Wani ƙaramin chemist ne da ke gefen hanyar da ta ratsa layin, tazarar da ke tsakanin sa da hanya bai wuce mita irin biyar din nan ba haka, a kan wata ƙaramar katanga da ke gaban shagon wacce ba ta fi ɗori uku na bulo ba samari ne da adadin su ya kai biyar, sai kuma ƴan mata masu talle da suka tsaya suna sa’insa da samarin, mafi yawan samarin sun kasance abokan mai chemist ɗin, ko kuma dai ƴan unguwa da ke zuwa wurin don fira a kowanne yammaci.
Tuni rana ta fara yin sanyi, sassanyar iskar yammaci tuni ta fara kaɗawa wacce ta yalwata a wurin, sakamakon isassun bishiyoyi da ke can wani lambu da ke gefe da unguwar, baya ga haka unguwar ta kasance mai yalwar bishiyu, sai dai wurin shine mafi daɗin zama, wata kila ma shi ya sa samari su ka nacewa zaman wurin.
Zaune ta ke a saman teburin da ke cikin chemist ɗi, wanda ya zama mazauni na mara sa lafiya da su ka zo a duba su. Sai kuma wasu mata biyu daga can gefe waɗanda su ka zo su ka tarar a wurin, sai dai da alamu sai an fara sallamar su, tukun wata kila don likitan abokin wanda ya ke shirin zama mijin ta ne nan da wani lokaci.
Sai dai ita a wannan karan ba wai rashin lafiya ce ta kawo ta ba, a’a, sun zo ne tare da masoyin ta don yin gwajin aure sakamakon saura sati guda kacal a sha bikin su.
Tuni, har an ɗibi duka sample ɗin da ake da buƙata, jini da kuma fitsari yanzu abinda kawai ya rage shine jiran sakamako, wanda a wannan lokaci ne ta samu damar afkawa duniyar tunani.
“Shin yanzu ya lamarin zai kasance idan aka samu cewa wanin mu yana da matsala?” Tambayar da ta fara zuwa ran ta kenan, sai kuma ta bawa kanta amsa a cikin zuciyar ta ta cewa, ga me da ita, ta san ba bu wata matsala, kai ko da ace za’a yi gwajin Genotype ne ita tuni ta san na ta kuma AA ne, don haka ba bu wata matsala ko shi SS ne da shi” sauran matsaloli ma tana fatan ba za’a samu ko ɗaya ba.
Murmushi ta yi yayin da ta ji a ranta cewa ko da ma an samu matsalar, ta na fatan cewa ba za ta taɓa guje masa ba, son da ta ke yi masa ya wuce yadda ita kan ta ta ke tsammani, don haka ba ta jin da akwai abinda zai dakatar da wannan auren na su, in dai daga ɓangaren ta ne, sai dai duk wannan tunanin da ta ke yi, ba ta taɓa kawowa cewa za’a samu matsala a tare da ita ba, ita ta na ji cewa komai lafiya ƙalau ta ke.
Sai dai rashin sani ya fi dare duhu in ji hausawa, tabbas da ace ta san me ke wurin wakana a rayuwar ta wanda masominsa zai fara ne daga wannan lokaci da ba ta samu damar tsayawa wannan tunanin ba, tabbas da ba ma ta yarda an yi wannan gwajin da ake gaf da kammalawa ba, sai dai shi ZAREN ƘADDARA ba ya tsinkewa, haka zalika komai GUDUN ƘADDARAR KA ba ka tsere ma ta, don haka ko da ta san abinda ya ke tunkaro rayuwar ta, babu yadda za ta yi.
Ta yi nisa a cikin tunanin ta, a daidai wannan lokaci ne ta ji ana kiran sunan masoyin na ta, Abba ne wanda ya ke gabatar musu da gwajin ya ke kiran sa, don haka tuni hankalin ta ya dawo jikin ta, sai dai abin mamaki batare da ta san meye dalili ba, ta ke ƙirjin ta ya fara bugawa da ƙarfi, ji ta ke kamar zuciyar ta za ta ɓullo waje saboda tsabar bugawa, wani abu da bai taɓa faruwa da ita ba kenan a rayuwar ta, da sauri ta rintse idanun ta ta na mai ƙoƙarin nutsar da kan ta, tare da nemo addu’o’i daban-daban tana mai karantawa ko Allah zai sa wannan rashin nutsuwar da ta dirar mata lokaci guda ta bar ta.
