Skip to content
Part 23 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Mami ko hannunta bata ɗaga ba, balle a kai ga ta iya kai wani abu bakinta, gaba-ɗaya Alhaji Mukhtar ya ji ba daɗi na rashin sakewanta amma kuma ba yan da ya iya, domin ba iya su ke cikin damuwa ba, shi ma karan kan sa da yake cikin duhu kan sa a ƙulle yake, ya aka yi General da ke can wata uwa duniya Lagos ya san Ramla, ita da take Adamawa, a Adamawan ma har cikin Mubi.

General kuwa yayi iya ƙoƙarinsa wajan ganin ya sai ta kan sa, amma duk da haka da mutum zai kula to tabbas, zai gane kujeran su Papi ba lafiya, domin yanayin su yanzu ya sha bambam da na ɗazu.

ACM Bunayd muguntansa ne ya mosta, so yake ya kunna kukan kule wa Banafsha amma kuma ba ya son ya je in da suke zaune, tun da su Majeeder na wajan, kada su rena sa a gabanta, ƙwafa kawai yayi, yana jiran a tashi taron.

Abeed fa ya dage da mita, domin ko shi da ba mijin Faɗima ba, ya ji kishin irin haɗuwan da tayi, ji yayi kawai yana taya mijinta kishi.

Dr Arshan kuwa hankalinsa na kan Umaima, wacce kwata-kwata ta ƙi ɗagowa ma ta kallesa,(wannan shi ake ƙira da kowa da abin da ya dame sa).

A haka dai aka yi taron har aka tashi, kowa ya ci ya sha, aka yi nishaɗi, duk da ba kiɗan da aka saka, su Papi ma sun yi ƙoƙarin danne komai ba wan da ya fahimci halin da suke ciki, har aka tashi taro.

Da yake daman da dare ne aka yi abun, to zuwa ƙarfe tara an tashi kowa ya kama hanyarsa.

Abeed saboda taƙaici bai tsaya jiran su Bunayd ba yayi tafiyansa gida, daman nusaibarsa bata samu zuwa family and friends ɗin ba, Dr Arshan kuma duk yan da ya so Umaima ta kulasa ta ƙi, dan haka shi ma part na Bunayd ya nufa, saboda baya son zaman gidan Bunayd har can nisa, gwanda a cikin gida.

ACM Bunayd kuwa yana miƙe wa ya bi bayan Banafsha da ke tafiya kaman ƙwai ya fashe mata a jiki, yana zuwa dai-dai in da suke tsaye ya kunna kukan kule, yayi fiska tare da wucewansa.

Banafsha kuwa ba ƙaramin zarana tayi ba, da sauri ta tamke Umaima tana faɗin, “Wallahi na kuma jin kukan kule yanzu, kema kin ji ko?”

Umaima duk da taji, tana dariya ta ce, “Ni ba abin da na ji.”

Banafsha ta ce, “Tabbas to akwai mastala, aljanune a gidan nan, kuma ni suke damu, Allah kai mu gobe zan fara tofe su.”

Umaima dariya ta din ga yi, tana mamakin storon kule irin na Banafsha, yanzu kuma idan ta kallesa ya za ta yi?, Banafsha har sai da ta ƙulu da dariyan Umaima, ta yi fushi ta juya za ta tafi, sai ga su Majeeder, suna isowa Majeeder ta ce, “sis Umaima lafiya kike dariya haka? Banafshata kuma ta haɗe fiska.”

Banafsha ƙwafa tayi ta ce, “ki ƙyaleta Majeeder, mugunta ke damunta daman ba ta da kirki.”

Umaima tana dariya ta ce, “Tun jiya fa Masoyiya ta dage wai kukan kule take ji a gidan nan, yanzu haka muna tafiya ta rikice wai ta ji kukan kule kuma ni ban ji ba, shi ne ta ce aljanune suka shafe ta a gidan nan, abun ne yaban dariya.”

Majeeder da Ramla murmushin su ma suka yi, Ramla ta ce, “Ai kam babu ko gashin kule a gidan nan balle kuma kule, wataƙila dai aljanun ne.”

Majeeder hararan Ramla tayi ta ce, “sai dai in ke ce aljanan ai, Banafshata ki kwantar da hankalinki ba komai a gidan nan, kawai kina storo ne shi yasa abin ke miki gizo, sorry ki ƙyale su mu tafi ko.”

Cikin gidan suka nufa suna dariya, Banafsha dai bata cewa komai, dan ita tabbas ta ji kukan kule, mamaki take da Umaima ta ce bata ji ba bayan tare suke, bata san Umaima ma taji ƙin faɗa tayi ba, tun da ita ba storon kule take ba.

Bunayd kuwa ransa fess ya wuce abinsa, ƙira ne ya shigo wayansa, ganin layin Chief nasu, sai ya ja guntun tsaki tare da ɗaukan ƙiran, a taƙaice kawai suka yi magana, fiskansan nan a haɗe, suna gamawa ta kashe wayansa, sashinsa ya wuce ya sallami Dr Arshan, zai wuce Lagos yanzu ana nemansa, Dr Arshan ya ce, “sannunku da ƙoƙari ACM, dare-dare ƙira haka kaman yaƙi ne ya ɓarke a Lagos.”

Guntun tsaki ya ja ya ce, “ƙyale mutanen nan, samun waje ke damunsu, amma idan nayi mata sun ma isa su mini wannan iskancin.”

Sallama suka yi ya fito, driver ya sa ya kai shi airport, daganan kuma sai Lagos.

Mami sashinta ta wuce jiki a sanyaye, Mama Hadiza da Ummu tambayanta suka yi ko lafiya, ta ce musu lafiya ba komai, tun da ta faɗi haka sai suka rabu da ita.

Momsee ma sashinta ta wuce, tana cike da mamaki, wato komai da idan aka ce ikon Allah to shikkenan an gama magana.

