Miƙewa yai ya shiga toilet ya dauro alwala gabaki ɗaya yarasa abunyi, hakan yasa shi tada sallah ko Allah zaisa yadanji sanyi cikin ransa.
Saida yai azahar sannan yabar office din, bayan ya gama nemawa Ummu sauƙi da fatan Allah ya raya abinda ta haifa.
Yunwa yakeji sosai hakan yasashi wucewa gida duda a ƴan kwanakinnan be cika san zama cikin jama’a ba.
Da Maryam ƙanwarsa yaci karo a farfajiyar gidan, tana baima Habu me tuƙi saƙo ta ƙara faɗa ɗa murmushin fuskarta “yah sannu da zuwa,” shima ya amsa yana dariya “yawwa” gami da shaqar numfashi hmmm! “ƙanwar me ake dafa mana ne,?” Juya idanuj ta ta yi ” wani abin daɗi ne” murmushi ya yi ” kamar kinsan yunwa nakeji”
Itama murmushin ta yi “aikuwa dai sha kuruminka yanzu cikinka zai cika” yabi bayanta batare da yace komaiba.
“Pls ƙanwar ki fadan me kike dafa mana ne?” Ya faɗa lokacin da ya ɗanyi sauri ya taddo ta.
“kaidai kawai kabari azubu” ta shige madafa yabi ta kitchen din zai leqa tukunyar “pls yaya,” ta faɗa tare da saurin rufe tukunyar tana dariya
“Abeg sanmin kar ƙamshi ya ƙosar dani” ya faɗa kai a langaɓe.
Ta dan debo miyar a ludayi ta bashi yana kaiwa baki yasaki wata ƙara gami da cillar da ludayin.
Tai saurin matsowa daf dashi “yah lafiya?” ya ɗago ya galla mata harara “anman ke muguwa ce wallahi kinsan da zafi zaki bani,” tasa dariya kai yaya “anman kai ragone wallahi, ni nadauka wani abune ashema dan zafinnan ne zaka wani saka ihoo”
Tsuke fuska ya yi “au dariya ma kike?,”
Juyar da kai ya yi ” to anma fasa cin abincin naki danma inai miki kara ina cewa kin iya girki, to ki sani ba abinda kika iya” fuuu ya fice daga madafar ta ci gaba da dariyarta.
Saida ya watsa ruwa yaji dagaske yunwa yakeji gashi ƙamshin abincin ya cika masa hanci ya sauko daga sama yai sa’a bata falon sai hajiya.
Kai tsaye dinning area ya wuce ya ɗebo a plate yai sama hajiya tace “ina zuwa haka?” Daga matattakalar ya ce ” inazuwa hajiya bari inkai ɗaki kar wannan mara kunyar ta ganni” hajiya tasa dariya kwaji dashi dai.
Saida yakai matattakala ta ƙarse yajiyo Maryam tana dariya ” ahab ashedai na iya abincin tunda har yasamu matsayin akaishi ɗaki aɓoye”
mtss ya saki tsaki ” anma fasa ci” yazo ya dire “eh ya ƙara afki”
“au haka kika ce to sema naci.”
Ya haukan kujera ya fara ci ” ai yarinya da da ace da kudinki kika siya to bazanci ba,”
Dariya take sosai “eh anman ni na dafa abinda”
Yana ci tamkar ai mai dole ya ce ” bama dadi ci karka mutu ne fa” yana fade yana yamitsa fuska yana turawa abaki kamar anai masa dole
“eh shiyasa naga anata saka loma.” Inji Maryam
Bai bata amsa ba ya dubi Hajiya dake ta murmushi “Hajiya innaje masallaci bazan dawo da wuriba zan biya ta gidansu mahfuz karkiga nayi dare”
“ok inka dawo nayi bacci katashi Maryam ta shiga daki katabbatar duk sun rufe dakunansu”
“ok hajiya.”
Yau ya yanke shawarar samun Mahfuz ya faɗa masa komai ko yaji sanyi aransa dan zatonsa rashin faɗawa kowa da barin komi cikin ransa yasa abin ke damunsa sosai.
Yaje gidansu Mahfuz sun dan gaggaisa da mutan gidan dan gidan yawane mahfuz baya ɗakinsa hakan yasa ya zauna a farfajiyar gidan suna fira da mamar Mahfuz ɗin ya tura ummi ta kira masa shi danshi bashi da al’adar zuwa gidan yai ta shige shige tun yana yaroma balle yanzu duda ba inda aka masa katanga da shiga.
