Tsabar fargaba da saurin da yake na ganin ya shigo cikin makarantar domin ganewa idonsa abin da ke faruwa har ƙoƙarin bi ta kan wasu ɗalibai mata ya yi ba tare da ya ankara ba. Tsakanin get ɗin da cikin makarantar ma a kwai tafiya mai ɗan tsayi, hakan yasa yana shiga ciki da motar tasa sai yaga wani malami ne a gefe yana magana da wasu dalibai shine dalilin da yasa yaga sauran ɗaliban suna leƙawa. Yana gyara pakin ya fito da sauri ya nufi cikin makarantar ba tare da yayi wa kowa magana ba. Ofis ɗin sa ya fara shiga ya duba baiga wayar tasa ba, hakan yasa ya fito da sauri ya nufi class ɗin da abun ya faru.
Koda ya shiga ɗalibai uku kawai ya gani a ciki, suka tashi suna gaida shi cike da mamakin ganinsa a irin wannan lokacin da sunsa ba shine zai karantar dasu ba. Bakin allon karatun yaje ya tsaya yana satar kallon gurin da abun ya faru a yammacin jiya. Sai dai bai ganta ba kuma bai ga wayarsa ba. Sake mayar da hankalinsa yayi izuwa gurin nan ma babu ita babu wayar. Duk da haka bai gamsu ba sai ya nufi gurin ya ɗan wayance harda sunkuyawa yana dubawa. Daidai lokacin kuma ɗalibai kusan su goma suka shigo cikin ajin mata da maza ana dariya, wasu ma zancen banza sukeyi.
Jin haka yasa ya ɗago da sauri yana mamaki to me ya faru. Yana ji suna gaisuwa amma yasa kai ya fita duk jikinsa yayi sanyi. Ɗaliban suka bisa da kallo suna ta mamakin yanayinsa, ko dan irin wankan da suka saba gani a tare da shi yau babu. Ofis ya koma ya zauna sai ya fara tunanin to ko dai ba mutuwa tayi ba, ai kuwa idan bata mutu ba dole yau zata zo school kenan. Hakan yasa faɗuwar gaban nasa ya ragu yana so sai karfe goma zai koma class ɗin ko zai ganta. Haka yaci gaba da zama a cikin ofis ɗin har karfe goma sannan ya fito ya nufi class ɗin amma yaji an kira sunansa ta baya. Kaman a tsorace ya waigo yana sauke idonsa akan wani malami wanda tun zuwansa school ɗin dashi suke ɗan gaisawa sama-sama. Ya ce “Malam Habib dama class ɗin safe kake dashi yau?” Habib ya ɗan sosai kai ya ce “Amm da kawai na zo gurin wani malami ne zan amshi abu, yanzu zan tafi” ya faɗa kamar a rikice. shi kansa Malam Ali ya fahimci kamar dai wani abu na damun sa. Ya ce “Ok Tom bari na shiga nawa class ɗin lokaci yayi sai na fito zan zo ofis ɗin na same ka” yana faɗa suka sake yin hannu Malam Ali ya tafi, shima Habib ɗin ya kama hanya.
Yana zuwa bakin class ɗin shi kuma malamin dake ciki zai fito hakan yasa ya yi saurin mika masa hannu suka gaisa. Ya shiga ɗaliban suka gaida shi. Nan ya fara raba ido ko zai hangonta. Gurin da take zama ya kalla yaga babu kowa a gurin, sannan ga wannan ƙawar tata da suke zuwa makarantar tare. Kaman ya kirata ya tambaye ta amma yana tsoron kar yaje daga yin tambaya ya tono wani abun. Haka ya wayance da tambayarsu wani abun daban sannan ya fita daga class ɗin. Wannan karan kam sai da suka buɗe fagen hirar Malam Habib, wasu na tambayar me yake damunsa, ko dai yana neman wasu dalibai ne jiya. Duk ya koma wani iri daga jiya zuwa yau, ya kasa sakewa yayi komai.
Gashi bai san gidan su ba, shi babu ma abun da ya sani game da ita. Cikin motarsa ya koma ya shiga yana dafe kan motar yayi shiru kusan minti biyar bai ko rintsa ido ba. Sai kuma ya tada motar ya bar cikin school ɗin. Hanyar gida ya nufa sai kuma ya nufi gidan iyayensa domin tun jiya da yau duk bai jeba kuma ko kiransu bai samu yayi ba. Haka kawai zuciyar sa ke raya masa in sha Allahu bata mutu ba, ai kuwa idan haka ta tabbata shida ita kuma har abada, ko kallonta ba zai sake yi ba, bare akai ga yayi yunkurin aikata wani abu da ita.