Wajan ƙarfe goma duk sun yi wanka sun huta, sannan Papi ya ɗau waya yayi ƙiran General akan ya taho tare da Momsee, sai kuma ya ƙira Mami ita ma ta taho tare da wanda ya kamata a yi wannan maganan a gabansu.

General da Momsee, sashin Papi suka nufo, a palourn sa suka same sa zaune, da sallama suka shigo suka samu waje suka zauna.

Mami ma magana ta yiwa Mama Hadiza da kuma Banafsha akan su biyo ta, suka fito tare su uku suka nufi sashin Papi, su ma da sallama suka shiga, Mami kan ta a ƙasa, Banafsha kuwa idanuwanta a kan General suka sauƙa, da mamaki take kallon kaman da yake yi, da Sojan da suka haɗu da shi a asibiti lokacin rashin lafiyan Mami.

Yan da Banafsha ke kallon General, haka shi ma yake kallonta, kallon stanstar kamanta yake da Ramla, kar dai ita ce yarinyar da Ramlah ta tafi da cikinta? Shi ne abin da yake tambayan kan sa a zuciyansa.

Waje su Mami suka samu su ma suka zauna, Banafsha dai a ƙasa ta rakuɓe kusa da ƙafan Maminta, gaishe da su Papi da General tayi tana wasa da yastunta.

Papi bayan sun amsa gaisuwan Banafsha, kallon Mami da General yayi ya ce, “Muna sauraranku, amma kamun nan Banafsha ki buɗe mana taron da addu’a.”

Banafsha kai a ƙasa tayi addu’a, suka shafa, sannan Papi ya ce, “bismillah.”

General ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa, “Ramlat bismillah, ki cire mu a duhun da muke ciki, daman kina raye? Me yasa kika yanke wannan ɗanyen hukuncin?”

Banafsha dai kallon General take da Maminta, ganin yan da yake ƙiran sunan Mami yana mata magana kaman wan da ya san ta, kuma ita duk iya wayonta bata taɓa kallonshi a wajan Mami ba.”

Mama Hadiza jin Mami tayi shiru ta ce, “Muna sauraronki Ramlatu, kin barmu shiru, mene dalilin taron?”

Mami wani irin wawan ajiyan zuciya ta sauƙe sannan a hankali ta ce, “Mama Hadiza ki yi haƙuri da ɓoye miki gaskiyan wacece ni da nayi, Alhaji ka yafe ni duk da nasan ka yarda da ni shiyasa ka aure ni a haka, sannan Banafsha ina fatan za ki buɗe kunnuwanki da kyau dan sauraran amsan tambayoyinki na kullum, game da Maminki.”

Duk idanuwa suka zuba wa Mami ba wan da ya ce ƙala, a hankali Mami ta numfasa tare da fara koro labari..

ASALIN LABARIN MAMI.

TARIHINTA DA SANADIN SHIGANTA WANNAN RAYUWA DA TA ƊAUKA A SANA’A…

Ramlat Hashim Abubakar, shi ne asalin sunana, ni ƴa ce ga Sarki Hashim Abubakar Sultan, Sarkin garin Sokoto.

Mahaifina Mai martaba Sultan Hashim, ya kasance mutum ne mai zafin zuciya, saurin fushi da kuma tsaststauran ra’ayi, duk da dai ya kasance Sarki mai adalci da kuma bin gaskiya, musamman da ya kasance Sarkin Musulmai.

Matan Mai martaba Sultan Hashim huɗu ne russ, Mama suwaiba ita ce ta farko, sai Umma Talatu ta tsakiya, sai Adda Habiba ta uku, sannan Ummata Rahama wacce ake ƙira da Amarya.

Duk tsawon shekarun da Mai martaba Sultan Hashim ya ɗauka da matansa, ko ɓatin wata babu wacce ta taɓa yi, sai da Allah ya sa ya auri Ummata, tana shiga ta samu ciki na, wata tara ciff ta haifo ni, ranan suna na ci sunana Ramlat, bayan haihuwana sai da Ummata ta haifi yara biyar duka maza, amma ba sa zama, kuma har lokacin matan Sarki babu wacce ta samu ciki har lokacin.

Bayan wani lokaci Ummata sai ta fara laulayin wani cikin, kuma lokaci ɗaya suka fara da Adda Habiba, dan ita ma da ikon Allah ta samu ciki wannan lokacin, bayan gwagwarmaya da laulayi da sauransu, suka haihu rana ɗaya, Adda Habiba ta haifo yarinyarta mace, Ummata kuma ta haifo ƴara maza har biyu wannan karon.

Mai martaba Sultan Hashim ba ƙaramin farin ciki yayi ba, ranan suna yarinya ta ci sunan Ummata Rahamatulla, dan sosai Sarki ke ƙaunar Ummata, wannan suna da Sarki ya saka wa yarinyan Adda Habiba, shi ya ƙara ta’azzara ƙiyayyan matansa ga Ummata.

Ina da shekaru goma a duniya, lokacin kuma ƴan biyun Ummata Hasan da Husaini, suna da shekaru uku da haihuwa, sai Ummata ta nemi izinin zuwa ganin danginta da ke ƙasar Kenya, domin ita balarabiyar Kenya ce, dalili ne ya kawo ta Nigeria har Allah yayi haɗuwansu da Mai martaba Sultan Hashim.

Mun je Kenya mun yi watanni kusan shida, sannan muka juyo muka dawo, sai dai muna dawowa ba jimawa kuma Hasan da Husaini suka kama cuta, nan fa matan Sarki suka fara yaɗa magana, suna cewa wai dangin Ummata mayu ne, su suke cinye yaran da take haifa, yanzu ma ga shi za su cinye Hasan da Husaini, kuma fa duk wannan kirsa ne, dan ba ƙaunar Ummata suke yi ba balle yaranta, musamman ma ni sun ɗauki stanan duniya sun ɗaura mini.

