Skip to content
Part 31 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Bunayd tuni ya buga IV na dinnernsu, yana ta shiri abin sa, Banafsha ma ko sani bata yi ba, so yake ya mata suprise kawai.

Lokacin da Abeed ya ga IV ɗin, dariya yayi har ƙasa ya ce, “Wato kai fa idan ana neman ɗan iska riƙaƙƙe to daga na ɗayan sai kai, sai da ka gama shawaginka a tukunyar zuma, da akwai rabo ku kisa ma da yanzu ita da ciki suna ture-ture, shi ne za ka ce yanzu za ka yi dinner, Allah Ubangiji ya shiryeka ya shiryi little Bunayd, dan idan ya ɗauko halinka to kai zan tattarowa shi na kawo sa, daman kyawunta idan aka yiwa mutum takwara ya riƙe takwaransa.”

ACM taɓe baki yayi ya ce, “Ka tabbatar dai ka gayyaci mutane yan da ya kamata, so nake ranan na sanya Wiffey farinciki sosai, so nake na ga farinciki mara misaltuwa a fiskanta.”

Dariya Abeed yayi ya ce, “To mijin tace, in Allah ya yarda har da waɗanda baka yi stammanin ganinsu ba sai ka gan su, Allah dai ya sa muna da aron rai lokacin.”

Bunayd ya amsa da “Ameen suka yi sallama.”

Ko da saƙon dinner ya riske Dr Arshan, shi ma sai da ya dara sannan ya jinjinawa hali irin na Bunayd da salonsa, wato ana dinner lokacin hidiman biki, shi kuma sai da aka kusa shekara ma zai yi nasa, haka dai duk suka fara shiri, amma Bunayd ya faɗa musu idan sun sanar da matansu, su hana su sanar wa Banafsha dan suprise ne, matan nasu ma dan yasan ba amfanin hana sanar da su shiyasa ya ce haka, dan muddin ya ce kada a sanar da su, to ko wanne ana bashi darasi a bed zai sake baki ya faɗa, ko shi ne yanzu ba’a sirri da shi, muddin Banafsha ta rikita sa bakinsa babu zip.

Gefe guda kuma shirin auren su Majeeder ake yi, Majeeder da ya Danish, Ramlah kuma da Ya Mus’ab, shirye-shirye ba kama hannun yaro.

Sati uku aka sa bikin, amare sun sha shiri dai-dai gwargwado, rana bata ƙarya sai dai Uwar ɗiya taji kunya, su Abbaa da tawagarsa sun zo kanawan dabo, anan aka ɗaura auren duka biyu, sannan aka ɗau amare aka yi Mubi da su, Umaima da Banafsha su ne amarori ƙirjunan biki, aka sha shagali ba na wasa ba, ana gama komai aka waste bayan sun gama zuga Majeeder da Ramlah ai komai normal ba zafi sai daɗi, Umaima da cikinta mai wata biyu sai dariya take yi.

Majeeder ta ce ko da zafi sai fa su ma sun yi atou, Ramlah ce dai ta ɗan saka dariyan Umaima a ran ta, tana tunanin anya ba saka su a corner suke yi ba(in ma kwana ne ya kika iya da saurayin kakanki, da haka kowa ya saba Ramlatu.)

Banafsha dai bata gane wa su nusaiba su Umaima ba, kowa sai taji yana cewa wani abu sai nan da sati guda, bata san da dinnern ya zo ba.

Nana bealkysu da Suhail sun taɓa rigimansu a wajan bikin nan, dan Suhail fitinanne ne, Nana kuma bata son reni, masu suna bealkysu da tsare gida, haka suke ta rigimansu, Nabeel na cin dariya.

A ranan da aka ɗaura auren su Ya Danish a ranan aka ɗaura na Malam Abbo, da amaryansa Saleema, su ma sun yi shagalinsu, kuma Malam Abbo ya ƙoƙarta ya mance da stabgan Banafsha ya rungume ƙaddara, suna soyewansu da amaryansa, ana ta buga love a gidan Malam Abbo jama’a, gaskiya ustazai ma duniya ne, wani abin sai idonka ya gane maka.

Su Banafsha sun tattara sun koma in da suka fito, Mami kam dama bata zo ba tana fama da cikinta da yayi girman wuce misali, wai kunyan shiga taro take da ƙaton ciki, yara na tura nasu tana tura nata, Mom dai sai tayi dariya kawai ta mata addu’an Allah ya buɗi ido lafiya, Papi kuwa yanzu tsakaninsa da Mami sai zolaya, ita kuma watarana idan abin ya ishe ta, sai ta ce tana juyewa ta gama atou sun ishe ta, Papi ya ce yanzu ta fara ba’a yi komai ba, sai tayi goma a haɗa da Majeeder da Bunayd su zama dozen, Mami kuwa sai ta kama kuka, Mom dai nata dariya, idan abin Papi yayi yawa ne sai ya lallashi Mami.

Ya Mus’ab washe-gari Litinin ya tattara Ramlah suka yi Camaroon, ai kuwa ya ga aikin ƴan fari, domin tun bai yi ba suke wasan ɓoyel-ɓoyel da ita, sai da ya gaji sannan ya lallaɓata ya samu ya gwangwaje, Ramlah tayi kuka har ta gode wa Allah, abin da ya ceceta ma washe-garin za su dawo Nigeria saboda dinnern saura kwana biyu kuma za su je, amma fa ko washe-gari ranan tafiyansu sai da ya buga amarcinsa, sannan ya shiryata suka taho tana ta fushi, ba su staya a Mubi ba, direct Lagos ɗin suka wuce, babban hotel da yake location na dinnern a can suka sauƙa, dan Bunayd ya riga da ya biya komai, duk wani baƙonsa a can zai sauƙa ya biya wa kowa, sai an gama tukunna, idan sun koma shikkenan, inkuma ba’a koma ba duk adadin kwanakin mutum kuɗin na wuyan Bunayd.

