Skip to content
Part 50 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

A hankali ƙurar da ta turniƙe wurin take bajewa, siffar Tafida ta bayyana a gabansu, tsaye yake ƙyam, ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja.

“Koda yaushe gargaɗinku nake a kan zuwan wannan ranar, amma babu wanda ya kula a cikin ku, yau ce ranar sakamako, za ku girbi abinda kuka shuka”.

Muryar Kundali ta karaɗe wurin, a sanda take sauƙowa ƙasa.

Maryam na ɗora idonta a kan Tafida ta miƙe da gudu ta yi inda yake, tana isa kusa da shi suka rungume juna, ƙanƙameshi ta yi da ƙarfi tana sakin kuka, shima ya ƙanƙameta a jikinsa yana shafa kanta, shi ba zaice ya san yanda akayi ba, amma yana wannan maganar, bau ƙara gane kansa ba sai yanzu da ya ganshi a wannan duniyar.

“Ya isa…”

Ta sake shi tana kamo fuskarsa a raunane, hawaye ya shiga share mata ya na girgiza mata kai.

“Ina nan tare da ke, bazan bari wani abu ya sameki ba Miriam…”

Sautin dariyar Subhu da ta karaɗe wurince tasa ya yi shiru, ya tura Maryam bayansa yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

Fuskar Subhu ɗin kawai ya gane, dan shine ke shigo masa a mafarki, sai kuma wannan wutar da ke ci a gaban Subhu ɗin, domin irinta ce sak take ci a hannunsa a duk sanda baƙin tuhinsa zai tashi. Har zuwa lokacin Subhu na ƙya-ƙyata dariyarmugunta hara riƙe ciki.

“Zaka kare ta……”

Ya kwatanta yana kwaikwayar muryar Tafidan, sannan ya ƙara bushewa da dariya.

“Kai ne wanda zaka kasheta da kanka yaro”

Maryam ta ƙara riƙe rigar Tafida ta baya gam, tana kallon Subhu ta ƙasan kafaɗun Tafidan.

“Waye kai?!, kuma me kake nema?!”

“Rayuwarka nake so, taka dama ta duk wanda kake so, yanzu ba kai zan kashe ba, matar ka zansa ka fara kashewa”

Cikin ruɗu Tafida ya ɗan jiyo ya kalli Maryam.

“Eshaan shine ya zama sanadiyyar mutuwar Maanka……”

Ta shiga bashi labarin da ya bata wanda shi sam ma be sani ba.

Cike da masifa bala’i da kata’i ya juya ya kalli Subhu, kuma tun kafin ya yi wani yun ƙuri Subhu ya shiga karanto wasu ɗalasuman tsafinsa yana watsa jan gari a cikin wuta.

“….Swastikam,namonamaham….fabrishka … fabrakam…oumm jeje bahim, oum nambakar…..”

Tafida ya ƙame ƙam, kafin duhu ya mamaye jiniyon ganinsa, kamar an kunna inji haka ya juya yakalli Maryam dake tsaye a bayansa.

Maryam ta zabura tana ja da baya, ido waje take kallon Tafidan da ya nufota, suna kaiwa ƙarshen bango ya damƙi wuyanta tare da ɗagata sama. Maryam ta shiga kakari tana kallon jajayen idanuwansa, magana ma ta kasa se bibbige hannunsa da take.

Da Kundali ta ga abun ba na ƙare ba ne, sai ta ɗuko wani botikin ƙarfe me ɗauke da ruwa, ta b’ace b’at, sannan ta zo ta tsaya a kan wutar tsafin gaban Subhu. Ta gwammace mijinta ya mutu, ta gwammace ɗanta ya mutu, dama ita tata ra ƙare, amma ko ba komai ya kamata a ce waɗanan masoyan sun samu rayuwar farin ciki, ba haka ta so ɗanta ya kasance ba, sai de ta yarda da ƙaddara, ta kuma san yanda ƙaddara ke sauya abubuwa da dama, ta so a ce Subhu ya yi karatu me zurfi, ta so ace ya zama wani abun a rayuwarsa, sam bata so a ce ya taso a matsayin boka ba, bata san sana’ar mahaifinsa, amma babu yanda ta iya, haka ƘADDARA TA SO.

