Skip to content
Part 10 of 15 in the Series Abbakar by Fadimafayau

Yadda ya tsura mata manyan idanun sa da sukai jajir yasa ta tsorata sosai, he looks different from the gentle Abbakar she know, duk ta ruɗe Cikin kuka take magana “Please Sir let me go I beg your pardon dan Allah,”

Taɓe baki ya yi tare da haɗe rai ya, mtss! yaja tsaki “au daman ke kinsan Allah ne?, da har zaki haɗa wani dashi, munafuka kawai” ya faɗa murya a kausashe.

Taisaurin Ɗagowa hawayen da ya cika mata ido ya gangaro. Ta yi sa’a suka haɗa ido wani abu ya daki zuciyar sa yayin da tsigar jikin sa ta tashi yar, ya daure tare watsa mata harara kafin ya ce, “Inkinga kinga kinbar office dinnan to Wallahi kin faɗan ke wace”

Ɗagowa ta kuma yi tare da saurin kallonsa gyaɗa kai ya yi “yes kinmaji na rantse”

A tsira ta ce “sir bangane ba, what do you want to Know about me?, all i know is I am ur student shikenan.”

Ɗaga mata hannu ya yi ” nop ba wannan relationship ɗin bake san sani ba, ki faɗan mene alaƙarki da Mahfuz, Ni, dakuma Yah Nasir”

Kallon sa ta yi saroro, who is Mahfuz?, We have nothing with dukan su da ka lissafo infact banma sansu ba, and for you ni bani da wata alaqa dakai da ya wuce student teacher relationship, balle su” ta faɗa cike da kwarin gwiwa.

Kallon ta ya yi sosai kafin ya Jijjiga kai cike da takaici, “ok kin shirya ma kwana anan ko?, Keep what you are hidden with you sai mu yi ta zama anan am ready for all your taurin kai” Ya shige toilet ya dauro alwala gami da fitowa ya tada sallah, bayan ya idarne yaci abinci ya miƙo mata sauran, ” inkinyi niya kyaci, ya sa hannu ya amshe babyn hannunta ya koma inda sallayarsa ke shimfide ya kwanta gami da ɗora babyn kan cikinsa, ya lumshe idonsa hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba ganin la’asar na shirinyi dagaske bazai barta ta tafiba, kenan yake nufi ko me?”

Wata irin yunwa takeji, abinka da me jego but batasan cin abincin sa dan bata yadda dashi ba yadda ta fuskanci yau ɗin ba Abbakar ɗin da ke koyar da su take tare ba, nasu malamin was very gentle and calm anma wannan kamar a buge yake dan ɗazu da ya daka mata tsawa ta kalleshi taga idanunsa sun wani sauya launi, batasan duk bacin rai bane kawai.

Dole in samu mafita ta faɗa a ranta, a yayin da a zahiri kuma ta ce, “naji zan faɗa ma alaƙata dasu inkamin alƙawarin barina in tafi” ta faɗa idanun ta na kan inda yake kwance tamkar mai bacci.

“ok ina jinki” ya faɗa batare da ya bude ido ba balle nuna concern on What she said, ” innaji bayaninki ya gamsar dani mai zai hana inbarki ki tafi.” Ya faɗa

Numfasawa ta yi tana ƙara tauna mai zata ce, ƙwarim gwiwarta ta samu ta haɗa wuri guda lafin ta ce “Mahfuz cousin ɗinane”

what! ya faɗa gami da saurin bude ido ta gyaɗa kai alamar da gaske take “eh causin dina ne haka ma Yaya Nasir and as for you kai Malami nane” ta faɗa tare da miƙewa, zan iya tafiya?”

Girgiza kai ya yi, baki gama bani amsa ba, apart from blood relationship meye alaƙarki da Yah Nasir fa ya faɗa, idanun sa a kanta ba tare da ya miƙe ba.

Tai shiru, kawai tana kallon sa, ya mayar da idanun sa ya rufe ” oh you are not ready to leave kenan?”

Taa kaɗa kai cikin hawaye, a sanyaye tace ” mijina ne” ya miƙe a tsorace sauran ƙiris babyn ya faɗi, ya tallafeshi “mijinki” ya faɗa.

“Eh” ta fada

“Oh i see. Shiyasa kuka haɗa kai kedashi zaku haukatan abokina ko? Dan kawai san zuciyarku dan zalunci.”

A rikice ta ce “pls kabarni in tafi na amsa maka duk tambayoyinka dan Allah.”

Naji zaki tafi but baki gama amsan tambayoyina ba baki fadan alaqarmu ba.”

“Sir ni bamu da wata alaqa da kai banma sanka ba sai a Bayero.”

Karfa ki rainan hankali nasan me nake, am 30 so kinga na fice kizo ki rainan hankali, inkasa ganowa taya zakice baki san niba bacin kinsan frnd dina, if i can recall ke kika fara turon frnd request a Facebook, sai yanzu na gane hakan duk yana cikin shirinku ne keda Yah Nasir.”

“Sir kayadda dani bansanka ba,” ta faɗa cike da ƙagara.

“e

“Eh naji baki sanni ba anman taya za’ai da aurenki ki dinga chat da wani harki dinga baima mijinki ku gaisa da wanin in baya shirinku.

“Sir in zaka tuna time in four years back muna chat but inka tuna bamaka  Nigeria, Na turo maka frnd request dan kawai post inka na burgeni inzaka tuna ai na fada maka.”

Yai dan tsai yana tunani yes yatuna, “ok yanzu zamuje ki fadama iyayen Mahfuz abokina da hankalinsa kafin inbarki ki tafi ta, zaro ido what!

“Eh, yanzu zamu tafi”

Hawaye ya gangaro mata “haba sir ba haka mukai dakai ba pls let me go, kazamto me cika alqawari, dan Allah, shiru ya yi kafin yace ok you go, zaki iya tafiya yabuɗe mata office din gami da bata baby ta wuce da sauri, tana sauke ajiyar zuciya.

Harta fita ta dawo, daga bakin ƙofa ta tsaya duda yabar ƙofar a buɗe, ” sir make up test in tawa?” yaja tsaki kawai, ” pls sir” tace kafin yace wani abu kallon ta ya yi yadda ta yin sai ya sa weakness din son ta da ya samu strength ɗin danne shi ya taso masa cikin sauri ya ce “jeki i will think about it”

Ƙara lankwasar da murya ta yi, “dan Allah sir ta kuma fade” yaja tsaki gami da faɗin “oppps kije during exam ki amsa all question in yaso se kisa C.A a biyun, zan gane”

“Thank you sir” ta fada tai saurin barin wurin.

Wayarsa ya dauko wadda ya danna recording ɗin duk abinda suka ce, ya hau sauraro at list yasamu evidence against ita da Nasir dole yai wani abu  to expose them dan kare martabar abokinsa.

Miƙewar dazaiyi wayar ta fadi kan dan daryar tiles ji kake taratsatsa, jiyai har cikin ransa faɗuwar wayar yai saurin saukowa, glass ɗin ya tarwatse, burin sa ta kunnu, sai dai yai yai ta kunnu taƙi “oh my goodness ya faɗa, yana dan dukan goshinsa memory din ya ciro yasa adaya wayar sedai ba recording shedar yana kan wayar, ya Allah ya fada gami da komawa ya zauna gumin ɓacin rai ya karyo masa ya rafka uban tagumi yana tunanin abinyi….

<< Abbakar 9Abbakar 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×