Alhaji Mujitafa ya ce" uhumm ai daman ramin ƙarya ƙurare ne, kuma shi daman shari dan aike ne , yau ga ranar jin kunya Bashir da Rabi'u".
Alhaji Munir kallon gidan yayi sama da ƙasa da sauyin da ya samu da baya nan ya kalli Bashir ya ce" Munir ne a tsaye gabanku ba mafarki ba, gani ga matata da ƴaƴana .
Ban mutu ba, ina nan da raina Rabi'u.
Kunci amanar zumunci , kun hada kai da bare abokina don ku cutar da ni, amma Allah yafi ƙarfin ku.
Da ace baku kashe min ɗana ba, wata ƙila na iya. . .