Skip to content
Part 40 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

*****

HARIS POV.

“Da da na tsaya a gaban microphone $in, sai na ji gaba na yana faɗuwa, na ji kamar bazan iya ba, dana kalli yanda Falaƙ da Djn nata suke kallo na sai na ji na ƙara tsorata, na sare gaba ɗaya. Amma a hankali dana rufe idona, sai na fsra jin ina rera waƙar haɗe da sautin kiɗan dake tashi”

Cewar Haris, yayin da suke zaune a falon gidansu, Hanam ce kwance a jikinsa, shi kuma yana shafa kanta haɗi da bata labari.

Wayar Hanam ɗince ta yi ringing hakan yasa ta ta shi daga jikin nasa ta miƙa hannunta ɗauko ‘Y Kamal’.

Ɗaga kiran ta yi sannan ta kai kunnenta.

“Hanam gaskiya baki kyauta ba, ai na yi tunanin bayan rasuwar Abba komai zai wuce, mu haɗa kanmu waje ɗaya, mu manta da baya mu rungumi sabuwar rayuwa, ashe ke ba haka ki ka ɗauka ba!”

Hanam ta sunkuyar da kanta ƙasa, dan yanzu ji take kamar Abba ne ke mata faɗa, dan an riga an bashi matsayin Abba a gidan, yanzu haka shirye-shiryen bikinsa suke.

Kums tasan faɗan ba a kan komai bane face Haris da ya aje aiki a kamfanin Abba, kuma ita A ganinta hakan yafi mata daɗi, dan ko ba komai mijinta zai fita daga cikin danginta, ita bata san guntsiri tsoma, a zo ana ta kace nace a kan dukiya.

“Ka yi haƙuri Yaya, ba wai dan baku isa ba ne yasa ya bar aiki, burinsa ne ya cika, ya samu aikin da ya fi wannan shi yasa”

“Nide duk da haka banji daɗi ba wallahi, amma Allah ya sanya da alkairi”

Daga haka kuma suka ɗan tab’a hira a kan tsare-tsare bikin nasa kafin suka yi sallama.

“Kamal ba?”

Ta gyaɗa masa kai tana ƙara kwanciya a jikinsa.

“Yaushe za’a yi recording ɗin vedion?”

“Inaga nan da jibi za’a fara”

“Kunyi magana da Falaƙ ɗin ?”

“Eh”

A yanzu haka waƙar da Haris ɗin suka yi shi da falaƙ ita ce ke trending a ko wani social media, duk da audio ce ba vedio ba.

Wakar ta ɗaukaka sosai, sbd record label ɗin Falaq ɗin shaharrare ne, dan tana da ɗaukaka sosai. Duk da ma tafi ƙamari a nollywood, kuma shima ba waƙar hausa suka yi ba.

“Hairs, zaka iya tunawa a wattanin da suja wuce, a parking lot ɗin wani shopping mall ka temaki wata mata me yaro?”

Ta tambaya tana kallonsa, sai ta ga ya ɗagota daga jikinsa, yana mata kaallon mamaki.

“Wai kece ?”

Ta gyaɗa masa kai tana kwanciya a jiki nasa.

“Ni ce, a time ɗin ai Ya Kamal ne yasa a sato Arya”

Sai ta ji yana dariya, ta ɗago ta kalle shi.

“Miye na dariyar ?”

“Kawai na tuno yanda kike ta kuka kin ihu’Help!, help!, wani zai sace min jaririna’”

Ya yi maganar yana kwatanta muryarta, Hanam ta ɗaka masa duka a kafaɗa tana turo baki.

“Ni wallahi ban yi ihu ba, kuma ko kuma banyi ba”

Sai ya riƙeda da kyau a jikinsa.

“Wasa bake miki ai, nasan ke jaruma ce, me zuciyar ƙarfe”

Ta yi murmushin jib daɗi, tana gyara zamanta, yayinda shi kuma ya ci gaba da bata labarin da ya fara.

MARYAM POV.

Taye take a ɗakin da aka basu, wanda Eshaan ya faɗa mata cewar ɗakinsa ne tun yana gidan.

Kayan sakawarsu take jerawa a cikin wardrobe, Allah ne kaɗai yasan kalar yunwar da ta ke ji, dan har yanzu ita ta kasa cin abincin su.