Ba tare da wani tunani ba ta ɗaga bukitin sama ta juye ruwan ciki tas a kan wutar.

Subhu ya ga ruwa na zubowa da ga sama yana kashe wutar da ya kunna shekaru talatin da ‘yan ka baya, wutar da ya sha zama ya na gadinta, wutar da ya yiwa alƙawari da ba ze yi wanka ba tsawon rayuwarsa, wutar da yake hana idonsa bacci domin kula da ita, yau itace ta mutu murus a kan idonsa.

Wata razannaniyar ƙara ya saki yana miƙewa. Fitar ƙarar tasa ta yi dai-dai da faɗowar Maryam ƙasa, sbd wuyanta da Tafida ya saki.

A hankali tunaninsa ya shiga dawowa cikin kansa, duk irin abinda ya yi wa mutane sanda baƙin rubin nan ya shiga jikinsa ya dawo masa.

“Kin cece shi yanzu, amma fa ki sani Kundali bazan barshi ba!”

Cewar Subhu yana kallon sama, duk da baya ganin Kundali ɗin amma yasan cewa tana jinsa, kuma itace ma ta kashe wutar.

Sauƙowa ya yi da ga kan kujerasa, ya nufo inda Tafida ke tsaye ya dafe kansa, Manikandan ne ya riƙo hannunsa.

“Kada kaje yaro, komai ya ƙare, zaka iya jawa kanka matsala ”

Subhur manyan ya kwace hannunsa daga riƙon da Manikandan ya masa.

“Ba zan haƙura ba, sai na ɗau fansa ta”

Yana faɗin hakan ya juya ya ɗaga sandarsa a setin Tafida, nan take Tafida ya tashi sama, ƙafafuwansa suka rabu da ƙasa, yayin da wani baƙin hayaƙi ya mamaye shi.

Da ƙyar Maryam ta iya miƙewa zaune, hannunta dafe da wuyanta, se faman tari take, idanuwanta sun ƙwalalo waje. Bango ta daddafa sannan ta miƙe.

“Eshaan ka kira sunan Allah!”

Da ƙyar Muryar tata ke fita, dan Allah ne kaɗai yasan irin dauriyar da ta yi wurin furatata, sama take kallo inda gangar jikin Tafida ke yawo a iska.

“Ka kira sunan Allah Eshaan!”

Wannan karon maganar tata da ɗan ƙarfi ta fito, amma babu ma alamun Tafin ya jita, sbd wata ƙara da ya saki.

“Ka kira suna abin bautarka yaro!”

Muryar Kundali ta ta ya Maryam wurin faɗin hakan, kuma har yanzu bata bayyana ba, tana da ga sama tana kallon abinda ke faruwa.

“Ka kira sunan Allah Eshaan”

“Yaro ka kira sunan abun abun bautarka”

Kusan a tare suka furta hakan, wasu hawaye masu ɗumi na sauƙowa daga idon Maryam.

“Ka furta sunan Allah Eshaan,nasan kana ji na, Allah shi kaɗai zai iya cetonka”

“La’il…”

Bakinsa ya rufe, sbd yanda Subhu ya ƙara ƙarfin tsafin da yake aika masa.

Amma Tafida be daddara ba, ya ƙara furta.

“Lahau…”

Muryar tasa ta fito dai-dai da kawowar hasken baƙin zaren da ke ɗaure a ƙafarsa ta dama, yana yin shiru kuma sai zaren ya ƙara komawa baƙi.

“Kada ka saduda, say it again!!”