Ɓangaren Ya Danish da Majeeder, ya bi ta a hankali kuma tayi dauriya, kunsan masu suna Hauwa’u jarumai ne, soyewansu suke ta yi su ma, sai da ya rage washe-gari dinner sannan suka shirya, suka haɗa hanya da su Umaima, suka bi jirgi sai Lagos, kamun su isa kuma daman Abeed sun jima a can.

Baƙi ta ko ina ganinsu ake yi, amma duk bidirin da ake yi Banafsha ba ta da labari, don duk wan da zai saka abin da ya shafi dinnern ko a status ne sai ya kulleta kada ta gani, ita dai mamaki take ganin busy da Bunayd ke yi kwana biyu, kuma kullum cikin waya, ga shi yau ya shigo da wannan, gobe wancan ya wuce ɗakinsa da shi, ita dai bata ce komai ba.

Washe-gari dinner da kansa ya saka ta, ta shirya ya kai ta saloon, abin mamaki har da mai ƙunshi ya samo mata ya kawo mata, tana dai ganin ikon Allah, dan tasan ko Mami ce ta haihu ai za’a faɗa mata, ba a dinga shirye-shirye ba’a sanar da ita komai ba.

Yamma nayi kuma again sai ga mai kwalliya, duk da haka Banafsha bata yi magana ba, da yake tana da haƙuri sosai da kawar da kai, aka gama cancara mata kwalliya, idan ka kalli Banafsha kaman ka sace ta ka gudu, amma kuma har aka gama komai, aka taimaka mata ta saka wani ranstatten gown ƙirar Egypt, bata ga idon Bunayd ba, har aka gama komai aka mata magana da ta fito, Banafsha a hankali cikin nistuwa take tafiya da takalminta mai stayi dai-dai, har ta iso wajan wani mota da ke Parke yana jiran isowanta, ita bata taɓa ganin irin motan ba a gidan, da alama kuma ranan aka fara shigansa.

Banafsha tayi kyau na fitan hayyaci, rigan nata designer ne, amma kuma na mutunci ya rufe mata ko ina na jikinta, sannan mahaifinsa ma na mutunci, kana ganinta kasan wannan matar aure ce, wacce mijinta ke son ta kuma yake kishinta.

Buɗe wa Banafsha bayan motan aka yi ta ɗage ƙafanta ta shiga a hankali, tana zama wani ƙamshi ya bugi hancinta, juyowa tayi dan tabbatar da shi ɗin ne ko kuwa muradin ganinsa ya sa ta ji ƙamshinsa.

Banafsha na juyo wa sai da ta mayar da idanuwanta ta lumshe su sannan ta buɗe su, dan tabbatar da shi ɗin ne ba mafarki take ba.

Bunayd ta gani a hakimce cikin motan, ya sha wani arnen haɗaɗɗen wanka wan da ya matuƙar masa kyau, ko ta ce shi ya yiwa wankan kyau, dan ba ƙarya Bunayd ƙarshe ne, babu misali.

Banafsha ba ruwanta da za ta ɓata kwalliyanta ko wani abu, haka ta ɓata fiska tare da cunna baki ta fara rigima, ACM Bunayd yana kallonta ya kashe mata ido guda ya ce, “Wiffey ya aka yi? Irin kyau ɗin nan za ki ɓata mini shi tun bamu dawo na baki tukuicinsa ba.”

Cunna baki Banafsha ta kuma yi ta ce, “Uhmn yaya wannan wankan a haka za mu fita? Ni ban yi niyan magana ba amma gaskiya zan yi, haka kawai a je a ta kalle mini kai a inda za mu je.”

Murmushi mai stadan gaske Bunayd yayi tare da sakar mata kiss a tafin hannunta, ya ce, “Kwantar da hankalinki kin gama da ɗan gidan General, idan ba ke ba sai rijiya, ba za na zauna da watanki ba, kwaɗo da makullin zuciyata tana wajanki kuma baki buɗe ba balle wasu su samu space, amma gaskiya fa kada mu je cikin mutane a dinga ce mini yaya, mutane su dinga mini kallon salihin yaya, atou ni dai ina yaye zani ba ruwana, ni yaya mai yaye zani ne, a faɗa wani sunan.”

Murmushi Banafsha tayi mai matuƙar kyau, sannan ta masta gare sa sosai daman maganan a raɗa suke yiwa junansu, ta ce, “Ni ba kai zan sa wa suna ba fa, kai yayana ne, Sweet stick zan sa wa suna sai dai a kira ka da sunansa.”

“Eh Wiffey na yarda.”

Murmushi tayi ta ce, “To my lollipop, kuma dai yayana.”

“Mai yaye miki zani.”

Sai duk suka murmusa, suna hiransu hankali kwance har aka isa wajan taron, Banafsha ƴar ƙauye ta zama wajan stayawa kallon ikon Allah, wajan ya haɗu ne na fitan hankali, ga shi kuma sunanta ta gani da na Bunayd BUNAYD & BANAFSHA WEEDING DINNER.

kallon Bunayd take yi, shi kuma ido ya kashe mata tare da kawar da kai, sannun a hankali suka bi kan abin da aka shimfiɗa musu suka fara taku ɗai-ɗai ana musu ɓarin kuɗi, waƙa na tashi mai sanyin gaske har suka shige wajan suka zauna, hannunsu nan sarƙafe da juna.

