“Lafiya lau take mama kwantar da hankalin ki yanzu ma zaku wuce gida da ita saboda babu gado shiyasa zamu sallame ta tunda Babu wata matsala kuma anyi mata allurai da magunguna sai dai hutu kawai da zatayi don tana bukatar hutu kamar awa biyar tana bacci abun ne da yawa amma da nan zamu rike ta har ta huta yanzu aka gama mata wanka tana shiri ne bari na taho muku da ita.
Nas din ta koma suka fito ita da Nadiya wacce tasha wankan ruwan zafi ga hasken jego tayi Shar da ita.
Ade ce ta fara tarbar ta tana mata barka ta amsa ba yabo ba fallasa yayin da haj ke mata barka ta rungume mama tana fadin
“Mama nasha wuya haka dama ake haihuwa? ni kam ban zaci zan rayu ba nayi zaton mutuwa don ina ta cewa a yafe mini wadan nan yaran bana son su bana kaunar su mama.
Da sauri haj Aliya ta buge mata baki tana fadin
“To kwashe su ki kai Rijiya ki zuba marar mutunci .
Suka fito haj tana ta zuba fada tamkar ta make Nadiya inda Kaisar ya fito mota yana karbar yaran dukan su ya rungume yana fadin
“Mama na kira Daddy na fada masa mun samu identical twins yayi murna yace in ya gama da wuri zai shigo ko an yi sallama ne,?.
“An sallame ta Kaisar.
ganin mama a fussce yasa yace
“Mama wani abu ya faru ne? .
“Barni da yar iskar yarinyar nan tana son kaini karshe ne saboda bata da mutunci har ni take fadawa bata son Ya’yan nan a bata son su tayi cikin su.
“Ni Ina son su mama in ma tace ba zata shayar da su ba duk zan iya.
“Ai batayi wannan isar ba don uban ta taci uwar karya ta kwana da yunwa.
Da haka suka shiga mota Kaisar taja su zuwa gida.
Da sauri abdulhameed ya balle marfin motar ya fita ya bar Tero a motar yana watsa yan kayan karawa sama jannaty.
Haj laila taka zaune a falon tana waya abdulhameed ya shigo da saurin yana zama kusa da ita ya fito da wayar shi yana fito da hoton yaran nan yayi zoomed din sa sosai ya dora wa haj laila wayar a cinyar ta.
Da sauri ta katse wayar tana daukar wayar tana duba hoton wanda ya yi mata sak lokacin da Abdulhameed din yana jariri.
“Da cikin yarinyar nan ya Isa haifa abdulhameed da nace wannan yaron bo tantama banayi dan ka ne.
“Yanzu mom kar kiyi tantama don an haife cikin nan kuma abin mamakin ma twins ne mom .
Da sauri haj laila ta mike tana fadin
“Kai da gaske kake ko kuwa wasa Abdulhameed? Twins Abdulhameed??.
“Da gaske mom dubi dayan hoton zaki gane twiins ne.
ya karbi wayar yana jera mata hotunan ta kuma yarda musamman da ta gansu rike a hannun haj Aliya.
“Amma dai kai wawa ne abdulhameed yanzu duk kaga hakan amma ka kasa yin hikimar kira na ko ka kira distinguish? yanzu a wace asibiti ce akayi haihuwar?.
“Suna health care ne.
Da sauri haj Laila ta kira wayar distinguish Mukhtar biro tana fadin
“Distinguish kaji yarinyar nan ta gidan iro ta haifi twins baby? wallahi yanzu yake fada min .
“Ai fa yanzu zan Isa asibitin da tayi haihuwar kaga sai na taho da Ya’yan twins fa? to mu hade a can .
ta datse wayar tana fadin
“Tashi muje ka kaini na ga Ya’yan na kuma ji yadda zamu kare don wallahi sai sun bayar da Ya’yan nan ko basa so don zan nuna musu karfin iko irin na uban ka wanda yake da dama mai yawa a hannun sa duk iskancin da iro yakeyi saku saku mukayi mishi bai ji dauri bane amma in masara taji wuta da kanta take fashewa.
Tero yana mota yaga fitowar Haj laila tare da Abdulhameed don haka ya san asibitin zasu koma sai kawai ya tashi motar suka auna a guje yana fafarar motar.
Keena tana gaban malamin wanda surayya tace taje ta fada mishi matsalar ta in sha Allah zaiyi mata kokari don keena ta kasa biya ayoyin karya sihirin shine surayya ta hada ta da wani wanda tace mata babu kaucewa a aikin shi
Ya miko mata rubutun a galan kafin ya ce mata.