Sai yatsina fuska ta ke yayin da cikinta ke ƙullewa. Hannunta ya aje riga ta ƙarshe, kafin ta rufe ƙofar wardrobe ɗin.

Ƙofar ɗakin a ka turo, hakan yasa ta klli ƙofar.

Eshaan ya shigo yana kallon Maryam, wadda itama shi take kallo.

“Me ki ke ne ?”

“Kaya na saka a loka”

Ta bashi amsa a sanda take zama a bakin gado, idon Eshaan ya kai kan abincin dake aje a kan coffee table.

“Wai baki ci abinci ba Miriam ?”

Ta yi shiru bata ce masa komai ba.

“Ba zaki iya ci bane ?”

A hankali ta gyaɗa masa kai. Shima sai ya gyaɗa nasa kan, sannan ya ɗauke abinci ya fita da shi.

Har bacci ya soma ɗaukar Maryam bai dawo ba, tana gyangyaɗi ta ji an turo ƙofa, hakan yasa ta buɗe idonta.

“Gashi noodles ce, ai zaki iya ci ?”

Ta gyaɗa masa kai tana karb’ar plate ɗin hannunsa.

“Nagode”

Shima kuma yana batan, ya yi jikin wardrobe yana tambayarta inda ta aje masa kayansa, tana cin abincin abincin ta bashi amsa.

Sweat trouser da T-shirt ya ɗauka, sannan ya shiga bathroom.

Sanda ya fito Maryam har ta gama cin abincin ta aje plate ɗin a kan coffee table.

Maryam ta bi shi da kallo, sumar kansa a jiƙe take, kuma duka ta barbaje a kan goshinsa, daga baya kuma a kan wuyansa.

Ta yi saurin kauda idonta a sanda ya juyo, sai kawai ta waske da cewa.

“A ina zan kwanta ?”

Ya ɗanyi jim, yana kallonta, hijabine a jikinta kamar yanda ta saba.

“Ga gado nan”

Sai ta kalli gadon sannan ta kalle shi.

“Kai kuma fa a ina zaka kwanta ?”

“A gadon mana ”

Ya amsa mata, yana taje sumarsa.

Maryam ta zoro ido, yayin da gabanta ya shiga bugu, ai ta yi tuanin cewa tsoronta ya barta, bata san cewa har yanzu yana tare da ita ba, wai me ?, a gado ɗaya zasu kwanta ?.

Juyowa ya yi ya ƙaraso jikin gadon yana sauraron bugun zuciyarta. Dariya ta so ta ba shi yanda take a tsorace.

“Ki kwanta mana, ko sai na kwantar da ke…”

Ba shiri Maryam ta kwanta a kan gadon, tare da juya masa baya, ta naɗe waje guda kamar curin nakiya.

Yanzu kam murmushi ya yi.Ya koma jikin wardrobe ɗin ya ɗauko chargers, ya dawo ya saka keypad ɗinsa a chargy, sannan shima ya kwanta a ɗayan bangaren.

Maryam tana jin gadon ya yi motsi ta ƙara ƙanƙamewa waje guda, zuciyarta kamar zata fito da ga ƙirjinta.

Kuma hakan be ishi Tafida ya gama da ita ba, saida ya saka hannayensa duka biyu, ya juyo da ita ta fuskanshi, sannan ya janyota jikinsa sosai.

Maryam ta ji komai ya tsaya mata cak, duniyar ma kamar bata juyawa, wata ƙila inner earth core ɗin ne ya samu matsala, abinda take ji ma a halin yanzu earth ɗin ba zata iya ɗauka ba, tana buƙatar ƙarin mars, wata ƙila ma sai dai Jupiter.

Eshaan ya saki murmushi yana jin yanda zuciyarta tata ke bugawa kamar a kunnensa.

“Miriam mu yi hira”

“Ummm ?”

“Nace mu yi hira, muyi hirar yanda bikin holi zai kasance”

Bakin Maryam ya mutu murus, ba zata iya cewa komai ba, dan a yanayin da take ciki, numfashinta ma da ƙyar ya ke fita.

Eshaan ya ƙara matseta a jikinsa

“Kin yi shiru cutie”

Yanxun ma bata iya cewa komai ba.

