Skip to content
Part 9 of 31 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Umaima tuni tayi nisa da tafiya ko jin Banafsha bata yi.

Sai da suka iso dai-dai wajan su Ya Danish sannan Banafsha ta ce, “Umaima na fasa binki.”

Ai da sauri Umaima ta ƙankamo hijabin Banafsha ta ce, “wallahi kin yi kaɗan Masoyiya, tunda kika ja mana ruwa dole ruwan nan ya dake mu tare, ba inda za ki je.”

Banafsha na danne dariyanta, suka gaishe da su ya Farooq, Umaima ce kawai ta gaishe da Ya Danish, amma Banafsha ko kallon inda yake bata yi ba, nunawa tayi ma kaman bata san da halittansa a wajan ba, shi kuwa Danish aikon masifan da ya ƙulla ko gaisuwan Umaima bai amsa ba, buri yake kawai Banafsha ta shiga gidansu, yau sai ya seta mata hankali ya gyara mata wajen zama, ga shi Abbaa ba ya gida balle ya ƙwace ta, dan cike yake da haushin abinda ta masa ranan, kuma tsaff ya shirya muguntan da zai mata, ta yacce ko da kuɗi aka haɗa ta akan ta ƙara faɗa masa magana ba za ta iya ba.

Umaima haka ta maƙalƙale Banafsha sai da suka shiga gidan tare, suna shigewa Danish ya mike stamm! Ya rufa musu baya yana sakin murmushin mugunta, cikin dabara ya faɗawa su Farooq bari ya ɗauko abu a ɗakinsa ya dawo.

Yana shiga ya samu har sun shige cikin gida, ƙwafa yayi tare da sakin murmushi ya wuce part nasu na maza da yake ta bakin ƙofa yana jiran fitowanta.

Umaima suna shiga cikin gidan ta saki hamadala tare da cewa, “To nidai na stira, saura ke mai fita ki koma gida, Allah shiga tsakaninki da masifan da ke bakin ƙofa yana jiran fitowanki.”

Banafsha Murmushi kawai ta sakar wa Umaima, ta nufi ɗakin Ummu, amma a bakin ƙofan suka kusa yin karo da Nana ta ce, “Banafshaty, ai Ummu ta bi Abbaa sun je asibiti dubiya tun ɗaxu.”

Umaima ma fitowa tayi a ɗakinsu ta ce, “sorry masoyiya mancewa nayi ban faɗa miki Ummu bata nan ba, duk storon Ya Danish ne ya cika ni, matar abokin Abbaa ce babu lafiya، shi ne suka je gaisheta a asibiti.”

Harara na aikawa Umaima dan taban haushi, storonsa sai ka ce ya zama wani mala’ikan mutuwa, ba tare da na saurareta ba na juya zan fice, Umma da fitowanta ɗaki kenan, ƙwafa tayi ta ce, “Idan na kuma ƙara ganinki a cikin gidannan ni nasan abinda zan miki, yarinya gaba-ɗaya bata da zuciya, wato har gida kike bin kabeeru ko? To kuwa zan baki mamaki idan kika ce za ki ɗaura shegun fistararrun idanuwanki akan yarana, ki ƙare can ke da karuwar uwarki, kuma idan ma shanyewa yarinyata zuciya kika yi take binki a baya kaman bindi, to ki sani ina dai-dai da maitanki, idan baki ƙyale mini yara kin fita harkansu ba to ba shakka zan saɓa miki.”

Umaima ta buɗe baki za tayi magana sai Umma ta kwashe ta da mari, saurin juyowa nayi rai na a ɓace saboda maganganun Umma, idanuwana akan Umaima na mata alama da ido kada ta ce komai, matar babban yaya ce ta aiko mini da harata tare da yin staki ta ce, “Wallahi idan baki fita harkan mijina ba sai na miki illa, shegiya, ƴar iska, ƴar karuwa…”

Kamun ta rufe baki tuni na dira gabanta na kwasheta da maruka biyu ba ruwana da cikin jikinta, amma kamun na ɗago tuni Umma ta kwashe ni da marin nima ji kawai kake tassss! tasss!, cikin masifa Umma ta ce, “Dan uwarki har kin isa ki taɓa mini surka yar gidan mutunci? Kina ƴar karuwa, ƴar shege”

Ba tare da na tankawa Umma ba, na kuma ɗaga hannuna na kwashe matar yaya babba da maruka, zuciyana na tafasa na ce, “ki bari manyan da babu yacce na iya da su suyi, dan su zan iya ƙyale su, idan ma basu riƙe girmansu ba to ni san basu mastayinsu, amma ke kika ce za ki shiga stabgata zan iya fige miki gashin mugun waje, ni ɗin nan ban da kirki ban da mutunci, kibar ganin wasu nayi ina shiru ki ɗauka ke ma za ki ci banza, wallahi kika masta a lamarina sai na saka zuciyanki ta buga, ƴar iskan kai na ce ni ɗin nan, mijinki da ya mini to ko kallonsa ba za kiyi ba balle ya aure ki.”