“MK” Abba ya ƙara ƙwalla kiran sunan na sa, sai dai tuni ya shagala da fira da samarin da ke kan katangar, sai dai shi a tsaye ya ke, suna tsokanar sa cewa yana gaf da shiga ciki.
“Don Allah, yi min magana da Mukhtar, ga shi can” ya nunawa wani mutumi shi, da alamu dai baƙo ne ko kuma dai ya nuna masa ne don ya gane shi da wuri.
Da wuri MK ɗin ya ƙaraso bayan an faɗa masa cewa ana kiransa, “Ya Abba, har an kammala ne” ya faɗi yayinda murmushim da ke kan fuskarsa ya ke shirin ɗaukewa.
“Eh, amma na yi tambaya, mana, wai ba auren wannan yarinyar za ka yi ba ne” ya ƙarasa maganar ya na nuna Munirah da har yanzu idonta ya ke a rufe, sai dai jin maganar Abban ya sanya ta buɗe ido.
MK cikin mamaki kamar ba zai bayar da amsar ba dai sai kuma ya bayar yana mai cewa “Eh fah, amma me ya sa ka yi wannan tambayar?”
Girgiza kai Abba ya yi batare da yin tunani ba, gaba-gadi kawai ya cigaba da magana yana mai cew “Ai abin da mamaki ne, na ga yarinyar ta na da ciki, har ma ya kusa wata biyu ina kyautata zaton, ko ma ya wuce hakan.”
Gaba ɗaya mutanen da ke cikin shagon tsit aka yi, yayinda a wannan lokaci da za ka taɓa ƙirjin MK ɗin da kuma Munirah da Allah ne kaɗai ya san irin bugun da su ke yi, ita Munirah kuwa sai da numfashin ta ya fara shirin ɗaukewa, sakamakon tsananin firgita da wannan maganar da bata taɓa tunani ba a rayuwar ta.
“Kenan ta ya hakan zata faru?, idan har da gaske ne, to ko dai ana shan ciki a ruwa ne? Ko kuma wata mu’ujiza ce da ita kamar sayyada Maryamu A.S mahaifiyar Annabi Isah A.S da za ta haifi ɗa batare da ta taɓa sanin namiji ba a rayuwar ta? Ko kuma a’a cikin na wani aljani ne? wannan sune tunane-tunanen da su ka cika fal zuciyarta, lallai dole a cikin wadannan dole ɗaya ya kasance, don dai ita a tsawon rayuwarta, ba ta san lokacin da wani namiji ya taɓa ko da hannunta ba ne.
Kallon ta MK ya yi, ganin halin da ta ke ciki ya yi matukar girgiza shi, don haka batare da ɓata lokaci ba, ya cakumo wuyan rigar Abban yana mai cewa “Kai don uwar ka, wa ya biya ka, ka yi mata sharri?” Kaitsaye ya fara sauke masa mari har biyu lokaci guda batare da ɓata lokaci ba.
Tuni hayaniyar su ta jawo hankalin mutanen da ke waje, Murtala ne ya fara shigowa shagon, wanda shine asalin mai Chemist ɗin kuma abokin MK ɗin, sai kuma saura su ka biyo baya, kafin nan tuni har Abban ya karɓi Marika sama da biyar, wuyan rigar sa kuwa ba don ƙarfin yadin ba, da tuni ya daɗe da yagewa.
