Skip to content
Part 2 of 20 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Cikin sigar firgici Anty Sakina ta ce, “Ke wai ni me yake damun ki ne? Me ya faru ne?”

“Haba Anty me kike fada ne haka? Na ce miki lafiyata lau, daga bacci fa na tashi shi yasa.”

Anty Sakina ta juyo da wani irin mugun kallon cike da ayar tambaya ga Usman, kallon nata shi ma ya yi tare da cewa,

“Wallahi bakya kyautawa duk kin bi kin takura wa yarinya da tambayoyi kamar ba ‘yar uwarki ba. Mutumin da ya yi barci ai dole ne jikinsa ya mutu ya ji babu kwari sai a hankali zai ji kwari.”

Anty Sakina ta maido da kallonta ga Humaira sannan ta ce, “Tashi ki wanke fuskarki ki zo na raka ki.”

Humaira ta kwarara jikinta ta mike ta shiga toilet ta wanke fuskarta. Ita ma gabanta sai faduwa yake, Allah-Allah take ta bar gidan. Tana fitowa ta dan yi kwalliya sama-sama. Anty Sakina ta ce da Usman, “Bari na raka ta titi.”

Fuskarta a daure take masa wannan maganar, ya mike ya shige cikin daki tare da kiran Anty Sakinar ta bi bayansa. Dubu daya (₦1,000) ya dauko ya ce, “Ga wannan ki ba ta tayi kudin mota.”

Anty Sakina ta ce, “Aa ka bar kudinka kawai zan ba ta, ina da kudi.”

Cikin daga murya Usman yavce, “Wai don Allah me kike yi haka ne? Tun da kika shigo na ga ranki a bace. Ko wani abin ne ya faru a gidan kitson?”

“Ni dai na ce ka bar kudinka kuma kada fito ka ce za ka ba ta da kanka, bana so na fada maka.”

“Amma gaskiya ba ki da adalci, ki hana a yi wa yarinya alheri, zuwan nata ba shi da amfani kenan.”

“Ka ga ya ishe ni haka daina daga mini murya, sai na dawo.”

Falon ta komo ta dubi Humaira ta ce, “Ke tashi mu tafi.”

Mikewa Humaira ta yi suka fice, fitowarsu keda wuya Anty Sakina ta sake bata rai sosai tare da cewa,

“Ke ki fada mini me Usman ya yi miki, karya kike ki ce gajiya ce ta saki barci, ban san ki bane?”

Kwalla Humaira ta fara yi tana cewa, “Haba Anty me kike fada ne, yanzu zargina kike yi? Na fada miki gaskiya kin ki yarda, ta ya ya zan zo gidanki na yi ba daidai ba, kin san hakan ba halina bane. Amma shi kenan kawai na daina zuwa tunda kin fara zargina.”

“Hmmm! Ba za ki fada mini gaskiyar ba, ya taba ki ko? Ita zuciya ba ta da kashi, haka kawai ba za ki yi bacci ba. Na san komai, to bari ki ji babu ruwana komai zai faru tunda kin ki fada mini gaskiya. Ni dake ne za mu yi maganin matsalar kafin abin ya fi karfinmu.”

“Na shiga uku, anty wallahi kin bani mamaki da har kika yarda zuciyarki ta darsa miki zargin zan aikata lalata, kuma na rasa da wa zan yi sai da mijinki. Insha Allahu na hakura da zuwa gidanki.”

“Humaira kenan ba za ki gane ba, ba zarginki nake ba. Wasu mazan da kike gani basu da tabbas, ba ke ba da kike matsayin kanwata, wani namijin zai iya yin lalata da kanwarsa da suka fito ciki daya. Ni abin da ya daga min hankali shi ne yanayin da na ganki a kwance a kan kujera, amma tunda kin ce babu komai shi kenan na yarda. Ki daina kuka ya isa, kin san ina son ki ne shi yasa bana son abin da zai taba rayuwarki.”

Haka dai Anty Sakina ta rarrashi Humaira har suka isa bakin titi, ta tsaida mata Adaidaita Sahu shata har gida ta biya kudin sannan ta kawo wasu kudin dubu biyar ta ce, “Ga wannan Mummy dubu uku ke kuma ki dauki dubu biyu, sai karshen wata zan zo gidan, ki gaida mini da su.”

Humaira ta karba hade da cewa, “To Anty na gode.” Mai Adaidaita Sahu ya ja suka tafi.

A kan hanya Humaira ta fara nadamar zuwanta gidan. “Babu shakka da Anty Sakina ta iske ni tare da Usman, da ban koma gida ba. Aiko insha Allahu ni da zuwa gidanta ma za a juma ba ta ga keyata ba, haka kawai mutum yana neman jefa ni cikin bala’i da masifa. Da ace na yarda ya zuba mini ruwan masifar nan, da ya gama cuta ta. Anty Sakina na da gaskiya, ta san halin mijin nata dan akuya ne. Daga zuwa na sai ka nemi ka lalata mini rayuwa, har da cewa wai kana sona, alhali kana auren yayata cikinmu daya. Lallai wasu mazan ƙudaje ne, babu ruwansu da haram

A zuciyarta take wannan maganar har mai Adaidaita Sahun ya isa da ita layin nasu, ta sauka ta shige gida.
*****

Wacece Humaira? Wacece Anty Sakina?