Banafsha da Bunayd na zama kallo ya koma kan su, zo ka ga ɗaukan pic(fan’s ku riƙe Dr seeyath ta turo muku photon ita ma ta ɗauke su, ni ina kwaso labari.)

A hankali aka fara gabatar da taro, sai da wai ƙawar amarya ta fito ta ba ta biography na amarya a taƙaice, sannan fa Banafsha ta ɗaga kai dan ganin ƙawar da aka mata, tun da bata da labari balle ta gayyato su Umaima, ai tunanin da take yi ne ya maƙale ganin Umaima cakwai-cakwai da cikinta da ya fara tasawa, sai kuma ta fara raba idanuwanta a wajan, da mamaki duk take bin su da kallo, har Majeeder da Ramlah amarya sun zo kuma duk sun yi ankonsu, har Suhaila da Nabeela da ke Lagos ga su nan, har su Suhail kai har Nana ma gata nan, sai can ta hango little Bunayd ya stuke cikin suit, sai lokacin Banafsha tayi murmushi ganin yacce yaron yayi kyau, kaman kuwa Abeed yasan abin da Banafsha ke wa murmushi, ya taso da kan sa ya kawo musu little Bunayd wai ga ƙaramin ango, duk suka murmusa aka zaunar da shi, da yake yaron mai sunan Bunayd ne ba ɓare-ɓare ba kuka haka ya zauna kaman wani babban mutum, sai abin ya ƙara ba da armashi ana ta kashe musu pic’s.

Umaima a taƙaice ta ba da labarin Banafsha da turanci, aka tafa mata dan tayi ƙoƙari sosai.

Abeed kuma ya ba da na Bunayd, ba wan da bai dara ba a wajan, Bunayd kuwa sai bin Abeed yake da harara, har Banafsha sai da ta ɗan yi dariyanta, wannan dariyan shi ya fi komai tafiya da imanin Bunayd, wannan dalilin ne ya sanya shi yin dinnern, kuma ga shi tun ba’a yi nisa ba ya fara kallon farincikin a fiskanta, wan da ya tabbatar har zuciyanta ne, ana cikin haka Momsee da General da Papi da Mom suka iso, Mami tana can da cikinta taƙi zuwa, suna tare da Mama Hadiza da ta zo duba ta, sai ta haihu za ta koma.

Ana fara taro kenan, shigowan wasu haɗaɗɗun larabawa ya ɗau hankalin kowa, ni da kai na uwar batoorl idanuwa na saka dan mamakin ganin larabawan da nayi a filin taron, alƙalamina ne ya kusa suɓucewa sakamakon ganin INNAI &DMD, ban gama mamaki ba suna shigowa sai ga JAY & ANAAM, eyye su ma suna wucewa sai ga MAGAJI & AFREEN sai kuma FAROOQ & AFRAH, amma Ahsan da sweedy ba su samu zuwa ba, suna can Yamen, yanzu gaba ɗaya Ahsan ya koma can da zama.

Abeed na hango su ya taso cikin farin ciki ya tarbe su, wajan zama na musamman aka basu, duk suka zazzauna, Abeed ya je ya sanar wa Bunayd, Bunayd yayi farinciki da kuma mamaki, wato gaskiyan Abeed da ya ce zai gayyato waɗanda sai yayi mamaki ma, lallai zuwan wannan manyan baƙin ya fi masa komai daɗi da kuma basa mamaki.

Banafsha ta ce, “Lollipop su waye waɗan can kuma? Waccan balarabiyar ta mini kyau ina son ta da ƙawa”, ta faɗa tana nuna Innai da ke magana da DMD ƙasa-ƙasa.

Bunayd ƴar dariya yayi ya ce, “Sweet beb ba lallai ki gane su ba, amma in kin taɓa jin sunan Mustapha Muhammad mai fata ɗan Gombe, to wancan ɗan sa ne, wannan ɗin kuma matar sa ce.”

Zaro ido Banafsha tayi ta ce, “Ba dai wannan da nake jin sunansa DMD ne ko me.”

“Eh shi ne, kin gane su a she.”

Murmushi Banafsha tayi ta ce, “Ji nake ma kaman na fire na je wajansu ai, lollipop ai na karanta labarinsu wayyo suna burge ni, Allah sarki ina suka baro kyakkyawan yarinyar su oho, Allah kaman ma Nabeel ya auro mana baby eysher.”

Bunayd da mamaki yake kallon Banafsha ya ce, “Wai duk a ina kika san su haka?”

“Ah haba lollipop kana ina na karanta labarinsu mai shegen daɗi JAHILCI KO AL’ADA, ai na faɗa maka har anguwan da suke a Canada na san sunan shi, wayyo ni gaskiya zan yi ƙawance da ita, ina son na je wajan kakanta Baabaa mero na ci dariya, Amma kai a ina ka san su?”

Murmushi yayi ya ce, “A Canada muka haɗu da shi, lokacin na je yin wani aiki, yana da kirki sosai, watarana Insha Allah muma za mu Canada, ban yi stammanin Abeed zai gayyato mana su ba ma.”

Banafsha kasa haƙuri tayi domin da aka ƙira su fili yin rawa, da su Innai suka shigo fili, sai da ta mata magana, Innai da ta zama wata balarabiya ta zama Hajiya, an girma, ai a take suka saba da Banafsha, su ba rawan ma suka yi ba, har da exchanging na contact sun yi.”