Umma kuwa jin abinda na faɗa, a fusace ta iyo kai na tana masifa, amma sai Umaima ta tare ta tana kuka tana cewa, “menene haka Umma? Dan Allah ki bari, da ƴar cikinki kike haka, wallahi idan Banafsha ta rama marin da kika mata ba ruwana ba zan ji zafi ba ke kika nema….” Bata rufe baki ba amma ta hankaɗata gefe ta iyo kai na, matar yaya babba kuwa da taji mari tuni ta zauna daɓas da cikinta a ƙasa ta kasa yin magana, ga haushina ga kuma shakka na.

Wani irin kallo na yiwa Umma tun kamun ta iso gareni, sannan na juya, sai ji na nayi na ci karo da mutum, idanuwana a rufe ban damu da wa nayi karo ba na ci gaba da tafiya, sai ji nayi an riƙe hannuna anyi baya da ni, a hasale na ɗago jajayen idanuwana cike da masifa, amma sai tozali nayi da yaya babba, rai na ƙara ɓaci yayi na ƙwace hannuna na juya, bi na yayi yana cewa, “kiyi haƙuri Banafsha, kada ki tafi a haka..”

Umma cikin ɓacin rai ta ce, “kabeeru idan ka kuma taku ɗaya sai na stine maka, dan Ubanka me haɗin ka da ita? daman gaskiya Hindatu ke faɗa mini kenan? Tunda ga shi har haƙuri kake bata, bayan rashin kunyar da ta mini, ta kuma mari matarka da juna biyu a jikinta.”

Babban yaya stayuwa yayi rai a ɓace bai cewa Umma komai ba, dan shi Banafsha ta masa dai-dai ko me ta musu su suka nema da kuɗinsu, kwafa yayi yana bin matar sa da mugun kallo, domin kusan duk abinda ya faru akan idonsa ya faru, kuma yasan laifinta ne, daman tun ranan ya fara ganin take-takenta, Umma ma harara ta aika masa da shi ta ce, “idan ka kuma yiwa yarinyar nan magana sai nayi mugun ɓata maka rai wallahi.”

Umaima da ke yashe a gefe can ta buge hannunta a jikin kujera har hannunta ya ɗan kumbura, kuka ta sanya kawai, cikin gaggawa yaya babba yayi wajanta yana duba hannun nata, tausayinta ne ya rufesa ganin har taji ciwo, dan sosai suke son Umaima yayyun nata.

Ni kuwa rai na a ɓace na fito bana ko kallon hanya haka nake tafiya kaman zan tashi sama, ba zato ba tsammani naji anyi sama da ni, saboda ɓacin rai da nake ciki ko ƙoƙarin buɗe baki banyi ba balle ihu, sai dai zillewa da nake ƙoƙarin yi dan bansan wa ya ɗaga ni ba, ganin da nayi an shiga sashin mazan da ni, nan na tabbatar da mai wannan aikin, muna shiga ciki aka dire ni a ƙasa har sai da na ƙafata ta lanƙwashe ta mini zafi.

Miƙawa nayi naja staki kawai na nufi ƙofan fita, dan ba sai na kalli waye bane, saboda nasan wa zai iya mini wannan aikin marassa hankalin, hijabina ya rike tare da jawo ni baya ya hankaɗa ni kan kujeran zaman mutun uku da ke cikin palourn, faɗawa nayi kai na buge bayana kuma, runste ido nayi tare da sakin ɗan marayan ƙara, sai lokacin na ɗago idanuwana na sauƙe su a kan sa, wani malalacin ɗan iskan kallo na aika masa da shi sannan na ce, “Wallahi ka fita a harkata idan ba haka ba zan iya kashe ka Danish, na tsaneka kaman yanda ka tsaneni, banason kallonka, ka dena taɓa ni idan ba haka ba zan iya illataka.”

Danish murmushin mugunta ya saki ya ce, “bayan kisa kiyi abinda za ki iya yi, ba dai ni kike faɗa wa maganan banza ba, to zan gwada miki iskanci irin nawa ganin idonki dan ki sani, ko a cikin kwartayenki babu sa’a na balle ke ƙaramar karuwa, har ni za ki cewa ba’a ɗan iska ɗaya sai biyu, to kuwa yau zan nuna miki irin nawa iskancin, gobe ko da kuɗi ba za ki yiwa wani ba balle ni Danish.”

