Skip to content
Part 39 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

HANAM & HARIS

Zaune suka a kasan carpet, yayin da Hanam ta jingina da jikin baby cradle ɗin Arya, shiru ɗakin kamar ruwa ya cinye komai.

Shi Uchenna yana mamakin yadda ta iya haɗiye baƙin ciki kala-kala a rayuwarta, amma sam bata nunawa.

Yayin da Hanam ke ƙoƙarin danne famun ciwon da ta yiwa zuciyarta.

“Gebriel shi ne mahaifin Aryaan, kaga nan?”

Ta faɗi tana nuna masa gefen fuskarta, Uchenna ya kalli tabon dake wurin.

“A sanda ya shigo gidan ya buga mun wani ƙarfe a wurin, kalli nan ma”

Ta nuna masa goshinta.

“Da bango ya buga kai na, saida ya dake ni sosai, kafin ya haike min, cikin rashin imani da rashin tausayi”

Uchenna ya rintse idanunsa, yana jin maganganun nata kamar tana watsa masa ruwan zafi ne, yana jin me yasa ɗazu da suka zo be kama Gebriel ɗin ya dake shi ba.

Babu ko ɗison hawaye a idon Hanam, babu komai sai hotunan abinda ya faru da ita ɗayan bayan ɗaya da suke haskawa a ciki.

“Na ci azaba sosai a sanda zan haifi Arya, kuma bayan na haife shi na tabbatar da cewa rayuwata ta sauya, na tabbatar da cewa na samu sauyi, matsayina ya ƙaru na zama uwa, uwa wadda zata zama katanga wurin faɗa da duk wani abun cutarwa ga ɗanta, bayan na sameka kuma sai na ƙara jin duniyata ta cika, a da ina ganin kamar duniyar duhu gareta, babu komai a ciki sai tashin hankali da b’acin rai, ina ganin kamar duniyar b’_an gare uku gareta, wanda ko wanne yake da duhu banda guda ɗaya, kuma wannan b’angaren na farko Abba ne, bayan zuwan Arya sai ɗayan b’angaren ma ya yi haske. Daga baya kuma sai gaka, wanda ka gama cike hasken gaba ɗaya, amma kuma bayan rasa Abba sai ɗayan b’angaren ya yi duhu, zuwan Masarrat da Mom ɗinka sai ya haske min wurin. Na ji ni a cikin duniya me ɗauke da hasken da zai iya haska min ko ina”

A hankali Uchenna ya jata jikinsa ya rungume, yana shafa bayanta.

“Bana cikin Damuwa Harees, damuwata ta ƙare, da yardar Allah”

“Inshaallah”

“Bana san na sake ganin Gabriel a kusa da ɗana”

“Sshhhhh, Arya ɗan mu ne mu duka, ba naki bane ke ɗaya”.

Maganar da Abba ya yi masa a ranar da aka ɗaura aurensa da Hanam ta gifta cikin tunaninsa.

“Harees, Be Hanam’s place of peace. She is tired of pain”

A lokacin bai fahimci komai ba da ga cikin maganar ba, amma yanzu da ya ji komai a kanta sai maganar ta dawo masa, gaskiya Abba ya faɗa, Hanam was tired of pain. A hankali ya furta.

“Allah yaji ƙanka Abba”

Be san cewa Hanam ta ji ba, sai kawai ya ji hannyenta sun ƙara kewaye shi tana faɗin.

“Ameen”.

A wannan daren.

*****

Gabriel ya zauna a kusa da Alice matarsa.

Wurin da suke wani hotel ne da suka kama a lagos, kallon Alice kawai Gabriel yake, wadda ido da hanci suka mata ja, sakamakon kukan da ta yi.

“Kin tabbata Alice wannan ita kaɗaice mafitar mu ?”

Alice ta juyo ta kalleshi.

“Shin kana ga za ta bamu shi ne ?Tun da har ta furta cewa ba ma tasan ganin mu ba bamu yaron nan za ta yi ba, nigerians suna da taurin kai sosai, ina san na zama uwa, amma babu hali, to me zan zauna na yi a duniya Gebriel ?”

Janta ya yi jikinsa ya rungume yana shafa kanta.

“Tunda de har kina so mu kashe kan mu ne za mu yi, amma ba’a nigeri ba, mu bari sai mun koma New york”

A hankali ta gyaɗa masa kai tana jan hanci.

