Skip to content
Part 4 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Maɓallan rigar shi ta makaranta yake ɓallewa, ya saka hannu a aljihu ya ciro links ɗinshi, kasancewar rigar mai dogon hannu ce. Hajja ce ta fito daga ɗaki tana kallon shi.

“Dogo ɗan baban shi, Sojan gidan Bugaje…”

Ta faɗa da alamun zolaya, ƙayataccen murmushin da ba ko yaushe ake gani ba Abdulƙadir ya yi mata. ‘Yan gidan Bugaje suna da tsayi babu laifi daga mazan har matan, don gajerun cikin gidan ba su wuce su huɗu ba, amma tsayin da Abdulƙadir yake da shi har mamaki yake basu, duk manyan yayyen shi tsayinsu ɗaya da shi, ga shi lokacin banda ball da yake yi har motsa jiki yake zuwa, gidan kaf babu wanda bai san burin Abdulƙadir shi ne zama soja ba. Tun yana da ƙarancin shekaru yakan ce shi Soja zai zama, tun suna ɗaukar abin ƙuruciya har ya fara tasawa yana cigaba da jaddada musu ƙaunar shi da aikin soja, ko a hanya yagan su sai ya je sun gaisa.

Ganin nasu ba ya mishi wahala tunda akwai barikin Sojoji ta nan ƙofar ruwa, ga abokan shi biyu Imran da Nawaf duka iyayen su Sojoji ne, abinda ya ƙara danƙon zumuntar su kenan da Abdulƙadir.

“Hajja”

Ya kira, sun gaisa da ya dawo daga sallar asuba, shi bazaie iya wannan wahalar ta sake sabuwar gaisuwa ba kuma.

“Har an shirya?”

Kai ya ɗaga mata ya ɗora da,

“Me kika dafa? Wai Mama koko fa tayi mana da safen nan.”
Dariya Hajja ta yi, don ita ba ta ma jima da tashi ba, ruwan shayi ta ɗora ba ta jin ko tafasa ya yi.

“Sai dai in za ka sha shayi…ban jima da tashi ba nima…”

Ɗaga ido ya yi yana kallon agogon da yake ɗakin haɗi da girgiza mata kai.

“Na ci wani abu idan na fita makaranta…”

Zahra ce ta shigo ɗakin tana saka Hijab ɗinta, ba ta kula da Abdulƙadir da yake tsaye ba ta kuwa bangaje shi.

“Subhanallah.”

Ta faɗa tana jan hijab ɗin ta saka da kyau, wani irin mari ya ɗauketa da shi da ya sa Hajja ƙarasawa ta riƙo Zahra da ta fashe da kuka tana faɗin,

“Wallahi Hamma banganka ba…”

Kallon shi Hajja ta yi.

“Me yasa kake da saurin hannu ne haka Abdulƙadir? Za ta tureka ne idan ta ganka.”

Zame jikinta Zahra ta yi daga riƙon da Hajja ta yi mata, kuka take sosai don ta maru yadda ya kamata, Abdulƙadir take kallo da ya kafe idanuwan shi akanta yana ƙarasa saka link ɗin a ɗayan hannun rigar.

“Ina kwana”

Ta faɗa muryarta can ƙasa, girar shi ya ɗaga duka biyun.

“Abdulƙadir”

Hajja ta kira, yi yayi kamar bai ji me ta ce ba ma, hankalin shi na kan Zahra.

“Ki saki ranki ki gaishe ni, faɗa muke yi ne?”

Kai ta girgiza tana share hawayenta, muryarta ta gyara ta sake faɗin,

“Ina kwana.”

Murmushin gefen fuska ya yi.

“Kin tashi lafiya?”

Da ƙyar tace,

“Lafiya ƙalau”

Tukunna ta wuce ɗaki, safa ta zo ta ɗauka dama, don girkin Mama ne duka suna dakinta za su karya acan. Alhaji Ahmad Bugaje mutum ne tsayayye, ba zaka rasa rikici a gidanka ba koda mata ɗaya ka ajiye, ballantana har huɗu, sai dai suna ƙoƙarin duk wani rikici da zai faru a tsakanin su ba ya ƙarasawa kunnuwan shi sai dole. Duk abinsu suna shakkar ɓacin ran shi, shi ya sa aka samu wadataccen haɗin kai a tsakanin yaran, don suna son junansu sosai. Ko a makaranta babu wanda yake taɓa ɗaya daga ciki, su dukan su za ka gani a saman kanka kamar ƙudan zuma. Girki a haɗe suke yi, sai dai ko in kana son dafa wani ɗan abin ka dafa a ɗakinka. Amma duk mai girki zai yi da duka yaran gidan a ɗakinshi za su je su ci abinci daga safe har zuwa dare.