Wasa-gaske jikin ƴan biyu yaƙi sauƙi, magani gida da asibiti ba wanda ba’a yi amma ba sauƙi, abu tun ba ya kama kunnen Mai martaba Sultan Hashim, har ya fara kama kunnensa, ya fara yardan ko cinye masa yara ake son yi da tsafi, nan fa suka fara samun damuwa da Ummata, amma tana haƙuri.

Kwatsam ƴan biyu suka warke lokaci guda daga aka samo musu wani magani a yankin Nijar, sai dai kuma suna tashuwa Ummata ta kwanta, kwata-kwata bata cika wata da fara ciwo ba rai yayi halinsa, duk da faɗan da suke da Sarki, amma abun ba ƙaramin taɓa sa yayi ba, musamman da mutuwa ya zama mai raba mutane na har abada, lokacin ni kuwa shekaruna goma sha ɗaya ne a duniya, dan haka da wayona, nayi kuka sosai dan duk da yarintata amma nasan matan Mai martaba basa so na, hantara zagi ƙiyayya duka ina gani, daman Ummata ke lallashi na ta din ga mini faɗa, yanzu kuma da babu ita sai dai na yi kukana na gama.

Karatu Arabic da boko duka ina da su dai-dai gwargwado, haka ƙannena ƴan biyu da Rahmatullah mai sunan Ummata, Mai martaba Sultan Hashim na ƙaunar mu duka, babu banbanci ko da kuwa tsakaninmu mu mata ne, da su ƴan biyu yara maza.

Amma fa a ɓangaren matansa muna ganin mugunta ni da ƴan biyu, kuma cikin ruwan sanyi suke mana ta yanda mai martaba ba zai taɓa lura ba, balle ya sani, ni kuma daman ba wata gwanar magana ba ce balle na sanar da Mai martaba, kuyangu kuma da ma’aikata ba su da bakin magana, dan sosai suke shakkan Umma Talatu, ita kuwa Mama Suwaiba macijin sari ka noƙe ne, domin kowa kallon salaha yake mata a gidan sarautan, amma a baɗini ta fi sauran matan baƙin hali, da ƙin mu.

Rayuwa na tafiya daɗi ba daɗi har na kai shekaru goma sha huɗu, lokacin kuma maƙerin budurci ya gama ƙera ni, ga shi Allah ya sa na haɗa kyawun mahaifina da na mahaifiya, musamman Ummata na ɗaukota sosai, kana ganina kasan ruwa biyu ce, kuma a ka’ida da wuri ake aurar da mu asali a garin Sokoto, dan haka a wannan lokacin sai Allah ya haɗa jinina da wani abokin yaron wazirin Mai martaba Sultan Hashim, saboda ina shiga ɓangaren su waziri, matar waziri na da mutunci Inna Salamatu, Ya Sufyan wan da yake aboki ga Ya Ahmad ɗan gidan waziri, Ya Sufyan Soja ne kaman Ya Ahmad dan haka soyayya muke hankali kwance, duk da ƙarancin shekaru na amma ina mutuwar son Ya Sufyan kaman yan da yake ƙaunata.

Ashe abin da ban sani ba shi ne su Mama Suwaiba, basu so soyayyata da wannan abokin Ya Ahmad ɗin ba, ni duk ɗaukana ma basu sani ba, to ashe sun sani, dan haka suka fara hantara ta wai ai ba soyayya muke ba, bin maza nake aure nake so, yarinya da ni idanuwana sun buɗe.

Ana ɗaukan lokaci mai ɗan stawo kamun Ya Sufyan ya zo wajena, zuwansa na ƙarshe wan da ba zan taɓa mantawa ba, ranan ya zo na yi kwalliyana kaman yan da na saba, na tafi wajansa muka yi hiranmu kaman kullum, daga ranan kuma bai sake zuwa ba, bayan wani lokaci kuma na fara jin kai na ba dai-dai ba, sannan ba’a jima ba na kama ciwo, kuma ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, Mai martaba Sultan Hashim da matansa duk sun ɗauka ko irin cutan su Hassan ne, na maitan da suka ɗaurawa dangin Ummata, amma ina abu ya ta’azzara, zazzaɓi bana iya cin komai, ko ruwa na saka a bakina amayar da shi zan yi.

Ina staka da wannan cuta Hasan da Husaini da suke da shekaru takwas lokacin, suka kama cuta su ma, kaman yan da ya yiwa Ummata haka ya musu ba su cika wata guda ba dukkansu suka rasu.

Rasuwan ƙannena ƴan biyu shi ya zama sila da sanadin bayyanar abin da ya zama tushen baƙin ciki a gare ni, domin a ranan da suka rasu ni kuwa na yanke jiki na faɗi, a haka aka ɗauke ni sai asibiti, da yake kowa kallon yarinya yake mini, to duk cutan da nake ba’a taɓa kawo a mini gwajin da ya shafi ciki ba ko wani abu, to wannan karon ina faɗuwa na fara zubar da jini (bleeding), abu da ya fi komai ɗagawa Mai martaba hankali kenan, zuba jinin da nake yi sosai.

Likitoci iya ƙoƙarinsu suka yi wajan ganin sun stayar da jinin, amma abu ya ci tura, sai da na galabaita sosai-sosai, sannan aka samu jinin ya staya, sai dai me kuma za’a gani, gwajin farko kuwa sai ga cikin wata uku maƙale a marana, cikin da ya zarana kowa ya gigita kowa, ni da ban ƙarisa cika shekaru sha biyar ba ina na samo ciki? Wa ya mini ciki?

Mai martaba ko da aka sanar da shi, to silan kamuwansa da hawan jini kenan, kuma zuciyansa ma abu kaɗan ne ya hanata bugawa, sai dai daf take da kamuwa da ciwon ita ma.

Maganan wannan cikin kamun a ankare ya rasta gidan sarauta ya cika sa, damuwa da baƙin ciki Wajan Sarki basa misaltuwa, ko da na samu sauƙi nima na ji labarin abin da ke faruwa, ai shikkenan sai kuka, domin ko kashe ni za’a yi bansan wa ya mini ba, ni bansan namiji ba, banma san ta yaya ake yin ciki ba.

