Skip to content
Part 13 of 13 in the Series Abbakar by Fadimafayau

Da sauri Abbakar yasha gaban sa tare da jawo shi zuwa cikin ɗaki, “haba Mahfouz kasan nasan da hankalinka ko?,  pls act like a man, serious mana katsaya ka saurareni” ya amshe wuƙar, komawa ya yi ya zauna tare da yiwa Mahfouz ɗin alamar ya zauna, kafin ya ɗora da maganar sa, we all know that love is a good portion of happiness in our life but love is not worth our Akira, if you kill him what about your Jannah? Besides I believe duk girman yadda kake son wani u can still do without him”.

Nisawa Abbakar ya kuma yi ” Ni ban yadda ummu matarsa bace” mahfuz ya zaro ido, “what bafa ka yadda ba kace?” gyaɗa kai Abbakar ya yi “Yes you heard me right,  ban yadda ba”

Kusa da shi Mahfouz ya zauna ” to sabida me?” Ɗan ɗaga kafaɗa Abubakar ya yi “sabida kawai ban yadda ba, ayanzu banda hujja anman ina ji ajikina ba matarsa bace, kawai suna maka haka ne dan ka fita daga rayuwarta.”

Dafoshi Abbakar ya yi “Ka yadda dani karka yi abinda zakayi danasani, a hankula komai zai koma dedai haka yaita tausarsa har ya samu ya sauko.” Kafin su taɓa hira ya ta shi ya wuce.

*****

Fatima ce riƙe da paper ɗin test ɗinsu tana faman mita, “wallahi dedai nayi mutumin nan zai soke min, dan Allah Aisha kalli nan ba haka ake ba?” ta faɗa tana saita takardar gefen Aishan, duba takardar ta yi ta kalla to ba gwanda keba nida ba’amin recording  bafa tunda ba Reg. Number bansa ba” hararar ta Fatima ta yi “to ba  inkin kai masa zai miki ba.”

“Pls ni ku rakani nai photocopy din paper dinnan” inji Amina, wadda ita batai test din ba, suna tafe fatima na mita yayin da Aisha itama keyin tata kan rashin mata recording duda yake lefin tane na rashin saka reg. Number dinta.

Ita dai Amina ba abinda take fadi se maganar absent da aka saka mata a last exam, yayin da Ummu tai shiru ita kaɗai tasan abinda ke damunta, gabaki ɗaya ta dena jin daɗin sch din kawai tana daurewa ne.

Kinsan Allah maidama mutumin nan zanyi jibi fa ko makamin nan beba yaushe zaki kaimasa ya shigar miki Fatiman ta tambayi Aisha ko yau ne sai muje inasan zuwa can chemistry lab ma ok se muje gabaki daya.

Sunyi rashin sa’ar samun me photocopy hakan yasa suka kira sauran frnd dinsu kan suzo su tafi daga nan zasu viya suyi ahanya.

Sun haɗu a CIT inda student ɗinnan suke graduating, murna kawai suke, sai anan ummu taɗan ji sukuni aranta dan ita ɗin mutunce mai san taga mutane sun kanmala karatu musan man data ga yara qanana sai taji dama ita ce.

Tuni ƙawayenta sunyi gaba, sakato ta tsaya tana kallom masu bikin, sunata selfie yau batazo da me rainonta ba, bata da lafiya koda zasu shiga exam sai wata yar level 4 ta roƙa ta riqe mata Abbakar.

Kukan da yasa ne ta tsaya ta haɗa masa abincincinsa, Da yake yafara shan kamu shi take bashi sha yake sosai alamun yunwa yakeji yadda yakesha da kuma tunanin da zuciyarta ya tafi yasa batasan sa’adda hawayen da suka cika mata idanu zubowa ba.

Jitai an dafata ta baya tai saurin jiyowa Hafsa ce kinsan tun ɗazu muke nemanki, ina su Fatima? inji Maryam, “assha kukan me kike haba Ummu ki dinga ragema ranki damuwa pls,” inji maryam ke wallahi kina da matsala nasan duk bazai wuce kan exam din yauba, kawai ki shareta exam luck ce kawai inji Hafsa, “to Allah ya bamu sa’a su suna waje jen Fais muje nace su jirani.”

