Skip to content
Part 2 of 13 in the Series Abbakar by Fadimafayau

Yana barin sch gate ‘din hawayen da ya boye suka kwace masa, saida ya yi nisa ka’dan da makarantar sannan yai packing, kuka kuwa me ‘karfi ya kwace masa bai taɓa sanin shi ba jarumi bane sai yau, wai shi yake kuka, kuma kukan ma kan mace, yai kuka sosai har saida dankansa ya fara rarrashin kansa da zuciyarsa, ya’dan jima a gun kafin ya goge hawayensa yabar wajen.

Acan sch kuwa bayan fitarsa ‘dalubai sukayo kan Ummu, suna tambayarta waike taya akai wannan ‘dan rainin hankalin yasan sunanki? ta ta’be baki taya zan sani “bakuga mutuwar zaune nayi ba dajin sunana abakinsa” “Ai wallahi naso ni yakira” inji Aisha “kunifa nasan da sansa zan mutu zainab ta fada suka saka dariya gabaki daya”

Zaune suke a falo Tv na yi ƙasa ƙasa Hajiya ta dubi Maryam da ke taɓa waya ” wai ni kuwa Maryam me ke damun yayanki ne?” Hajiya ta tambaya “wallahi bansani ba naga dai kamar yana cikin damuwa”

Numfashi Hajiya ta furzar ” bari inje ‘dakinnasa inji” ta miƙe tai section d’insa, yana zaune kan doguwar kujera kansa na kallin sama sai filo dake ri’ke a ‘kirjinsa sam baima san mai yake tunani ba”subhanallahi mezan gani?” inji Hajiya

Zumbur ya miƙe zaune sai a lokacin yaji danshij hawayen dake kwance kuncin sa, da sauri ya hau goge su sai dai ta gansu.

Kusa da shi ta matsa “Mai ke damunka ni mamarka ce kafa’dan meke damunka I a sure u i will clear them all in sha Allah” cikin zuciyarsa yace “Naso zaki iya mum sedai wannan ya wuce tunaninki, naso zaki iya sharen hawayena, saidai bazaki iyaba bakuma naso in saka ki cikin damuwa, ya faɗawa ransa ” Allah hajiya ba komai” kallon sa ta yi cikin fushi ” yanzu kanunan ban isa dakaiba, tinda bazaka iya fadan damuwarka ba” ta faɗa tare da juyawa zata fice.

Da saurin sa ya kamo hannunta “wallahi ba haka bane, kawai na tuna da Baba Alhaji ne, shiyasa nashiga damuwa bakuma nasan kema insaki cikin damuwa shi yasa naga gwanda inzauna a’daki” a hankali ta juyo jiki a sanyaye hannu tasa ta goge masa hawayensa bata iya cewa komi ba tabar ‘dakin dan batasan yaga hawayenta.

Ahankula yace “ki yafemin Hajiya na miki ‘karya na kuma tuno miki da Alhaji ki yafemin.”

Matashin saurayi ne ɗan kimmanin shekaru ashirin da tara zuwa talatin da biyu sanye yane cikin manyan kaya na hausawa, tsaye yake bakin ƙofar ɗakin yana faɗin ” Ummu pls kiyi sauri karki makara,”

Daga ɗaki cikin ɗan ɗaga murya ta ce “katafi kawai i can drop my self”

Girgiza kai yayi “kinga ni kiyi sauri bakya ganin cikin dake jikin ki, kina dai ji likita yace ki rage ɗawainiya”

Fitowa ta yi tana gyara mayafi tana dariya “na rasa me yasa kullun kake ganin kamar wannan cikin zaisa nazama lazy”

Dariya yasa ” lallaima yarinyar nan to da ke din mece? pls be quick kin isheni da surutu”

Gyaɗa kai tayi tare da danyin kwafa ” au surutu nake ma to na fasa shiga motar taka,”

Ɗan haɗa hannun saya yi “haba abar sona pls ki tawo mutafi”

Dariya ta yi shikenan muje ta faɗa tare da yin harabar gidan, ta bude mota ta shiga tana turo baki, ya rufe motar gami da jan motar yabar gun.

