Skip to content
Part 5 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Lumshe idanuwana nayi, muka haɗa baki duka wajan amsa sallaman su Abbaa.

Nana dake zaune a gefena tashuwa tayi da gudu ta nufi wajan Abba ta rungume sa tana faɗin, “Sannu da dawowa Abba na.” 

Abbaa murmushi yayi ya ce, “Yauwá maman Abbaa sannunku ko”, mayar da kallonsa yayi kan mu ni da Umaima ya ce, “Ummul-khultum da Faɗimah babu yiwa Abbaa oyoyo ko? Yanzu kam yarana sun girma sun zama budurwaye, an daina mini oyoyo” ya faɗa yana sakar mana murmushi. 

Cikin jin kunya nayi ƙasa da kai na ina murmushi, Umaima ma murmushin tayi muka haɗa baki wajan cewa, “Abbaa sannu da dawowa.” 

“Yauwá ƴan biyun Abbaa, ƴan albarka sannunku ko.” 

Ummu idanuwanta akan mijinta ta ce, “Alhaji in dai ka biye musu ba za ka huta ba fa.” 

Murmusawa Abbaa yayi, ya miƙe ya nufi ɗakin Ummu ita ma ta tashi ta mara masa baya, Umma Sabeera taɓe baki tayi ta bi Ummu da kallon banza, sannan ta juyo kanmu, amma kamun tayi magana muka haɗa baki har da Nana muka ce, “Umma sannu da dawowa.” 

Umma wani dogon tsaki ta ja ta ce, “mstwwww! Iyayen kalen dangi, Allah ya rufamin asiri na zama uwarki tun da dai ni ba karuwa ba ce” ta ƙarishe maganan kaman tana yi da sa’arta ba sa’ar ƴar cikinta ba. 

Ni kuma a take naji raina ya ɓaci, sai naji gidan ya gundure ni ma, miƙewa nayi zan fice ba tare da na kuma yin ko tari ba, sai Umaima ta tashi ta riƙo hannuna kamun ta buɗe baki ta yi magana, Umma ta rigata ta ce, “Umaima kika kuskura kika ƙara taka ƙafanki kin ji waallahi to sai nayi mugun saɓa miki, shashasha kawai mara zuciya.” 

Umaima tura baki ta yi, da yake shagwaɓaɓɓiya ce sosai har da ɗan buga ƙafanta ta ce, “Masoyiya kiyi haƙuri kinji, ki dawo mu zauna.” 

Kallonta nayi da idanuwana da har sun tara ƙwalla na ce, “A’a Umaima, ki ji maganan Umma, nima gida zan tafi dare tayi”, ina gama faɗan haka na juya ina danne hawayena.

Umaima biyo ni tayi ban sani ba, muna zuwa dai-dai bakin ƙofa kawai na ji sauƙan mari, ina ɗagowa naga Umaima ta dafe fiskanta, cikin ranaza duka muka kalli wanda ya mare ta, ashe ya Danish tare da su Umma ya shigo, duk abinda ya faru akan idonsa, daman yana staye a bakin ƙofan yana jin mu, haushinsa da tausayin Umaima ne ya rufe ni, na ƙwace hannuna a riƙon da Umaima ta mini, na fice da gudu dan muddin na staya to zan iya ramawa Umaima ko da kuwa kashe ni Ya Danish zai yi. 

Umma tsaki taja ta ce, “Ka mini dai-dai Danish, Allah ya maka albarka, ke kuma dan ubanki wuce ciki tun da ita ba ƙanwar uwarki ba ce, munafukan yarinya sai liƙewa ƴar karuwa mara tarbiyya take yi, dan son zubarwa mutane mutunci, shashashar yarinya kawai.” 

Da gudu Umaima ta wuce ɗakinsu tana kuka, Umma ganin ya Danish ya fice sai ta wuce nata ɗakin ita ma, tana hararan ɗakin Ummu. 

Ya Danish kuwa ashe bin bayana yayi, amma ya tarar na jima da shigewa gidanmu, sai guntun tsakin da yaja ya ce, “Wallahi da na kama ki cikin daren nan zan gwada miki digiri na a iskanci, ni ɗin babban ɗan iska ne, amma babu komai, muddin kura na yawo zabo na yawo to watarana za’a haɗu, sai na tabbatar na gyara miki zama.” 