A dai-dai lokacin a cikin kansa tunanin rayuwarsa ta baya ga shiga dawowa masa.

Shine zaune a kan kujera, baƙin zaren da Roshni ta saba ɗaura masa riƙe a hannunsa.

“Kai Eshaan, ba ka jin magana ko?!!”

Muryar Roshni ta faɗi tana zama kusa da shi, tare da karb’ar baƙin zaren hannunsa. Ta ɗago ƙafarsa ta dama sanna ta shiga ɗaura masa zaren.

“Kana ji na ko?!

Kada ka sake cire zaran nan”.

Ta saki ƙafar tasa tana shafa sumar kansa.

“Maa, me yasa kowa yake saka baƙin zare a ƙafar dama?”

Roshni ta janyo shi jikinta.

“Kowa ma a india yana ɗaura baƙin zare a ƙafarsa ta dama, ‘yan addinin hindu sun ce kariyace da ga abun bautarsu, mu kuma musulmai, muna sakawa ne sbd kariya, domin addi’o’i da ayoyi ne a jiki, kamar yanda ayatul kursi ke bada kariya ga gida muma haka baƙin zaren ke bamu kariya, sbd haka kada ka ƙara cirewa kaji ?”

Ya gyaɗa mata kai. Roshni ta kai hannunta tana tura sumar kansa baya.

“Yeh mera bacca hai!(That’s my boy!)”

Ya yi dariya yana kwanciya a jikinta.

_“Tashi kaje ka yi wasa, maza,maza,maza!, hhhhhhhh”_. Ta ƙarashe tana masa cakulkuli.

“Hhhhhh, Maa, Chor mujeh, (Ki bar ni)hhhhhh!”.

*****

Shi da Auwal ne tsaye a ɗakin wani mara lafiya, kullum idan Auwal ɗin ya dawo gida se ya bashi labarin wani yato da suka karb’a a asibitinsu.

Auwal ɗin yace masa yaro ne ƙarami, ya gamu da ciwon Cancer, shi ne yau Auwal ɗin ya ɗauko shi yace su zo su duba yaron.

Hannun Eshaan ɗi sanye cikin na Auwal, yana kallon yaron cike da tausyawa.

“Appa yana jin ciwo ko?”

Auwal ya sunkuyo da kansa ya kalle shi.

“Sosai ma kuwa”

“Amma ai ze warke ko?”

Inshaallah

“Idan ma be warke ba idan na zama likita zan masa magani”

Auwal ya sunkuya ya ɗauke shi a hannunsa, suka ci gaba da kallon yaron.

“Na sani My Boy, na san cewa idan ka girma zaka temaki kowa, ka saka kowa farin ciki”.

Shine tsaye a gaban teburi me ɗauke da cake, wanda aka rubuta ‘HAPPY BIRTHDAY ESHAAN’, duka danginsa na india dana nigeria sune tsaye a bayansa suna taya shi murna.

Shi da Neha ne suke guje-guje a lambun gidan Daadi. Yayin da shi ke riƙe da ball, Neha ɗib kuma na binsa da gudu tana faɗin.

“Bhai ka bani, ka bani mana!”

Shi kuma ya ci gaba da gudu yana dariya.

Shine zaune a gaban Me martaba da Fulani Kahdija, Chiroma, Turaki da Mairama, ranar da aka ce masa Maansa da Appansa sun rasu, a lokacin da Fulani tace.

“Ni zan kula da shi, dan Allah a bar min shi…”

Shi da abokansa na jami’a ne suka buga wasan cricet a filin criket na jami’ar su.

Yayin da shi ya daki ball ɗin, ta tashi sama, kuma ta tsallke layin da ake buƙata.

Abokan nasa suka iyo kansa da gudu suna kiran sunansa.

Shine tsaye a cikin ɗaliban da suka yi graduation, sanye yake da acadamic gown, hannunsa riƙe da certificate ɗinsa.