Miƙewa nayi tare da sakin murmushi mai nuni da bai san abinda yake faɗa ba, kallonsa nayi sama da ƙasa duk da belt na wandonsa da yake ƙoƙarin cirewa amma hakan bai dame ni ba, sai ma dogon stakin da naja na ce, “Na faɗa, na kuma faɗa, kuma zan ƙara faɗa, jikin Banafsha ya fi ƙarfinka Danish, na wuce sa’ar yinka, kai mata-maza nake maka kallo, ka je a kuma maka kaciya sannan ka tunkare ni, ” ina gama magana na yi hanyan fita.

Wannan karon cikin zafin rai ya jawo ni ya haɗa ni da bango har sai da na buge kai na, a cikin mugun ɓacin rai ya ce, “Zan kuma gwada miki cewan nafi ƙarfinki yanzu, sai na miki kaca-kaca, sai na illataki, sai na miki abinda babu wanda ya taɓa miki irinsa duk yawon iskancinki, za ki ga mata-maza ganin idonki yau” yana gama magana cikin zafi ya ja hijabin jikina ya yage sa, saboda kada nayi ihu ya haɗe bakinmu waje guda sannan ya fara kiciniyar cire mini kayan makarantan da ke jikina, ni kuwa tunda ya haɗe bakinmu waje guda tuni wani irin storo ya ziyarce ni, banason zina, na tsani zina, bana son mai aikatasa, ko mahaifiyata babu yanda na iya da ita ne shiyasa, ita ɗin ƙaddarata ce.

Abbaa da Ummu dawowansu kenan daga asibitin da suka je, da yake a waje Abbaa ya bar mota, to tun shigowansu suke jin kaman ana kokuwa a sashin su Sadeeq, har za su wuce sai Ummu ta ce su duba dai su gani ko lafiya, Abbaa ba musu suka juya suka nufi ƙofan palourn samarin, suna isa kuwa suka jiyo kaman shessheƙan kukan mace, da sauri Abbaa ya tura ƙofan.

Kiciniyar ƙwacewa na fara yi, ina son nayi ihun naiman taimako ganin ya Danish da gaske yake, amma yaƙi bani daman hakan, ba shan bakina yake ba amma ya rufe mini baki da nasa, nan muka fara kokawa da Ya Danish, da yake ya fi ƙarfina sai samun galaba yake a kai na, har ya kai ni ƙasa ya danneni, kaman yanda zuciyana ke buganawa nakan iya jiyo nasa sautin bugun zuciyan tunda ƙirjinmu ya haɗe waje guda, yana ƙoƙarin zare wandon jikina kawai aka banko ƙofa aka shigo, waye za mu gani? Abbaa ne da Ummu, cikin hanzari Abbaa ya zo ya janye ya Danish tare da kwashe shi da maruka, Ummu kuma ta ɗaga ni tana kuka ta ja hannuna, bata koma cikin gidan da ni ba ta yafa mini ɗankwalinta hannunta cikin hannuna tayi gidanmu da ni, nima a nawa ɓangaren hawaye kawai nake yi dan nayi mugun storata, stanar Ya Danish ya ƙara rufe ni, nayi nadaman sanin wannan gidan nasu a rayuwata, tuna har ya haɗa bakinsa da nawa sai kawai na fashe da kuka na faɗa jikin Ummu dai-dai mun shiga haraban gidanmu.

Abbaa kuwa ba abinda yake yi sai aikin marin ya Danish yana faɗin, “Ni za ka tozarta Danish? Ni za ka wulaƙanta a garinnan? Yarinyar mutane za ka yiwa fyaɗe dan baka da kirki? To wallahi gwanda na kashe ka na huta da ina gani na bari ka ƙetawa yarinyar mutane mutunci, abun kunya za ka jawo mini ina zaune lafiya.”

Ya Danish ko ajikinsa maganan Abbaa bai damesa ba, shi haushi ɗaya yake ciki kawai da bai koyawa Banafsha hankali ba, ƙwace kansa yayi ya fice tare da barin gidan gaba-ɗaya, a lokacin ya shige motansa yabar mubi ya nufi Camaroon tun weekend ɗin bata ƙare ba.

Abbaa cikin haushi yayi cikin gidan, nan kuma ya tarar da Umaima na aikin kuka, kallonta yayi har yanzu ransa a ɓace ya ce, “Me ya same ki?”