Matan Mai martaba su suka saka ni gaba da tambaya, amma amsa guda nake badawa ni ban da ciki, ba namijin da ya taɓa ko riƙe hannuna.

Sarki yana da zafin zuciya da fushi, dan haka ko kaɗan bai yi duba da ƙarancin shekaru na ba, ya ce idan ban faɗa masa ba sai ya sa an jefe ni, ni kam amsa guda nake badawa har yau bansan wa ya mini ciki ba, kwata-kwata ma ban yarda ina da ciki ba, dan gani nake ƙarya ne kawai dan a ƙulla mini sharri a haɗa ni da mahaifi na.

Kaman yan da Sarki ya faɗa haka ya saka aka mini dukan kawo wuƙa, ko yastana bana iya mostawa, amma hakan bai sa sun ji abin da suke son ji ba, domin nima ban da amsa ko da kuwa kashe ni za’a yi.

Matan Sarki suka kuma zugasa akan a zubar da cikin, ni kuwa na ce ban isa ba, masu ciki ma idan sun zubar suna mutuwa wajan zubar wa, balle ni da ban da komai, aka yi aka yi da ni naƙi karɓan magani balle allura, ƙarshe ma ko ruwa idan an kawo mini bana sha, dan gani nake kawai suna son kashe ni ne, duk da rayuwa ta mini zafin da na gwammaci mutuwa, amma ba irin mutuwannan nake son yi ba.

Da dabara da makirci irin na Mama Suwaiba aka samu aka na sha maganin zubar da ciki, ba tare da sani na ba, a ranan da na sha a ranan na fara mahaukacin ciwon ciki da mara, sannan jini kan zuba yake a jikina, wannan dama da aka samu shi aka kai ni asibiti tun da bana hayyaci na, aka ƙarisa komai har da wankin ciki aka mini, duk da ƙanƙantar shekaru na amma babu wan da ya tausaya mini, ciki kuwa har da mahaifina, dan yana kan karagan zugan matansa ne, musamman Mama Suwaiba da yake ganin kaman tana matuƙar ƙaunata.

Azaba kam na sha shi iya azaba, na ji ciwon da tun da uwata ta haifeni ban taɓa ji ba a rayuwa, dan sai da na kwashe wata guda curr kamun jiki na yayi sauƙi na dawo gida, daga nan kuma na fara fiskantan abubuwa iri da kala a masarautan.

Duk abin da ake da kuma stawon lokacin da aka ɗauka, ba Ya Sufyan ba alamansa, Ya Ahmad ma baya nan, wan da ina da tabbacin ba zai wuce wani aikin suka tafi ba, amma abun na damuna ga ciwo ga kewan Ya Sufyan, haka na ci-gaba da fama da kai na, amma abun mamaki duk da kuwa halin da nake ciki hakan bai hana ni kumbura ba, na yi ɓul-ɓul, ƙirjina da ƙuguna duk suka ciccika, har cikina ya ɗan mini tauri, nima karan kai na sai abin ya fara bani storo, tun da nasan sun zubar da cikin da suke faɗan ina da shi, amma abin mamaki shi ne har da mosti ina ji a cikina, wan da hakan ya fara sani yardan anya to ba wani cikin ne da ni ba? Sai na fara storon ko aljanu ne suka ajiye mini abunsu a ciki.

Bayan watanni uku zuwa huɗu, ciwo ya riƙe ni, bayana ne, marana ne, cikinane, sai na rasa wanne zan riƙe, kuka kawai nake yi, ina cikin halin haka, wata kuyanga ta zo ta sameni, tayi saurin sanar da Mama Suwaiba, babu jimawa sai gata nan, tana ganina ta hau salati da salallami tana tambayan wani cikin nayi ko me.

Haka aka jide ni sai asibiti, ikon Allah ciki ne na wata takwas a jikina yana neman wata tara, wannan abu kuwa shi ya saka mai martaba zuciyarsa ta ƙarisa kamuwa da ciwo, likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu komai ya lafa, dan ba haihuwa ba ne, wannan karon kam nima na yarda cikin ne a jikina, dan haka ba abin da nake sai istigfari gani nake mutuwa kawai zan yi, haka kawai na ga ciki a jikina ba tare da nasan wan da ya mini ba, tabbas aikin aljanune.

Mama Suwaiba ta faɗa musu su mini alluran naƙuda kawai na haife abin haka, ansan ba fitowa zai yi da rai ba, amma sun ce su ba za su yi ba, a yi wankin ciki a yi komai ciki yana maƙale bai fita ba, dan Allah ya nuna ikonsa, sannan yanzu su ce a mini alluran naƙuda, a’a ba za su ja da ikon Allah ba.

Mai martaba suka samu suka faɗa masa akan na dage cikina nake so, bana son a mini alluran da zai sa na haifa abin cikin na huta, sai ran mai martaba ya ɓaci, a haka yana fama da ciwo ya ajiye ni ya ce na zaɓa ko abin cikina ko su, tun da na ce ba zan bari a taimaka mini na haife abin cikin na huta ba.

Ina kuka nake bai wa Mai martaba haƙuri, amma ina zuciyansa ya riga da ya hau, kuma daman akwai shi da kafiya akan magana idan ya yi ta, juyin duniya Mai martaba ya ce sai dai nabar masa gida an sallameni a masarauta, tun da ba zan yi abin da yake so ba, ni kuwa bana jin zan iya yin wannan kasadan na je na mutu na faɗawa mahalicci na me? Nasan duk da ban san wan da ya mini wannan aika-aikan ba, amman kuma tabbas dole ina da nawa kason laifin a wajan Allah, dan haka ba zan ƙara laifi a kan laifi ba.