Kamar yadda kuka ji kuma kuka karanta, Humaira da Anty Sakina ‘yan uwan juna ne ciki daya. Wa da kanwa ne, su hudu ne a wajen iyayensu, Anty Sakina ita ce babba sai Humaira na bi mata, sai Haidar, koda yake tsakanin Haidar da Humaira akwai tazara mai yawa. Zainab ita ce ‘yar autarsu wacce take bin Haidar. Zaune suke a dan gidansu na rufin asiri dake unguwar Zaitawa ta cikin birnin Kano.

Mahaifiyarsu sunanta Sadiya, amma suna kiranta da mummy, ita ‘yar asalin garin Jigawa ce aure ne ya kawo ta garin Kano. Shi kuma mahaifinsu sunansa Alhaji Adamu mai goro. Dan kasuwa ne a kasuwar ‘yan goro ta Ujile.

Huamira za ta kai kimanin shekaru goma takwas (18) da haihuwa, tana ajin karshe a makarantar sakandiren ‘yan mata ta Masaka dake kofar mazugal. Humaira yarinya ce mai garin jiki, tana da tsayi da jiki sosai. Fara ce kyakkyawa akwai ta da kyakkyawar da sura mai jan hankalin ‘ya’ya maza, musamman dukiyar fulanin nan dake makare a kirjinta. Kallo daya lafiyayyen namiji zai yi mata, ya ji wani abu ya darsu a cikin zuciyarsa.

Anty Sakina, mata ce ga Usman kamar yadda ya gabata, ya aure ta shekaru hudu da suka wuce, har kawo yanzu basu haihu ba. Koda yake shi Usman din ne baya son haihuwar, magani hana daukar ciki yake bata ba tare da ta sani ba. Shekara daya da yin auren nasu bayan ta kammala karatunta na N.C.E a kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi, sai ta samu aikin koyarwa. Yanzu haka dai ita malamar makaranta ce.

Anty Sakina mace ce mai cikar kamala, tana da tsananin kula akan dukkan al’amura musamman wanda suka shafe ta. Dukkan abin da ta saka a gaba sai ta cimma shi da izinin Allah, bata taba fara abin da ta san ba za ta iya kammalawa ba. Kaifi daya ce, bata da boye-boye, sannan ta kasance mai matukar biyayya da girmama duk wanda ya girme ta.

Tsananin biyayyarta ne yasa ta amince har ta auri Usman, amma ba dan tana sonsa ba. Sam bashi da wani kyakkyawan hali ko kamalar da za ta so shi, cika umarnin mahaifinta ne da rashin son bata masa rai yasa alatilas ta aminta da auren Usman. Duk da kasancewar bata sonsa, hakan bai sa ta nuna masa wulakanci ba ko kuma ta rika bata masa rai. Sai idan ya yi abin da bai dace ba, takan nuna masa ya yi ba daidai ba ta hanyar da ta dace…

Shin to waye Usman kuma???

Cikakkken sunansa shine Usman Bala mai doki, koda yake tuni wasu daga cikin abokan aikinsa suka sauya masa suna, suke kiransa da….Dan asalin unguwar Jakara ne duk a cikin birnin Kano. Ma’aikacin damara ne wanda ake musu kirari da “Abokin kowa” igiya uku ce a kafadarsa.

Usman ya yi sa’ar mace salaha, amma ita kuma ba ta yi sa’ar miji ba. Tataccen dan bariki ne, club-club da gidajen magajiya har ma da gidajen barasa babu wanda Usman bai sani ba. Tun kafin ya shiga aikin damara yake wannan harkar barikin ta sa, bayan ya shiga aikin, sai likkafa ta cigaba domin tamkar lasisi ne ya samu na cin karensa babu babbaka. A da can abubuwa biyu ne suke takure shi a harkar barikin, wato rashin samun kudi da kuma kamen da ‘yan sanda ke masa. Yanzu kuwa ya samu damar yin duk abin da ransa ke so babu mai hana shi.

Duk macen da ya kwallafawa rai, sai ya yi duk yadda zai yi hakarsa ta cimma ruwa, sai ya ketara ta, ya bi ta kanta. Bashi da kunya ko kadan, koda *case* ne ya ritsa da wata macen kuma ya biyo ta hannunsa, to babu shakka sai ya yi yunkurin bayyana bakin kudirinsa ga wannan macen. Wasu lokutan idan case din ba ta hannunsa ya zo ba, indai ya ga macen zazzafa ce kuma tana da sakin fuska sai ya san yadda ya yi ya shiga cikin case din ko ma ya karbe case din gaba daya.

Baya ga neman mata kuma Usman kasurgumin kartagi ne, caca babu irin wacce baya yi. Cacar ful, cacar kati, kai har ma da wannan sabuwar cacar ta zamani wato Bet9ja. Wannan ta sa babu wani abu da yake albarka a hannunsa, kamar me rariyar hannu yake. Albashinsa mai nauyi ne babu laifi amma baya isar sa a kwanaki talatin, kafin a sake yin wani albashin ya shiga damuwa sai caca da karbar cin-hanci hade da maula a wajen mutane.

