Amera ta ce "Karatu kuma, wa yake ta wa ni karatu yarinya ta samu wanda yake sonta, to idan ma karatun ne ba sai ta yi a gidan mijin nata ba" Ta ƙarasa maganar da muryar da ke nuni da ɓacin ran da ta ke ta ƙoƙarin danne wa. Adam ya ce "Honey wai me kike nufi ne, ko kin manta yanzu haka yarinyar nan ta na shekarar karshe a makarantar ne, kuma yanzu haka text suke yi, suna ganawa kuma sai exam, so kike a katse mata karatun nata ne saboda wani yazo ya ce ya na sonta. . .