Da sauri Murtala ya shiga tsakani, yana mai tambayar ba’asi, sai dai MK ɗin bai iya magana ba, kawai ya fice yana mai cewa da Munirah ta taho su tafi, shi kuwa Abba bakinsa bai rufe ba, cewa ya ke wacce yarinya ce ta isa na yi mata sharri, wannan kucakar yarinyar mai ƙirar maza, ka je kuma duk asibitin duniyar nan wallahi sakamako ɗaya za ka samu, shine tana da ciki, Allah ne ya san ma adadin mazan da ta yi mu’amala da su.
“Kai dakata, kai wanne irin mahaukaci ne, haka ake aikin likitanci, ba confidentiality ba sirri, kenan ya dace ko da wannan maganar ta ka gaskiya ce ka zo ka faɗe ta a gaban kowa da kowa, kai wallahi ban san mahaukaci ba ne ba sai yau.” Wata mata da su ke tare da Munirah ɗin ta faɗi, yayinda ta fara yunkurin lallashin Munirah ɗin da tasar da ita tsaye, domin fita kamar yadda MK ɗin ya buƙata, daga can kuma sai ta juyo ta ƙara cewa “kuma wallahi, ka san Allah da ni ce ka yi wa wannan zubar da ƙimar, ko da gaskiya ne sai na shigar da kai ƙara, tun da dai ba inda dokar aiki ta ba ka wannan damar.”
Daga nan ta miƙar da Munirah ɗin tana cigaba da ba ta baki, sai dai tuni hawaye ya mamaye fuskar ta, zuciyar ta tana yi mata zafi, tana da tabbacin tuni jinin ta yayi hawan da ya wuce 200/120 ko ma sama da haka ma, don tana da tabbacin a ko da yaushe jini zai iya haurawa ƙwaƙwalwar ta ta faɗi a wurin, kuka ta ke so ta fara sai dai sautin na shi ma ta san ba zai fito ba, ƙaramin tashin hankali a ke wa kuka, tashin hankalin da ta ke ciki kuka ba zai yiwu ba.
MK shi ma cije baki kawai ya ke yi, Allah ne kaɗai ya san abinda ke zuciyarsa, sai dai shi kasancewar sa namiji ba za ka iya ƙiyasta adadin tashin hankalin da ya ke ciki ba, sai dai ya ja ya tsaya a ƙofar chemist ɗin yana jiran fitowar ta, yayinda mutane duk su ka bishi da kallo, matsala ɗaya ma, wai da zai zo gwajin kawai sai ya zo unguwar su, tabbas a cikin kankanin lokaci, labari zai kai inda ba’a taɓa zato ba.
Fitowar ta ke da wuya, matar nan na cigaba da bata baki, kawai sai ya wuce zuwa ga mashin roba-roba ɗin sa, tare da tayar da shi ya juya yana jiran ƙarasowar ta, duka mutane an zuba musu ido ba wanda ya ke da shirin tankawa a wannan lokaci.
Suna ƙarasawa matar ta taimaka mata ta hau, daga nan bai tsaya ɓata lokaci ba, kawai ya ja mashin ɗin sa ya wuce batare da ya yi wa kowa magana ba, ita kuwa wannan matar komawa ta yi tana ƙara zuba musu masifa, da tabbatar musu da cewa da ita ce hmm, da sun yi mamaki, jama’ar wurin ma abinda su ke faɗi kenan, tuni, suna kuma nuna cewa gaskiya duk da su ba likitoci ba ne, amma sun san abinda aka yi ba’a kyauta ba, tuni jikin Abba ya yi sanyi, shi kuwa Murtala tagumi kawai ya yi, shi kansa tunanin matakin da zai ɗauka akan Abban ya ke yi, don bai taɓa tsammanin mahaukaci ne shi ba sai yau ɗin.
Game da MK kuwa kaitsaye asibiti ya nufa, ba don komai ba sai don ƙara jaddada gwajin da aka yi, don ya na ji a ransa cewa tabbas ƙarya ne, sharri Abba ya ke yi mata, a hanya ma abinda ya ke faɗa mata kenan, tare da tabbatar mata da cewa, ta kwantar da hankalin ta, za’a gano gaskiya, kuma zai ɗauki tsautsaran mataki akan mahaukacin yaron.