Umaima cikin kuka ta nunawa Abbaa hannunta, ta kuma faɗa masa duk abinda ya faru, ƙara tunzura Abbaa yayi, ransa ya kuma ɓaci, lallaɓa Umaima yayi ya shige ɗakin Ummu dan idan yaje wajan Umma yanzu ya tabbata zai yi abinda ba zai yi kyawun gani ko ji ba, amma dai dole ya ɗau mummunan mataki akan Umma da Danish, dole ya take musu birki zuwa yanzu, abu shekaru da shekaru amma kullum cikin stanan yarinya da tsangwamarta, to zai nuna musu iyakar su, yasan abinda zai yi.

Ummu stayar da nata hawayen tayi ta ce, “kiyi haƙuri Umaima, in Allah ya yarda haka ba zai ƙara faruwa ba, Abbaanku zai ɗau mataki kin ji?”

Ɗagawa Ummu kai kawai nayi ina stagaita kukana, sai da Ummu ta rarrasheni sosai sannan ta ce, “Da banso ɓoye lwa Maminki wannan abinda ya faru ba, amma kiyi haƙuri kada ki faɗa mata kinji, ki bari muji daga bakin Abbaanku, amma dai ba wai ina nufin hanaki zuwa wajan ƙawarki ba kinji, kiyi haƙuri ki rage shiga gidan can, in Allah ya yarda komai zai dai-daita, kada ki faɗawa Maminki dan hankalinta zai tashi sosai, kuma ba za taji daɗi ba, kede ki kiyaye, kada ki ƙara ko haɗa hanya ne da shi.”

Jinjina kai kawai nayi, tare da share hawayena, Ummu ta fice ta koma gida ni kuma na shige cikin palournmu, cikin rashin sa’a na samu Mamina zaune a palour, kai na a ƙasa na seta muryana na ce, “Sannu da gida Mami” ina gama faɗa nayi ɗakina da sauri.

Mami da kallo ta bini, ganin ina ɗingisa ƙafana, ga shi kuma wani ɗankwali na rufe kai na da shi a maimakon taga hijabin makaranta, tun ɗaxu tasan muke dawowa amma taganni shiru, sai abin ya dame ta, tashuwa tayi tabi bayana, amma tana shiga ta samu har na shige banɗaki, daga waje ta ce, “lafiyanki kuwa Banafsha?”

Daga cikin banɗakin na ce, “Lafiya lau Mami, wanka nake yi.”

Mamina ba dan ta yarda ba ta fice kawai, ni kuwa a banɗaki sai da na gama shan kukana, sannan na dirje jikina kaman ba gobe, sai da jikina ya fara zafi sannan na fito, da haushin Ya Danish ya haɗa jikinsa da nawa, sallah nayi na miƙa kukana wajan Allah sannan na yi addu’an musabaƙan gobe Allah bamu sa’a, sai da nayi isha’i sannan na fita, abincin dare na ɗiba na ci ɗan dai-dai, Mami ta sani gaba da tambayan me ya hanani dawowa da wuri? Me ya samu hijabin makarantana? Duk tambayoyin Mamina amsa guda take samu, ba komai ba kuma abinda ya faru, da ta gaji sai ta ƙyale ni ta tambayi batun musabaƙa nan ma na faɗa mata sai gobe za muyi namu in Allah ya yarda, addu’an sa’a ta mini, can ba jimawa na mata sai da safe na shige ɗakina, yau gaba-ɗaya na kasa karatu saboda taƙaici, karshe kawai kwanciya nayi dan nayi bacci ko zan samu nustuwa.

Ummu haka ta koma gida ta rarrashi Abbaa da ya bari ya bi abun a sannu, dan Abbaa ya faɗa mata duk abinda Umaima ta faɗa masa, kuma Ummu bata yi musu ba dan tasan staff Umma Sabeera za ta aikata abinda ya fi haka ma, saboda irin stanar da ta yiwa Banafsha mara dalili, Ummu dai wani abu take tunani a ranta amma ta bari ba yanzu za ta bawa Abbaa shawaran ba, yanzu dai ya kwantar da hankalinsa tukunna, sai da ta samarwa mijinta nustuwa, sannan taje wajan Umaima ta rarrasheta ta bata abinci a baki ta bata magani ta shafa mata na shafawa, dan babban yaya sai da ya kai ta chemist kamun ya tafi, ita ma Umaima bata iya karatu cikin wannan daren ba, kwanciya kawai tayi baccin wahala yayi gaba da ita.