Usman ba mai laifi kawai yake kamawa ba, kowa da kowa kamawa yake, idan ya kama mutum ya rasa wane irin sharri zai lankaya masa sai ya bige da maula. Idan kuwa har ya kama mutum da laifi dumu-dumu, wohoho! babu shakka wannan mutum sai dai Allah ya kwace shi, cin-hanci zai yanka masa mai kauri, idan kuwa mutum ya yi tirjiya to la-shakka zai ga sharrin da bai taba gani ba. Allah ya isa ba a bakin komai take ba a wajen Usman, indai za ka bashi cin-hanci to duk Allah ya isar da za ka yi masa ka yi ta yi. Wannan kadan kenan daga tulin miyagun halayen da Usman ya tara.

*****

To ita kuwa Humaira ba jimawa ta isa gida, shigarta keda wuya ta iske mummy a kitchen ta fara shirin hada abincin dare. Canja fuska ta yi ta hau Humaira da da fada, “Wannan wane irin iskanci kike neman farawa, daga cewa za ki je ki kai littafi tun safe sai yanzu da yamma ta yi za ki dawo. Humaira, bana son yawace-yawacen banza da sakarci, zan yi matukar saba miki. Ki shiga hankalinki.”

Humaira dake tsaye ta yi tsamo-tsamo, tabe baki ta yi tare da cewa, “Mummy ba ki tsaya kin ji mai ya faru ba kawai sai ki fara yin fada, tambaya ta za ki yi mai yasa na dade ba fada ba. Gidan Anty Sakina fa na biya bata nan ta je kitso shine na jira ta fa, gashi ma ta ce na kawo miki wannan tana gaishe ku, kuma karshen wata za ta zo.”

Ta fada tana mika mata kudin da Anty Sakinar ta ce ta kawo mata, karbar kudin mummyn ta yi tare da cewa, “To ai ban sani ba domin ba ki ce za ki je can ba, kuma da kin yi min waya kin fada min kin ga ai da hankalina ba zai tashi ba.”

“To ki yi hakuri mummy insha Allah ba zan sake yin hakan ba, kuma wayata ce babu kati fa, kema kin sani.”

“Shike nan, ya ya Sakinar tana lafiya dai ko?”

“Lafiyarta kalau wallahi.”

“To madalla, bisimillah ko sai ki karbi aikinki, dama rage miki na fara saboda na ga marece ya fara yi.”

Dariya Humaira ta yi tare da cewa, “Kai mummy maimakon ki cigaba kawai tunda kin fara, yau nima na huta, koda yake shike nan barshi ma na tuna kada ki yi mana girkinku na mutanen da can.”

“Iyeeee ku ji ni da ja’ira, girkin mutanen da din kika ci har kika girma ko. Marar kunya.”

“Hahahah!  Ai dan ban sani bane lokacin ina karama da ba zan ci ba.”

“Hmm! Ja’ira mai surutun tsiya, haka kike da iya zance kamar za ki sauke sarki daga kan doki.”

Aikin girkin Humaira ta kama gadan-gadan duk da cewa tana jin kasala amma sai ta daure domin kada mummyn ta fahimci wani abin a tare da ita. Tana aikin tana zolayar mahaifiyar ta ta har magariba ta yi, mummyn ta yi alwala ta yi sallah.

 *****

Ita kuwa Anty Sakina komawarta gida keda wuya bayan ta raka Humaira, Usman ya tare ta da cewa, “Ki rika yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi, yanzu kishin naki har ya kai ki rika zargina da kanwarki, Allah ya kyauta.”

“Malam kai ka fahimci abin ta wannan fuskar, ni ba zarginka nayi ba. Kai ma ai ka san bai kamata ka ajiye ta ba, kamata ya yi tunda bana nan kawai ka sallame ta ta wuce.”

“To wai me ma ya kawo wannan zancen, kawai dai zargina kike, dama kin riga kin saba.”

“E ka je a zargin naka nake, idan nayi zarginka ai ba laifi nayi ba domin na san hali ne.”

“To ya ishe ki dakata haka, ko kuma yanzun nan na saba miki kamanni, marar mutunci kawai shashasha marar tunani. Kuma bari ki ji baki isa kin goga min bakin jini ba a cikin danginki, saboda haka ko gobe Humaira ta zo gidan nan bakya nan, ba zance ta tafi ba, ni ba marar mutunci bane irinki.”

Yana gama maganar ya ja tsaki tare da mikewa ya shiga toilet ta yi wanka ya fice dgaa gidan, bai zame ko ina ba sai sabon gari. Nan ya bar Anty Sakina ranta ya yi matukar baci, zuciyarta cike da tsananin damuwa. Babu shakka tana karfafa zargin lallai akwai abin da ya gudana tsakanin Humaira da Usman din, kawai dai yarinyar ta ki fada mata gaskiya ne gudun me zai faru.

<< Ƙuda Ba Ka Haram 1Ƙuda Ba Ka Haram 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×