Skip to content
Part 1 of 13 in the Series Abbakar by Fadimafayau

GODIYA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, da ya ba ni ikon rubuta wannan labari. Fatan Allah ya nunan ranar dazan kawo karshensa.

Kazalika ina godewa iyayena fatan Allah ya saka musu da alkairinsa.

JINJINA

Jinjinata gareku take, masoyan novels ɗina bazan gaji da jinjina mukuba masu bada lokacinsu su karanta littattafaina.

DAN BAYANI

Wannan labarin ƙirƙirarrene na ƙirqire shine dan faɗakarwa da nishaɗantarwa. Duk wanda ya ji wani abu dai-dai da nasa, a yi hakuri, akasi aka samu.

Kuskuren dake ciki amin afuwa ajizanci ne na ɗan adam.

Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai

Juyi kawai yake baccin yaƙi zuwa, tun bayan hutun dasukai na semester ending bacci yai masa ƙaura, koya ya kwanta baya iyawa saidai yaita juyi farin ciki tuni ya daɗe da masa k’aura komai yake yaƙe kawai ya ke yi. Yau take jajiberin komawarsu makaranta, duda ba al’adarsa bace shiga sch ranar da aka koma anman segashi tun watan da ya wuce yake tsimayin ranar dawowa.

Ji yake gabaki ɗaya daren ya masa nisa, gani yake kamar garin bazai wayeba ganin da yai baccin da gaske bazaizo ba yasa shi miƙewa dan dauro alwala.

Asubar fari ya farka, daga gajeren baccin da besan sanda ya ɗaukeshi ba, duda kuwa yadda wani bacci me dadi ke dibansa ayanzun haka ya daure yai wanka yafice masallaci.

Shida dai-dai ya gama shiryawa, ko abinci bai tsaya ci ba ji yake kamar yai tsuntsu yaje makarantar, Da ɗan saurinsa ya sakko daga samansa yai sashin Hajiyarsu yana ‘daura agogonsa.

Kamar yadda ya zata tana zaune tana wutiri, kamar yadda al’adarta take ya’dan zauna kamar minti talatin bata shafa ba yana duban agogo yaga shida da rabi ya mik’e yai wajen falon yana kiran Maryam dasauri ta fito daga madafa rik’e da cokali….”Yaya ina kwana” tace “lafiya lau agogo sarkin aiki har’antashi kenan” “eh yaya” ta fada “to yayi kyau kicewa Hajiya nazo tana addu’a nafita” “to yaya abincinfa?” a’a kibarshi innaje office nasha ruwan zafi “to yaya seka dawo.”

Harya kai bakin k’ofar dazata sadashi da babban falon gidan Hajiya tace “Allah ya dawo dakai lafiya” dasauri ya dawo ya zube har ‘kas “ina kwana Hajiya” “lafiya lau” ta fada tana murmushi “ni zan futa” “to Allah yakaika lafiya ya dawo da kai lafiya” Amin Hajiyarmu ya mi’ke yabar falon.

Bakwai da rabi a B.U.K ta masa office dunsa ya wuce ya ‘dan shisshirya takardun dazai bu’kata yasha tea sannan ya fito zuwa
class.

Ahankula yake tafiya burinsa koda sau dayane ya doro idanunsa akanta dan abinda yada’de yana muradi kenan.

Kamar daga sama yaji ance “good morning sir” har cikin ransa yaji wani abu yar yasokeshi tabbas ita ce dan muryarta ta da’de da zama daram a kwanyarsa duk inda ya jita cikin mata ‘dari sai ya ganeta.
Be juyo ba ko nuna alamar ya kula ya amsa da morning yai gaba kamar ko yaushe bata damuba, Aisha “tace kuyi sauri mu tafi aji kunsan halin mutumin nan inyashiga minyi rashin tayau inyaso se yai attendance”…….”gaskiya ni fitsari nakeji kamar ya zubo sai dai inna rasa dan bazan iya zama dashi ba” inji Ummulkhairi se kindawo inji Aisha.

