Skip to content
Part 4 of 18 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

To tun shigar Humaira Adaidaita Sahu, ta fara juya maganganun da Usman ya fada mata. “Gaskiya wannan babban al’amari ne mai hadari fa, duk ranar da asirina ya tonu ban san yadda su mummy da Abba za su mini ba. A gaskiya ba zan sake sauraren Usman ba, ko ya kira ni babu inda zan je. Haba ke kuwa Humaira, to mene ne idan kin je, tunda dai ya ce ba wani abu zai riƙa miki ba na cutarwa ai kin ga da sauƙi. Shi ma ba zai taɓa yadda ya yi miki ciki ba, kuma yanzu ki duba ki ga kuɗin nan da ya ba ki, ga su a hannunki, ‘yan matsalolinki duk za su warware. To amma idan na amince da buƙatarsa, a ina za mu riƙa haɗuwa da shi ke nan, ga shi Anty Sakina ta ce kada na sake zuwa gidanta idan ba ta nan, koda yake ya ce ya san yadda zai tsara komai.”

Wasu zuciyoyi biyu ke nan da dake ba wa Humaira shawara a cikin zuzzurfan tunanin da take yayin da mai Adaidaita Sahu yake ƙoƙarin kawo ta gida. Ɗaya zuciyar kyakkyawa ce, ɗayar kuma mummuna ce, Shaiɗan ya baibaye ta.

Kuma da alama mummunar nan ce ta yi rinjaye a kan kyakkyawar. Ma’ana dai Humaira ta biye wa ruɗin Shaiɗan da son zuciya. Hausawa kuwa sun ce, “Son zuciya ɓacin ta”, Allah ya raba mu da son zuciya, Allah ya kiyashe mu aikin assha.

Babu jimawa mai Adaidaita Sahu ya iso da ita layin nasu, ta sauka tun kafin ya ƙarasa kofar gidan, ta isa da ƙafa har zuwa gidan.

“Har kin dawo da wuri haka, ashe ba jimawa za ku yi ba. To ya ya ina fatan dai babu matsala ko?”

Mummy ce ta yi wa Humaira wannan tambayar bayan Humaira ta shiga gidan, amsa mata ta yi da cewa, “E wallahi babu wata matsala komai ya yi daidai, an ce ma an kusa yin admission, idan Abba ya dawo zan faɗa masa ya ba ni kuɗi zan yi wasu ‘yan saye-saye kafin mu fara lecture.”

“Kai Masha Allah, Allah dai ya taimaka Allah ya ba da sa’a. Addu’a za ki yi Allah ya sa ki samu admission ɗin tukunna ba wai batun saye-saye ba. Samun gurbin karatun shi ne mai wahala.”

“Mummy ai results ɗina mai kyau ne, credits tara (9) fa gare ni, kuma a JAMB ina da maki (215), admission kamar da ƙasa ne in ji mai ciwon ido, Insha Allahu mu ne sahun farko.”

“To Allah ya tabbatar. Wai to ya ma za a yi da maganar Najib ne?”

“Mummy ke nan, ke ma da mayar da hannun agogo baya kike, mun riga mun gama magana da shi ya ce, ba zai iya barina na je makaranta ba bayan ya aure ni, don haka ya amince zai jira ni har sai na kammala to ba shivke nan ba sai ya jira ɗin. Rashin yarda ce ma ya nuna da zai ce ba zan je makaranta ba, bayan duk ga matan aure ne suna zuwa makarantar, wasu ma mazan nasu ne suke kai su kuma su koma su ɗauko su, amma shi ba zai yi ba, yana namiji sai kishi.”

“Yo ai yana da gaskiya, domin gurɓacewar zamani ne ya kawo hakan, kuma abin da ake so shi ake nuna kishi a kansa. Idan har ba ya son ki to ba zai taɓa nuna kishinki ba, sai ya ƙyale ki ki je ki yi koma mene ne. Wanda duk ba ya kishin matarsa ma ba mijin aure ba ne, domin babu tabbas ya iya kare miki martabarki.”

“Hmm! To ai ko sai ya je ya yi ta kishinsa, rashin wayewa ce kawai ke damun sa, kamar wani ɗan ƙauye ko irin mutanen da ɗin nan masu duhun kai. Kwata-kwata ba ya gane rayuwa ta sauya kai ya waye yanzu.”

