ta je asibiti Benedita ta faɗa mata cewar tana da juna biyu.

Abun ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, amma haka ta je asibiti aka gwadata, sannan aka sanar mata da tabbacin shigar ciki a jikinta.

A ranar ta yi kuka kamar ranta zai fita, amma koda wasa bata ji san ta cire abinda ke cikin ta ba, ta ɗauke shi a matsayin ɗaya da ga cikin ƙaddarorinta na duniya, kuma tasan a ranta cewar Allah zai bata Ikon cinyewa.

Haka ta yi ta renon cikin dake jikinta, kuma ko da second ɗaya, bata tab’a jin sansa cikin ragu a cikin zuciyarta ba. Ita da Benedita suke kula da cikin.

Ga kuma su Camilla suma da suke tausaya mata, duk da cikin dake jikinta baya hanata zuwa aiki. Dan Hanam bata haɗa aiki da komai. Haka kuma duk wannan badaƙalar cikin da take bata tab’a faɗawa Abba komai a kan cikin ba.

Ana haka har ranar haihuwarta tazo, kuma daga ita sai Benedita da Camilla ne kwai a asibitin.

Sannan ko a wurin haihuwar taci baƙar azaba, dan har an afara shirin mata tiyata, Allah ya temaketa ta haifo yaron, kuma cikin ƙoshin lafiya. Amma taci azaba sosai. Dan sai da likitan da ya karb’i haihuwar ya sanar musu da cewa ba lalle ta sake samun wani cikin ba, sbd mahaifarta da ta samu matsala.

Tun da ta ɗora idonta a kan yaron, ta ji duk duniya bata da abun so da ya wuce Abba da shi, ta ji bayan Abba wani ya samu matsugunni a zuciyarta.

A da bata da wani wanda take so sama da Abba, amma a yanzu, ta samu wani, wani wanda ta ji har ƙahon zuciyarta zata iya komai dominsa.

Kuma wani abun mamaki sai yaron ya iyo kamarta gaba ɗaya, abu biyu ya rabata da shi, farin fatar da ya fita da kuma shuɗayen idanuwan da yake dasu.

Ita da Benedita suka ci gaba da kula da jararin da ta raɗawa Muhammad Aryaan, Har zuwa lokacin da aikinta ya ƙare a The House of Sofia couture .

Ta tattara komai ta koma Nigeria, babu abinda ta yi kewa a USA sai Benedita da Camilla, dan sune waɗanda suka rakota har zuwa airport, Benedita har da ƙwallarta.

Ƙalubale na farko da Hanam ta fara samu bayan ta dawo gida shi ne, ‘yan gidansu da suka kira Aryaan da shege. Dama can ba shiri suke da ita ba, kullum cikin faɗa suke, duk da bata kula kowa a cikin su.

Amma a ranar sai da akayi fito na fito ita da su, ta shafawa idonta toka ta tsigesu tas, haɗi da kakkauran warning a kan kada su ƙara kiran ɗanta da shege.

Abba kansa abun ya ɗaure masa kai, yana san ya san wannan wani yaro ne ‘yarsa ke ɗauke da shi tana kirarin itace uwarsa da ubansa, bayan yasan ba ta yi aure ba, kuma bata faɗa masa za ta yi aure ba.

Duk da yana waya sosai da ita sanda tana USA ɗin, amma bata tab’a masa wani batu a kan wani yaro ba.

Dan haka tana da sati ɗaya da dawo nigeria ya kirata babban parlonsa.

“Bannute waye wannan yaron ?”

Hanam ta sunkuya ta kalli kyakyawan jaririn da take ganin fuskarta a kan tasa, sannan ta ɗago ta kalli Abba.

“Ɗana ne Abba”

Abba ya girgiza kansa.

“Maman babanta ni ban miki Aure ba, kuma nasan ba ki yi aure ba, yaya aka yi ki ka samu yaro ?”

Cikin murmushi ta tsara masa komai, ta faɗa masa duk abinda ya faru, kamar labarin baya ƙona mata rai, kamar ba a kanta abun ya faru ba, kuma kamar wadda ta zauce.

Shi kansa Abba sai da yabyi kuka, dan shi yasan irin halin da take ciki a yanzu ma, amma kuma ga wata ƙaddarar Allah ya ƙara ɗoro mata.

“Abba ka dena kuka, nahan ma’anna kayal, yalli sha’atulul ƙadar huwa yalli rah yisir”

(Bamu da zabi Abba, YADDA ƘADDARA TA SO haka zata kansace”

An wuce lokacin da zata zauna ta yi kuka, a baya ne ta sha kulle kanta a ɗaki ta risgi kukan rashin uwa, a baya ne ta sha zubar da hawaye a kan abinda ‘yan uwanta suke mata.

Amma yanzu komai ya sauya, an wuce wannan lokacin da zata zauna tana kuka kamar ƙaramar yarinya, yanzu ta girma, ita uwace, wadda take jin zata iya kula da nauyin ɗanta da Allah ya bata, ji take zata iya kareshi daga duk wani abun ƙi, ji take zata iya sadaukar da komai nata domin ya samu farin ciki.

Dan haka zata ta sadaukar da lokacin ta, ta sadaukar da auren da take shirin yi, ta sadaukar da duk abin da tasan zata iya duka domin Aryaan, ba zata gudu ta bar shi ba, domin ita uwa ce.

Abba ya miƙo mata hannu, alamun ta bashi Arya, Hanam ta yi murmushi tana miƙa masa shi.

“Kamar ke sanda kina ƙarama, amma kuma ke baki da blue eyes, kuma shi ya fiki farar fata”

Kusan a tare su ka yi dariya da Abba, tana kallonsu su duka, Haka Allah ya so su kasance ita da Arya, shi ita ce zata rene shi, yayin da ita kuma Abba ne ya renata.

Sai kuma ta godewa Allah, domin ya mata ni’imar da wasu basu da ita, wasu gaba ɗaya iyayen ma basu da su, tun tasowarta bata rasa komai ba, dawammamen farin ciki ne kawai ta rasa.

Kuma ta dan gana, domin babu wani abu me dawwama a duniya, komai me ƙarewa ne.

“Menene suna sa ?”

“Muhammad, Aryaan”

Abba ya kalli yaron sannan ya kalleta.

“Sunana ?”

Ta gyaɗa masa kai tana murmushi.

“Ba ni da kamar kai Abba”.

<< Yadda Kaddara Ta So 37Yadda Kaddara Ta So 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×