“Ya ya za mu yi? Guba zamu sha ko rataye kanmu za mu yi”

“Mu sha guba kawai”

“Shikenan, sai idan mun koma gida, na ɗaukar miki alƙawarin tare zamu mutu, ba zan tab’a barin ki ke ɗaya ba, raina fansa gareki Alice”.

(Allah mun gode maka da kasa muka zama daga cikin musulmai).

*****

Navi Mumbai International Airport, India

08:00am

ESHAM POV.

Eshaan ne ke turo trolley ɗin kayan su, yayin da Maryam ke biye da shi a baya, yanayinta kawai zaka kalla kasan cewa a gajiye take.

Dan gaba ɗaya jikinta babu wata gab’a da bata mata ciwo, musamman ma ƙafarta, Jiya daddare jirginsu ya taso, dan haka kwanan jirgi su ka yi.

Tafida ya ɗan tsaya sbd wayarsa da ta yi ƙara, ya kai hannu cikin aljihun wandonsa ya zarota. ‘NEHA’ ya gani rubuce a kan screen ɗin.

“Ke ‘yar ƙauye ina ki ka shiga ?”

“Bhai nifa ina india, yaushe zaku ƙaraso”

“Ni na fasa zuwa sai gobe”

“Kya ?!(me ?!)”

Ya ji yadda sautin ta ya fito a razane, ya kunshe dariyar sa yana faɗin.

“Sai an jima”

Ɗif!, ya katse kiran, sannan ya juyo ya kalli Miriam dake tsaye a gefensa.

Sanye take cikin wani maroon chickankari, wanda akayiwa wuyan adon embroidery, wandon da rigar kalar su ɗaya, rigar ta sauƙo mata har ƙasan guwa. Ta yafa mayafin chickankari ɗin a kanta, ta ratayoshi ta kafaɗarta.

Bawai kama ta masa da indians ba, dan bata da kamarsu, amma kayan sun amshi jikinta sosai.

“Ko na goye ki?”

Ta zaro ido tana kallon tarin jama’ar dake wajen terminal ɗin.

“Ke, nan ba nigeria bace, nan ƙasar martaba soyyayace, ba’a wasa da soyyaya a india, hasali ma ita kanta ƙasar soyyaya ce”

Ita de bata ce masa komai ba, sai bin mutanen dake wajen take da kallo, ba zata ce bata tab’a ganin irin su ba, dan ga Tafida nan, shi kaɗai ma ya isa misali, amma ita ko da a mafarki bata tab’a zaton ganin kanta koda a abuja ba ne, bare kuma lagos, daga nan ma sai ta wuto india. Allah ƙadirun ala man ya sha’u.

Duk taxi ɗin da ta zo wucewa sai Maryam ta shiga ɗaga musu hannu alamun su tsaya, amma ko kallonta basa yi.

Dariyar Eshaan ta ni a bayanta, hakan yasa ta juya ta kalle shi.

“’Yan matan Tafida kenan, nan basa taxi basa tsayawa a haka, bari kiga ikon Allah”

Hannunsa ya ɗaga,ya haɗe babban ɗan yatsansa da manuniyarsa, suka bada shape ɗin circle, ya kai ya saka a bakinsa sannan ya hura.

Ya bada sautin fito, kiiii!, ka ke ji taxi har biyu sunci birki. Maryam ta bisu da kallo, Tabbas wannan shine ikon Allah,wato ikon gaske.

Tafida ya sallami ɗaya, sannan aka saka musu kayan su a booth ɗin ɗayar, suka shiga.

Kuma suna shiga Tafida ya janyo Maryam jikinsa, tare da kwantar da kanta a kafaɗarsa.

“Nasan kin gaji, ki kwanta kawai”

Bata ƙara ce masa komai ba, sai ta yi shiru, dan da gasken ne ta gaji, ita bata ƙi a ce ta samu gado ta kwanta ba ma.

Survey NO. 1433, Shiv Mandir Talo St, Chikoli, Mumbai, India

Mutum biyu ne tsaye a filin cricket, ɗayar macace, kuma wadda za’a iya kira da budurwa, ta riƙe ƙaramar ball ɗin cricket, wadda take shirin wurga ta.

Shi kuma ɗaya na miji ne, wanda ba zai wuce 15 yrs ba, shi kuma ya riƙe cricket bat a hannunsa, ya ɗau matsayarsa yana jiran ta cillo ball ɗin.

Daga can gefe kuma wata farar dattijiwa ce sanye cikin Saree fari, tana zaune a kan garden chair, hannunta riƙe da sandar dogaronta.