“Rayuwa ta sauya ta rashin mutunci da rashin kunya ba, wallahi Humaira ki kiyaye ni. Ki guji ruɗin zamani da kururuwar shaidanu. Abin da yake daidai har abada sunansa daidai, abin da yake kuskure ne shi ma har a naɗe ƙasa yana nan a matsayin kuskure, komai yawan masu aikata shi ko kuma ganin kyawunsa ba zai canja ba.”

Humaira ta ɗan ɓata rai tare da zumɓurar baki, alamun zancen da mummyn take mata ya ishe ta, zai fi kyau ma su canja hirar. Don haka sai ta ce, “Mummy me za a dafa da rana ne?”

Hararar ta mummyn ta yi sannan ta ce, “Au nasihar da nake miki ce ta ishe ki, shi ne kika kau da zancen kika kawo wani daban, to Allah ya ganar da ku gaskiya. Duk abin da kike dafawa da can ni nake zaba muku ko kuwa kuna neman shawarata. Ku ne masu zaɓin abinci, ni duk abin da Allah ya ba ni ina so kuma ina masa godiya.”

“Mummy ke nan, yau dai rigima kike ji na ga alama Allah ya huci zuciyarki. Bari zan miki naki girkin na musamman don ki ji daɗi.”

Mummy ta yatsina fuska tare da cewa, “Kamar da gaske.”

Dariya Humaira ta yi sannan ta ce, “Da gaske ne mana, ki faɗa mini me kike so na yi miki? Ke zan fara girkawa ma.”

“A’a ni ba na jin yunwa, ki fara yi muku tukunna idan kin gama sai ki yi mini tuwon alkama, bari na tura Haidar ya sayo mini kuɓewa ɗanya.”

“To shi ke nan mummy bari na tashi.”

Tana faɗa ta mike ta shiga kicin ta fara haɗa musu abincin rana, dafadukar fatan doya da wake ta yi musu mai matukar daɗi. Kafin ta kammala tuni an haɗo kayan tuwon alkama, an yo cefanen miyar kuɓewa kamar yadda mummyn take buƙata. Humaira na sauke tukunyar girkinsu ta ɗora na mummy, tuwo da miya a lokaci ɗaya, da yake da gas mai uku suke amfani. Babu jimawa ta yi tuwon da miyar ta gama, ya yi matukar kyau ga kamshi sai tashi yake. Miyar kuɓewar ma ta sha kayan haɗi da mai wadatacce da ɗanɗano sannan kuma ga mana da aka saka wanda ya karawa miyar zaki sosai.

Humaira gaza cin fatan doyar ta yi, tuwon ita ma ta bude ciki ta kwasa sosai, ta ci me isarta. Mummy kuwa tsokanarta ta rika da cewa, “Yanzu da cewa nayi nayi tuwon za’ayi gaba daya, ke ce ta farkon cewa ke ba za ki ci tuwo ba, amma yanzu gashi an zauna kalam-kalam cinye min abinci saboda kwadayi.”

Dariya Humaira ta yi sannan ta ce, “Haba mummy dandanawa fa kawai nayi na ji ko ya yi dadi.”

“Lallai kam na yarda dandano kika yi, duk wannan uban tuwon da kika share a cikinki a dandano yake, to madalla. Tashi ki zubo fatan doyar ki zo ki ci mu gani.”

Dariya hunairan ta sake kwashe da ita ba tare da ta ce komai ba.

Haka halin Humaira yake duk lokacin da ta bata wa mummy rai ko kuma ta ga ranta a bace sai ta san yadda ta yi ta kauda mata bacin ranta, I walau ta hanyar yi mata wasu aikace-aikacen ko yi mata girki na musamman ko kuma ta dauko wata hirar nishadi tana zolayarta har sai ta ga ta fara sakin fuska tana fara’a.
*****
A bangaren Anty Sakina, da rana ta yi, ragowar taliyar nan ta dafa ta ci da sauran miyar da ta rage musu. To da yake shi Usman aikin rana yake zuwa yamma, misalin karfe 12:00pm na rana ya shirya ya tafi wajen aiki, bai ci abincin ba. Sai da marece ya dawo gidan, shiru-shiru bai ga an kawo masa abinci ba kamar yadda ya saba gani. Sai ya kada baki ya tambaya, “Ina abinci ne?”

“Yana inda ka ajiye.”