Zahra na barin wajen, Abdulƙadir ya juyo, fuskar shi a daƙune yake kallon Hajja.

“Kina min faɗa a gabanta, kina so su rainani ne Hajja? Ya za ta shigo ɗaki fuskarta lulluɓe da hijab? Me ya sa ba za ta tsaya ta saka ba tukunna ta shigo? Shi ne za ki min faɗa a gabanta.”

Hararar shi Hajja ta yi tana faɗin,

“Kai yanzun me kake yi?”

Sake daquna fuska ya yi.

“Ni dai ba na so.”

Yace ya sa hannu ya ɗauki jakar shi ya saƙalota yana rataya tare da juyawa ya fice daga ɗakin. Harabar gidan ya fita inda babbar motar da ake kaisu makaranta gaba ɗayan su take, shekara ɗaya dai ta rage mishi ya gama makarantar nan ya huta da saka uniform, duk da ba wasu shekaru ne da shi ba, yana cikin ta goma sha bakwai ne, amma tsayin shi ya sa ana tunanin ya girmi shekarun shi. Bakin motar ya tsaya, ya sa hannu a aljihu ya ciro agogon shi, bakwai da kwata.

“Duk yaran da ya sa nayi latti sai na ci uban shi wallahi.”

Ya faɗa a fili yana ɗaura agogon, duk da shi yake riƙe da muƙamin mai horar da ɗalibai na makarantar ba zai hana principal ɗinsu yarfa shi a gaban yara idan ya makara ba, duk da zai huce a kansu ba ya so dai, duk wani abu da zai ja a ci mishi mutunci a gaban yara a makarantar yana guje mishi. Din ma ba ɗaliban da suke ƙasan shi ba, har ‘yan ajinsu shakkar Abdulƙadir suke yi, banda Imran da Nawaf babu mai tunkarar inda yake kai tsaye, don su kaɗai ne abokan shi na har wajen makaranta, dama abokai huɗu kacal gare shi, sauran biyun Anwar da Tijjani, unguwar su ɗaya, islamiyyar su ma ɗaya, duk tare suka tashi.

Amatullah, Nusaiba, Nabila da Kabir ya hango suna ƙarasowa wajen.

“Ke kamar Hamma Abdulƙadir ne tsaye fa…”

Nabila ta faɗa, tan saka Nusaiba kallon wajen a firgice.

“Innalillahi… Ƙarfe nawa?”

Nusaiba ta tambaya, duk da tsiran sati biyu ne tsakaninta da Abdulƙadir ɗin, ajinsu ɗaya ma a makaranta, amma hakan ba ya hana shi jibgarta. Babu mai agogo a cikinsu balle ya amsata. Sa’adatu kuwa kallon Kabir ta yi.

“Kabir don Allah ce duk su fito.”

Juyawa Kabir ɗin ya yi da gudu, su kuma suka ƙaraso wajen suna gaishe da shi a tsorace, amsawa yayi, da sauri suka shiga motar suka samu waje suka zauna, Zahra ce ta fito ita ma , fuskarta a kumbure da kukan da ta yi, ga shatin ‘yan yatsun shi nan kwance saman fuskarta, ko da ta shiga motar babu wanda ya tambayeta, duk sun san ba zai wuce Abdulƙadir ba. Ba kullum yake binsu a tafi makaranta haka ba, ranakun duk da yahau mashin ya yi gaba abinshi ransu wasai, motar kamar za su tasheta da hira, in kuwa yana ciki ba za ka ji bakin kowa ba.

Kabir ɓangaren Mama ya nufa, duk suna falon nata, wasu na ɗaura takalma, wasu na saka safa.

“Wallahi Commander ya fito.”

Ya faɗa yana dariya, Commander shi ne sunan da suka laƙaba wa Abdulƙadir ɗin, suke kuma kiran shi da shi a bayan idon shi. Ba su jira ƙarin bayani ba da gudu suka kwasa, wani takalmi ɗaya a hannu suka fita. Kusan a tare suka ƙarasa suna maida numfashi.