Yaya babba kuwa ransa yanda yayi mugun ɓaci, ko takan matarsa Hindatu bai bi ba, haka zalika wai ita ma fushi take da shi, an mareta bai yi komai ba sai ma haƙurin da ya bawa Banafsha, ga shi kuma a gabanta ya riƙo hannun Banafsha, kuma ita ko sannu bai ce mata ba, sai ta hau dokin zuciya.

Washe-gari Lahadi da wuri su Banafsha suka tafi makaranta, daganan aka wuce wajan musabaƙa, yau da makarantan su Banafsha aka fara, cikin ikon Allah suka yi lafiya suka gama, aka cigaba da sauran makarantun da suka rage, har sai yamma yau ma aka tashi, amma yau kam an kammala sai jiran sakamako.

Bayan wani lokaci su Banafsha suka cigaba da zuwa tahfiz, kuma a lokacin hutun boko ya kusa ƙare wa, a haka har sakamakon musabaƙa ya fito, Banafsha ce tazo ta ɗaya, sai Umaima da wata yarinya daga wani makaranta daban suka yi bracket suka zo na biyu, makarantar su Banafsha dai su ne na farko, sai makarantar su ɗaya yarinyan su kuma na biyu, haka dai har wanda suka zo na ƙarshe, kuma an yanke a iya na ɗaya zuwa na biyar ne za’a je na jiha da su nan gaba, dan wannan da aka yi iya na cikin mubi ne, yanzu nan gaba na Adamawa State gaba ɗaya za’a yi kamun kuma aje ga na State da State, wannan nasara ba ƙaramar daɗi ta yiwa malaman su Banafsha ba, kyautar da suka ciyo kuma anbar wa makaranta za’a ƙara gyara abubuwan da ya kamata.

Sai da aka kwashe wata guda Ya Danish bai kuma zuwa weekend ba, wanda ganin haka sai Banafsha ta cigaba da shiga gidan, saboda Abbaa da kansa ya bata haƙuri kuma ya ce kada ta yarda ta ce za ta daina shigowa, ita ma gidansu ne kuma shi mahaifinta ne, Umma dai taƙaici kaman ta kashe kanta, duk da girman Umaima kuwa hakan bai hanata jibganta muddin ta gansu da Banafsha, Ummu abun ya isheta dan haka ta yanke hukunci, ta samu Abbaa ta faɗa masa ita dai a shawaranta tana ganin ya auri Mamin Banafsha kawai, Abbaa ba ƙaramin daɗin shawaran Ummu ya ji ba, tunda ita da kanta tayi maganan to yasan ba za ta kawo masa mastala ba, ya amsa shawaran zai auri Mami ko dan Umma ta gyara halinta, dan yasan tabbas ya auri Mami to Umma za ta dawo hayyacinta, sannan ya faɗa mata shi ma zai ƙira Danish ya fito da mata yayi aure, tunda iskanci yake ji, abin nasa tun daga gida zai fara danne yaran mutane, to bai isa ba gwanda yayi aure kamun ya jajuɓo musu abin kunya, nan ma Ummu tayi na’am da wannan hukuncin, ta bisu da addu’an alkairi a cikin lamarin auren daga na Abbaa har na Danish ɗin, amma tare da Farooq za’a haɗasu su fito da matan auren, tunda daman sa’anni ne su ɗin, wannan hukunci Ummu da Abbaa suka yanke, da yake Ummu matar rufin asiri ce kuma mace ce ta gari fatan samun ko wani namiji, shiyasa take ta daban a wajan Abbaa, ita ya aura daga baya, amma baya jin zai iya samun wata kamarta, sosai Abbaa ke ƙaunar Ummu, kuma halayyanta masu kyau ne suke jawo hakan, yana son Umma Sabeera ma, amma dai halayyanta sai a hankali suna ɓata masa rai.

Mamina cigaba da rayuwanta tayi, wannan ya zo yau gobe kuma wani daban ya zo, ni har mamaki nake yi ma a ina Mamina ke samo wasu mutanen, gata nan dai ba wai mai yawan fita ba ce, amma kuma jama’a ne da ita kaman mai kasa kanta a tire ta fita da shi, Alhaji Mukhtar kuwa har yau bai zo gidanmu ba, kuma wannan karon ne kawai ya jima, dan wata har da sati guda kenan bai zo ba.

Tsakanin yaya babba da matarsa kuwa, mata da miji sai Allah, tuni suka shirya bayan ta gama ginɗaya masa sharuɗan ya fita harkan Banafsha, sannan ta basa haƙuri, shi dai kallonta kawai yake yana murmushin shiririta irin nata, in ba haukan kishi da ya rufe mata ido ba, ai da yana son Banafsha to ba ita zai aura ba, Banafshan zai aura tunda tare ta gansu, kawai ya amsa haƙurin ne ita ma ya bata sun dai-daita, tunda duk sun gaji da fushin da suke yi da juna.