A harabar makarantar ya sauketa ɗan neaa kaɗan da kawayen ta, sai da ta leƙa motar sukai ɗan magana kafij tayi wurin ƙawayenta tana murmushi, “Allah ummu ban ta’ba ganin couples da suka dace da junaba kamar keda yayanki,” Fatima ta faɗa

Murmushi Ummu ta yi ” Allah ko?”

Gyaɗa kai Fatima ta yi alamar tabbaci ” sosaima”

Ummu dariya kawai ta yi. “kinga kuma ni ban taɓa ganin dacewarmu dashi ba,”

Dariya sukai ” shi yasa ai kullin kike sansa kamar ranki” inji Hafsa ” baki da dama Hafsa ni nace miki ina sansa any way mu bar maganar.”

Zaune suke a zaman jiran lectures Ummu ta dubi Fatima “Pls Fatina wai mene da mu ne?” ummu ta tambaya.

Ɗan shiru Fatiman ta yi “ina zaton 3304”

Jijjiga kai Ummu ta yi ” lallaima au kina zato ne ma? u are not serious wallahi,”

“anman ai nafiki tunda ke tambaya ma kike,” sukai dariya baki daya kinga mutafi aji koma mene magani acan suka wuce ajin.

Duk yadda Abbakar yaso mantawa da ummulkairi abin yaci tura kullin kamar ‘kara masa santa ake “innalillahi wa’inna ilaihirraji’un waime kesan samu nane Allah ka yaye min ka kuma yafemin “ya fa’da.

Wayarsa ya ‘dauka ya kira khairiyya wata frnd ‘dinsa ta facebook be ta6a ganin yarinyar ba anman ya rasa me yasa ya yadda da ita sosai.

Wayar tata akashe take hakan yasa ya kunna Data ‘dinsa ko Allah zaisa tana online aikuwa kafin ya shiga inbox ‘dinsa message ‘dunta ya shigo sallama ce kamar kullin wani ma ya shigo “yayana yakake kwana biyu banjika ba na kira number dinka akashe” murmushi yayi

“Lafiya ‘kalau ‘Kanwata na’dan shiga matsala ne anman Alhamdulillah everything is back to normal” ya tura mata wasu ‘yan seconni sa’konta yashigo “ayya Allah ya sau’ka’ka komai” ” amin ‘kanwata.” Shima ya tura mata

Shirun da sukai ba tare da turawa juna sakon bane yasa shi fadin “Wai yaushe zamu hadu ne?” Ya tambaya ta turo hoton emoji alamar she is thinking, “matsalarki kenan kullin na miki maganar ha’duwa sekiyi tamin wala wala” tai dariya let’s give time some time,” yai dariya “kullun haka kike cewa” “yayana mu hadu anjima yanzu malami ya shigo” ta turo yayin da shi kuma ua ce “ok .” Kawai Yau sati biyu kenan rabon Abbakar da sch tun randa yaga ummul kairi da ciki yaji ya tsani makarantar ji yake kamarma yabar aikin sedai tuno yadda yasamu aikin nashi dolensa ya yanke shawarar komawa kodan kar ya cutarda students dinsa.

Yau yashirya zuwa, hakan yasa yagama komi section din Hajiyarsu yaje sukai sallama ya wuce.

Yana tu’ki yana addu’a Allah yasa yau bata gaba wata’kil inbata gaban inbaya ganinta sosai yafijin kwarin gwiwar yin lecture din.

Aikuwa yana ‘dora kafarsa acikin ajin idanunsa ita suka fara gani tana dariya ita da Fatima ‘kawarta da alamun tanajin dadin firar dasuke tai masa kyau sosai a ido innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un abinda kawai ya fara fa’de kenan jiyai kamar ‘kafafunsa bazasu ‘daukeshi ba juyawa yai dan barin ajin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abbakar 1Abbakar 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×