“Wane irin rashin hankali ne wannan?”

Abdulƙadir ɗin ya tambaya yana ƙare musu kallo.

“Ina kwana Hamma.”

Suka faɗa kusan su duka, madadin tambayar da ya yi musu, tsaki kawai ya ja ya buɗe gaban motar ya shiga. Su ma soma shiga suka yi, tukunna Waheedah ta ƙaraso wajen, hijabinta a hannu ko sakawa ba ta samu ta yi ba. Gaba ɗayan su Sheikh Bashir suke yi. A ɓangaren Waheedah banda sunanta da ya banbanta da nasu ko ita da kanta da ba za ta taɓa sanin ba Alhaji Ahmad bane mahaifinta, balle kuma ‘yan makarantar su, daidai da rana ɗaya bai taɓa nuna mata cewar ba ta fito daga jikin shi ba, kuma a cikin gidan ma babu wanda ya taɓa ɗaga mata kai akan zaman agolancin da take yi. Sai kuma kalarta da ta banbanta da tasu, fara ce har shiga ido take yi, sukan tsokaneta da cewar da taku ɗaya ta guje wa zuwa duniya a zabiya, duk da su ma akwai fararen a cikin su.

Za ta iya cewa ta fara sanin labarinta ya canza ne a ranar, lokacin tana aji uku a sakandire, a gaban motar ta ganshi a zaune, duk da gefen fuskarshi ta gani sai da zuciyarta ta yi wata irin bugawa da ba ta da alaƙa da tsoron shi da kusan su dukansu suke yi. Yanayi ne da ba za ta ce ga lokacin da ya fara ba, ko muryarshi ta ji sai zuciyarta ta fara doka mata irin hakan, don za ta rantse wasu lokuttan har wani gashi ne yake miƙewa a bayan wuyanta. Jikinta da wani irin yanayi ta saka ƙafarta a cikin motar, dariya ta ga suna yi mata ƙasa-ƙasa, motar ta cika taf.

“Ku matsa min.”

Ta faɗa cikin sanyin maganar ta.

“Babu waje fa.”

Nabila ta amsa mata da murmushi a fuskarta, a raunane Waheedah ke kallon su, ta sauke idanuwanta kan Nazir da yake zaune a gefe, Hararar ta ya yi yana faɗin,

“Taɓ”

Yazid da shi ne zai kai su ya ƙaraso wajen motar, cikin sanyin halinta ta gaishe da shi, ya zagaya ya buɗe gaban motar ya shiga ya mayar ya rufe.

“Wai waye bai fito bane?”

Abdulƙadir ya tambaya yana juyowa, Waheedah ya gani a tsaye.

“Uban me kike da ba zakie shigo ba?”

Idanuwanta ta ji sun ciko da hawaye, ga zuciyarta na ci gaba da bugawa da wani irin yanayi da ba ta da kalaman fassara shi.

“Babu wajene anan ɗin.”

Kabir ya amsa mata.

“Ba ga waje anan ba?”

Abdulƙadir ya faɗa yana kallon su, hannu Nazir ya saka ya ja murfin motar ya rufe, don babu yadda za a yi ya koma gaba, ba zai zauna waje ɗaya da Abdulƙadir ba. Kar ma ya ga shi ne a gefe yace ya tashi ya koma, ita Waheedah da ba ta fito da wuri ba, ita za ta zauna kusa da shi, tsaye ta yi a wajen ta rasa yadda za ta yi. Ba zama waje ɗayan da shi bane tashin hankalinta, luguden da zuciyarta take yi duk idan ya wuce ta gabanta ma kawai, balle kuma ta zauna ga ƙugunta ga nashi tana jin kusancin shi. Tunda take shi ne namiji na farko da ba ta san me yasa take jin hakan akan shi ba.

Hannu Abdulƙadir ya sa ya buɗe murfin motar.

“Idan bakina ya sake magana sai ranki ya ɓaci.”

Ba ta san lokacin da ƙafafuwanta suka motsa zuwa gaban motar ba, tana gani ya ƙara matsawa, shiga ta yi jikinta a sanyaye, kafin ta zauna ta ɗora hijabin kan cinyar shi tana rufo murfin ƙofar tukunna ta zauna a takure, ta sa hannu ta ɗauki hijabin nata.