Suna tafe Hafsat na selfie da ɗan surutanta wani, tayi musu su biyu wani ta jawo Maryam, yayin da Maryam ke faman tambayar Ummu wace amsa ta samo a questions din yau, wasu Ummu ta bata amsa wasu kuma tai shiru.

Sun yi photocopy din inda Fatima da Amina suka wuce toilet na CIT mosque basu jima ba suka dawo.

A bus stop suka hadu da Halima da sauran frnds dinsu, sun hau mota tare yan hanya sun sauka ahanya yayin da su suka sauka a old side din sch din tasu dan can ne gun da zasu.

Sinyi rashin sa’ar samun duk wanda sukaje nema hakan yasa kawai ko wannen su ya wuce gida kan zasu hadu ran alhamis.

A gida ummu ta rasa me ke mata daɗi dan tun randa Abbakar ya titsiyeta batajin dadi ita ba abin ta faɗawa Nasir ba, tsoronta daya kar yaje ya ballo mata ruwa, abinci ma ba koyaushe take ci ba ko tanajin yunwa data fara ci zataji ya fita aranta.

Ran alhamis da sassafe ummu ta shirya tai sch dan sunyi zasu haɗu dasu Hafsa 10 na safe.

Basu wani makara ba sukazo duda kuwa ta dade da zuwa Fatima ce last din zuwa suka dunguma sai math department sunyi rashin sa’ar samun wanda sukaje gunsa bayan sun tambayi maƙocinsa ko zaizo ya basu tabbacin zuwansa suka koma qasa dan jiransa.

Zaune suke suna hira sama sama yayin da karatin paper din dazasuyi yau yafi qarfi Maman Amira ce ta ɗauko wata paper suna ɗan tattaunawa akai dagowar da Aisha zatai taganshi yazo suka miqe dan bin bayansa.

Faduwar da Hafsa tai ne yasa har isarsu bakin office din basu bar dariya ba, ganin office din abude yasa su shiga taitayinsu suka jira na ciki ya fito kan su shiga.

Bayan sun gaisa cikin haɗe rai ya ce lafiya me ya kawoku paper dinta Aisha ta nuna wadda ya rubuta not recorded ya amsa da Id dinta ya shigar yayin da fatima tace complain gareta ya karba yana dubawa.

Ya dago a fusace haka na koya muku tai tsuru tsuru ya miqo mata paper dinta yayin damaman humaira tamiaqa tata itama fadan yasa hafsat na gefe tana dariya qasa qasa.

Ganin da gaske ficewa zaiyi yasa Fatima yin qarfin halin qara miqa masa nanto sir bakamaka ba ya karba ya soke sir but ka makawa wasu dedai yai tsaki itama ya maka mata

Sir wai zaka bada attendance inji wa ni nai attendance ne a class dinku gabaki daya sukai tsuru tsuru pls ku fita sauri nake.

Aisha ce ta miƙa masa, “Sir nima baka makan nanba kuma nan nayi dai dai” ya amsa tare da yin tsaki, kowa ma ban maka masa ba” takardar ya karɓa, tare da faɗin muje am busy pls, abakin office ɗin ya tsaya kafin ya miƙo takardar nnan sawa kikai” ya faɗa tare da miƙo paper ɗin. Ran Aisha ne ya ɓaci kafin ta ce “wallahi sir bafa sawa nayi ba” cikin faɗa ya ce to bazan maka ba ya faɗa tare da barin wurin.

Sunfi minti goma suna mita, yayin da ita dai Ummu bakin maganarma babu jitake kamar tai kuka dan ita bama tayi test dinba, gashi exam din se a hankali shi yasa takejin su mitar daɗi ma suke.

Sai wajen sha biyu Maryam tazo suka bata labarin yadda sukai da malamin tai ta dariya kafin su juya akalar firar zuwa karatu.