Malam Abbo da Banafsha kuwa yanzu stakaninsu ba’a magana, ɗalibai har sun fara ƙus-ƙus ɗin soyayya Malam Abbo ke yi da Banafsha, Umaima ta samu Banafsha ta mata maganam, amma Banafsha ta nuna mata babu komai tsakaninsu, Umaima ma shiru tayi dai tana kallonsu, Banafsha kuwa duk bata kallon abinda ake nufi, ita ta ɗau hakan shaƙuwa ce kawai, yayinda Malam Abbo ke fama da zuciyarsa, kuma zuwa yanzu yana jin ba zai iya haƙura ba, idan bai bayyana mata ba zuciyarsa akwai mastala, shiri yake kawai gadan-gadan na tunkarar Banafsha ya baje mata sirrin ƙalbinsa.

Bayan sati biyu muka koma boko inda muka fara sabon aji, semester na farko a ajinmu na ƙarshe, in Allah ya yarda mun kusa gama College of health, ranan juma’a mun je school mun dawo ni da Umaima hankali kwance, mashine ya kawo mu har ƙofan gida, muna sauƙa na hangi motan Ya Danish, nice ma na kula da shi da yake na gane motan nasa, amma Umaima bata kula ba sai hira take mini, ina ganin motan naji haushi ta kama ni amma na kawar, muka yi sallama da Umaima ta wuce gidansu, na shige namu gidan, tun da na hangi mota danƙareriya a cikin gidanmu na ce to Alhaji ya samu zuwa kenan, ajiyan zuciya nayi na shige palourn da sallama, samunsa nayi shi kaɗai zaune a palourn yana waya, stugunnawa nayi na gaishesa ya amsa mini da kai kawai yana murmushi, dan da alama waya mai muhimmanci yake yi, miƙewa nayi na shige ɗakina.

Ya Danish da ya kwashe wata guda bai dawo ba, Abbaa ne ya ƙira sa yana buƙatan ganinsa idan bai zo ba zai saɓa masa, shiyasa ma ya zo wannan weekend ɗin, amma ba dan yaso ba, kuma bai haƙura ba shi sai ya koyawa Banafsha hankali.

Bayan na wasta ruwa na huta, fitowa nayi dan na samu abinda zan sakawa hanjaye na, da Mamina muka kusa yin karo tana ƙoƙarin shigowa ɗaki na, murmushi ta sakar mini ta ce, “Ai na ɗauka kin zama Amaryan ƙulle ne, abincinma sai na zo na ce ki ci.”

Cunna baki nayi cikin shagwaɓa na ce, “Uhmn! Ai gani nan na fito Mamina.”

A gaba Mami ta saka ni har palourn, abincin da ta ɗebo mini ta nuna min na zauna na ci, zama nayi tare da shagwaɓewa na ce, “Mami a bani a baki.”

Girgiza kai kawai Mamina tayi ta ɗau cokalin ta fara bani a baki, a haka Alhaji da fitowansa kenan daga ɗakinsa ya same mu, wata dakakkiyar haɗaɗɗiyar shadda ya saka yayi mugun kyau, Mamina tun da ya fito ta ke ta binsa da kallo tana murmushi, nima murmushin nayi kai na a ƙasa, Mami ta ce, “Alhaji kyau haka kaman sabon ango.”

Alhaji Mukhtar hannunsa ya zura cikin aljihun garensa ya ce, “Sabon angon ne ma Insha Allahu, nan ba da jimawa ba, angon Ramlatu.”

Hararansa Mamina tayi, shi kuma idanuwansa ya mai da kai na, ya ce, “Yarinyata ya kamata yanzu dai ki dinga yi wa Maminki faɗa tunda kin girma, Maminki bata son ta haifa miki ƙanne, ko kema bakya so?”

Girgiza kai nayi a hankali na ce, “Ina son ƙanne.”

Mami hararana tayi, Alhaji kuma murmushi yayi ya ce, “To yanzu dai na yi latti kada na rasa sallahn juma’an nan, bari idan na dawo za mu yi magana, ki labarta mini yanda musabaƙan naku ya tafi.”

Daga ni har Mami a dawo lafiya kuka masa, sannan ya fice, Mami ta dubeni ta ce, “Faɗima kika ce kina son ƙanne?”

Da sauri na ɗaga kai ina murmushi na ce, “Eh Mamina, ki haifa mini ƙani namiji tukunna, sai ki haifa mini mace na dinga mata kisto, kinga nima na samu waɗanda zan dinga yiwa faɗa ina musu wasa, kuma ina cewa ni auntynsu ce.”