Ina shiga gidanmu na share hawayena na kuma seta kai na, ba tare da na ƙarewa palourn kallo ba na wuce cikin ɗakina, dan bana ƙaunar ƙara wani mummunan ganin irin na ɗazu. 

Washegari da ya kama asabar da sassafe na gama duk ayyukan da zan yi, ganin Mami bata fito ba cikin taƙaici na fice a gidan ban tunkari ɗakinta ba, dan nasan rashin fitowan ta ba zai wuce tana tare da yaron da na gansu tare jiya ba. 

Ina fitowa na nufi gidan su Umaima dan mu wuce Tahfiz, amma sai na haɗu da Abbaa a ƙofa yana ƙoƙarin fitowa, ganinsa sai na tsugunna na ce, “Ina kwana Abbaa.” 

Abba na murmushi ya ce, “lafiya Alhamdulillahi Faɗimah, ina kika tsaya haka baki tafi makaranta ba har yanzu?” 

“Uhmm! Abbaa na tsaya aiki ne, kuma na biyowa Umaima mu tafi tare ne.” 

Abbaa murmushi yayi ya ce, “Ai Ummul-khultum ta jima a makaranta Faɗima, ina ji Mamana ma yanzu ta fitaba jimawa.” 

Miƙewa nayi na ce, “To Abbaa sai mun dawo.” 

“A dawo lafiya Faɗima, Allah ya taimaka ya ba da sa’a.” 

Da “Ameen” na amsa na wuce cikin sauri, dan ina storon dukan latti. 

Ban bi kan kwalta ba sai nabi ta cikin anguwa duk da kuwa nasan da sassafen nan kam iyayen sa ido basu zauna ba, tunda tukunna yanzu safiya ne, ina isa makaranta na hangi Nana tana shiga ajinsu, nima ajinmu na wuce na shiga da sallama inda na tarar ko malam bai shigo ba, hamdala nayi sannan na nufi kujeran da muke zama da Umaima na samawa kai na mazauni, na dubi Umaima na ce, “Sabahul khair ya Aminiyaty.” 

Murmushi tayi ta rungumeni ta ce, “Masoyiya yau kuma ƴar larabci ne tun malam bai shigo ba?” 

“Na’am yau larabce malam za muyi, me yasa kika taho kika barni amma?” Na faɗa ina hararanta da manyan idanuwa na. 

“Banafshaty wallahi ke dai kin sani, labarin gizo ba ya wuce na ƙoƙi, in dai ya Danish na gari to fa sai dai haƙuri za muyi, Umma ce ta sanya ya sako ni gaba dan kar na biya miki, to da muka zo gada ya juya nima sai na juya aikam muka ci karo da shi, nan ya rakoni a guje na ƙariso har cikin makarantar nan” faɗin Umaima tana tura baki kaman ya Danish ɗin ko Umma wani yana kallonta. 

Na buɗe baki zan yi magana sai malam ya shigo, nan muka dinga gaishe sa shi cikin harshen larabci shima yana amsa mana da larabcin. 

Malam Abbo nan ya sa muka yi muraja’a aka fara karɓan hadda, kusan sai da rabin ajin suka bada hadda kamun aka iso kan mu, Umaima ce ta fara rero nata karatun cikin zazzaƙar muryanta har ta idar ita ma ba ɓata ko ɗaya, sai kabbara kawai ake yi, tana gamawa malam ya dube ni ya ce, “Bismillah malama Faɗimah Sufyan.” 

Sanin idan an ƙira sunan mutum an iso kan sa kenan, sai na gyara zama na nayi ƙasa da kai na, na fara rero haddan Suratul Taubah, karatu nake cikin muryana mai sanyawa mai sauraro nistuwa inda ba iya ƴan ajin ba hatta Malamin namu in dai zan yi karatu to idanuwan sa na kai na, sai da na kai ayaa sannan na share hawayen dake idanuwana dan ayoyin cikin Suratul Taubah in kasan fassaran su to dole jikinka yayi sanyi duk da wani sashin nata akan kafirai masu munafurtan Addinin Allah suke, wani gefen kuma akan yaƙin Manzon Allah SAW ne. 

Malam Abbo har nayi shiru idanuwan sa na kaina, sannan ya cigaba da ƙiran sunan sauran ana bada hadda har dai muka gama karatun. 