Su Abeed kuwa ana nan tare da su Jay, tafiya ta tarar da mu je, yau Abeed yayi dariya kaman ba lafiya, domin ya ga iskancin Jay ɗan biyun na Bunayd ne, indai magana ne, shi kuwa DMD yana nan har yanzu da halinsa na kame fiska, amma kuma har yanzu ba ruwansa da idon jama’a indai akan my loff ɗin sa ce.”

Wannan dinner ba ƙaramin daɗi tayi ba, an yi shagali na ƙure hankali, su Jay an samu abun nema sai ajiyeta suke da su Dr Arshan, DMD dai shi kaman ko yaushe sai dai yayi murmushi, Magaji ma bai cika saka baki sosai ba, amma Jay, Farooq (malam ba wasa), Dr Arshan da kuma Abeed ba dan kiɗa da ke tashi ba da ta tabbata sun haukata wannan taro da dariyansu.

Sai can dare sosai taro ya waste, su Innai ma a masauƙi suka kwana.

Bunayd da Banafsha suka yi gida, washe-gari sai ga su Innai dan a ƙara gaisawa, Umaima duk kaman su haɗiye Innai, duk sai jinjina mata suke na ƙoƙarin da tayi na rayuwan da ta fiskanta, sannan Umaima ta kawo wani dariya ta ajiye ta ce, “Amma duk da lamarinki akwai iska amma fa kin ba da mata a first night.”

Murmushi kawai Innai tayi, ta ce, “Duk ba za ku gane ba ne.”

Mata daman idan an haɗu yawanci labarin guda ne, ko gulma ko zancen aure, yau Umaima ta dara dai-dai gwargwado, nan take suka zama ƙawaye duka, suka yi exchanging contacts, a take Afrah ta buɗe musu group chat a WhatsApp na manyan mata.

Nusaiba ta ce, “Hajiya jikar Baabaa mero ya kaman ciki ne da ke?”

Innai ta kuma murmushi kawai, ai sai Umaima ta saka shewa ta ce, “Sweet-land available, ba period candle na aiki.”

Haka suka din ga hira abin su kaman kar a rabu.

Ɓangaren su Abeed ma sun yi ta da Bunayd, da Abeed ya ke faɗan har yanzu ai Bunayd ba su da ko ciki tukunna, dariya Jay yayi ya ce, “Ba ta basa wajan ƴaƴan ne, wajan daɗin suke wa aiki.”

Farooq ya ce, “Ku ji daɗinku ACM, ai rayuwa sai da hutu, muma ga shi idan yaran suka dame mu wajan kakanunsu muke kai su.”

Abeed ya ce, “Ashe akwai wajan ƴaƴa akwai wajan daɗi?”

Dr Arshan dariya yayi sosai ya ce, “Idan ma baka sani ba yau ka sani.”

Bunayd ya ce, “Duk za ku ji da shi, Sweet beb na da ciki ma Insha Allah.”

Sai lokacin DMD ya jefa musu baki a maganan ya ce, “Amman kam ka dage tayi, domin ni yanzu da kuka ga bana magana tunanin anjima kawai nake, babycute tun da tayi wannan cikin aka samu akasi, babu maƙiyi period amma babyn baya son farincikin babansa, baya son muna gaisawa sosai.”

Duk dariya suka saka, Abeed da Jay sun samu yacce suke so, sai da lokaci ya ja sosai sannan su DMD suka sallami su Bunayd, Magaji ne ya ƙira afreen tasa a waya, suka fiffito suka sallami juna, Banafsha ta cika su da turaruka da stabarmu ta mata, suka kama hanya, sai wani jiƙon kuma(Masu tambayan labarin Innai da DMD, kun ji har da ɗan ƙaramin cikinta gare ta).

Dr Arshan da Abeed ma a ranan suka tusa matansu gaba kowa ya koma gidansa, aka bar Banafsha da Bunayd da halinsu.

Banafsha already ta sani, tun da Bunayd ya ƙyaleta jiya, ya ɗaga mata ƙafa saboda gajiyan dinner, to yau akwai shagali dai-dai gwargwado, kuma daman ita ma ta shirya faranta masa na daban yau, saboda farincikin da ya sanya ta, na wannan dinner da har yayi sanadin ta haɗu da wacce take burin haɗuwa da ita(Innai JAHILCI KO AL’ADA), saura kuma mutanen Qatar idan da nisan kwana, Gimbiya mehwish(ƳAR SARKI CE).

Wannan dare wani irin raya sa suka yi, cike da kauna da stanstar begen juna, daga salon da suke yiwa junansu kasan furta abin da ke zuciya da baki ba zai yiwu ba, sai dai a aikace irin haka, banafsha ta kunce wa Bunayd lissafi yan da ya kamata, ta faranta masa, haka shi ɗin ma, ya jiyar da ita daɗin da ake faɗa ana ji, wanda ko mutuwa fata take ta ɗauke su tare, Allah ya tashe su a aljanna tare ita ce shugabar matansa a can ɗin ma.

Tun da aka yi dinner da wata ɗaya fa yanayin Banafsha ya fara sauya wa, wan da Bunayd ya kasa gane mata, kuma ko zai shekara tambayanta menene ba za ta ce masa komai ba, ƙarshe sai dai ma ta saka masa kuka, watarana haka kawai za ta tashe sa a bacci da kuka, yana dawowa ta tarbesa da kuka, abin ya ishe sa ya dame sa, sauƙinsa ɗaya kawai, duk bala’inta indai maganan magic stick ne ta faɗin ta, to ita da kanta take nema, watarana sai su kwana yin abu ɗaya, amma in Allah ya yarda da asusussuba za ta saka masa kuka ta ce, ita sam ya daina son ta, baya ƙaunarta, ko Palace ɗin ma ya daina so, shikkenan sai ya daina mata yan da ya saba, ita yanzu ko gamsuwa bata yi, kullum mitan kenan da sassafe, kuma da zai mata har ya gaji, to ba za ta ture sa ba, Banafsha ta zama harija jama’a a kawo wa Bunayd ɗauki, za ta shanye masa ruwan kai.