Muje in raka ki inji Fatima a’a Fatina ki tafi karkiyi missing banso mu biyu mu rasa inkinanan kamar inanan ne a’a wallahi se naje kina da matsala muje.

Ina captain yake? ya fada yana tsaye jikin madogarar malamai bezoba yayi kyau wani yazo ya gogen allo ya fada yana mik’o duster din .

Yayin da ‘dalibi guda ke goge allo shikuma yana duba takaddun da yazo dasu saidai ahak’ik’anin gaskiya bawai takaddun yake dubawa ba afakaice ‘daliban dake zaune yake kallo kaf ya dubesu sedai idanunsa sun kasa hango masa ita wato bata zo ba kenan kome.

No to muryar wa yaji hakan kenan na nufin santa yafara zautar dashi ta yadda inyaji muryar wata zai zata ita ce …..wani tunani ne yazo masa yai bakin k’ofa inda makararun ‘dalibai ke tsai tsaiye duda sunsan bazai barsu su shigoba.
Kaf yabisu da kallo bata cikinsu yadan fito kadan suna zaune ita da k’awarta sai wata dabai saba ganinsu tareba sai namijin da indai zaigansu zaigansu dashi shima yana zaune kome suke tattaunawa yafada aransa oho.

Sannunku wato kune shafaffu da mai ko dabazaku iya tsaiwa ba sukai zuru zuru da ido suka kuma kasa mik’ewa yayi kyau yace .

Kuna tsayen zaku iya shigowa wannan yazama last time dazaku zomin aji a makare. Mungode malan ku godewa kanku ya shige ajin sukuma suka bi bayansa.

Bayan ya rubuta Topic din dazasuyi yau yajuyo kamar yadda na fada muku a first semester wata’kil in zama mutumin da zan daukeku wannan course din wata’kil a canza to ba’acanzaba kunsan dokoki na dan haka bana bu’katar sanar daku wanda suka mance su tambayi sauran ‘Yan aji.

Yadan matsa bakin k’ofar kai yanzu bakaji kunya ba kana namiji kana cikin mata azaune ragwanci ba na maza bane yai shiru any way wato ku baza ku iya mik’ewar ba ko? a’a malan munyi zaton bazaka barmu mushigo bane inji Fatima, yayi kyau to yajuya Sorry sir yaji muryarta ta daki zuciyarsa, yadan murmusa burinsa daman tai magana be juyo ba yace sorry for ur self pls sir amana afuwa ta kuma fade, yadan juyo fuskar nan murtuk zaku iya shigowa but this should be ur last time coming to my class late. Ya shige ciki.

Yana rubutu suka shigo juyowar dazaiyi Ummulkhairi na ‘kok’arin zama me idonsa zai gani ciki gareta dan da’kyarma ta zauna anya kuwa ba gaskiya idansa ya fada masa.
I have to get my self prove ke da kika zauna yanzu dawo gaba, Ummi da suka shigo tare ta mi’ke, no bakebafa I mean Ummulkhairi bemasan ya fadi sunan ba gabaki daya ajin suka juya suna kallon Ummulkhairi, watoyama san sunanta kenan wannan dan girman kan malamin.

Itakuwa mutuwar zaune tai jin yakira sunanta wato bama afuska kawai yasantaba harda by name wai bakiji ni bane Fatima ta tab’ota ki koma karya koreki.

Ta mik’e daK’yar tayo gaba innalillahi wa’inna inna ilaihirraji’un dagaske cikin gareta mesan samu nane yafa’da cikin ransa wato matar aure yake ma masifar so, san da baijin zai iya rayuwa without ita a rayuwarsa.
Tazo inda ya nuna mata ta zauna da sauri ya juya ya ya goge hawayen da yatawo masa dan besan sauran ‘daliban su gani.

Wayarsa ya’dauka kamar yana waya ya hau salati to ganinan ya maida aljihu captain dinkuwa yazo ya mi’ke ‘dalibin dake zaune dasu ummu ne ungo wannan out line yana ciki gameso zai iya photostat dinsu, inada wani abune me mayin manci pls am sorry yafice bai jira amsarsu ba.

Zan ci gaba insha Allah.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Abbakar 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×