Hararana Mami ta yi ta ce, “Da dai maganan ki haifa mini jikoki haka kikayi da ya fi, amma kibar batun ƙanne, ke kaɗai ma da Allah ya bani alhamdulillahi nagode masa, Allah miki albarka ya nuna mini aurenki, Allah stare mini ke ya stare miki mutuncinki.”

Wani ɓoyayyen ajiyan zuciya na sauƙe, ina ƙoƙarin kokawa da tunanin da ke son zuwa mini, hamdala nake ta yi a zuciyana ina faɗin, “Ameen.”

CAS Bunayd suna cin abinci amma hankalinsa gaba-ɗaya yana kan waya, General ne yayi gyaran murya ya ce, “My Man za mu ɓata fa.”

Sosa ƙeya CAS Bunayd ya yi ya rufe wayan, a hankali yake cin abinci cikin yanga kaman mace, sai da suka gama ci duka sannan suka tashi suka koma cikin palourn da ke nan a downstairs, babbar budurwan ce ta masto kusa da Bunayd ta ce, “Yaya yaushe za ka tuna promise da ka mana?”

Ɗagowa Bunayd yayi idanuwansa akan ƙanwar ta sa mai shekaru 19 ya ce, “Wanne alƙawarin fa Ramlah?”

Yarinyar marairaicewa tayi ta ce, “Yaya zuwa Kano fa, ka ce za ka kai mu wajan Majeeder.”

Bunayd lumshe idanuwansa yayi, sannan ya buɗe su alaman irin ya mance ma da wannan maganan, ba tare da ya kalleta ba ya ce, “banda yanzu sai wani lokacin.”

Kaman za ta yi kuka ta fara masa magiya, sauran yaran ma mastowa suka yi, suka saka shi a gaba kaman za su yi kuka, duk sun haɗa bakinsu suna cewa, “Please Our Air Force.”

Gajiya da ihun nasu da yayi a kunnensa ya sanya shi haɗe fuska tare da buga musu wani irin mugun tsawa ya ce, “shut-off!!”

Wani irin zabura dukansu suka yi, suka sha nistojin suka koma gefe suka zauna, duk suna muzurai kaman ba su ke masa shagwaɓa yanzu ba, General da ke zaune a gefe yana kallonsu dariya yayi ya ce, “that’s My Man, yaran nan duk basa ji gwanda ma ka daina musu dariya.”

Momsee murmushi ta yi ta ce, “da rabon dai za ka sha kunya Dear..”

Bata gama rufe baki ba kuwa, Bunayd ya nunawa yaran gefensa duk suka masto, murmushi ya sakar musu ya ce, “Zan kai ku Insha Allah soon, muna zuwa za mu ɗauko Majeeder ita ma ta dawo nan ɗin, sai ku daina damun mutane da Majeeder-majeeder.”

Dukkansu murmushi suka yi, ƙaramar ciki mai shekaru 14 ta rungume hannunsa ta ce, “Allah bar mana kai Yayanmu, Allah nuna mana matarka da yaranka.”

Murmushi yayi ya shafa kanta ya ce, “Ameen Nabeela my love.”

General kawar da kai yayi tare da haɗe fiska ya ce, “Daman an ce ba’a shiga tsakanin ƴan uwa, to kun fi kusa, ni na daina saka baki ma a harkanku, yanzu nasan maganan Nabeel ma haka za ka biye masa, ko a kanka aka fara yin ƙannene oho, to dai alhamdulillahi nima ina da su Allah ne ya ɗauki abinsa, kuma ƙannen kowa ma za su mutu.”

CAS Bunayd murmushi yayi tare da miƙewa ya je yayi hugging na General ya ce, “Allah huci zuciyan General namu.”

Murmushi General ɗin ma yayi ya ce, “Ameen, kuma Allah ya muku albarka, Allah ƙara haɗa kawunanku, yana da kyau kuje Kano ɗin, sannan idan zai yiwu ku taho da mamana Majeeder ɗin, duk ku zo mu zauna ina kallonku hankalina kwance, aikin sojan ma na bar musu.”

Duka yaran dariya suka saka har Momsee, Bunayd ya juya zai tafi sai ya tuna glass nasa ya bari a palourn sama, kallon yaran yayi ya ce, “Suhaila je sama ki ɗauko mini glass na.”

Yarinya mai kimanin shekaru 17 ne ta miƙe, da alama ita ce Suhaila ɗin, General kallon Bunayd yayi ya ce, “ka fa gama aikin naka da wuri ka dawo.”