“Ba ki ga inda za ki ajiye ba sai a jikina?”

Kai ta girgiza mishi, ƙaramin tsaki ya ja yana gyara zama, farinta yake ji yana shigar mishi idanuwa, a ɗakinsu shi da Babban Yayan su Muhsin ne baƙaƙe, shi ya ɗan fi Muhsin hasken fata ma, amma farin Waheedah na mishi wani iri, duk in ya ganta tana ƙara saka shi yana jin yadda babu abinda zai haɗa mishi hanya da auren farar mace, ko kaɗan ba sa burgeshi. Hijabinta da ya sha guga ta warware tana shirin fara sakawa.

“Idan kika bige ni sai na mareki Waheedah, ban san iskancin da zai sa ba zaku saka hijab tun daga gida ba.”

Yazid dake tuƙi ya girgiza kanshi yana murmushi.

“Wallahi ka cika shegiyar masifa…”

A hasale Abdulƙadir yace,

“Hamma ba na so…”

Waheedah kuwa hannuwanta ta sauke tana riƙe da Hijabin, numfashin kirki ma ba sosai take yin shi ba, kar ya ji iskar ta mishi yawa a kusa da shi ya sauke mata wata masifar tashi da bata ƙarewa. A haka suka ƙarasa makarantar babu wanda yake ko motsin kirki.

*****

Kitchen ɗin Mama ta shiga, tana buɗe ƙatuwar kular da ta zuba abincin a ciki ta ga ko rabi ba a ɗiba ba. Jinjina kai ta yi.

“Kun wa kanku Wallahi, gaba ta kai ni.”

Ta faɗa tana ɗauko wasu manyan robobi masu murfi guda uku ta soma rage dafa-dukar shinkafar a ciki. Da ma bayan sun tafi makaranta, tunanin abinda za ta dafa take yi, ta buɗe fridge ta ga ba ta da cefane, dubu uku Abba ya ba ta kafin ya fita, zubin adashi za ta yi da dubu biyu, akwai bikin da za su je na ɓangaren kishiyar Ummanta, dole a kece raini a nuna banbanci, don ba tun yau take wa bikin tanadi na gaske ba. Sauran guntayen miya da ta gani, wasu ma Allah kaɗai ya san tun yaushe suke ta ɗauko ta haɗe su waje ɗaya ta sheƙa ruwa ta ƙara mai da niƙaƙƙen yaji a ciki, ta ga wani tsohon crayfish ta watsa a ciki, ko tsincewa bata tsaya ta yi ba, ta san ba ci za ta yi ba, ta yi musu dafa-dukar shinkafa.

Da daddare tuwo za ta tuƙa, tana da sauran miyar kuɓewar da suka bar mata wancan girkin nata, ita za ta juye ta ƙara wa ruwa ta ƙara kaɗa wata kuɓewar ta tashe ta, don ita ba ta zubar da abinci, yadda suka barshi ba su ci ba, in wani girkin nata ya zagayo shi za ta yi wa kwaskwarima su zo su ɗiba. Dubu ɗayan za ta aiki Salim ya yo mata cefane ko na ɗari ne naman ɗari biyu ta yi ‘yar miya ta dafa wa Alhaji Ahmad taliya, dama hakan takan yi, don idan ya san kalar abincin da take dafa wa yaran tashin hankali zai mata marar misaltuwa. Shinkafar take kwashewa tana faɗin.

“Haba yara, wannan shinkafar ruwan jakara ce, in kun ƙi ci yau, kun ci gobe.”

Abdulƙadir ya shigo, ya ɗan tsoratata din ganin shi kawai ta yi.

“Kai don ubanka ba ka iya sallama bane?”

Kallonta ya yi rai a ɓace.

“Karki sake zagina gaskiya tunda na yi sallama tun daga falo, ba laifina bane in baki ji ba.”

Baki a sake Mama take kallon shi, rashin kunyarshi ƙaruwa take duk rana.

“Za ka rama zagin ne Abdulƙadir?”

Raɓata ya yi ya ɗauko plate, ko Hajja in ta zage shi ji yake kamar ta watsa mishi ruwan zafi, don gani yake a shekarun shi ya girmi zagi, in yara suka ji ai sai su raina shi. Balle kuma Mama da bai ga dalilin da take da shi na zagin shi ba. Wani ludayin ya ɗauko yana shirin sakawa cikin kular abincin da ko kaɗan yanayin shi bai kwanta mishi ba.