Bayan ya ƙara mana mun maimaita sai ya fita, nan malamin Tauhidi ya shigo, bayan ya fita shi ma malamin da ke ɗaukan mu Hadith ya shigo. 

Tun ƙarfe 6:30am da muka je makaranta mu ne ba’a tashemu ba sai ƙarfe 10:30am. 

Ana tashi ni da Umaima sai bamu tafi ba muka nufi office na Malam Abbo, sallama muka yi da neman izinin shiga sannan ya umurce mu da mu shigo, durƙusawa muka yi duka, amma sai ya mana nuni da kujera nan muka zauna, sai da ya gama haɗa litattafan gabansa kamun ya ɗago ya kallemu, da larabci ya ce, “lafia kuwa?” 

Ƙasa nayi da kai na sannan na fara koro masa bayani akan musabaƙa, kallona yayi ya ce, “Faɗimah ai kun makara sai dai na gaba kuma, tun farko kun nuna ba za kuyi ba wanda dama dan na saka baki shiyasa aka barku a makarantar ba’a kore ku ba, sai dai ku bari na wani shekaran, domin waɗanda suka yi yanzu, su za’a je na gari da gari da su.” 

Marairaice wa nayi kaman zan yi kuka, nan muka dinga basa haƙuri, dan munsan Malam Abbo in yayi magana dole a saka mu a masu yi, ba wani babba ba ne shi amma kuma ana ji da shi a malaman makarantan saboda iliminsa, numfasawa yayi ya ce, “Shikkenan zan yi iya ƙoƙarina naga anyi da ku in Allah ya yarda, amma fa sai kun ƙara dagewa da muraja’a, dan an jima da yin nisa a karatun da ya shafi musabaƙan, muddin kuna buƙatan a yi da ku to sai kun dage dan a maye gurbin waɗanda ba sa mayar da hankali da ku.” 

Nan muka dinga godiya muka tabbatar masa da in Allah ya yarda za mu dage, ba za mu basa kunya ba, sannan ya sallamemu muka tashi muka fito a office ɗin, gaba ɗaya makarantar muka bari muna farin ciki dan duk mun saka rai akan wannan musabaƙa, sai addu’a muke kwarara wa malam Abbo. 

Malam Abbo bin bayan su yayi da kallo yana murmushi, dan ya rasa dalili baya iya yiwa wannan yarinya musu in za ta faɗi abu ko kuma idan abu ya shafe ta…, shigowan wani Malami ne ya dakatar da shi daga tunanin da yake yi, yana murmushi. 

Zama a kujeran dake kallon sa matashin malamin yayi ya ce, “Haydar na fa raba ka da maganan yarinyar nan, kasan dai wacece mahaifiyar ta da kuma sana’ar ta ko?” 

Malam Abbo na murmushi ya ce, “Zubair ko me na ce maka ba zaka fahimta ba, amma ina tausayin yarinyar nan akan jarabawan rayuwa da suke ciki da mahaifiyar ta, kuma tsakani da Allah da aure nake ƙaunar ta, sai dai a yanzu tana ɗalibata banjin zan iya furta mata, amma in Allah ya yarda muna yaye su tunda ba zai wuce shekara guda ba zan bayyana mata komai a yi bikinmu akan lokaci da yardan Allah.” 

“Hmmn! haydar kenan, kana tunanin wannan yarinya ta dace da zamowa uwa ga yaranka? Kasan fa ance zina bashi ce to baka tunanin laifin kaka ya shafi jikokinta?” 

Malam Abbo hallau murmushin ya kuma yi ya ce, “Zubair ina sonta, ina ƙaunarta a haka, kuma in Allah ya yarda ba wannan abu da kake fata, ita ma mahaifiyar nata Allah ya dai-daita al’amuranta ya shirya ta, in Allah yasa Faɗimah rabon Aliyu haidar ce, kuma alkairi gare ni to Allah Ubangiji ya mallaka mini ita, ya rabamu da sharrin masu sharri da masu mugayen magana irinka” ya ƙarishe maganan yana mai da kansa kan takardun gabansa yana murmushi. 

Malam Zubair taɓe baki yayi ya ce, “kayi nisa baka jin ƙira, kuma koma menene kai za ka jiyo.” 

“Sosaima in dai akan soyayyan Faɗimah-batoola ne, to bana jin komai ba ma iya ƙira ba, ban da mastala da Ummi da kuma Malam duk nasan za su amince dan haka ma na fasa sai ta kammala makaranta, dan a bari ya huce shi yake kawo rabon wani, dan haka ana kammala musabaƙa zan fito da buƙatata in Allah ya yarda, kuma Insha Allahu zan samu karɓuwa.” 