“Ok to ki yi bacci, nasan kin gaji”

Ya yi mata peck a kai, sannan ya ƙara gyara ruƙon da ya yi mata, ya sunkuyo da kansa kaɗan, yana kallon idonta ta cikin hasken ɗakin da bai kashe ba.

“Can i kiss you ?”

Maryam bata san sanda ta sunkuyar da kanta ƙasa ba, sannan ta ƙara shigar da kanta kirjinsa.

Ya yi dariya har jikinsu na jijjiga a tare.

“Yanzu baza’a ban ɗani ba?, guda ɗaya fa zan yi”

Bata ɗago ba sai ma hannunta da ta saka ta maƙalƙale shi.

Ya kuma yin dariya, dama hakan yake so. Yanzu da cewa ya yi ta riƙe shi haka bazata iya ba, amma da ya mata haka ai gashi ta yi.

Hannunsa ya ɗaga ya yi nuna da switch sannan ya motsa hannunsa, hasken ya ɗauke, ɗakin ya yi duhu.

Wanda ya ƙara tsorata Maryam ta maƙalƙale Tafida jikinta na ƙara yin rawa, tsabar tsoro bata san sanda tace.

“Sundar bana san duhu, tsoro nake ji”

Tafida ya tsira mata ido duk da babu wani haske sosai a ɗakin ss sanda yake shigowa ta taga, shi kam yanzu mamakinta ya fara kama shi, shi bata tsoronsa duk irin halin da zai shiga, amma kuma tana tsoron abubuwa da dama, bacin shi ne ya kamata ace ya zama abin tsoronta. Wato shi yasa kullum yake ganin wutar ɗakinta a kunne da daddare.

A hankali ya lalubo kunnenta sannan ya ɗora a hannunsa akanta, yayin da ɗayan hannun nasa ke sakale a ƙugunta.

“Ssshhhhh, kada ki ji tsoro ina nan tare da ke, kin ji ?”

Ta gyaɗa masa kai, kuma ta ji ɗin, tama ji abinda yafi hakan, dan yanda ya mata maganar cikin raɗa yasa ta dawo cikin hayyacinta ta gano abinda take shirin yi.

Eshaan ya cigaba da shafa kanta kamar wata ƙaramar yarinya.

“To ka kunna hasken”

“Ni bana bacci a cikin haske, ki kwantar da hankalin ki fa, ina nan, babu abinda zai sameki”

Yanzunma kanta ta gyaɗa masa, peck ya kuma mata a ka, sannan ya furta abinda bai tab’a faɗa mata ba.

“I love you Miriam, i love you”

Maryam ta ji zuciyarta ta narke nan take, kamar yanda butter ke narkewa a cikin pan, kamar ba a kan gadon take a kwance ba, kamar tana kwance a kan wani gajimare me laushi ne, taji wani sa shi na zuciyarta ya rufta.

Tunda take da shi bai tab’a faɗa mata yana santa ba sai yau, yana faɗa mata amma ba a irin wannan sigar ba, sai dai yace he is nust about her, ko she complete him, amma bai tab’a furta mata haka kai tsaye ba.

Maryam ta ƙara riƙe shi, tana jin kamar itama tace masa tana sansa, tana san fiye ma da yanda shi yake santa wata ƙila.

Eshaan be rintsa ba saida ya battara da Maryam ta yi bacci, sannan ya kuma Pecking kanta, ya dawo kan lips ɗinta ya yi pecking, sannan shima ya rufe idonsa. Yana rayawa ransa cewa ko da shuɗin ruhi ne ke jikinsa bai isa ya tashi yau ba, dan ba zai bari ya lalata masa wannan moment ɗin ba, for the first time yana kwance gado ɗaya da Miriam.

Washe gari

Da 08:00pm

Eshan ya sauƙo daga kan stairs, cikin wannan takun nasa na aji da ƙasaita, sanye yake da farin chinos trouser, da baƙar printed shirt, sai denim jacket baƙa da ya ɗora a samman T-shirt ɗin.

Ya tsaya yana kallon mutanen dake falon, Daadi da neha ne suke magana da masu decorating gida idan anaa biki ko shagali. Sun zube musu hotuna kala-kala, suna zab’ar irin wanda suke so a musu.

