Bai tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su, yayi pakin a ɗan nesa da gidan kafin ya ciro waya ya kirata. Yana sauke wayar ya ɗora kansa a jikin sitiyarin motar ya yi shiru yana tunani. Har ga Allah zuciyar sa bata son aikata wannan abun da yake ƙoƙarin yi, amma kuma ransa na yaba wa sosai, idan zuciyar sa ta ce Allah na ganinka sai ransa ya raya masa cewar ai sau ɗaya ne kawai zai yi, kuma idan yayi zai tuba, Allah zai yafe masa. Kansa ne ya ƙara sara wa kaman zai fita, hakan. . .