JIGAWA STATE.
(Dutse Local Government)
Sanyayyar iska ke kaɗawa mai haɗe da zubar yayyafi sakamakon ruwan sama dake shirin zubowa hadari ne ke gangame baƙiƙƙirin a sararin samaniya kallo ɗaya Isma'il ya yiwa hadarin ya tabbatar da zai zubda ruwa a lokacin ne Major John Arman ya ɗago dara-daran idanunsa farare sol ya kalle su. Fari ne tarr fuskarsa zagaye da saje mai ɗauke da dogon hanci, bakinsa ɗan dai-dai Yana da kaurin jiki. Jikinsa sanye da kakin sojoji jikin rigar an rubuta J Arman.
Fuskarsa na haɗe tamau har yanzu wani. . .