Malam Zubair miƙewa yayi ya fice a office ɗin bai ce komai ba dan yana cike da haushin abokin nasa da ya kasa fahimtarsa. 

Malam Abbo kuma cigaba da dudduba takardun yayi, dan yana azumin kamawan sabon watan musulunci dan haka sai yamma zai koma yayi wanka ya dawo kamun ɗalibai sun zo tunda ranar weekend safe da yamma ne makarantan nasu. 

Cikin farinciki Umaima da Banafsha ke tafiya, Umaima ta ce, “heehuhuuu! wa ya ga su Ummu-khultum ɗin Abbaa an zama Hajiya, hhhh! Hajiya Umaima sama, Hajiya Umaima ƙasa, ai wallahi kullum cikin dariya nake dan haƙori yayi ta qyalli, ga mu da wushirya dukanmu, ya kika hango mu masoyiya?” 

Murmushi nayi na ce, “Kai Umaima kin cika zumuɗi wallahi, yanzu in bamu samu ba fa?” 

Ɓata fiska Umaima tayi ta harareni ta ce, “Kai amma masoyiya a’uzubillah da wannan mugun fatan, ai in Allah ya yarda mu ne za mu cinye, dan haka in Allah ya yarda zuwa Makka very soon, Madinatul Munawwara is loading.” 

Kallonta nayi na ce, “Amma kinsan wannan na iya cikin Mubi ne ko? Ba lallai mu samu kujera ba, dama dai na jiha da jiha ne ko kuwa ƙasa da ƙasa, wannan kam in Allah ya yarda za’a samu.” 

Murmushi Umaima tamun ta ce, “koma dai menene in Allah ya yarda mun kusa zuwa Makka…” Maganan dake bakinta ne ya maƙale sakamakon abinda muka ji ana faɗa a bayanmu. 

”Ƴar Karuwa ! Woooo!! ‘Yar Karuwa!!! Mai kyawun ɗan maciji, asa hijabi kaman musulman ƙwarai a je makaranta da najasa a jiki, ake ɗaukan Qur’ani wa ma ya sani ko malaman ma raba musu majalisar ake yi, ‘Yar Karuwa!! Woo!!!!” 

Cikin taƙaici muka juyo dukanmu ni da Umaima, murmushin da yafi kuka ciwo ne ya ƙwacemini ganin Garba ne ke maganan kuma ga yara kusan uku a gefen sa yana sanya su faɗin ƴar karuwa, suna taya shi yin haukan nasa wanda a tunaninsa yayi dan ya ƙuntata mini ne, bai san yayi a banza ba domin a yanzu ina jin zan iya danne zuciyata ko ma me za’a ce mini, saboda sosai na ji faɗan da Umaima ta mini. 

Umaima za tayi magana sai na yi saurin taran numfashinta na ce, “Umaima ki ƙyale sa da ƙaramin haukansa, dan ina fara magana ko kuwa kika tanka masa to wallahi sai na kwaɗa masa mari, kinsan halina, muje kawai ki ƙyalesa. “Hannunta na kama muka ci gaba da tafiya ina mata hira kaman ba abinda ke damu na amma ita kuma kana ganinta kasan ta sanya abun a rai, ni ake yiwa isgilin amma ita yake damu, Umaima tawa kenan, ina mugun ƙaunarta. 

Tun daga nesa da muka hango ya Danish tare da abokin sa na yi gefe, ganin bai ganmu ba sai nayi saurin sake hannunta tayi gaba ina bin bayanta ina magana kaman taƙi kulani, saboda kada na ja mata faɗa duk da sai da na lallaɓata, sannan ta yarda da hakan, ina binta a baya ina cewa, “haba Umaima me yasa ba zaki staya mu tafi tare ba? Yau duk kin ƙi kula ni me na miki ne wai?”

Har muka isa wajan da yake staye da abokinsa abinda nake faɗa kenan kuma da ƙarfi yanda zai iya jiyo mu, Umaima da ke ƙunshe dariyanta, tana wuce su ta shige gida tana dariya har da kama ciki, idanuwansu duka biyu na kai na har na iso dai-dai su ina magana, na nufi hanyan gidansu Umaima zan shiga sai ya sakarmun wani gigitaccen stawa ya ce, “Keee…! Kar ki sake ki shigar mana gida, tunda kuna da naku ɓace mana a gaban gida.” 