“Karka ɓata min wani ludayin, ga wani nan…”

Ta faɗa tana miƙa mishi, karɓa ya yi ya saka a ciki yana jujjuya abincin.

“Meye wannan baƙi-baƙi a ciki?”

Ya tambaya yana daƙuna fuska.

“Abin crayfish ne…”

Kallonta Abdulƙadir ya yi.
“Crayfish kuma? Meye yasa za a saka mana a abinci…me ya sa ba za a yi mana da nama ba.”

Shi ya sa ta ƙi fitowa tun ɗazun, ta ɗauka duk sun gama ɗibar abinda za su ɗiba tunda ta ga lokacin tafiya Islamiyyar su ya kusa, duk a cikin yaran gidan shi kaɗai yake tsareta da tambaya kan abinda ta dafa musu, ba mai mata wannan fitsarar sai Abdulƙadir, har ba ta so ya ganta ranar girkinta, tana kuma shakkar ya je ya samu Abba da maganar don ta san tsaf zai iya. Ɗan murmushi ta yi.

“To ai ana sakawa, ya ma fi nama zaƙi…”

Ta faɗa a fili a ranta tana; ‘Ɗan iskan yaro mai baƙin hali irin na uwar shi.’

Ci gaba da jagula abincin yake yi da ludayi, ranshi yake jin yana ƙara ɓaci, duk kwana biyun da za ta yi a jigace suke yin shi har yaranta, saboda kalar abincin da take dafa musu.

“Ni kam gaskiya ba zan ci wannan jagwalgwalon ba.”

Ya faɗa yana ajiye plate ɗin da ya ɗauka ya bar mata ludayin a cikin kularta ya juya ya fice daga ɗakin.

“Karka ci don ubanka, in girkina ya zagayo ita ɗin za ka sake dawowa ka samu, shegen iyayin banza da wofi. Yaro ga rashin kunya malam…”

Mama take cewa tana kwashe sauran shinkafar a robobin ta rufe su ta saka a fridge, har ta koma ɗaki ba ta daina kwashe wa Abdulƙadir albarka ba. Shi kam ɓangaren su ya koma ya samu Zahra ta ɗauko uniform ɗin Islamiyyarta a hannu.

“Sannu Hamma.”

Ta ce mishi, don ba ka isa ku haɗu ka wuce ba kai masa ko da sannu bane.

“Zahra ki dafa min ko taliya ce.”

Ware mishi idanuwa ta yi.

“Hamma guga zan yi… Lokacin Islamiyya kuma ya kusa, don Allah ka yi haƙuri.”

Ta ƙarasa maganar idanuwanta na cikowa da hawaye. Agogo ya kalla, uku da rabi har da wasu ‘yan mintina akai.

“Tsayuwar me kike? Da yanzun kin kai kitchen, ki yi sauri, wallahi kikai latti ubanki zan ci.”

Uniform ɗin ta ajiye akan kujera ta nufi kitchen, ta san da gaske yake, zai iya yana gama cin abincin shi ya fita Islamiyyar, tana da tabbacin zai iya riga ta zuwa, kuma babu abinda zai hana shi dukanta, fiye da na kowa ma, don in ya tare latti su gefe yake sawa su ware, in ya yi wa sauran bulala biyar-biyar nasu sai ya kai goma. Wani lokacin za ta rantse da Allah yanayin murmushin shi yakan canza duk idan ya kama wani ya zane, kamar akwai nishadi na musamman da duka yake samar mishi. Lokuta da dama ko faɗa Hajja ta yi mishi akan su yake hucewa, motsi ma in ka yi bai mishi ba zai iya ja maka duka.

Sai dai yana da wani hali ɗaya, babu wanda ya isa ya dake su a waje, babu malamin da bai san rikicin Abdulƙadir ba duk Islamiyyar, tun bai kai haka ba, hannunsu yake kamawa har inda malamin da ya dake sun yake ya tambayi dalilin da zai sa ya yi musu kalar dukan da ya musun, tun ana ba shi suspension, har suka gaji da halin shi suka ƙyale shi, su da kansu ba sa son a dake su ya sani, ba sa ma fara zuwa suyi labarin inda zai ji. Kan kujera ya samu waje ya zauna yana jiran Zahra ta dafa mishi taliyar ta kawo.