Mami ta sauƙa lafiya ta haifo yaranta ƴan uku, duka maza, innalillahi wa inna ilaihirraji’un, kada ku ga farincikin wannan iyali, Papi rasa in da zai saka kan sa yayi.

General yayi farinciki na wuce misali, Allah ya azurta su da ƙara samun ƙaruwa ta staston Mami.

Bunayd ya fi kowa rawan ƙafa, musamman da yanayin Banafsha yake yanzu sai a hankali to ko ƙuyan sintiri a Kano baya yi, ya samu ƙanne daɗi yake ji, Banafsha dai tun da ta ƙira ta yiwa Mami sannu bata kuma cewa komai ba, bata ce za ta je Kano ba, bata ce komai ba, da Bunayd ya mata maganan zuwa barkatu ma kuka ta saka masa, haka ya ƙyaleta.

Ranar suna ba wan da bai zo ba amma babu Banafsha, juyin duniya taƙi zuwa ƙarshe ma kukan da tayi har da zazzaɓi sai da tayi, haka Bunayd ya ƙyaleta ya zauna jinya, daga zazzaɓi kuma kaman kada a ce an bai wa Banafsha magani, shikkenan aka ɓallo amai, Banafsha kaman za ta mutu, hankali tashe ya jide ta sai asibiti, tana kuka tana faɗin ita mutuwa za ta yi tun da kowa baya son ta har shi, kuma ta daina ƙiransa yayan ma, Bunayd haka za ta din ga kiransa, shikkenan ita an tsaneta, Mami daman so take ta haihu kuma ta haihu ta daina son ta tana son yaran mijinta, tun da ita ba ta da uba, ba da aure aka haife ta ba, Bunayd har ransa ya sosu ya ɓaci, kaman zai rufe ta da duka haka ya kama mata faɗa, a asibiti suka ta rigima, ƙiran Dr shi ya stayar da faɗan nasu.

Kuma sai Banafsha ta shige jikin Bunayd ta rungumesa suka tafi wajan likita, da murmushi bayarben ya yiwa Bunayd congratulations tare da ba sa result, wata idanuwa Bunayd yayi da kyau, Dr ya tabbatar masa da eh matar sa na da cikin sati biyar, wata ɗaya da sati guda kenan, a asibitin gaban likita ya ɗaga ta ya dinga juyi da ita, ita ma kaman ba ita ta gama masifa da kuka ba, sai ga ta tana dariya.

Bunayd dabara ne ya faɗo masa ya sanar wa likita mastalan da suke ciki, na saurin fushin da take yi yanzu, likitan ya faɗa masa normal ne cikin ne ya jawo, ayi haƙuri tana haihuwa komai ya ƙare, kawai yanzu a dinga bin ta a yacce take so, a guji ɓacin ran ta, domin idan aka yawaita mosta mata ɓacin ran, to daga haka zai iya zama mata hawan jini, kuma babban ƙalubale ne gare ta da abin da ke cikinta, a kiyaye.

Bunayd bai yi ƙasa a guiwa ba yayi maganan sex, nan ma likita ya ce normal cikin ne ya ja hakan, amma ya daina biye mata, idan ya yawaita yi to za su iya ɓaro da cikin ya zube, suyi dai kar ya wuce misali, idan ma cikin ya kai wata shida za ta koma dai-dai, wataƙila har maganan yawan fushin ma.

Bunayd sai da yayi wa likitan kyauta, sannan suka fito, daga cikin mota kuma ta fara rigima, ACM stayar da motan yayi, daman da za su fito ta ce bata son driver shi zai yi driving nasu, kuma bata son wasu motoci, dan haka stayawa yayi ya gyara musu tinted glass nasu, sannan ya jawota jikinsa, a hankali ya haɗe bakinsu, cikin nistuwa yake stostan ƙaramin bakin nata, har ya zame mata riga, ya ɗaura hannunsa kan life saver’s nasa, da sai yanzu ya kula da cikan da suka ƙara, kuma daman ga shi da wuya ka ga Banafsha da bra.

A nan cikin motan suka gama haukata junansu, sai da suka yi laushi duka, sannan ya janye jikinsa ya kunna mota suka nufi gida, Banafsha tayi luff ta daina masifa, suna isa ya ɗauke ta sai bedroom, sai da suka kashe arna sannan suka starkake jikinsu, suka yi kwalliya suka fito palournsu suka zauna, Bunayd na shafa cikinta wai babynsa, sannan ya ciro waya ya ƙira su Papi, su Abeed su Arshan, ya dinga ƙiran mutane dai yana sanar da su, kamun ka ce me kowa yasan Banafsha na da ciki sai addu’an Allah ya raba lafiya.

Tun daga ranan Bunayd ya dena biye wa Banafsha, tana fara kukanta kuma zai haɗe bakinsu, sai ya tabbatar tayi laushi sannan zai ƙyaleta, shikkenan daga haka suka samu kwanciyan hankali, da ya sanar da Mom ma ta ce ko zai kawo Banafsha wajanta to su goya cikin, Bunayd ya ce kawai sai anjima Mom ya kashe wayansa, yana kashewa ya ce yo hauka nake da zan yi nisa da Wiffey, musamman yanzu da ta ƙara wani garɗi na musamman, ai idan ta haihu ma babu mai tafiya mini da mata, akan haka sai na tashi yaƙi a Lagos.

