Skip to content
Part 5 of 9 in the Series Zinariya by Queen-Nasmah

Zango Na Biyar (Ƙara-Ƙara-Ƙara Ga Akuya Ga Kura)

Kwanaki uku aka kwashe a masarauta ana gwagwarmaya da Juhaina amma ta kafe. Sarauniya Jahiyana ta yi tafiya zuwa garin Gazmil domin ganin babbar bokanya Firmal.

Zinariya na kwance cikin raɗaɗi Hibshiyana ta shigo ɗakin ta durƙusa gabanta ta ce “Allah ya tashi kafaɗunki, ya ƙarfin jikin “, Zinariya da ba ta iya ko da ɗaga murya ne ta gaɗa kai, Hibshiyana ta kalli yadda fatar jikin Zinariya ta ɓare duk ta caɓe ba kyan gani kamar wadda aka yi ɓarin ruwan batir a jikinta, ta ce “Ranki ya daɗe kiyi haƙuri kar ki ce na cika matsanta miki, ba zan gaji wurin tunatar da ke addinin musulunci ba, domin garkuwa ne mai matuƙar ƙarfi a gare mu, babu wata halitta, mutum, aljanna, dabba, ko kuma wani abu da ubangiji ya halitta da ya isa ya ja da ƙarfin mulkin Allah, shi ne mai ba da kariyar da idan ya bayar babu wanda ya isa ya  baki ko da makamanciyarta ce, shi ne wanda idan ya hana babu wanda ya isa a duk duniyar nan ko wane ne shi ya ce e, shi ne wanda idan ya bayar babu mai amshewa, shi ne wanda ya ke ba da lafiya, kuma ya bada arziki, idan ya amince miki babu wanda zai ƙi ki, ki yarda ki karɓi addinin musulunci ke da kanki zaki ji daɗi “, babu wata kalma da Hibshiyana ta faɗa da bai ratsa jikin Zinariya ba, ta ɗaga baki zata yi magana Jamina ta shigo ɗakin, kai Hibshiyana ta saukar ƙasa ta ce “ranki ya daɗe Allah ya ƙara tsawon kwana”, hannu Jamina ta ɗaga mata, Hibshiyana ta miƙe tsaye tana faɗin “Allah ya baki lafiya ” ta juya ta fice.

Jamina ta kalli Zinariya ta ce “Mama Sarauniya ta dawo daga wurin bokanya Firmal, amma Zinariya ba haske, ba za mu iya dakatar da Juhaina ba”, a hankali tana jin ciwo ta ɗaga hannunta ta damƙo na Jamina ta runƙe Hannunta, hawaye suka gangaro ma Jamina saman kunci ta sa ɗayan hannunta da Zinariya bata riƙe ba ta share ƙwallar sannan ta kalli Zinariya ta ce “Abar bauta tana tare da ke, za ta baki kariya, yanzu haka Mama Sarauniya tana can gaban abar bauta tana kai kukanta, ki yi haƙuri zai wuce ” sai kuka ya ci ƙarfinta. Zinariya ta ɗaga baki a hankali can ƙasa-ƙasa ta ce “Hibshiyana”, Jamina ta waiwaya bayanta dan ganin ko Hibshiyana ce ta shigo ɗakin amma kuma ba ta ganta ba, ta juyo ta kalli Zinariya, Zinariya ta sake kiran sunan Hibshiyana, Jamina ta ce “me za ta miki “, Zinariya ta rufe idonta kaɗan wanda take ji da ma cire mata su aka yi ta huta da zugi da raɗaɗin da take ji, sannan ta buɗe su ta kallo Jamina ta ce “ki…. Ki kiraa mi..min..it…taa” Jamina ta jima tana ƙoƙarin fahimtar me ta ce, sannan daga baya ta fahimci so take a kira mata Hibshiyana, idonta ta rufe ta buɗe a take wata ƴar  ƙaramar  tsuntsuwa ta bayyana saman kafaɗunta, Hannunta ta sa ta kama ta  ta ce “ki je ka zo min da Hibshiyana” Jamina ta saki tsuntsuwar, ta tashi sama.

Juhaina ta kai ƙoluwa wurin ɗauka fansa domin kuwa a cikin wani dutsi take tsaface-tsaface, wasu manya-manyan duraruwa (drum) ne na ƙarfe ta cika maƙil da jini ta ɗora su a wuta sai tafasa suke yi suna kumburuwa kamar za su zube, ido ta ƙura ma ruwan jinin yayinda idonta ke canza launi ƙwayar idon na fitar da  launukan Ja, kore, da tsanwa,  ta ƙyalƙyale da dariya  sai kuma ta haɗe fuska kamar ba ita ke dariya ba. Ta fara zagayen duraruwan da ta cika da jini suna ci a da wuta tana zuba musu wani baƙin gari, a hankali jinin ya sauya yayi baƙi-ƙirin, maganar bokanya Kamila ta fara dawo mata a kunne _zaki sha , kuma ki yi wanka da ruwan jinin, sannan ki tunkare Gimatuwa tsirara ba kaya a jikinki, ki tabbatar kin kawar da numfashin duk wani wanda zai shige miki hanya, sannan ki tunkare ta ki kasheta, ki tabbatar bata numfashi. Idan ba haka ba zaki ƙasƙanta, kuma martabarki zata zube, kuma dole ki yi biyayya gare ta_.  “ina ba zan bar haka ta faru da ni ba ” ta faɗa, “ina a’a, ba zai yuyu ba” ƙwayar idonta ta canza launi zuwa ɗorowa sannan ya dawo ja, ta ci gaba da zagaye tana zuba baƙin garin da bokanya Kamila ta ba ta.

Tsuntsuwa na gaba Hibshiyana na biye da ita har suka isa ɗakin da Zinariya take, Hibshiyana na shiga ɗakin ta durƙusa gaban Jamina ta yi ƙasa da kanta ta ce “Ranki ya daɗe ga ni “, Jamina ta ce “Zinariya ke son Magana da ke”, Hibshiyana ta ɗago ta kalli Zinariya tare da matsawa kusa da ita ta ce “ga ni ranki ya daɗe  Allah ya dube ki ya dubi halin da kike ciki ya baki lafiya “, Hannun Hibshiyana ta kama ta riƙe  a hankali ta ce “na…. Na.. Kwa.. Umhmm” sai kuma ta kakare jini ya fara fito mata a baki, Hibshiyana ta ce “yi magana, yi ina jinki me kike so ki ce? “, Zinariya ta ƙara ɗaga baki tana magana amma babu abunda ke fita, jikinta ya hau kakkarwa, tana ta ciccira tana ƙanƙamewa, Jamina ta tashi da sauri ta dafe ta, Hibshiyana ta miƙe cikin zafin nama ta riƙe Zinariya tana faɗin “ La’ilaha illal lahu Muhammadur rasulillahi, sallal lahu alaihi wasallam.”

Juhaina kuwa ta gama dafa ruwan jinin ta ɗauko wata Ƙatuwar ƙwarya ta zuba ciki ta ɗaga kanta ta shanye su tas kamar yadda bokanya ta umarce ta , suna ƙunar jiki saboda tsabar zafi ta fara ɗiba tana zuba ma jikinta, tun daga kanta take zuba ruwan har su sauko ga jikinta tana ihu saboda tsananin zafi da azabar ƙunar da ruwan ke mata, haƙoranta duka sun zazzago har ƙasan gemunta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Zinariya 4Zinariya 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×