*****

Yau ba ta jira kowa a gidan ba, don ranta kal take jin shi, tunda Mami ta siyo musu sabon takalmin makaranta ita da Amatullah, ta tambayeta ko za ta iya ba wa Nuriyya wancan natan, don Kjafar su ɗaya. Kai kawai Mamin ta ɗaga mata, don ta san ko ta hanata ma a sace za ta ɗauka ta ba ta. Da takalman da atamfar da wata ‘yar uwar su Mami ta ba ta, taƙi rabawa da Amatullah ta roƙi Ammi ɗin ta ƙara siya musu wani yadi aka ɗinka musu doguwar riga ita da Nuriyya, duka ta haɗo ta saka a leda ta shiga gidansu Nuriyya da yake jikin nasu, ba wani babban gida bane, ɗaki uku ne a cikin gidan, Nuriyya ce babba a gidansu, kuma yarinya ƙwalli a wajen mahaifiyarta da Allah ya yi wa rasuwa wajen haihuwarta ɗin, tana da ƙannai guda huɗu yanzu haka da matar babanta ta haifa da shi, ga cikin na biyar a jikinta.

Za ka yi ƙarya idan ka ce Mama kamar yadda su Nuriyya suke kiran matar baban nata Maryama tana muzguna mata, da zuciya ɗaya matar take riƙe da ita, wanda abune mai wahalar samu a wannan zamanin, yadda mata suke muzguna wa yaran mijin su da zaman kishi sam bai ma haɗa su da iyayen yaran ba abu ne mai matuƙar muni da ya zama ruwan dare. Sai dai Baban Nuriyya talakane sosai, don sana’ar kanikanci yake yi a wani gareji, da kuma kacokan din sana’ar suka dogara, don ma mutum ne da yake tsaye kan iyalan shi da dukkan ƙarfin shi.

Waheedah za ta iya cewa ta tashi ne ta ga Nuriyya a rayuwarta, don a lissafi da akayi, wata ɗaya Nuriyyan ta ba ta, ƙawancen su abune da zai ba ka mamaki, don tun da ƙarancin shekarun Waheedah ko abu aka ba ta sai ta tambaya ina na Nuriyya, tun Mami na hanata shiga gidan su Nuriyya don ita macece da ba ta son tashin hankali a rayuwarta, har ta Haƙura da ta ga ƙawancen na ‘yarta da Nuriyya abu ne da ƙaddara ta haɗa. Yanzu ma sallama ta rangaɗa tana gaishe da Mama da ta amsa ta ɗora da,

“Hassanar taki na ciki…”

Dariya kawai Waheedah ta yi ta wuce ta nufi ɗakin su Nuriyyan. Abba shi ya fara musu tsokanar nan ita da Nuriyya gashi kowa ya ɗauka, duk idan ya siyo mata abu zai ba ta wani irin shi yace na Hassanarta ne, don shaƙuwarsu za ka rantse ‘yan biyu ne, duk da kamannin su da halayensu ya bambanta, Waheedah fara ce sosai, kuma siririya ce ta gaske, tana da kyau da in za ka tsaya ka kalleta sosai za ka ga bashi da alaƙa da hasken fatarta, sannan komai nata da sanyi take yin shi, gashi babu wanda zai ce ya taɓa ganin ɓacin ranta balle kuma faɗa, shi ya sa tasu ta zo ɗaya da Nuriyya, ita kaɗai take iya haƙuri da halinta. Sannan Waheedah za ta iya sati fuskarta ba ta ga ko hoda ba, don ma farace, ba za ta ce bakinta ya taɓa ganin jambaki ba, kwalliya kwata-kwata ba abu bane da yake gabanta, in dai ta saka kaya masu kyau ta ɗan goga turare mai sauƙin ƙamshi, shikenan.