A hankali suke renon cikinsu cikin soyayya da ƙauna, yayin da ciki ya kai wata shida sai rigiman Banafsha akan dragon ya ragu, amma fa maganan ɓata rai bata daina sa ba, sai dai ta rage yawan kuka, abin da ke saka ta farinciki daga ta ɓata rai shi ne idan cikin ya mosta, yaro ya harbeta, sai ta fara dariya tana shafa cikin tana magana ita kaɗai, wai hira suke da babynta, Bunayd ya ga ikon Allah, wataran sai dai ya tusa su gaba yana kallo, kuma babynma kaman wan da ake sanar da shi, muddin ta ɓata rai to sai yayi mosti, shikkenan kuma ɓacin rai ya wuce, shiyasa tun baby na ciki Banafsha ke mugun ƙaunar sa, haka ma Bunayd son wannan baby suke na wuce misali.

Cikin Banafsha na da wata shida Umaima ta santalo yarinyarta, zankaɗeɗiya kyakkyawa mai kama da ubanta, da Dr Arshan ya ce jininsa ya fi na Umaima ƙarfi shiyasa ta yi kama da shi, Umaima ta ce sam a’a, sai dai a ce lokacin da aka samu cikinta shi ya fi ta son abin ya fi ta jin daɗin chajin shiyasa, amma yanzu da ta gane wa daɗin Sweet stick ai yaran da za’a haifa gaba dole ma duka da ita za su yi kama, Dr Arshan ya dinga dariya.

Saboda yanayin Banafsha, haka bata samu zuwa sunan yarinyar Umaima ba, ranan suna yarinya ta ci sunan maman Dr Arshan, Hamdiya, suna ƙiranta da Ammi.

Amare su Ramla ma duk babu wacce ba ta da ciki, ko wacce suna renon abin su da wan da ya mata cikin soyayya.

Ƴan ukun Mami kuwa suna girma abin su gwanin sha’awa, Muhammad, Ahmad da kuma Mahmoud, kuma ko wanne sa sunansa ake ƙiransa, sai da Mami ta gama wanka, sannan suka je Sokoto, lokacin kuma mai martaba ya mata maganan sarauta, ya buƙaci ta turo masa Papi, bayan sun koma ta sanar da Papi, ba jimawa ya kama hanya ya je Sokoto, suka gama magana da Mai martaba aka yanke za’a naɗa Papi a karagar mulki, haka Papi ya amsa ya dawo suka fara shirye-shirye.

Adda Habiba har yau jiki sai a hankali, Umma Talatu kuma ta dawo shiru-shirun dole, Mama Hadiza dai lafiya lau take zaune da matan duka, haka ma Mai martaba.

Cikin Banafsha na shiga watan haihuwa Momsee ta zo ɗaukanta, amma Bunayd har da kukansa wai a bar masa matarsa, idan tafiya ne ya same sa to zai kawo ta, amma yana nan kam ayi haƙuri.

Momsee haka ta haƙura ta taho ta ƙyale su.

Bunayd yayi ƙoƙari domin iya iyawarsa yana kula da Banafsha, amma fa cikin ba ya hana su shagalinsu, su yi su ƙara, ko ranar haihuwar ta ma, sun gama soyewansu da safiya kenan ciwo ya fara murɗanta, a hankali tana daurewa har zuwa dare, sai dai dare nayi yaro ya ce shi fa zai fito duniya, haka suka tattara suka yi asibiti, Banafsha ta sha baƙar wahala dan ita ce bata haihu ba sai asuba, Bunayd ya sanar wa Momsee, haka suka kwana a asibiti cikin jimami, Bunayd sam baya hayyacinsa yana Sallah yana rafkanuwa, sai da ta sauƙa da asuba sannan hankalinsa ya kwanta, Banafsha ta jikkata sosai, ga shi kaman ta fama da taune-taune, idan ka kalleta sai ka kusa kuka, Bunayd rasa me ke masa daɗi yayi, har kasa ɗaukan babynma yayi yana ta matarsa.

Momsee ce ta sanar da haihuwan Banafsha ta samu ƴa mace, ba wan da bai ji ba, ana ta murna Banafsha ta haihu, sai da suka kwana huɗu sannan aka sallamesu a asibiti, Banafsha ga ciwon ciki abin dai sai a hankali kawai(Allah ka kawo mana da sauƙi 🥹).

Ranar suna yarinya ta ci sunanta FAƊIMA, dan Bunayd ya ce shi matarsa zai yi wa takwara, sai da aka gama hidiman suna sannan suka wuce gidan Momsee ba dan Bunayd ya so ba, asali ma bai san tafiyar su ba.

Bayan suna da kwana biyu yarinya ta koma, Banafsha tayi kuka har ta gode wa Allah, Bunayd ma abin ya dame sa amma ba yan da aka iya da lamarin Ubangiji sai godiya, ba dabaranka bane ya baka, sannan dan ya karɓi abinsa to kai dai ka kasance mai godiya ga Allah a ko da yaushe, yarinya dai sai da ta tarawa mahaifiyarta sha-tara ta arziƙi sannan ta tafi, dan ba ƙaramin kyaututtuka suka samu ba, uwar da ƴar, har da Bunayd ɗin da kan sa.

Mami sai sannan ta zo Lagos da ƴan ukunta, sosai ta yiwa Banafsha nasiha sannan ta saki ran ta.