Sai ƙarfe Ɗaya da wani abun suka bar old campus zuwa new campus, inda zasuyi exam ɗinsu ta yau suna tafe a mota suna fira yayin da kadan kaɗan suke taba muraja’ar abinda suka karanta.

*****

Gidan su Abbakar Hajiya ce ta shigo ɗakin ɗan nata da sallama, ya ɗago daga kan computer ɗin gami da dan matsar da ita ya amsa sallamar bata zauna ba tace “leƙowa nai inga ko lafiya tunda kazo gaisheni banji motsinka ba, bakuma kazo kace min ka fita ba” ya yadan sosa ƙeya gami dayin murmushi “yanzu nake shirin fita ina da jire dalibai wajen ƙarfe biyu da rabi inata faman duba wani assignments ne, dana baima yara tai dariya yayi kyau ai gwara ka hanzarta yanzu sha biyu ta kusa ya mike “ahto bari in wanka ta fice shi kuma ya shiga toilet.”

Saida ya shirya sannan ya sakko Abinci kaɗan yaci dan baya san cin abinci da yawa inzai fita yana kuma san zuwa gidansu Mahfouz, yasan indai time in cin abincine sai hajiyar mahfuz tasa yaci abinci ko baya so.

Tsaf ya fito cikin manyan kayan sa masu ƙara masa kamala ɗakin Hajiya ya nufa kamar ko yaushe yana kishingiɗe, “Hajiya ni zan wuce” ya ce da ita, “harka shirya?” Ta tambaya “eh” ya ce a taƙaice, “to Allah ya kiyaye” amin hajiyata ya faɗa yana yin gaba.

Haryakai bakin falon ya dawo ” waiko Hajiya ina wannan mara kunyar take?” tai dariya “maza taji kana ce mata mara kunya, ta tafi exam” af fa hakane tacemin jiya sunada paper yai waje.

Yana shirin barin main falo din wanda dagashi sai farfajiya suka shigo zainab ce ƙanwarsa wadda take aure a katsina, sai yaranta guda uku nan danan fara’arsa ta ƙaru a’a manyan baƙi yaran sukayo kansa suna ihuuu uncle uncle ya daga su dai dai kafin su rungumo juna shida sister din nasa suna yaushe gamo ciki ya bisu dauke da ƙaramin ɗanta da ta ke goyo ina hajiya ma na ganinsu murnarta ta ƙaru.

Yaran sukayi kanta da gudu ƙaramin ma yasa ihu saida ya saukeshi shima ya faɗa kanta “ohni fiddo yarannan so kuke ku ƙarasani” Abbakar yai saurin cewa “ku ɗaga mun uwani karku karya min ita” a’a kaga malan ka ƙyalen yan jikokina su mori kakarsu suka juyo suna masa gwalo suka saka daria gabaki ɗaya.

“Ke da ma gidanne?” yake tambayar ƙanwar tasa “a’a mu kadaine sai zamu tafi zai zo sai su gaisa da Hajiya” gyaɗa kai ya yi ” ok yayi kyau” yaɗan kalli agogo “opps zanyi latti inna dawo dai koma mene ne ma tattauna ” ya miƙa mata hannu sukayi musabaha kamar yadda al’adarsu take sun riga sun saba “to sai nadawo to” murmushi ta yi ” yah sai kadawo da labari, naga alamu ko dai?” dariya kai ɗai ya yi ” bari kawai sai kadawo nagama duk kayi baƙi” numfashi ya fuurzar “dama can baƙin nake kinga sai nadawo” ya fice aiko Malan ƙarami ya taso da gudu yabi bayansa yana kuka uncle uncle mamanshi tai saurin daukoshi ta dawo dashi ciki.

Ko gidansu Mahfuz din baijeba ya wuce sch dan yaga ya makara.

Wayarsa ce ta fara ƙara time in da suke raba booklet ga student ya migama Malama zainab dan ta basu “ina zuwa” sunan ummi mabiyar autansu ya gani kan wayar “towo” ya faɗa yasan yanzu ai yakamata tana exam room yai saurin ɗagawa cikin kuka take magana “yah ina cikin matsala” ruɗewa ya ya yi sai dai daurewa ya yi tare da fadin “subhanallahi mene badai malpractice aka kamaki dashi ba ko” tai saurin goge hawayen kamar tana kusa dashi kaji kuma yaya Abinda banyi da ba zanyi yanzu.