Maman Mahfuz tace “kudai zanga lokacin da zakuyi hankali” yasan kwanan zancen dan haka yai shuru ace ku duk ƙannenku sunyi aure, ku goɗai goɗai daku kun kasa, sai yawo kuke waiku samari bakusan kun tasanma zanya tuzurai ba,” sosa ƙeya yai gami da fadin “aishi Hajiya aure lokacine,”
Hmm ” eh haka kullin kuke cewa” Mahfuz da yafito riƙ da yaro ne ya miƙawa Hajiya, kai kana da matsala ace kai bazaka taba zama dan gida ba Tashi muje sukai bangaren mazan gidan.” Mahfuz ya faɗa
Sun dan taɓa fira kafin Mahfuz yace ” nasan da magana dan haka kawai bazan ganka da daddareba “
“kaidai bari” inji Abbakar “ina cikin matsala.”
Mahfuz ya zaro ido “matsala”
Gyaɗa kai Abbakar ya yi “eh wallahi am in love”
Mahfuz yasa dariya kaji wai matsala “love isn’t a problem malan, wace me sa’a ce haka?”
Uhum ” student ɗina ce and she is married with baby mafa”
what! mahfuz ya fada a razane.
Taya haka ta kasance zakayi kuskuren kamuwa dasan matar aure, are out of your mind or I know u are not in to drugs nare in ce.
Furzar da iska Abubakar ya yi “nima bansani bafa se daga baya, sai da na yi zurfi”
“subhanallahi da matsala babbama” in ji Mahfuz
“Matsala bama daya ba wallahi Mahfuz kullin wallahi kamar qaran santa ake a zuciyata narasa meke min dadi.”
“Don’t worry man I have a solution” Mahfuz ya faɗa lokacin da ya dafa kafaɗar Abbakar.
Abbakar yace “mafita kamar ya?”
“Eh mafita kace she is ur student right?”
“Yes she is” Abbakar ya giggiga kai
“Ok that’s good, kasan students can do anything to pass there exam, kayi anfani da wannan daman ta zama secret wife inka” Mahfuz ya faɗa tare da juyar da kai.
“what me kake nufi, are you mad, may be you are drunk right” Abbakar ya faɗa tare da ƙoƙarin shin shina Mahfuz.
“Nasan ka gane, nasan kasan am not drunk, all am trying to do shine baka mafiya, ka nuna mata if bata yadda dakai ba she is going to failing ur course”
Miƙewa kawai Abbakar ya yi yaja tsaki “wannan ai ba mafita bace shirmene. Cemaka nai inasanta bawai ina sha’awarta ba and i wanted us to be together for the rest of our life not for wani lokaci in ta yadda muka aikata tsiya dole se tayi passing course dina kenan kaga tana gama sch zata mance dani santa ya ci gaba da damuna.”
Miƙewa Mahfouz ya yi tare da dafo shi ” kayadda dani once ka sameta zakaji abinda ke daminka aranka akalla rabi ya ragu.”
Janye kafaɗar sa ya yi “ko kuma ta ƙaruba,” yaja tsaki “ko a da banyi shashanci ba sai yanzu da girma ya fara kamani” ya fice daga ɗakin afusace.
Zaune yake yana marking test ɗin da ya yi aka kwankwasa kofar yace “yes shigo ta shigo da sallamarta “ummu ce” ya fada a ransa dan ko cikin mata dari yaji muryarta sai ya ganeta .
Ita dince kuwa tai masa kyau sosai kana ganinta kasan me danyen jego ce, nan da nan shaidan yafara ƙawata masa ita maganar Mahfuz ta fara dawo masa .
Bangaren zuciyarsa da shaiɗan ke iko da shi ya fara fada masa yes maganar Mahfuz is the only solution to ur problem, this is the best chance tazo dan test ne kayi anfani dahakan wani barin na fadin no karkayi .
Sai dai kamar barin shaiɗan ɗin ya yi yadda ya yadda This is the best chance and the right time y miƙewa yai inda take a tsaye itakuwa sai baza ido take yayin da zuciyarsa ke bugawa anya kuwa dedai ne hakan ya faɗa but this is the only solution u have, if not ka mutu da ciwon santa ganin yazo dab da ita yasata faduwar gabanta ya qara ƙaruwa……….
Zan cigaba in sha Allah