Ki nemo zam zam sai ki nemi lemun tsami guda dari da goma sha hudu a yanka shi biyu sai ki zuba ruwan rubutun nan da robar ruwan zamzam a ciki Kusha ku kuma shafe jikin ku ke da wannan mutumin har tsayin sati biyu in sha Allah kafin cikar satin biyu zakuyi mamaki komai kenan sai kizo ki sanar da ni in da akwai wani Abun yin sai a kara yi
“to malam nagode sosai Allah ya biya da aljanna meye abinda za a bayar?.
“Abin biya kiyiwa ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam salati adadin da zaki iya sai kuma sadaka ko ta abunci ko wa k’ana nan yara irin alawa ko wani abu dai sune kawai amma kudin aiki bama karba in dai anji dadi an samu biyan bukata to daga Allah ne ba daga mu ba sai a gode mishi ayiwa manzon sa salati.
Keena tayi godiya sosai ta kuma gamsu malamin babu zarmiya a aikin sa
tayi mishi sallama ta nufo hostel din su tun a nesa kuwa take hango motar malam Ango yana Dakon zuwan ta
ta Isa da sauri shima ya fito mota yana mata tarba .
“Sannu da zuwa sakeena kwana biyu ina cike da tashin hankali ban saka ki idona ba kin guje min na san saboda nacin da nake miki ne ko? to kiyi hakuri ba laifina bane laifin zuciya ta ne nima ba dadin hakan nakeji ba Ina fatan Allah ya yankee min ko zan huta don al amarin ya soma tab’a ibada ta kullum bani da aiki sakeena sai tunanin ki da neman me zanyi miki na farantawa Rayuwar ki.
Hawaye suka biyo fuskar keena wacce tausayin malam Ango ya kamata matuka gaya musamman da ya fada mata halin da yake ciki har da ibadar shi al amarin ya tab’a anya kuwa Allah ba zai kamata ba very soon?.
ta goge hawayen ta tana fadin
“Kayi hakuri don Allah kaji ? nima ba dadin hakan nake ji ba Al amarin ne yaxo da akasi don Allah ka yafe min.
“Ke babu fa komai Allah yayi mana mafita.
“Ka sani nayi wani abu ne da niyar ya fada kan wani sai ya fada kanka amma har ga Allah nayi kaicon haka amma in na baka wani abu zaka yi amfani da shi ? Ina fatan sauki ni da kai akan wannan al amarin.
“Me zai hana kuwa? wallahi zansha Ina so .
ta mika mishi dayan galan din wanda tace sai ya nemi lemun tsami da ruwan zamzam
ta fada masa yasha ya kuma shafe jikin shi na karya sihiri ne har tsayin sati biyu
Ya amsa Yana godiya sukayi sallama ya wuce itama ta shige hostel tuy daga ranar da batawa malam Ango maganin bata kuma ganin shi yazo ba abinda ya tabbatar mata da al amarin malamin azimun ne don ita kanta ta soma jin canji matuka gaya.
Daddy yana rike da jariran yana musu ADDU A yayin da yayiwa Nadiya fatan alheri ta shige daki zata kwanta haj Aliya ta kawo mata farfesun naman kaji mai romo ta sha kafin Ade ta kawo mata kunun kanwa wanda yaji kayan kamshi da zuma
Haj ta tsare ta sai da ta cika cikin ta kafin ta nika Mata jariran tana fadin
“Suma sallame su da nonon su duk da na kula Ubangiji ya baki masu hakuri wata kil ya duba yaga uwar su ba mai I’mani bace shiyasa ya rabautar da su da hakuri to ba dai anan ba kam ko zaki zalunce su in sha Allah ba dai Ina kallo ba inda ma bana kallon zan barwa Allah ya zama makarin su
ta karbi yaran ba don taso ba ta kai su ga nonon ta suka kama suna finciko shi ta kuwa kwalla ihu saboda zafin da taji tana shirin cire shi haj tace bata isa ba wallahi
haka ta tsare ta har tayi feeding din su duka suka barta da zugin kirji
ta kwanta bacci ya fige ta yayin da haj ta kwashe yaran ta kaiwa Daddy wanda yake rike da su Kaisar ya shigo yana fadin
“Daddy kaga kudurar Ubangiji ko? twins a gidan nan.
Alh iro ya mika mishi su yana fadin
“Lallai kudurar Ubangiji Kaisar shiyasa duk abunda ya samu bawa na dadi ko na akasin sa to ya godewa Allah don bai san rahamar da ya saka a ciki ba. Ungo yaran nan kaine mai musu huduba Kaisar Kaine mai zaba musu suna don duniya idan suna da mai musu kara to Kaine ko akan zaryar kai uwar su asibiti da Kuma kokarin da uban su ne kawai zaiyi abinda kayi bai kuma yi ba don haka Kaisar wadan nan ya’yan kaine mai su kaine mai iko da su karar ka garesu ta Isa ta baka su don haka ni din na baka su maza kayi musu huduba ka kuma zaba musu suna.