Sai yanzu yadanji normal ” to mene?” Ajiyar zuciya ta yi ” wallahi yaya ina cikin matsala kana ina ne? Kamar bai san inda ya ke ba sai da ya kuma kallon wurin kan ya ce ” ni ina chemical engineering” “ok ganinan” bata jira cewarsa ba ta kashe ya tsaya kawai yana kallon wayar kome wannan yar rikicin ta jawo musu kuma oho, dan ko autansu baya abinda take kai tama zama tafi autan taɓara Hajiya kuma tai ta goya mata baya kodan shi autan baya ƙasar ne oho.

Minti biyar sai gata kamar wadda tai gudu, ta yi futu futu da ita kallo daya yamata daga ajin da yake yaja tsaki sannan ya kuma yima malamar da suke kula da daliban magana pls ina zuwa.

“Waike lafiya kika dokan kira haka?” tasa kuka ” yah na mance ID dina kuma sun hanani shiga” zaro ido ya yi “towo ni me kike so na miki yanzu?” ta kamo hannunsa “so nake kaje ja roqesu nasa Bala yaje ya karbo min kwace hannun sa ya yi ” to se ki bari yakawo ai.”

Ƙasa ta yi da murya “Dan Allah yah kaji ƙaina kasan in aka fara fitowa bazasu barni inyi ba,” yai shigewarsa ajin yana faɗin “ni nace ki dinga sakaci gobe kya rage lalaci da mantuwa” aikuwa ganin ya shige ajin ta fashe da kuka.

Abokinsa ya kira da yake faculty dinsu Ummi din ya masa bayani “ok ganinan yace masa.”

Wajen minti biyar saiga Malan Mansur yazo ya shiga ajin suka gaisa kafin su fito tare tasan Mansur lecturer dinsu ne sai dai yayan nata bai taba ce mata yana da aboki a faculty ɗinsu ba balle department ɗin datake kullun sai dai ya dinga cewa ta dage tai karatu danshi ba abinda zai iya mata.

Ya dagota “yawwa gashinan abokina zaije ya rakaki anman wallahi inkina irin haka karma ki yi tunanin kinsanni” tai tsalle tama mance a inda suke ta fada kansa ” that’s why i love u” mansur yace muje kina kuma makara tai saurin saukar da ido a Ƙasa wai taji kunya tabi bayansa suka wuce.

Duk abinda suke Ummu na kallonsu ta tagar ajin da sujey wani abu yazo ya tsaya mata arai ita kaɗai tasan mene kawai ta cigaba da rubutunta.

Ta gama rubutunta tas tana kuma dubawa na kusa da ita ya mata mgn juyowar da zatai tace me kace a idon Abbakar aikuwa yayo wajen ” submit” yace sorry tace ” bazaki bayar ba kenan? Girgiza kai ta yi ” no ba haka bane” “to ko ki bayar ko ki cike form dinnan” ya miƙo mata malpractice form tai saurin bashi tana singing out hawaye na bin idanunta ita kadai tasan hawayen me take dan bawai na anƙwace bata gama bane.

Tunda ta fito take kuka har Aisha ta fito dagyar suka sa tai shiru ita da Halima azahiri kenan anman a ɓaɗini tai shiru ne kawai bawai dan taji nasihohinsu ba dan sanin bata da wata mafita inma kukan ta cigaba dayi shirun ma shine mafi alkairin kawai.

Sun fito suna masallaci danyi la’asar su tafi gida Hafsa ta dube ta idonnan yai fayau dashi tana riƙe da Abbakar ” Allah Ummu mutumin can sanki yake” kallon ta Ummu ta yi “wa kenan?” Dariya Hafsa ta yi “Malam Abbakar mana” taja tsaki Maryam tace “mene haka Hafsa da aurenta fa yanzu in mijinta yaji yace mene?” Juya ido Hafsa ta yi ” haka nefa na mance ai wallahi kinyi sa’ar miji me sanki gashi me kyau” Halima tai dariya “a’a Hafsa kimana shiru karkisa yanzu muga ta miƙe ta hau jibgarki kinsan kishi” ga bakiɗaya sukai dariya inka dauke Ummu da kana kallonta kasan yaqe take.