Anty Sakina ta ba shi amsa tana daga kwance ba tare da ta daga kai ta dube shi ba. Kai kawai ya jinjina bai sake cewa da ita komai ba ya juya ya shiga kitchen din. Ba abinci ya tafi nema ba, domin maganar da ta fada masa ta nuna cewa ba ta yi abincin ba. Lemo ya tafi daukowa a fridge, yana budewa ya ga wayam babu komai, ta kwashe duka ta boye shi, ruwa kawai ta bari. To dama duk wadannan kayayyakin lemon ita ce take sayo su da kudinta, kusan dai ita ce ke rike da gidan. Babu wani abu da yake tsinanawa sai faman kiran babu, kamar beran masallaci.

Kai ya sake jinjinawa bayan ya ga babu komai a cikin fridge din, wani kududun bakin ciki ne ya taso masa daga zuciyarsa ya zo makogwaro ya tokare. Kamar ya rufe ta da duka yake ji, amma babu dama domin kayanta ne kuma ba ta yi laifi ba.

Daki ya koma ya kwanta sai bayan Isha’i ya shirya ya fice daga gidan kamar yadda ya saba. To da yake yana da agenda da yarinyarsa Blessing, bai damu ba sosai. Yana fitowa daga gida, kiranta ne ya shigo wayarsa, yana dagawa ta ce, “Usman I dey waiting for you naw, pls don’t disappoint me.”

“Haba dear calm down I’m already on my way, just give me some minutes. Which room you dey naw?”

“I dey for room No. 35.”

Babu bata lokaci Usman ya isa hotel din yana shiga dakin Blessings ta rungume shi tare da cewa, “Welcome my baby, how una dey.”

“Thank you.”

Ya fada tare da zama gefen gadon, manne take a jikinsa, sumbata ya yi mata sannan ya ce, “Food or drinks”

Cike da shagwaba ta ce, “Drinks, I no dey feeling hungry.”

Landline ya kira ya yi order aka kawo musu abinci da kayan drinks, har da giya, koda yake Usman baya shan giya, amma zina caca wannan duk aikinsa ne, Blessing ce ta kwankwadi barasar. Shi kuwa sai ya ci abincin dama da yunwa ya bar gida. Bayan ya gama cin abincin, ita ma Blessing ta durawa cikin ruwan barasa, sai ya mike ya rage kayan jikinsa ya kwanta bisa gado. Ita ma abin da ta yi kenan, ta haye kan gadon suka fara romancing, daga karshe kuma suka aikata masha’a.

A wannan rana Usman bai ma dawo gida ba, can ya kwana tare da Blessing, sai da gari ya waye sannan ya dawo. Shi a tunaninsa ya yi hakan ne domin ya rama abin da Anty Sakina ta yi masa na hana shi abinci.

Allah sarki, ita kuwa Anty Sakinar gaza bacci ta yi, da yake tana yin sallar dare, a wasu lokutan tana cikin yin sallar yake shigowa, wasu lokutan kuma sai ta idar tana lazimi zai shigo. To a yau bayan ta idar da sallar ta yi tsammanin dawowarsa amma shiru bashi babu labarin, kusan karfe daya da rabi na dare (1:30am) har zuwa karfe biyu (2:00am). A nan ta fara tunani ko lafiya kuwa, wayarsa ta kira amma a kashe take, nan da nan hankalinta ya fara tashi domin bai taba kaiwa wannan lokaci a waje ba. Duk da kasancewar yawon dare sana’arsa ce, amma dai duk rintsi idan karfe daya ta kawo jiki zai komo gida.

Tana nan zaune bisa sallaya idanunta sun bushe babu wani alamar bacci. Sake-sake kawai take, a ranta har karfe 3:00am na dare, lokacin ta fidda ran ganinsa a wannan rana. Karfe hudu na asuba shiru 4:00am shiru, har aka fara kiran sallah farko. Misalin karfe 4:30am ta mike ta shiga toilet tayi brush, sannan ta dauki furar da ta dama domin ta yi Sahur, da yake tana yin azumin ranakun Alhamis da Litinin. Ba wani shan furar ta yi sosai ba, bayan ta gama misalin karfe 5:00am aka fara kiran assalatu.

Mikewa ta sake yi ta dauro alwala ta zo ta gabatar da raka’o’i biyun Raka’atainil Fajr, kafin ta gama wasu masallatan sun tada sallar asuba. Tana idar da nafila sai ta dora da farilla. Cikin sujjadar raka’ar karshe, ta jima tana addu’ar Allah yasa dai lafiya, Allah kuma ya shirye shi….

<< Ƙuda Ba Ka Haram 3Ƙuda Ba Ka Haram 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×