Bai ce mata komai ba shima ya shige na sa ɗakin a ransa ya na jinjinawa kishin Amera, domin yasan dai idan ba kishi ba yaya za'ayi ta ce wai Haura zata iya cewa bata sonsa, ai wannan maganar banza ce, ta san yadda kuwa haura ta ɗauke shi da har take tunanin zata iya cewa bata sonsa, Allah dai ya kaimu gobe zai bata mamaki, idan ma ta kama kawai auran za'a ɗaura ko a cikin satin nan ne, ba sai ya bawa kansa wahala ba, domin dai shine mai ba da auren kuma shine mai kar. . .