A ƙofar gidan ya ajiye motar tasa ya shiga da sallam. Mahaifiyarsa ta amsa ya ƙarasa ciki da ɗan rashin kuzari. Ita kadai ce a gidan sai ƙanwarsa da yasan tana school yanzu haka. Zama yayi akujera yana ta kokarin ganin ya kawar da komai dake kan fuskar tasa. Ya ce “Mama ina uni ya ƙarfin jiki?” Ya faɗa yana ɗan ƙirƙirar murmushi. Mama ta amsa tana tanbayarsa lafiya dai taga ya ɗan zube ko baiji daɗi ba ne. Ya ce “Eh Mama zazzaɓi ne ya ɗan dameni tun jiya, amma dai yanzu da sauki” ta ce “To Allah ya ƙara afuwa, ya ita Nadiyar da jiki, yanzu haka kake fita ka barta ita ɗaya a gida ga tsohon ciki?” Habib ya ce “Ai ina koma gida idan bani da karatun safe, yauma sai biyar zan shiga class ɗin duk muna tare da ita. Yana rufe baki sallamar Nadiya ta karade palon. Kasa amsawa yayi sai Mama ce ta amsa tana mata maraba. Itama tsaye tayi ganinsa a gidan sai tayi kamar bata gansa ba ta gaida Mama ta samu guri ta zauna fuskar nan a haɗe. Ƙanwarsa ce domin su ɗin ƴan ya ne da ƙanwa.
Mama itace tasha nono ta sakarwa mahaifiyar Nadiya ɗin da Allah yayiwa rasuwa shekaru biyar kenan. Hakan yasa Nadiyar ta dawo gidan da zama, kuma dama tun kafin rasuwar a kwai shaƙuwa a tsakaninsu, da ta dawo gidan ne kuma ta koma soyayya har akayi aure. Nadiya na sonsa sosai, domin bata haɗa son da take masa da komai, sannan ita ɗin mace ce mai kishi sosai hakan yasa take godiya ga Allah da ya bata Habib domin shi mutun ne da bashi da lokacin mata, hakan yasa take ƙara alfahari da shi a ko ina.
Tana iya bakin kokarin ta wajen rufa masa asirin gidan sa, domin tunda suka yi aure ba’a taɓa jin kansu ba, bata taɓa cewar yayi mata abu, tana da hakuri sosai wanda ya haɗu da son da take masa. Duk abun da yace ta bari to babu shakka ta bar wannan abun kenan, haka idan ya saka ta. Yanzu haka zuwan nan da tayi tazo ne domin ta bigi cikin Mama ko taji abun da yake damun sa saboda ta kasa natsuwa kuma gashi yaƙi ya sanar da ita, domin tabbas ta lura akwai abun da yake ɓoye mata kuma ko menene ba karamin abu bane. Mama ta ce “Yanzu kuwa nake tambayarsa cewar haka yake barinki ke ɗaya a cikin gidan?” Nadiya ta ɗan yi murmushi ta ce “Ai kusan muna tare dashi a gida, yanzu ma ban san nan zai zo bane yasa bamu zo tare ba. Mama ta ce “To ma sha Allah, Allah dai ya raba lafiya Kinga kema kya samu abokiyar hira ko abokin taya hira. Habib ya ɗan saci kallonta suka haɗa ido yayi saurin kawar da idonsa yana jin gabansa na faduwa da zuwan nata.
Dukda yasan bata saba kawo ƙararsa sa ba, amma yana jin kaman sauyin da ta gani ne yasa taxo ta sanarwa da Mama. Tashi Mama tayi ta barsu a palon. Ya dawo kusa da ita ya ce “Wa kika tambaya kika fito? Kuma me kika zo yi a wannan lokacin kamar an koroki?” Ta ce “Ai koroni ɗin kayi, kuma ba zan koma ba har sai ka faɗa min abun da yake damun ka, na gaji, gaba ɗaya ka sauya min, baka zama kaci abinci, jiya ina kula da kai ko barci ba kayi ba, yau da safe ka fita babu ko magana, ko ka gaji dani ne, idan ka gaji ka faɗa min sai na bar maka gida?” Ta ƙarasa da kamar faɗa. Habib sai rufe mata baki yake tana ture shi. Ya ce “Haba Beb ina ce na faɗa miki cewar wani sharri ake son ƙulla min a makaranta kuma Allah ya ƙwace ni komai ya wuce”
ta ce “To mai yasa baka koma gida ba?”
Ya ce “Ai daga nan gidan zan koma”
ta ce “Ka min alƙawarin cewar komai ya wuce ba zaka sake yimin irin abun da ka min ba?”
Ya ce “Nayi alƙawarin komai ya wuce”
Ta ce “To kayi dariya kuma kace beb ba zan sake ba harda riƙe kunne?” Ya ce “Idan kuma Mama ta shigo fa, kizo muje gida har doki sai nayi miki?” Ta ce “No ni yanzu nake so kuma anan” Habib ya sunkuya ya kama kunne ya ce “Beb ba zan sake ba” ya faɗa yana miƙewa.
Ta yi dariya tana jin daɗin hakan. Ta kalleshi ta ce “Ya Allah duk masu son ganin sun tonawa Beb asiri Allah ka tona musu?” Ya amsa da amin. Ta ce “Mu dage da addu’a Allah na tare da mai gaskiya, duk yadda suke son ganin bayanka Allah ya fisu.