Ƙarshe dai Mai martaba ya ce ya yafe ni, babu ni babu su, kada na kuma sawa a rai na ko tunanina cewa ni ƴar sa ce, ba haɗina da masarautan Sokoto, tun da na zaɓi ciki mara uba akan su, to in je ga duniya nan ta ishe ni riga da wando, idan na so ma na ci-gaba da bin mazan kada na daina.

Kalaman Mai martaba ba ƙaramin sosa mini zuciya suka yi ba, dan haka nima a wannan lokacin zuciyata ta riga da ta bushe, ko stinke ban ɗauka a gidan sarautan ba na bi dare na yi tafiya na, kuɗi ne wan da Ya Sufyan ke bani a cikin starabansa su na haɗa na yi kuɗin mota, bansan ina zan je ba, ban san ina na nufa ba, ina ji an ce motan Kano kawai na shige muka nufi Kano dare-dare.

Mun isa Kano lafiya-lafiya wajan asuba, rasa in da zan tunkara nayi bani da kowa bani da komai, ko kayan da zan sanja a jikina ba ni da shi, kwanana biyu ina tanyariri a kan hanya kaman almajira, idan ka kalleni ba za ka so ƙara kallona ba, ga ciki stoho tuni na jikkata na wahala da yunwa da azaban rana, ga ni kuma yarinya ƙarama.

A kwana na uku na nemi gidan Masu ƙarfi dai-dai, saboda wanke-wanke amma sam bana samu, sai dai abun mamaki da mutanen duniya shi ne a haka da nake, yarinya ƙarama ga laluran ciki, amma bai hana wasu ɓata garin al’umma nemana da niyan ɓatanci ba, ba za’a taimaka mini ba sai dai ana son yin lalata da ni, kuma ina da tabbacin wasu ma saboda tsafi ko wani neman duniyan za su yi haka.

Idan ina bakin hanya a cikin gari, to da yawa mahaukaciya suke mini kallo, dan ba zan manta ba, akwai wani bawan Allah da ya kawo mini abinci, kaman abin kirki wai na zo ya kai ni gidansa a taimaka mini, na yarda da mutuminnan amma ƙarshe ya ci amanar yardan, dan ikon Allah ne kawai bai bashi daman yi mini fyaɗe ba.

Na kuma neman aiki a wani gida, nan nayi sa’a na samu, ina wanke-wanke kwana ɗaya biyu, har wanka nayi, matar gidan ta bani kyautan kaya na saka, abinci duka ina ci, sai dai kuma ita ma mijinta ya nemi ƙeta mini mutunci, ni fa har mamaki nake duk da ƙanƙanta na ga ciki, ga ba lafiya ishashshe ba amma hakan ba ya hana wasu neman ƙeta mini mutunci na.

Da abin ya gagara na baro gidan wannan baiwar Allah, na sha wahala na kuma ga rayuwa a garin Kano, sai da cikina ya cika wata goma ciff saboda rashin zuwa awo, ko duba lafiyan ciki, dan ban da kowa ban da komai, cikinnan haka nake fama yau ciwo gobe lafiya duka akan hanya kaman almajira.

Cikin ikon Allah, Allah mai kawo wa bawansa ɗauki, da sassauci a kan komai, sai ya haɗa ni da wani bawan Allah stoho mai suna Malam Salisu, ɗan jihar Adamawa, wannan stoho yana ganina ba tare da duba yanayin zamani ba’a yarda da mutum ba, ya sameni akan taimakona zai yi stakaninsa da Allah, shi ɗan Adamawa ne, kasuwanci ya kawo sa Kano, in bisa Adamawa Insha Allah matarsa za ta kula da ni, ba tare da musu ba na biyo sa, bayan abinci da komai na buƙata da ya saya mini.

Mun iso Adamawa lafiya, tun da kuma na shigo Adamawa na ji nistuwa na stirga mini fiye da a Kano, Adamawa garin Fulanine wan da yawancinsu marowata ne, kan su kawai suka sani, amma Allah ya ɗaura ni akan sa’a domin mutuminnan ya fita zakka duk da shi ma Fulanin ne, sai dai damuwa na farko da aka samu shi ne, dattijuwar matarsa ta shafawa idonta toka wai sam ba zan zauna a gidanta ba, stohon ne ya mini ciki shi yasa zai ɗauko ni ya kawo mata, daga ƙarshe da naga ina ƙoƙarin zama sanadin rabuwan shekararrun ma’aurata, sai na siɗaɗa nayi tafiyana, a wannan halin ma bansan ina zan shiga ba, to nan ne kuma Allah ya ƙaddara asalin ƙaddarata, domin cikin jikina bai hana kyawuna fitowa ba, ƙaddarata ta farko kuwa ita ce wani bawan Allah ba tare da ya damu da halin da nake ciki ba ya ƙoƙarta ya ƙeta mini mutunci na, abin da na sani dai lokacin da yake ƙoƙarin samun nistuwa ni kuma ciwon mara ya murɗeni, na samu daman ture sa, na miƙe ina kuka ina jan jiki har jiri ya ɗibeni ni, daganan kuma bansan in da kai na yake ba.

Lokacin da na dawo hayyacina, wata baiwar Allah na gani a gefena ga likita a kai na, wannan baiwar Allah ba kowa bace face Mama Hadiza, da kallo duka na bi su ita da likitan, sannan na daga hannuna a hankali na shafa cikina, abin mamaki babu ciki a jikina, yunƙurin miƙewa nayi amma wani irin azababben ciwon da naji kame ƙam a ƙasan cibiya na, shi ya sanya nayi baya na kwanta ina runste ido, cikin azaba na yi ɗan ƙara.

Wannan baiwar Allahn riƙe ni tayi tana aikin jera mini sannu, likitan ma ta mini samnu tana faɗin nabi a hankali a kwai ciwo a jikina kafa na fama.

Ba tare da na amsa sannun da suke mini ba, na buɗe bakina a wahalce na ce, “Ina cikina?”