Murmushi nayi wanda ya kawar da damuwan dake raina sannan na juyo na tako har inda suke dan dama ina da cikin sa, stayawa nayi a gabansa ba tare da na kalli abokin sa ba na ce, “Mai digiri a iskanci tun da ba gidan ubanka kai kaɗai bane sai na shiga, kuma Allah ya sa ma muma muna da gidan kai ma ka sani, mtswwww!”, Juyawa nayi na shige gidansu Umaima hankalina kwance, rai na fess na ci masa mutunci a gaban abokinsa, shi ma yaji idan da daɗi. 

Rai a mugun ɓace ya juya zai biyo ni amma ganin Abbaa sai ya fasa ya tsaya yana huci, ni kuwa ganin bai biyo ni ba ko da na leƙo naga Abbaa na ƙofan ai cikin sauri na fito na wuce gidanmu dan dama na riga na gaishe da Abbaa, kuma dan nasan Abbaa na gida shiyasa na masa haka, saboda ba zai taɓa bari ya taɓa ni ba. 

Abokinsa yana dariyan abinda ya faru ya ce, “Danish wacece yarinyar nan haka?” 

Ya Danish wani mugun staki ya ja, cikin taƙaici da haushina ya ce, “Mtsww! Dauda ka yi shiru kar ka tambayeni komai, Hmmn! Har ni yarinyar nan za ta dage da qira ɗan iska bayan ga ta cikakkiya tunda uwarta karuwa ce, to wallahi ni nasan abinda zan mata” ya Danish kaman zai daki babu haka ya dinga huci, abokinsa sai dariya ya ke, shi kuma duk ya bi ya cika yayi fam kaɗan yake jira ya fashe. 

Mun yi hutun weekend cikin kwanciyar hankali da farincikin kasancewanmj cikin masu musabaƙa, dan kuwa Malam Abbo (haydar) ya tsaya mana komai da mu ake damawa, taƙaicin rayuwa kuwa ba abinda ya ragu sai ma ƙaruwa dan bazan fita na dawo gida ba tare da an jefe ni da mugun magana ba, tsakanina da ya Danish kuwa ba komai sai tarin stana da kuma burin quntatawa juna bai ƙyaleni ba, nima ban ƙyalesa ba, ba ya tausayina ni kuma bana storonsa ko zai kashe ni sai na masa abinda na ga dama. 

Yau da yake Monday muka shirya muka tafi makaranta, bayan mun gama class bayan azahar muka dawo ba hutu muka shirya 4:00pm muka tafi Tahfiz, mu ne bamu dawo ba sai 6:30, muna dawowa Umaima ta shige gidansu, nima nayi namu dan kuwa yau ya Danish baya gari dama daga juma’a zuwa Lahadi kaɗai ake ganinsa a gida. 

Bayan wata guda abubuwa sun taru sun mini yamun yawa, yanzu ya zamana ma banda lokacin yawan yin tunani ko kuka dan kuwa exam’s ne a gabanmu na fita aji biyu a makaranta, sannan ga musabaƙa ya zo shi ma saura sati biyu, exam’s kuma Monday mai zuwa za mu fara wanda yau yake Thursday, Allah ya so dai a satin da muka gama exam’s,sati mai kamawa shi ne na musabaƙan. 

Zaune nake a palourn mu daga ni sai under-wear da vest na baza hangout a gaba na ina kan duba wa, kai na ba ɗan kwali kiston ebra da Umaima ta mini manya da qanana jelar har kusan ƙugu na, ba tare da naji sallama ko mosti ba kawai naji hannun mutum a kai na yana jan jelar gashi na, ɓata fiska nayi na ɗago dan duk a tunanina Umaima ce za faɗa mata bana so, domin nasan ita ce mayyar gashina idan tamin kisto sai ta dinga damuna kenan sai na kulle kai na nake hutawa, maganan dake baki nane ya maƙale ganin wani babban dattijo da shirgegen ƙaton cikinsa yana washe mini bakin da na tabbata haƙoransa sauran babu, yana murmushin da ke ƙara masa muni ya ce, “Yarinya kin yi kyau ƴar shila da ke haka.” 