Shine yake gaisawa da wani babban likita, a ranar da aka karrammashi sakamakon bajinta da ya nuna a aikinsa na likita.

Shi da Muktar ne suke zaune a chikin wani restaurant suna hira har da dariya.

Shine durƙushe a gaban su Me martaba ranar da suka faɗa masa cewar sun ɗaura masa aure da Maryam.

Shi da Maryam ne tsaye a gaban indian gate, yana ta mata bayani a kan tarihin ƙofar, sai ya lura da kamar hankalinta ba ya kansa, dan yaka ya tab’a ta.

“Miriam!”

“Hmm!”

“Lafiya?”

Sai ta girgiza masa kai, hannunta ya kama, sannan ya motsa kunnensa yana sauraron bugun zuciyarta, Maryam ta kalli hannunsa sannan ta kalli nata, ta ɗago ta kalleshi.

“Ina tare da ke, komai zai yi dai-dai…”

*****

“Ka faɗi sunan Allah”

Muryarta ta farkar da shi, ba shiri ya buɗe idonsa.

“La haula wala ƙuwata illah billahil aliyul azim!, La’ila ha’illa huwa, wahadahu la sharika lahu, hasbinnalahu la’ilaha’illalah!”

Wani abu sabo, wani abu da ya manta rabonsa da ya furta.

Fitar muryar ta sa ta fito tare da bajewar baƙin hayaƙin da ya mamaye shi, baƙin zaren ƙafarsa ya shiga kawo haske, wani irin farin haske da ya mamaye gaba ɗayan kogon.

Hasken da ya yi tafiya ya isa zuwa ga Manikandan da Subhurmanyam ya ɗaga su sama.

*****

A hankali Maryam ta shiga ƙifƙifta idonta. Kafin ta buɗe shi gaba ɗaya abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata daki-daki.

Kafin ta bi wurin da take da kallo, cikin ɗakinta ne, dai-dai inda Subhu ya ɗauketa, kamar mafarki take, kamar idonta ta ƙifta sannan ta buɗe, haka take ganin faruwar komai.

Kuma kamar yanzu ta shiga ban ɗaki ta fito. Sai dai raɗaɗin da wuyanta yake mata da wanda goshinta ke mata ya tabbatar mata da gaske ne, duk abinda ya faru gaske ne.

A firgice ta miƙe zaune, dubanta ya kai kan Eshaan dake yashe a gefenta, kamar ma ba ya numfashi, kamar ba shi da rai!!

*****

“Baban Ilham dan Allah ka temaka mana, Esh…Eshaan ne ba shi da lafiya, ka kira emergencyn Alaro pls”

Muryar Maryam ta faɗa a sanda Ƙofar gidan su Ilham ta buɗe, Baban Ilham ya bayyana a gabanta.

Ta tashi Eshaan amma ko motsi baya yi, hatta da numfashinsa ma babu. Hakan yasa ta fito da ga gidan, kanta ko ɗankwali babu.

“Ki nutsu Maryam, ina Eshaan ɗin yake ?”

Ta kasa magana sbd kuka, ta fita hayyacinta baki ɗaya, ta kasa banbance baƙi da fari, ta gaza gane meke shirin faruwa da su, wace iriyar ƙaddara ce haka?. Side ɗin gidan kawai ta nuna masa da hannu.

“Maman Ilham, ki kula da ita, bari naje na duba Eshaan ɗin”

Maman Ilham da ke tsaye a bayansa ta gyaɗa masa kai, a lokacin dare ya yi.

Baban Ilham zai fita Maryan ta bi bayansa da gudu. Maman Ilham na riƙita sai de ina, hankalinta ya yi gaba.

A kan idonta a ka fita da Eshaan ɗin a ambulance, sannan ita ma aka wuce asibitin alaro ɗin da ita, dan goshinta da ke zubar jini har zuwa lokacin.

<< Yadda Kaddara Ta So 49Yadda Kaddara Ta So 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×