Daga gefenta kuma wani magidanci ne, yana zaune suna ɗan hira da shi, amma gaba ɗaya rabin hankalinta na kan wasan cricket ɗin da jikokinta ke bugawa.

Budurwar ta cilla ball ɗin, yayin da yaron ya daketa da bat ɗin hannunsa, kwallon ta ta shi sama, kowa ya bita da kallo yana san yaga inda zata tsaya.

Sai dai me ?, cak, suka ga ta tsaya a iska, kuma ko ba’a faɗa ba sun san waye me wannan aikin.

Dan haka gaba ɗaya su huɗun suka juyo suka kalli hanyar shigowa garden ɗin.

Kuma kamar yanda suka zata shine, ya ɗaga hannunsa setin ball ɗin. Matashin yaron ne ya rugo da gudu ya yi kansa yana faɗin.

“Bhaiyya!”

Yana ƙarsawa kusa da shi su ka rungume juna suna dariya, a lokacin kuma ya saki ƙwallon ta faɗo a kan budurwar.

Ta dafe wurin tana sosawa, tare da sakin ‘yar ƙara.

“Kefa soja ce, ai ba kya ji zafi ba”

Cikin yaran hindi ya mata maganar, ta ɗauki bat ɗin da yaron ya jefar, ta yi kansa, sai ko ya fita a guja, itama ta saka gudun tana bin bayansa.

Dattijuwar nan ta miƙe ta na kallonsu, yarintarsu kaf tana dawowa sabuwa a idonta, sanda suna yara kamar haka suke daren gudu a lambun.

Da ƙyar ya iya samu ya ƙaraso wajen dattijiwar, yana zuwa zai rungumeta ta ja baya, haɗi da kawar da kanta.

Sai ya yi murmushi tare da kama kunnuwansa.

“Sorry Daadi, mujh maaf kardo”

(i am so sorry)

Taƙi ko kallonsa, sai ya kalli magidancin dake tsaye a kusa da ita

“Aree Chacha, kaise ho tum ?”

(iyee kawu, to ya kake ?)

Ya yi maganar yayin da suke yin side hug.

“Ina lafiya Eshaan, ya aiki ?”

“Kawu aiki ba daɗi, ka saka baki wannan tsohuwar ta yafe min mana…..”

A dai-dai lokacin wani duka me ƙarfi ya sauƙa a gadon bayansa, ji kake b’ass!, abu na karyewa.

Budurwar ta cillar da sauran bat ɗin da ta rage a hannunta, dan rabin bat ɗin ya karye, amma shi wanda ta bigawan ko a jikinsa, dan ko motsawa be yi ba, ta saba ganin hakan, dan ko ƙarfe zata buga masa sede ya lanƙwashe.

“Daadi pls, ai de na cika alƙawari, kalli sumar dana tara a kaina, kuma ma ai Bikin holi ɗin jibi ne”

“Gaskiya Eshaan baka kyauta ba, kafi shekara rabonka da india, ko bikin Neha ma fa baka zo ba”

“Na sani kawu, amma ka shawo min kan ‘yar tsohuwar nan”

Daadi ta juyo ta kalleshi, sannan ta kai hannu ta mirɗe masa kunne.

“Kai baka ji ko ?”

“Aaahhh, Daadi za ki cire min kunne”

Sakin kunnen nasa ta yi tana wurga masa harara.

“Zonan my boo, kinsan ai ina sanki ko ?”

Ya faɗi yayin da yake rungumeta, Daadi ta yi dariya, Allah ya saka mata tausayin jikokinta, musamman Eshaan da Neha da kuma Gulzar, dan sune marayu a ciki.

“Ke kuma na dawo kanki”

Ya saki Daadi yana kallon Neha, hannunsa ya dunƙule sannan ya buɗe, kyankyanso ya bayyana a tafin hannun nasa, kuma daga haka ya cilla mata jikinta. Neha ta fita da gudu ta koma cikin gidan ta ƙofar kitchen.

“Kai ina matar taka ?, ko banda ita ka zo?”

“Mts, shiiiiii!!”

Ya faɗi yana dafe goshinsa, alamun mantuwa, shaf ya mance da Maryam dake bakin ƙofar garden ɗin.

“Ek minit Daadi”

(one minutes Kaka).

Ya nufi ƙofar Garden ɗin, kuma suma sai a sannan suka lura da ƙofar garden ɗin.