Murmushi kawai Bunayd yayi ya amshi glass nasa da Suhaila ke miƙa masa, ya ce, “goodnight General namu, Momsee goodnight, my love’s goodnight.”

Duk amsa masa suka yi, ya fice yana murmushi kawai, dan yasan idan ya staya to General zai iya hanasa tafiyan ma gaba-ɗaya, General ma da murmushi ya bi sa da kallo har ya fice, sannan ya sauƙe ajiyan zuciya, kallonsa ya maida kan yaran nasa ya ce, “tunda baku yi wa yayan naku karatunku ya saurara ba, sai ku ɗauko ƙur’ananku ku kawo ni naji, duk wacce bata iya ba kuma tasan sauran.”

Yaran miƙewa suka yi, kowacce ta ɗauko ƙur’aninta, General na sauraran karatunsu, suka gama ya musu ƙari.

CAS Bunayd yana ficewa a palourn ya maida glass nasa, tare da haɗe girar sama da ta ƙasa, hannayensa ya jefa a aljihunsa yana taku cikin ƙasaita, yana fitowa tuni aka buɗe masa ƙofan mota, yana shiga aka kulle suka yi wa mota key, kaman yanda suka zo da mugun gudu haka suka juya da gudun ta da gari, kai sojojin nan basa tausayin kwalta aradu.

Maimakon su ɗauki hanyan banana island sai suka ɗau wani hanyan daban, a gaban wani ɗanƙareren gate suka buga horn, suna shigewa suka yi parking, ko da aka buɗe masa ƙofa yanzunma sai da ya ɗau mintuna sannan ya fito, haɗaɗɗen arnen club ne na gani na faɗa, wanda shegun ƙasa kawai ke zuwansa, wajan ya haɗu ya gaji da haɗuwa, tun daga haraban wajan za ka ga kowa da gang nasu, daga masu shanye-shayensu sai masu romance, wasu kuma sex ɗin suke a idon jama’a hankali kwance, mata kuwa gasunan daga masu yawo stirara, sai masu mutunci waɗanda ke saka pant ba bra ko kuma bra da pant.

CAS Bunayd tunda ya sauƙa a motan matan wajan ke binsa da kallo, wata ma shafe-shafe suke yi da wani amma ta janye jiki ta tunkaro Bunayd tana girgiza, mata ne suka zagayesa kaman za su yi bandansa kowa na iya juyinta dan ya gani ko zai ƙyasa, amma kaman yanda suka saba kullum hakan ne ta faru, idan mace za ta staya setin idonsa ta buɗe ƙafa to ba zai kalleta ba balle yasan da halittanta a wajan, ko kallonsu baya yi haka ya ci gaba da tafiyansa yana jin waƙansa ta headphone ɗin, sai dai yana ta jan guntun staki kawai saboda haushi, shi gani yake duk basu waye ba tukunna, basu san rayuwa ba, cikin club ɗin ya shiga, classic Bar ya nufa, vip na manya, a wani table ya sama wa kansa wajan zama, ga wani ɗan babban mutun da wata mace suna lashe juna, guntun tsaki ya ja tare ɗan buga table ɗin ya ce, “kabar wannan shashancin ko nayi tafiyana” cikin yarbanci yayi maganan.

Babban mutumin wanda da alama Yoruba ne, da sauri ya ture yarinyar gefe ya ce, “Yi haƙuri bansan ka iso ba.”

Tsakii Bunayd yaja ya ce, “kana karɓan salihin iskanci ina za ka sani, da nayi magana kuma ka ji, da yake Palace ɗin ya jima da hucewa yayi sanyi, da mai ɗumi kake karɓa ai da ko ihu nayi ba ji na za ka yi ba.”

Mutumin dai haƙuri ya bawa Bunayd, sannan suka tattauna abinda ya kawo sa, suna gamawa ba ɓata lokaci ya miƙe, sai da ya je wajan rawa ya ɗan taɓa, tunda mata suka fara yanyame sa ya buga musu rashin kirki ya fito yana ta jan staki yana cewa, “aikin banza aikin wofi, za ku tadawa mutum Moransa bayan kunsan Palace naku ya salafce, da masu Palace da ɗumi ake harka ba wanda suka barsa ya gama shan iska ba”, haka ya dinga surutu har ya shiga motansa suka nufi gida, yana isa ya wásta ruwa ya haye makeken gadonsa yana juyi, ko da baccin ya gagaresa miƙewa yayi ya ɗaura alwala ya tada nafila kawai.

<< Yar Karuwa 8Yar Karuwa 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×