Bai fita da mota ba haka ya dinga yawo a ƙasa ya rasa ina zai je, har bakin babban titi ya zo ya tsaya yana ta bin motocin mutane da kallo. Ganin dai kaman ya na neman mayar da kansa wani mai motsi ne yasa ya kama hanyar gida yana tafiya yana tunanin rashin wayon Haura da rashin hankalinta, idan ba haka ba ta yaya zata shiga motar saurayi da irin wannan shigar su fita wani guri, ko shi da yake uba a gare ta ai bai dace ta shiga motarsa a haka ba, bare kuma wani ɗan iskan saurayi. . .