Wani irin farin ciki ya ziyarci Kaisar ya karbi yaran yana fadin
“Daddy ga babban nan kawo shi na fara mishi huduba daddy kaga ta inda zaka rika gane su ta wannan tabon wannan shine babba wannan kuma shine karamin
“Nagode sosai daddy da wannan alfarmar na kuma gode .
Ya yiwa yaran huduba inda yace wa daddy ya bar musu sunan su na al hassan da al hussain amma yayi musu lakabi da sha aban da kuma Ramadan kasancewar an haife su a cikin wata sha aban.
Daddy yayi murmushi yana fadin
“Madallah da kai Kaiser madallah kuma da al amarin ka Allah ta ala ya jikan iyayen ka yayi musu Rahama yasa suna dausayin Aljanna.
Kaisar ya amsa da jin dadi matuka gaya.
Haj laila da su teero suka iso asibiti inda suka soma tambayar mai haihuwa amma aka rasa Gane wacce suke nufi sai da Abdulhameed yace wacce ta haifi yan biyu a nan ne nas din da ta karbi haihuwar Nadiya ta sanar da su an sallame ta ta wuce gida saboda babu gado ne sai ana sallama ba sai anyi hutu ba.
Haj laila ta na fada tana cewa abdulhameed yayi wauta da bai sanar da ita tun wuri ba gashi har sun koma gida amma can gidan ma zata bisu ta karbo jariran.
Distinguish Mukhtar biro ya iso asibitin kamar wanda aka koro yana fatan ya dora Ido akan identical twins din da aka ce mishi ya’yan abdulhameed ne.
Anan Haj laila ke fada mishi an sallame su sun wuce gida .
“Bisu har gidan laila ki karbo min ya’yan nan tunda har ta haife su to yanzu ne wasan mu da iro zai soma don wallahi wannan karon sai ya bayar da kai jeki idan kika ga zai ja miki zance ki dawo ni na iske shi . cewar distinguish Mukhtar biro wanda ya juya ya bar asibitin yayin da Tero ya ja motar tare da haj laila suka nufi gidan Alh iro. Cike da mamaki haj Aliya take duban Kaisar da yake nuna mata akwatunan jariran na baby care akwatu biyu cike da kayan jarirai foreign one masu tsada tun daga mai lotion da oil zuwa hoda da riguna da famfas kai komai an hado masha Allah.
Haj Aliya ta dube shi cike da tausayawa idon ta yana tara kwalla take fadin
“Kaisar ? ka manta da yadda aka sami yaran nan ne ? ka manta da ba aure ne ya bayar da su ba kake ta hidima haka kamar dai ace jinin ka ne kakewa wahalar nan?.
“A a mama don Allah kar ki zamo wacce zata rika tunawa yaran nan asalin su Mama. ban manta ba amma ni a idona basu da wani datti ko zunubi wannan yana wuyan uban su da yayi amfani da damar sa yayi abinda yayi . Naji na gani mama Ina son yaran nan har a raina ya’ya na nake kallon su in ance waye uban su nine zan daki kirji nace nine.
“Allah ya taya ka rikewa Kaisar ai kuma ni na sallamawa karimcin ka da jajirtacciyar zuciyar ka Allah ta ala ya yi maka sakayya da mafiyin alheri.
“Ameen ameen mama nagode. ni kam yau naga Daddy tunda sassafe yana shiri mama Ina ya tafi.
Mama tayi murmushi tana fadin
“Daddy yau ya tafi gombe ne Kaisar na san yanzu ma sun kai shi da malam Ango sukayi tafiyar.
“Ayya Daddy yau yaje Billiri kenan mama? si kuwa da na san zai tafi da na bashi sako ya kaiwa yar tsohuwa Baddo amma nayi mishi uzuri wata kil yana sauri ne amma nima naso zuwa mama Allah ya dawo dasu lafiya nayi kawar mutanen gombe .
“Kar ka samu damuwa Kaisar in ya dawo sai kaje tafiyar ta gaggawa ce shiyasa ma baiyi maka magana ba yaga kana ta hidimar yan biyu ne don ya san ba lallai ne ka yarda da tafiya Billiri a yanzu ba.
“Eh kuma gaskiya mama har da wannan ma don na soma sabawa da sm baki ga suma sun fara gane ni ba? .
“Ai kuwa na gani Kaisar.
cewar mama da tayi maganar tana dariya.