Matar ta ce sunanta Hadiza, inyi hakuri samun lafiyana shi ne babba a yanzu.

Hawayen da ya zubo mini na share tare da faɗin, “Mama abin cikin ya mutu ko? Shikkenan ya kashe mini shi, Allah zai saka mana, na yafe maka yarona Allah sa ka zamo silar cetonmu mu shiga aljanna da mahaifinka”, haka na dinga sumbatu bana ko jin abin da Mama Hadiza ke faɗa mini, ganin haka likita ta mini wani allura, tuni bacci yayi gaba da ni.

Ni ce ban farka ba kuma sai cikin dare, nan ma matar na gani zaune a gefena, sai dai wannan karon da yarinyarta ƴar ƙarama, sannu duka suka mini, amma ban ce komai ba, sai hawaye da nake yi, ba abin da nake tunawa sai kalaman Mai martaba, ga kuma da ikon Allah abin cikin ya koma.

Ina kukana ban fargaba sai muryan likita naji a kai na, cikin lallashi ta faɗa mini nayi hakuri, abin da na haifa tana lafiya lau, ƴa mace ce kada na damu, na kwantar da hankali na za’a kawo mini ita na ganta.

Tun da naji maganan likita tuni farin ciki ya lulluɓeni, haka ma daure Mama Hadiza ta mini duk abin da ta kamata, aka bani abin da zan iya sawa a hanji na, na saka, sannan ba jimawa aka shigo da haɗaɗɗiyar baby girl a cikin towel.

Mama Hadiza ita ta riƙe mini ita na kalleta, ina ɗaura idanuwana akan yarinyar na ji wani irin soyayyanta da ƙaunarta ya lulluɓeni, a take a lokacin na ji ba iya barin iyayena ba, akan yarinyar nan ba abin da ba zan iya yi ba, ko da kuwa rasa rayuwata zan yi, yarinya kyakkyawa da ita, tun tana stumman goyo ma ta fi ni kyau, kana ganinta kaga ƴar larabawa kawai, kyawunta ƙara ruɗani yayi dan ban isa na ce ga uban da take kama da shi ba, nidai na haifi ƴa daga Allah bansan ubanta ba, kuma na bar kowa na saboda ita.

Sai da muka yi kwana bakwai a asibiti ana kula da mu ni da yarinya ta, Mama Hadiza baiwar Allah ita ke dawainiya da mu da komai, yarinyarta mai suna A’isha kuwa kaman dan ita aka haifi jinjirar nan, kullum tana maƙale da ita, muna cika sati aka kunce mini ɗinkin aka sallamemu, dan aiki aka mini aka ciro yarinyar.

Satinmu biyu a gidan Mama Hadiza daga ita har mijinta ba wan da ya ce mini komai, kawai suna kula da mu ne, mijinta ya sayo rago da komai da komai, ya tambaye ni sunan da za’a saka wa yarinya, ni kuwa na faɗa masa sunan da nake so, wato Faɗima, ina faɗa kuma ba wanda ya faɗo mini a rai sai Ya Sufyan nawa, domin shi ke burin saka wa ƴar farin mu sunan idan muka yi aure, sai ga shi kuma da ikon Allah ƙaddara ta riga fata, ƙaddara ta hana faruwar hakan, ƙaddara ta raba mu.

Baba Salisu mijin Mama Hadiza shi ke ɗawainiya da ni da yarinyata Faɗima komai da komai, Mama Hadiza kuma kula take da ni kaman ƴar cikinta, A’isha tana matuƙar son Faɗima, Baba Salisu shi ya ce a dinga ƙiran Faɗima da Banafsha, da yake yana mana wasan jika haka, to wai ita kyakkyawa ce ta dace da sunan, har muka yi arba’in, muka yi wata shida Faɗima tayi wayo ba su tambayeni komai ba, nima kuma ban ce musu komai ba.

Ganin lokaci ya ja sosai, na na gaji dan kai na kawai na shirya tafiya na bar musu gida, Mama Hadiza mamaki tayi ba kaɗan ba sanin dai ba wani abun suka mini ba, Baba Salisu ta ƙira ta sanar masa, hankali tashe ya dawo daga kasuwa, suka sanya ni a gaba suna tambayan lafiya kuwa, ko kuma sun mini wani abun ne.

Kuka kawai na saka, da ƙyar Mama Hadiza ta lallasheni nayi shiru, sannan a ranan na basu labarin kai na, wan da ya ke na ɓoye musu gaskiya gaba-daya, bayan asalin sunana da na iyayena ba abin da na faɗa musu wan da yake gaskiya, domin faɗa musu nayi daga Kenya nake, mastala ce ta auko a ƙasar mu, in da na rasa mijina da kowa nawa, sai wasu stirarun mutane da muka stira tare ne da su na biyo su zuwa Nigeria, to daga Kano kuma wani ya ɗauko ni zuwa Adamawa, matar sa bata amince ba sai na baro musu gidansu, kada na haɗa su faɗa, to daga nan kuma sai hastarin da ya faru tsakanina da wani bawan Allah wan da bayan hakan ne ban kuma sanin komai ba sai ganina da nayi a asibiti.

Mama Hadiza har da kukanta, ina yi tana yi, ni ina yin na tuno mahaifana da ƙaddaran rayuwa da ta riskeni, ita kuma tana yin na tausayi na, Baba Salisu ne ya rarrashe mu bayan ya mana nasiha, sannan ya ce nayi hakuri nayi zamana daga nan har zuwa iya in da rayuwa ta dakatar da numfashinmu, shi a yarinyarsa ya ɗauke ni, domin haihuwa ne ba su yi da wuri ba sai a kan A’isha, amma da sun haifi kama ta.

Na zauna da su Mama Hadiza cikin amana da soyayya, babu abin da suka rage ni da shi, har banafsha ta yi shekaru uku, lokacin kuma Baba Salisu ya sanyata makaranta.