Yayin da Maryam ke zaune a kan kujera, wayarta riƙe a hanunta tana dannawa. Anti Saffah ce zaune a gefenta, ita kuma tana waya.

Daadi ce ta lura da shi, ta juyo ta kalleshi da kyau.

“Ina zuwa ?”

Ta tambaya cikin yaren hindi, Eshaan ya kai hannu ya tab’a sumar kansa.

“Aski zanje sumar nan ta min yawa, kuma zanje na haɗu da Arjit ta can”

“In zo muje ?”

Cewar Neha, Eshaan ya wurga mata harara.

“Inje ina da ke ?, da matata zan tafi”

Sai a lokacin Maryam ta ɗago da kanta ta kallesu, dama tun da ta tashi take jin zaman ɗakin babu daɗi, Neha ce ta zo ta kirata a kan ta zo zasu ci abinci.

Kuma ko da suka zo cin abinci yau ta iya cin abincin nasu, dan tikka masala ce da plate bread, haka ta ɗan ci kaɗan. kuma bayan sun ci abinci shine suka dawo falo suka zauna, har waɗanan mutanen suka zo.

Wayarta ta ɗauka ta shiga buɗe comments, kuma taga duk magana ce akan me yasa jiya da yau bata saki recipe ba.

“Eh ya kamata kuje, kaga sai ka kaita ta zaga garin namu”

“Yauwwa Daadi zanje na duba ƙanin nan nawa a asibiti”

“To sai kun dawo….. Maryam ki tashi ku je”

Su je ?, ina za su je ?, Bata de ce komai ba sai ta miƙe, mayafinta yafe a kanta.

“Ba dan halinki ba zo muje”

Neha ta miƙe tana faɗin.

“Ai ko baka ce na zo ba zan zo”

Mayafinta ta yafa a kanta, sannan suka fita a tare.

Daadi ta kalle su tana murmushi, a lokacin kawu Irfan ya sauƙo daga sama, fitar su Eshaan ɗin kawai yaga.

“Waɗanan ƙafar yawon ina zasu je ?”

“Zaga gari za su je”

“Maa yaron nan ya sauya sosai”

Ya yi maganar yana zama a gefen ta.

“Ya sauya sosai, gashi har ƙiba ya yi, kuma ya faɗa min abun nasa baya tashi sosai, saide mu godewa Allah”

“Hakane kam”

“Ka yi waya da yayan naka ne?”

Tana nufin Imran, mahaifin Neha, kawu Irfan ya gyaɗa mata kai.

“Eh na faɗa masa, yace ba zai samu zuwa ba, amma Mahima zata zo(Matar Imran ɗin da ya aura bayan rasuwar mahaifiyar su Neha)”

“Ta yi zamanta bama buƙata”

Kawu Irfan ya yi dariya, yasan me yasa tace haka, sam Daadi bata san Mahima, sbd itama bata nunawa Neha da ƙanwarta Gulzar kulawa.

MARYAM POV.

Suna fita daga gidan Taxi suka hau, Eshaan da Neha ne suka ce yawo a ƙafa yafi daɗi.

Wani babban wajen gyaran gashi suka fara zuwa, Eshaan ya shiga b’angaren maza, yayin da Neha da Maryam suka yi b’angaren mata.

Irin gyaran kan da akayiwa Maryam ba kallarsa aka mata a lagos ba, dan na yau yafi kyau, gashinta ya ƙara miƙewa, yayi laushi sai sheƙi yake, kuma Neha ta sa a mata kala a gashin nata, daga ƙasa aka saka mata maroon color.

Yayin da ita Neha ɗin aka saka mata purple color.

Bayan an gama musu sun fito suna ‘yar hira, suka iske Eshaan tsaye a reception yana waya, kansa sanye da hular sanyi, wadda a samanta aka rubuta ‘ESHAAN’.

“Kiga wai fa duk dan kada muga kalar askin da aka masa, shi yasa ya saka hular”

Neha ta faɗa mata murya can ƙasa, sai suka yi dariya a tare.

“Kun gama ?”

“Eh mun gama muje”

<< Yadda Kaddara Ta So 39Yadda Kaddara Ta So 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×