Tun da me taxi ɗin ya sauƙe su a cikin gidan, Eshaan ya saka masu aikin gidan su shiga da jakukunansu ciki, yasan cewa duk yanda akayi war haka suna garden, kuma ya yi sa’a, dan suna garden ɗin.

Da suka ƙaraso bakin garden ɗin sai yace wa Maryam ta jira shi a nan, ta jingina da jikin ƙofar shiga tana kallon irin farin cikin da yake da ‘yan uwansa.

Kamar yanda ya faɗa mata ne, yafi farin ciki idan yana india, dan a nigeria ya cika kame kai, ba shi da surutu sosai, amna kuma a nan ta ga ba haka bane.

Hannunta ya kama bayan da ya ƙaraso kusa da ita, Maryam ta kalleshi a tsorace, zuciyarta na bugawa, yayin da shi kuma yake saurarin sautinta.

Ta kalleshi ta kalli su Daadi, wannan sai a ce basu da kunya ai, be saketa ba haka ya shiga janta har zuwa gaban Daadi, tana tirjewa amma sai da ya kaita.

Daadi ta kalleta na ‘yan sakkani, Maryam ta rasa wace irin gaisuwa zata mata, ita ba wani hindi take ji sosai ba, kawai sai ta yanke shawarar cewa.

“Namaste!”

“Kace tana jin hindi ?, dama akwai indians a nigeria?”

Bisa ga mamakinta sai ta ji tsohuwar ta mata hausa, duk da ba ta fita da kyau, Eshaan ya yi dariya.

“Ba haushiya ce Daadi, bata san cewa kina jin hausa ba shi yasa”

“Maryam ko ?”

A hankali Maryam ta gyaɗa mata kai. Daadi ta rungume ta tare da faɗin.

“Barka da shigowa ahalin Iqbal Khan”

*Da Misalin 05:04pm*

Maryam ta tako da ga kan stairs a hankali, ita tun ɗazu ta je ta kwanta ta ke hutawa, sallah ce kawai ke tashin ta, kuma har abinci an aiko mata, abincin da kwata-kwata ta kasa cinsa, dan ita bata cika cin baƙon abinci ba, cikinta baya san baƙon abu.

Ta ɗan tsaya da tafiyar, tana kallon mutanen dake falo, Daadi ce da kawu Irfan, sai xan kawu Irfan ɗin da a ɗazu ya ce mata sunan Atif, amma kuma akwai karin wasu mata biyu da bata samu ta gansu ɗazu ba, sai kuma Eshaan, wanda rabonta da shi tun zuwansu.

Wadda ta saba gani a hoton nan ce ta taso harda gudunta ta rungume ta.

“Oyoyo Yayata!”

Da ga muryarta Maryam ta fahimci cewa Neha ce, ita sai ta yi murmushi a sanda Neha ɗin ke sakinta.

Murmushin da Neha ɗin ke yi ne ya ƙara bayyana mata kamarta da Eshaan, amma kuma duk da haka Eshaan ɗin ya fita kyau, hasken fata kawai ta fishi, a yanda ta lura ma kowa na gidan ya fishi fari, ita da take ganin ya fita fari sosai, ashe shi ma ‘yan uwansa sun fishi fari.

Neha ta ja hannunta zuwa cikin falon, inda Maryam ta ƙara gaida su Daadi. Maryam Kawai binsu take da kallo musamman Neha, babu abinda ke bata mamaki irin yawan gashin Neha ɗin.

“Bhabi (sirikata) wannan itace Anti Saffah, matar kawu Irfan ce, kuma itace babar Atif”

Maryam ta gaishe da matar da hausa, amma sai ta amsa mata da turanci.

“Tana jin hausa, amma bata iya mayarwa”

Maryam ta gyaɗa kanta tana ci gaba da kallonsu, ashe Tafida so yake ya mayar da ita kalar ‘yan ƙasarsu, wata ƙila shi ya ga cewar hakan zata iyu, amma ita a ba ta ga iyuwar hakan ba, dan babu yanda za’ayi ta zama kamar su, sai dai ta kwatanta.

“Ke!, kin isheta da surutu, wai ni ina mijinki ne ?, me yasa ya barki ki ka taho ?”

“Kai kuma ka fita idona Bhai, da de kafin ka zo ina kewarka, amma yanzu duk ka isheni Allah”

Haka Neha da Eshaan suka ci gaba da faɗa, Su Daadi kuma suna ta hira, inda suke ɗan sakota a ciki jifa-jifa.

<< Yadda Kaddara Ta So 38Yadda Kaddara Ta So 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×