Samari da zawarawa duk suna mini cincirindo, sai dai yawancinsu ba kowa ke zuwa da niyan aure ba, ko niya mai kyau, yawanci ɓatanci ke kawo su, ni kuwa sau tari maganganun Mai martaba ke mini gizo a kunnena, dan haka na rubuta na ajiye ba zan taɓa yin aure ba, tun da mahaifina ya koreni akan laifin da ban aikata ba, ya kuma mini baki idan naga dama na ci-gaba da bin maza, to sai na bi mazan, dan haka dai nima na fara rashin ji na, duk da hakan bai hanani yiwa Faɗima tarbiyyan da ya kamata ba, duk da dai Mama Hadiza ke wannan ƙoƙarin, kuma tana mini faɗa sosai akan wasu abubuwan da nake yi.

Banafsha na da shekaru biyar Allah ya haɗa ni da Alhaji Mukhtar, watarana na je kasuwa ina dawowa, tun da Alhaji Mukhtar ya ganni ya maƙale mini, kuma nima tun da na kallesa na ji ya kwanta mini a rai, sai dai ba aure ne a gabana ba, kuma shi da zancen aure ya zo, ba ɓoyel-ɓoyel na faɗa masa ba zan yi aure ba, ni rayuwa nake yi, idan ya ga zai iya to.

Alhaji mamakina kawai ya dinga yi, amma duk da haka bai fasa bi na ba, har dai ya isa ga Baba Salisu, Mama Hadiza ta saka ni a gaba sai na amince da auren, dan zamana haka bai yi ba, ai tun da jimawa na gama takaba, ba auren kowa a kai na, nayi aure kada na biye wa mazan yanzu lalatani kawai za su yi.

Abin da Mama Hadiza bata sani ba nayi nisa bana jin ƙira, dan haka tayi ta gama naƙi yarda, Baba Salisu ma yayi ya gama naƙi yarda, ƙarshe da suka masta mini cikin dabara na tattara Faɗima da komai namu muka yi tafuyanmu, sam-sam aure baya rai na baya gabana, kuma bana son na ɓatawa su Mama Hadiza, shiyasa na zaɓi tafiya na bar su.

Wannan tafiyan ba ƙaramin ɓatawa Baba Salisu rai yayi ba, Mama Hadiza har da kukanta, sam-sam bata ji daɗi ba, wai an takura mini ga shi na gudu, kuma basu san hanun da zan faɗa ba, duk sai suka ji ba daɗi, Baba Salisu da Mama Hadiza addu’an alkairi kawai suke mini, wan da ni kuma a gefe na a cikin jimeta na ya da zango farko, ina tunanin su Mama Hadiza sun riga da sun yi fushi da ni, a ankare nake komai, tun da cikin Yola da cikin jimeta kusan ɗaya ne, to kada watarana su kalleni, ƙarshe ma ƙoƙarin sauya gari na fara yi.

Yan da na so hakan ne ta faru, domin kuwa samari manyan alhazawa masu ji da kuɗi da siyasa nake yi, duk da ba wai ina sake musu jikina sosai bane, amma dai ina samun kuɗi, wani Alhaji na faɗa wa ya kai ni wani wajan bana son cikin jimeta, nan ya tattara ni ya kai ni Mubi, ya kama mini ɗaki, na tattara kuɗina na mayar da Faɗima makaranta, inda ita kuma ta haɗu da ƙawarta Umaima.

Da wannan Alhajin ya fara neman sai na basa kai na dole kaman masu zaman dadiro, nan muka yi kaca-kaca, na fice a gidan da ya kama mini haya, ban da kuɗi ba komai, ga Banafsha na makaranta, aikatau na fara nema a gidan masu ƙarfi, amma abin da ya faru a kano shi ya kuma faruwa, domin wannan karon ba iya ni ba har da yarinyata da nake matuƙar ƙauna, yarinya mai kananun shekarun da ko bakwai bata gama rufawa ba, har ita ake ƙoƙarin lalatata, daga lokacin na stani aikatau, kuma duk rinsti ba zan yi abin da zai sa a lalata mini yarinyata ba, shiyasa na zaɓi zubar da nawa mutuncin.

Stunduma nayi cikin harkan da na sani, harkan da na ɗauka ba sana’ar da ta fi mini shi, gwada na sayar da mutunci na nayi wa yarinyata farincikina komai, akan a ce an lalata mini yarinya saboda kuɗin, da basu taka kara sun karya ba.

Kuɗin albashin da aka bani na tattara na biya mana kuɗin hayan gida kusa da na su ƙawarta Umaima, tun da mahaifin Umaima Alhaji Aliyu ya ga halin da muke ciki na babu, sai ya saka Banafsha a makarantar su Umaima na Arabic, ya sake mata uniform na boko, komai idan zai yi wa Umaima ƴar sa, to zai yi wa Banafsha ta, dan haka yanzu sai hankalina ya ɗan nistu, ina kuma kan yin harkokina da jama’a, ba wani riban kuɗi sosai a karuwanci, amma dai ya fi mini aikatau da za’a ɓata mini yarinyata.

Banafsha na da shekaru goma, mun fita yawo da ita da Umaima, kwastam muka ci karo da Alhaji Mukhtar, duk iya guje-gujena sai da ya biyo ni har gidan da nake, nan ya dinga faɗa kaman wani yayana, akan me nabar gidan mutanen da suka riƙe ni da amana, na tayar musu da hankali.

Ba tare da na ɓoye masa komai ba, na faɗa masa saboda ya dage sai ya aure ni, ni kuma ba aure ne a gabana ba, su ma kuma suna son na aure sa, na musa musu dan haka bana son na musu butulci na ɓata musu rai, na nuna basu isa da ni ba, gwanda na bar musu gidansu kawai.