Nuriyya na da faɗa sosai, ba za ka ɗaga mata ɗan yatsa ka sauke ba tare da ta lanƙwasa shi ba, ba fara bace, za ka iya saka hasken fatarta a mutanen da ake ma laƙabi da masu kalar cakuleti. Kusan kyawun mahaifiyarta ta biyo, don kowane irin kaya Nuriyya ta sa sai ka ga sun amshi jikinta, tana da matsakaicin tsayin da mutane da yawa za su iya kiranta gajera, amma a dire take, tun da ‘yan shekarun tan nan za ka fahimci Allah ya halicci mace a wajen, cikar lokaci kawai take jira ta ƙarasa fitowa. Gashi fuskar nan tana ɗaukar kwalliyar da ke ƙara fito da ita, da wahala ka kalli Nuriyya ba ka sake kallonta ba. Ita ma aji uku take a sakandiren gwamnati ta mata da ke nan cikin barikin sojoji, sannan Islamiyarsu ɗaya da Waheedah.

“Kar dai kice ba ki shirya ba…”

Waheedah ta faɗa ganin Nuriyyan a kwance kan katifar da ke tsakar ɗakin, bayan ta yi sallama ta ɗaga labulen, takalman ƙafarta ta zare a bakin ƙofa ta shiga ɗakin sosai. Sai lokacin Nuriyya ta tashi tana faɗin.

“Na yi wanka, har alwalar la’asar na yi, uniform fa zan tashi in saka…”

Gefen katifa Waheedah ta zauna ta ajiye jakar makarantarta da ledar kayan da ta kawo ma Nuriyya tare dabin farantin day ke ajiye a gefen katifar.

“Kai don Allah Nuriyya, me kuka dafa mai manja ba ki kawo min ba?”

Waheedah ta buƙata, don ita duk abinci mai manja ba ya wuce ta, ga ‘yan gidan nasu ba su cika son manja ba, ko alala sai ace da farin mai za a yi aci da sauce, ita kam tana son abinci mai manja, kallon ta Nuriyya ta yi.

“Gero da wake ne…”

Bakinta Waheedah ta ji yana tara yawun kwaɗayi, don in ba gidansu Nuriyya ba ba ta taɓa ganin inda aka dafa gero da wake ba, sai kuwa in sun je Bugaje ne da Abba, akan kawo musu, ba mai ci sai ita.

“Za ki ci ne in zubo miki?”

Nuriyya ta tambaya a daƙile, wani lokaci irin rainin wayan nan na Waheedah yana sa ta jin wani maƙaƙi a maƙoshin ta, ta tabbatar abinci ne mai rai da lafiya aka dafa wa su Waheedah a nasu gidan, da wahalar gaske in babu naman kaji, amma tana nuna mata kamar su wanda suka dafa ɗin ya fi nasu, ba don ba ta son mahaifinta ba, tana jin shi har ranta, amma idan akai mata tayin musayar rayuwa da Waheedah da gudu za ta amsa, ko don ta dinga zuwa makarantar kuɗi tana turanci kamar yadda ta ji suna yi, duk da itama nacinta ya sa tana da ƙoƙari na ban mamaki, kuma tana kwaɓ turancin duk yadda ya zo mata, Waheedah na gyara mata sosai.

“Kema kin san zan ci ai.”

Waheedah ta faɗa, dama ba wani abin kirki Waheedah ta ci ba, girkin Mama sai godiyar Allah. Miƙewa Nuriyya ta yi ta nufi ƙaramin kitchen ɗin su ta samu faranti ta zubo mata gero da waken ta zuba mata manja da yaji a gefe ta ɗauki cokali ta saka mata a ciki, ɗakin ta koma ta ajiye mata plate ɗin a gabanta.

“Allah dai ya miki albarka yarinyar nan.”

Harararta kawai Nuriyya ta yi, ledar dake gefenta Waheedah ta ɗauka ta miqa wa Nuriyyan da faɗin,

“Anty Asabe ta ban atamfa kwanaki, sai Mami ta bayar akai mana doguwar riga ni da ke.”

Da sauri Nuriyya ta karɓi kayan da murmushi a fuskarta ta ma kasa tsayawa ta kwance ledar, yagawa ta yi ta fito da doguwar rigar da ɗinkin ya yi matu=ar burgeta, ƙasan rigar ta tsugunna ta tattaro sai lokacin ta kula da takalman da suka faɗo, ƙafa ɗaya ta ɗago, ba don ta san Waheedah da takalman ba, za ta ce sabo ne yadda ta wanke shi fes.

“Ke banza har da takalmi kika haɗo da shi.”

Kai Waheedah ta ɗaga mata, don ta cika bakinta da abinci, sai da ta fara haɗiye wani daga ciki tukunna tace,

“Naki ne… Mami ta siyo mana sabo.”