A old side Hafsat tace ita zata ta amso wata takadda Aisha tace “tunda muka fito nakira Mama nace mata munfito nidai na tafi” to sai gobe suka hau dan sahu ita da Ummu da Fatima da Halima halima ce ta fara sauka a danja su kuma aka wuce dasu.

Halima na sauka Ummu ta dubu Aisha “ina san magana daku ina cikin matsala wallahi” cike da kulawa suka ce ” but me yasa tun ɗazu baki fada mana ba” numfashi ta furzar ba gashi yanzu zan faɗa ba ” to yanzu muna jinki” “no ina so mu samu guri ne anman yanzu ki bari sai gobe.” Inji Aisha

“Gobe kun mance an gama exam” ah hakane suks ce “Ɗansahu pls tsaya anan” ya tsaya daidai legal college of islamic studies “ku fito” what kina nufin ba ki ji nace miki na ce mama na tawo ba” kamo hannun Aisha ta yi “pls ina buƙatar shawararku ne da gaggawa.”

Aisha tad8an tsaya jim tana tunani me adai daita sahun yace “zaku saukanne ko mu wuce?” Fatima ta fito tana juyar da fuska wai ita kar wani da tasani yaganta ta sauka a ƙofar sch din akai gulmarta gida Ummu ta miƙa masa kuɗi Aisha bata da zabi ta fito.

Sun nuna ID dunsu na BUK sun kuma yi sa’a anbarsu sun shiga cikin kujerun da aka tanada dan zaman students na bakin bishiya suka zauna.

Ai kuwa suna zama ummu ta fashe da kuka dagyar tai shiru saida Fatima ta miƙe kinga inbazaki fada mana ba ni zan tafi ta rugo hannunta alamar ta dawo ta zauna.

Ta komo ta zauna ina cikin wani hali mene ya faru munce ki dena wannan damuwar kinƙi.

Yah Nasir ne matsalata me ya miki inji Aisha Fatima ta dafe ƙirji badai cewa yai kibar masa gida ba? Girgiza kai ta yi in wannan ne ai me sauqi ne to mene suka faɗa cikin tsoro.

“Wai cewa yai yana sona?” mtssss suka ja tsaki atare “to saime ke ba abin farin cikinki bane mutumin da duda yasan komi game dake ya da6uki kasadar riƙeki duda yasan hakan zai iya rabashi da iyayansa, ya ɗauki nauyinki ya rufa miki asiri kika zo cikin Abbakar nanma bece komi ba ya ɗauki ragamar komi to mene na damuwa.?”

Cikin kuka tace “ni bana sansa indai so na aure ne” “what Ummu kinsan me kika ce kuwa? Inji Fatima “eh nasani” Aisha ya numfasa ” to wa kike so in bakya sansa? “A nitse ta ce Abbakar” suka mike gabaki ɗaya arazane suka maimaita Abbakar! “eh shi” riƙo hannun ta Fatima ta yi bayan ta dawo ta zauna ” wai wane Abbakar din, badai lecturer dinmu ba? badai thermodynamic ba wanda ya koroki yauba?” Murmushi ta yi mai ciwo “eh shi ne, shi nakeso nayi nayi na cire abun araina nakasa.”

Tabdi! kin ɗauko dala ba ganmo inji Fatima, Aisha tace haba ummu karki zama butulu mana ta ture hannunta da ta dafata “ni shi kadai nake so shi kadai nake gani shi kadai ne burina, shi kaɗai nake gani dashi na shirya rayuwata gabaki daya” rufe mata baki Fatima ta yi” pls ya isa haka” Fatiman ta fada cikin fushi bansan shirme wallahi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abbakar 12

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×