Cikin baccin da baisan lokacin da ya ɗauke shi ba ya ji wayar shi na ruri, idanuwan shi a rufe ya lalubota, har kiran ya yanke, numfashi ya sauke yana ɗora wayar a ƙirjin shi tare da gyara kwanciya. Wani rurin ya ji wayar ta sake ɗauka, da ƙyar ya buɗe idanuwan shi yana ganin Nuriyya ce, ɗagawa ya yi ya kara a kunne ba tare da ya ce komai ba.
"Masoyi"
Ta kira ta ɗayan ɓangaren, shirun Abdulƙadir ya sake yi, sosai ta ɓata mishi rai, Waheedah ce a tunanin shi da komai shi yasa bai yi. . .