Ta ƙarasa maganar tana ƙara kai wani cokalin bakinta. Takalmin Nuriyya ta mayar ta ajiye kan katifa tana jin wani irin abu a ƙasan ranta da ta kasa fassara shi. Bawai ba ta yi murna da kyautar bane ba, tana tunanin har lokacin da za ta kai tana saka kwancen abubuwan Waheedah, tana da wani irin buri a rayuwarta, tana son ta ga ranar da za ta zo ace ita ce take da damar yi ma Waheedah irin hidimar da take yi da ita, ba za ta ƙi ace idan damar ta zo Waheedah bace a ƙasanta, hakan zai mata daɗi ba kaɗan ba.

Idan ba ta samu damar yin karatu ta zama wani abu ba, ba za ta taɓa auren marar hali ba, za ta auri mai kuɗi, irin mijin da takan ji a cikin litattafan hausar da ba ta jima da soma karanta su ba.

“Kisa uniform don Allah Nuriyya.”

Waheedah ta faɗa don ta kusa cinye abincinta, kayan ta linke ta ajiye su a gefe ta ɗauko uniform ɗinta da su kansu tsofin na Waheedah ne ta bata bayan an ɗinka mata sabo, abinda take ji a ƙasan ranta girma yake ƙarawa, ba tun yanzun ta jima tana jin yanayin ba, yana ƙara girma ne duk lokacin da za ta ga Waheedah da sabon abu, ko kuma Waheedah ta ba ta abinda ta riga da ta yi amfani da shi. Kayan ta zira ta ɗauko dogon hijabinta ta saka, Waheedah ta rigata fita ta nufi randar ruwan su Nuriyyan da ke ajiye a tsakar gida ta sa kofin da ke sama ta ɗibi ruwa ta sha.

“Nuriyya don Allah ki bar kwalliyar nan ki fito haka, wallahi za mu yi latti.”

Daga can cikin ɗakin Nuriyya ta amsa da,

“Don Allah karki isheni, hoda kawai nake shafawa…”

Don ana duka kan yawan kwalliya a islamiyar tasu, duk da haka sai da ta ƙara wajen mintina goma ba ta fito ba. Sallama suka yi da Mama bayan Nuriyyan ta fito suka nufi hanyar ƙofa a tare, suna fitowa ƙofar gidan suka ci karo da Abdulƙadir, wani irin bugawa da zuciyarta ta yi sai da ta riƙo hannun Nuriyya.

“Ina yini Hamma. “

Nuriyya ta faɗa a tsorace ita ma, prefect ne a makarantar, ba tun anan tasan shi farin sani ba, duk da in ba a makarantar su ba, bai taɓa dukanta ba. Asalima ko gidan ta shiga gaisuwarta ma can ƙasan maƙoshi yake amsawa kamar ta mishi dole. Yanzun ma amsa ta yayi da.

“Lafiya…”

Ya tsayar da idanuwan shi kan Waheedah da ko’ina a jikinta ɓari yake yi.

“Ban hanaku tsayawa wani waje in kun fito islamiyya ba?”

Ɗagowa da idanuwanta da suka tara hawaye tayi tana kallon shi, ko ba ta yi wani abuba ya kafeta da idanuwan shin nan masu kama da na ‘yan Japan saboda ƙanƙantarsu ji take komai ya kwance mata ba tare da wani dalili ba.

“Ka…ka hana mu.”

Ta faɗa a daburce, kai ya jinjina ya wuce su, hannun juna suka kama ita da Nuriyya suka wuce su ma, wani irin sauri suke zumbuɗawa kamar za su tashi sama, Waheedah na da tabbacin in ya riga su isa makaranta zai ƙirƙiro dalilin da zai mata dukan biyawa gidansu Nuriyya, ita kuma Nuriyya laifin Waheedah ɗin ta san shi zai shafeta, juyawa Nuriyya ta yi ta ga ko yana gab dasu, ta sauke idanuwanta cikin nashi da ya sa wani irin yanayi tsirga mata daga ɗayan tsakiyar ƙafarta zuwa ɗan yatsan ƙafarta, kafin da sauri ta juya tana kiran duk wani sunan Allah da ya zo bakinta ko zuciyarta za ta rage gudun da take yi. Ta sake damƙe hannun Waheedah tare da janta don su ƙara sauri.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 3Abdulkadir 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×