Alhaji Mukhtar faɗa ya mini sosai, sannan ya faɗa mini indai saboda bana son aure ne to ya haƙura, nayi haƙuri nima na koma gaban su, ya fi mutunci, amma na dage ba inda zan koma, saboda nasan ran su a ɓace suna fushi da ni, Alhaji ya labarta mini yan da suka yi da su Baba Salisu bayan tafiyana, da yaje sun faɗa masa sun yafe mini damuwansu su ganni, basa fushi da ni, Dan haka kada na damu na koma.

Ni kuwa runste ido nayi akan ba in da zan koma ina kunyar abin da na musu, Alhaji sai da ya dinga sintiri sannan da ƙyar ya shawo kai na, na yarda zan je amma haƙuri kawai zan basu na dawo, zaman Mubi ya fi mini daɗi, Alhaji ya ce ya amince, kuma yabar maganan aure shi ma zai yi rayuwan da nake yi, saboda ƙaunata da yake yi.

Ba jimawa da aka yi wa su Banafsha hutu, na yiwa Abbaan su Umaima bayani, na ɗauki Umaima da Banafsha, Alhaji ya saka mu gaba sai Adamawa, na je na samu Baba Salisu na cuta, nan na dinga basu haƙuri ina neman yafiyansu, suka yafe mini babu komai.

Da yake Alhaji ya riga ya musu bayanin komai, to ba su wani damu da sai na zauna kuma tare da su ba, tun da bana so, na ce Mubi ya fi daɗi, sati biyu muka yi suka cika mu da sha tara ta arziki, suka kuma mini faɗa da nasiha, sannan na musu sallama, Alhaji ya kuma sako mu gaba da yarana muka dawo Mubi, ina dawowa na dinga mamakin yan da gidan da nake haya ya koma, sai da muka huta, sannan Alhaji ya faɗa mini yanzu gidan ya zama mallaki na, shi ya saya mini kuma ya sa aka gyara mini, komai ya saka a gidan, abin da babu kuma nake buƙata na masa magana.

Rasa bakin yi wa Alhaji godiya nayi, kuma ko da na tinkare sa da niyan na samar masa nistuwa, saboda ina tunanin ta haka kawai zan saka masa, kuma dan haka ya mini wannan hidiman, amma ashe akasin fahimta na yi, domin har da ɓata rai Alhaji yayi, ya ce dan Allah ya mini ba dan jikina ba, idan son samu ne ma nabar wannan rayuwa, ko ba zan aure sa ba, zai mini komai na rayuwa.

Talaka da zafin rai, ni kuwa na runste ido, in da nake shiga ba nan nake fita ba, na ce sana’a ta ce haka zan yi ta, idan baya iyawa ban saka sa dole taimaka mini ba, ya bari Nagode, hakuri ya bani amma na hau fushi na ƙi sauƙowa, gajiya yayi kawai ya yi komai da ya kamata ya tattara yayi tafiyansa, bayan ya cika mana gida da kayan abinci da komai na buƙata, ni dai ko Allah kai sa lafiya ban faɗa masa ba, domin duk a tunanina ɗan Adamawa ne shi, bansan daga Kano yake ba, tun da ni ba wani sauraransa nake ba, lokacin da ya kawo mini zancen aure.

Rayuwa na tafiya haka daɗi ba daɗi, Alhaji na iya ƙoƙarinsa da mu, Abbaan su Umaima ma yana ƙoƙarinsa akan Banafsha, ina mutunci da matar sa guda Ummu, amma bamu shiri da Uwar gidansa Umma sabeera.

Ina leƙa su Mama Hadiza, su ma sukan leƙo ni sa’i da lokaci, har dai Allah ya yiwa Baba Salisu rasuwa lokacin Banafsha na shekara sha-biyar, da ni da Banafsha da Umaima muka je ta’aziya, kaman Yan da muka je auren A’isha ƴar sa.

Akwai abin da ke ɗaure mini kai da abokana sana’a ta, da yawa wasu idan suka zo gare ni sai naga sun fasa abin da ya kawo su, ko kuma wasu dai ba sa iya shiga jikina, amma duk da haka ban saduda ba, damuwa ba irin wan da bamu samu da Alhaji Mukhtar ba, kuma shi ma labarina da na bai wa su Mama Hadiza haka na bashi, mu ɓata da shi mu shirya a haka har Allah ya nufa kuma ya ƙaddara auren mu.

*****

CIGABAN LABARI.

Ajiyan zuciya Mami ta sauƙe kaman wacce tayi gudu ta gaji, saboda kukan da take yi, hawaye ne kawai ke sintiri a kumatun ta, cikin kuka take faɗin, “Alhaji ka yi haƙuri ka yafe mini da gaskiyan da na ɓoye maka, Mama Hadiza ke ma ki mini afuwa, Banafsha ki yi hakuri wannan shi ne cikakken tarihin Maminki, wannan shi ne asali na kuma asalinki, ki yi haƙuri haka Allah ya ƙaddaro mana ni da ke.”

Banafsha da wani irin azababben kuka ta fashe da shi, tare da rarrafawa ta koma jikin Mami, ta rungume ƙafanta tana kuka mai cin zuciya, ga tausayin Maminta, ga tausayin kan ta, me ake nufi da ganin cikinta kawai aka yi haka, me haka ke nufi, da gaske kenan ita ƴar shege ce.

Alhaji Mukhtar ne ya sauƙe nauyayyan ajiyan zuciya shi ma, cikin stananin ƙaunar Ramlatunsa, da ya ji ya ƙaru a zuciyarsa ya ce, “Ramlatu ki yi haƙuri, ki ɗauki komai a ƙaddara, kuma alhamdulillah kin cinye ta sai fatan samun gwaggwaɓan rabo daga mahaliccin mu, komai ya wuce ai, tun da ga shi yanzu labari ne kike bayarwa.”

General kam duk dauriyansa sai da hawaye ya zubo masa, kunsan abin da zai sanya soja hawaye ba abu ne ƙarami ba, balle soja irin General, cikin ƙoƙarin danne abin da yake ji ya ce..

*****

<< Yar Karuwa 22Yar Karuwa 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×