Kusan karfe sha ɗaya suka koma gida bayan ya biya sunyi siyayya na kayan kwalliya harda abubuwan sha da take so. Suna komawa gida suka shiga kichin tare yayi kokarin kawar da komai ya tayata sukayi girkin rana, kuma suka zauna suka ci. Suna ci suna hira amma hankalinsa naga agogo domin baya so ya makara, so yake biyar tayi masa yana cikin class ɗin yadda zai kori duk wanda ya shigo daga baya. Kamar daga sama yaji Nadiya ta watso masa tambayar da sai da ta hautsuna masa kayan cikinsa, har abincin da yaci na yunkurin dawowa tsabar tsoro.
Ta ce “Na kira number ka ɗazu naji an ɗaga ina ta magana naji shiru, hakan ne yasa hankalina ya tashi, kuma ina ta kira ba’a ɗagawa, lafiya dai ko?” Ta faɗa tana zama kusa da shi. Tsabar firgita bai san lokacin da ya furta cewar “Ta ɗaga?” Nadiya ta kalleshi cike da rashin fahimta ta ce “Ita wa ɗin, number ka fa nake magana?” Sai lokacin ya kula da abun da yayi. Gaba ɗaya abun ne yayi masa biyu, farincikin bata mutu ba, da kuma tsoron abun zatayi da wayar gashi babu security a wayar. Ya ce “Eh ita wayar nake nufi, yanzu haka take min sai ta ɗaga kanta da kanta ko tana aljihu ne” ya faɗa ba tare da yasan lokacin da ya shirya karyar ba, kawai dai yaji tana fitowa ne daga bakinsa.
Ganin kamar ta yarda sai ya ɗora da cewar “Faɗuwar da nayi jiya ne na zauna a kanta, to shine ɗazu da na fita na kaita gurin gyara, to ko tana gurin ne kika kira, yanzu ma haka zan biya ne na amsota idan zan tafi makaranta”. Ya faɗa yana kuma jin ko shi ya gamsu da wannan batun. Ta ce “To Allah ya ƙara kiyaye wa beb. Ya amsa da amin. ƙarfe huɗu ya baro gida ya tsaya a wani masallaci yayi sallar la’asar. Yana fitowa ya nufi school ɗin. Bai shiga ajin ba sai biyar yana ta mamakin yadda Nadiya tace an ɗaga wayar to kenan ita ce ko yaya. Koda ya shiga class ɗin ya tarar an zo da yawa, amma ga guraren wasu nan da yawa basu zo ba. Nan take ya fara yin abun da ya kawo shi, duk wanda yazo sai ya kora shi waje.
Sosai ya ya haɗe ransa Kamar kullum baya ko bada fuskar raini ga kwanni ɗalibi. Ya gama bayani kenan ya juyo yana neman ƙarin bayani a gurin ƴan ajin yaji ana shigowa, yana ɗaga kai ya ganta tana tafiya kamar mara lafiya, sanye da wani sket ɗan ƙarami ya ɗangale mata, fuskar nan tata babu ko kwalliya sai ma wani ɗan haske da tayi, jakar school ɗin ta rataye a kafaɗarta ta dama. Tsayawa tayi tana kwallonsa shima ya shagala da kallonta har ya manta da cewar a gaban dalibai yaƙe.
Bai san lokacin da yace mata “Get in” ya faɗa har lokacin yana jin yanayin nata har cikin ransa. Lokaci ɗaya dalibai suka fara kallon-kallon, bayan kowa yasan halinsa na hana kowa shiga idan har ya shigo class. Ganin haka yasa ya yi saurin yiwa na waje alama da hannu akan suma su shigo. Haka suka shigo yaci gaba da jawabi amma hankalinsa na gareta. Ita kanta shi take kallo domin ko rubutu ɗaya batayi ba, yana ɗago kai sai ya samu shi take kallo. Dogayan ƙafafuwanta dake waje masu haske suna daga cikin abun da suke ɗauke masa hankali idan ya kalleta. Idan bai yi ƙarya ba har kanne masa ido yaga tana yi tana murmushi, zuciyar sa ce ke harbawa da karfi yana ta ƙoƙarin ganin ya natsu sosai
Haka ya gama koyarwar ya fita ya ya nufi ofis ya yi mata alama da ido akan ta same shi a cen. Yana shiga ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai zagaye yake yi yana ta alla-alla ta shigo ya amshi wayarsa ta ƙara gaba shima yasan inda dare yayi masa, tunda Allah yasa bata mutu ɗin ba. In sha Allahu ya ɗauki darasi daga wannan abun, ko kallonta bai zai ƙara ba. Yana cikin haka yaji ta turo ƙofar a hankali kuma ta rufe tana kwallonsa, shima kallonta yayi har yana haɗiye yawu ba tare da ya sani ba. Jakar hannunta ta jefar gefe ta nufo gurin da yake tana masa wani irin kallo mai tafiya da imanin mutum. Habib sai ya tsinci kansa da kasa daina kallonta. Ta tsaya a gabansa ta ce “Sir” sai kuma tayi shiru ta dafa girjinsa sai kuwa gashi ya zauna a kan kujerar dake kusa da shi…