Banafsha na gama wanka, Bunayd ya bi dare ya ɗauke ta, da yake Momsee ta ce za’a barta ta huta tukunna, ta kuma kai ziyara ko Sokoto ne, Bunayd kam ya dauke matarsa ya ce, ba da shi ba dan hutu bata gan su ba, wannan ta koma ne dan cikin wani da ke shirin zuwa, a bar zuwa Sokoto ɗin sai ta ƙara haihuwa, an taɓa zuwa yawon arba’in ba yaro ne, a’a a bari su kuma yin wani cikinsu su haihu tukunna sai a tafi yawo mai dalili, yanzu ina dalili zai sake sabon amarci.

Banafsha kuwa biye masa tayi, wai suyi su ƙara samun wani cikin su haifi babynsu.

Momsee da ta ga abin da suka yi, jan baki tayi ta yi shiru bata ce komai ba, ta ce ta fita harkansu, ko haihuwa Banafsha ta kara yi to sai dai a tura musu mai musu wanka, amma ba a gidanta ba, tun da halinsu kenan, ita Banafsha ana mata gwaninta bata gani tana biye wa miji, ko ɗan gyara babu, Bunayd dai ya ce a bar masa abarsa a haka yake so hhhhh lol.

Ranan wani sabon amarci aka yi, Banafsha da Bunayd ikon Allah, don Bunayd aikin da yayi ranan, Banafsha a jikinta ta ji cikin ya samu kuwa.

Wannan cikin bai wani saka Banafsha laulayi ba sosai, fitinan ma da sauƙi, daga haka Bunayd ya ce to wannan ciki dai nasu ne, haka suka din ga renon abin su har ya kai haihuwa, ranar haihuwa ma Banafsha kaman sadaka aka bata, don da fara naƙudanta da haihuwanta bai wuce awa biyu zuwa uku ba, ta santalo ɗan ta namiji ƙatoto da shi mai kama da ubansa.

Wannan yaro ya fi yarinyar goshi, domin irin kyaututtukan da iyayensa suka samu abin sai kana baki, hatta da fan’s ƴar karuwa sai da suka kai nasa, sannan kuma ba wan da bai koma da kyauta na gani na faɗa ba, ga kaji ga ababen sha, ga kyautan kuɗi da dai sauransu, yaro dai sunan mai martaba ya ci HASHIM, ana ƙiransa da King Sultan.

Mami da Papi da Mom, shiryawa suka yi da ƴan ukunsu suka tafi ƙasa mai starki, a can suka yi umura, har sai da suka jira aka yi aikin hajji sannan suka fara shirin dawowa, Mami sosai tayi addu’oe a ɗaki mai starki, tayi addu’a tayi kuka, roƙon Allah take ya yafe mata kura-kuranta, abubuwan da ta aikata, Mami tayi addu’a ba kaɗan ba, saboda kuka har sai da muryanta ya dishe, bayan wani lokaci suka tattaro suka dawo.

Su Mami na dawowa aka fara shirin naɗa Papi a kujeran Sarki, amma Mami sai da ta kai kan ta court akan maganan zinan da tayi kamun aure, kuma aka mata bulala tamanin kaman yan da addini ya tanadar, da Mai martaba ya ga abin da tayi ba ƙaramin daɗi ya ji ba, ko ba komai ta sauƙe haƙƙin addini, sai addu’an Allah ya yafe mu duka, General ma ya je an masa nasa bulalan, Papi dai bai taɓa aikata zina da Mami ba, ko kuwa kamun aurensa, sai dai gafaran Ubangiji da ya nema na zaman da suka yi ba aure.

Lokaci na yi Mai martaba yayi murabus aka ɗaura Papi, sosai aka yi shagali ba kaɗan ba.

BAYAN WASU SHEKARU

Umma talatu rai yayi halinsa, amma lafiya lau ba tare da cutan komai ba, daga kwanciya sai kuma gawanta ne aka ɗaga a kan gado.

Adda Habiba jiki har yanzu sai godiya, hannu ɗayan ma an yanke sa, yanzu haka take ba hannu ba ƙafa, kowa na kawo mata mutuwa, amma a lamari na Ubangiji sai Umma Talatu ce ta rasu ba ita ba, tana nan dai rayuwa sai a hankali.

Mai martaba ya stufa kucuf dan daman dalilinsa na yin murabus kenan, suna nan tare da Mama Hadiza da Adda Habiba, amma zuwa yanzu ba maganan Adda Habiba, dan ko shi fama yake da kan sa, sai albarkacin Mama Hadiza da ke kula da shi sosai, wan da hakan yake farantawa Mami, ta ke kuma ƙara yin alfahari da gamuwanta da Mama Hadiza a rayuwa, tun da ga shi da ikon Allah yau ita ke kula da Mai martaba.

Allah ya ja kwanan Sarki Sokoto, Mai martaba Sultan Mukhtar Sule kwalli, Papi ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba, domin yana yin duk abin da ya dace bisa ga gaskiya da kuma koyarwan addini, ya riƙe amana ya kuma ji storon Allah.

Zuwa yanzu Mami ta kuma haihuwa sau biyu kuma duka ƴan biyu, sauran maza sauran mata, mazan Hassan da Hussaini ake ƙiransu, macen kuma ya yiwa Mom takwara da kuma Momsee, Mom Kam gaba-daya ta ɗauke mai sunanta tun da aka yayeta ta koma wajanta da zaman.

Anyi auren Ya Sadeeq da wata Samira ƴar cikin jimeta, har sun haihu da yaransu biyu.

Ya Danish angon Majeeder ma yaransu biyu mace da namiji.

Umaima yaranta huɗu, Ammi da ƙannenta maza uku, ɗaya daddy mai sunan baban Dr Arshan, ɗaya Abba mai sunan baban Umaima sai kuma Omer mai sunana yayan Dr Arshan.