Cikin taƙaici na miƙe na ɗaga hannu da niyan kwaɗa masa mari, sai kuma na tuna babban mutum ne ya yi jika da ni ma ba ƴa ba, ƙwafa nayi tare da jefansa da mugun kallo na tsana na ce “Stohon banza da wofi wanda bai san daraja da mutuncin ƴa mace ba, kai dube ka fa sa’an kaka na kana wani washemun shaddan bakinka stohon najadu kawai, wallahi ka ci albarkacin musulunci da stufan ka, da abinda zan maka ba za ka iya ɗauka ba”, ina gama magana na rarumi hijab nawa na saka, na sunkuya ina tattara takaddu na. 

Muryansa na ƙara stinkayowa yana cewa, “Haba ƴar shilah ai kyawunki ne ya ja kuma bar ƙira na da stoho, nan da kika ganni sai na miki abinda yaro ɗan shekara 30 ba zai miki ba domin kuwa kayan aikin da ƙarfinsu ko mamarki bata sharewa a buga wasa da ni.” 

Ɗagowa nayi idanuwa har sun kaɗa dan baqin ciki da taƙaicin maganansa na ce, “Wallahi idan har kana da kunya to kaji kunya, kuma ka yi asara dan daka ganni nan nafi ƙarfin ka kuma uwata ma daga yau ina tabbatar maka ba kai ba ita” na faɗa ina wucewa ɗakina tare da banko ƙofana. 

Ina cire hijab na zube kan gado ina jin kuka nason ƙwace mini, sai kawai naga mutum ya shigo min ɗaki daga shi sai boxer da vest, tashuwa nayi a storace cikin in’ina na ce, “kaa kaaa, memm… me.. ya kawo ka ɗaki naa?” Na faɗa murya na rawa ganin stoho ba kaya ga kuma wani abu da nake hangowa a wandon sa ya miƙe kaman katako aka sanya masa a cikin wando. 

Kai na ya iyo yana washe baki, kamun na buɗe baki da niyan lwala ihu na ji muryan Mami na cikin mugun stawa ta ce, “Alhaji sabooooo! Yarinyar tawa za ka ƙetawa mutunci a gidana?” 

Cikin razana tsoho ya juya yana rarraba ido ganin Mamina, ai da gudu nayi wajanta na ɓoye a bayanta ina sakin marayan kuka, rungumeni tayi taja hannuna muka fice a ɗakin ta yafamun mayafin jikinta, ba tare da ta ce mini ko ƙala ba.

Muna zaune a palourn sai stohon ya fito yana sussunne kai, ya buɗe baki zai yi magana Mamina ta miƙe ta kifa masa mari, cikin mugun ɓacin rai ta ce, “Kai Sabo mara mutunci, mastiyaci, ɗan iska, stohon da baisan daraja da mutuncin yara ba, ka fice mini a gida tunda bada kuɗin ubanka na gina ba, ko kuwa na ƙira maka hukuma yanzun nan, kai ba hukuma ma ni nan na ishe ka, indai a kan wannan yarinyar tawa ce to zan iya kashe mutum.” 

Tsohon nan jin zagin Mami sai ransa ya ɓaci ya ce, “naji ba da kuɗin ubana kika gina ba domin kuɗin ubana yafi ƙarfin ki, kuɗin ubana kuɗin halal ne ke kuma karuwa ce ita kuma ƴar taki da kike tunani tana da mutunci to bata da sauran mutunci, don kuwa ƴar karuwa ce ita, maras mutunci har ni za ki gani ki zaga? To wallahi ba yarinyarki ba aure, kuma ita ma Insha Allahu sai tayi abinda kike yi, sai ta lalace, sai ta yi abinda ma ba ki yi ba tunda kika ɗaura hannunki a jikina saboda ita” ya faɗa yana ficewa a palournmu da kayansa a hannunsa. 

Cikin kuka nake bin su da ido, shi da Mamina duka har ya fice, Mami zuwa tayi wajena ta zauna, tana ƙoƙarin ɗaura hannunta a jikina na miƙe cikin gaggawa ina kuka na shiga ɗakina da gudu ina kuka mai cin rai, abubawan da ke faruwa ya fara isa ta, bana jin zan iya daurewa, abin da yawa wai shege da hauka, ga shi shege ga shi mahaukaci. 

*****

<< Yar Karuwa 4Yar Karuwa 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×