Nusaiba haihuwanta uku, little Bunayd da ƙannensa mata biyu, ɗaya takwarar Banafsha, ɗaya takwarar Maman nusaiba.

Ramla yaranta biyu duka maza sai cikin na uku haihuwa yau ko gobe.

Malam Abbo ma da matarsa Saleema sai da suka shekara uku ba su haihu ba, tun da suka haifi guda ɗaya Mace kuma Mai sunan Banafsha, shikkenan har yau ba su kuma samun haihuwan ba.

Sai uban gayya da Uwar gayya, Tun da aka haifi King Sultan, sai da yayi shekara biyar sannan suka kuma haihuwan ƴan biyu mace da namiji, aka yiwa Mami da General takwara, ana ƙiransu Hassan da da Hussaina.

Bunayd da Banafsha ba ƙaramin soyayya suka shimfiɗa mai stafta ba, duk da kuwa rayuwa fa dole mun sani ta ƙunshi abu guda da kishiyar gudan, wato farinciki da kuma baƙin ciki, balle ma zaman tare da komin haƙuri da soyayya Dole watarana sai an saɓa an kuma samu akasi, sai dai mu ce Allah sa mu fi ƙarfin zuƙatanmu.

Banafsha ta zama Hajiya, don sun yi national kuma sakamako yayi kyau, sun je Saudiyya ya fi abin da za’a ƙirga, sannan sun koma Spain da zama gaba ɗaya, sai dai su leƙo Nigeria, auren Suhaila da Nabeela ma duka sun zo.

Auren Suhail da Nabeel da suka zama manyan Samari yanzu shi ake ƙoƙarin yi, dan haka Bunayd da Banafsha suka shirya da tawagar su suka taho Nigeria, Suhail da Nana bealkysu aka yi aurensu, sai shi kuma Nabeel da ya auri Emaan ƴar aunty A’isha.

An yi shagalin biki Masha Allah, anyi bidiri na gani na faɗa da yake auren autan General aka yi, su Banafsha sun sha hidima, su Umaima har yanzu ana nan da hali, in ji nusaiba wai an girma ba’a san an girma ba, anyi ‘ya’ya amma ana kan raba maganan Palace da dragon, Umaima dariya take ta ce, “Ai batun dragon da Palace mu da barinsa sai kuma rai yayi halinsa, dan ko an stufa shi ba’a stufa masa, kana danganawa da Sokoto ka samo mai da stohuwa yarinya, shi kuma aka basa na ƙara ƙarfi, ai idan ba hankali ba sai a karya gado.”

Banafsha sai dai ta ji su kawai, amma ba ta tanka musu, domin yanzu sam-sam bata ganewa kan ta, kuma zargin ciki gare ta take, amma ta bari sai an waste aure za ta yi test, abinda bata sani ba idan sammako tayi to Bunayd a hanya ya kwana, dan kuwa ya fi ta ganin sauyawanta, a ranan da aka waste a ranar ya kai ta asibiti sai kuwa ga cikin sati uku maƙale a maranta, sai sannan hankalinta ya kwanta ta tabbata cikin ne mai saka ta wannan yanayi, shi kuwa bunayd dariya ya din ga yi wai tarihi zai maimaita kan sa, za’a kuma haifo wata Faɗima kenan, dan irin cikinnan to na masu suna Faɗima ne, rigimammu tun a ciki, ita dai sai ta bi sa da harara, dan wannan karon ba yawan kuka, amma fa maganan maitan dragon sai dai a ce Allah kawo sauƙi, dan Bunayd sai da ya ɗaura ruwa ya ce saboda staro kada ruwan jikinsa ya ƙare.

Ciki na wata tara ta haifo santaleliyar yarinyarta kyakkyawar gaske mai kama da su dukansu biyun, sunan ma a can Spain aka yi, sai wane da wance ne suka samu halarta, amma fa fan’s ƴar karuwa gaba-daya sai da na hango su a can.

Yarinya ta ci sunanta FAƊIMA ana ƙiranta da Baby.

ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN

TAMMAT BI HAMDALLAH

Wannan ahali gabaɗaya, gaba da baya ba wanda baya farinciki sai godiya ga Allah, don kuwa kowa ya amshi jarabawansa da hannu bibbiyu kuma kowa ya ga sakamakon hakan, kowa ya ga sakawa ga mai haƙuri da Allah ya ce yana yi, Musamman BANAFSHA DA MAMI, domin kuwa kacokan labarin na yi sa ne domin ƴaƴan shegu da suka yawaita a wannan zamani, su yi haƙuri su riƙe Allah komai yayi farko zai yi ƙarshe, su bar ce wa an haife su ta haka ba mai auransu su ma iskancin za su yi, da kuma iyaye mata masu taɓɓara wa yaransu baƙin tabo, dan Allah kowa ya gyara, Allah kuma ya yafe mu duka, ina mai fata da addu’an duk wani darasi da ke cikin littafin nan al’umman Annabi za su ɗauka su yi aiki da shi, shirme kuma da abin da yake ba dai-dai ba a watsar da shi.

Magana ta gaskiya ba ni da bakin da da zan muku godiya fan’s na Amana, masu daraja habibtiees, kun bani haɗin kai, kun taimaka mini, kun bani guduwama, kun kuma ƙara mini ƙwarin guiwa wajan ganin wannan labari yayi kuma ya bayar da darasin da ake buƙata, ina mai matuƙar godiya, ina matuƙar ƙamnarku.

Duk abin da yake daidai a labarin nan, Allah ya bamu ladansa gaba-daya ni da ku masu karantawa, wan da yake ba dai-dai ba kuma, Allah ya yafe mu baki daya.

<< Yar Karuwa 30

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×