HAFSAT POV
Isar ta zauren gidan ke da wuya suka yi suka yi ido hudu da Nasir ya rungume hannayensa.
Shigowarta ce ta sanya shi warware hannayen na shi tare da sauke bayyanannar ajiyar zuciya.
Murya kasa ta ce “Ina wuni Ya Nasir?”
“Ya ƙarin hak’uri?” ya tambaya a raunane
Ta dauke hawayen da take ta kokarin ganin basu zubo ba ta ce “An gode Allah.” Sai kuma ta fashe da kuka sosai.
Ya yi shiru yana sauraron sautin kukanta wanda ke kara saka mishi tausayinta.
Shi kansa ya san dole ta yi kuka, ya san tana da dalilin kuka, tana kallon rayuwar da za ta yi a nan gaba ba tare da mahaifiyarta ba.
A da idan an bata mata tana da wurin kwantawa ta yi kuka, yanzu kam a ina za ta kwanta ta yi kukan.
A da tana da wurin fadin abin da ke damunta, yanzu kam babu.
Babu mai lallalashinta a kan komai, ba mai damuwa da damuwarta, yanzu kam ita ce mai sharewa kanta hawaye ya mai yi wa kanta fada mai shagwaɓa kanta, mai ba kanta shawara. Dole na yi ta yi kukan wannan canjin da ya zo mata.
Ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin “Ki yi hak’uri Hafsat, ki yi wa Inna addu’a, ita ce kawai gatan da za ki nuna mata. Sannan ki yi hak’uri da canjin rayuwar da za ki fuskanta, in Sha Allah za ki yi dariya nan gaba. Sannan ni din nan ina tare da ke, duk abin da kike so Hafsat kai tsaye ki zo wajena zan yi miki shi ko menene, ko ba ni da shi zan nemo shi in Sha Allah.”
Ita dai ba ta ce komai ba, kukanta kawai take yi, tana kara jin tausayin kanta.
Ya nisa kadan tare da fadin” Zan koma, dama cewa na yi a kira min ke in yi miki gaisuwa. “
” Na gode “ta fada cikin muryar kuka
Ya juya jiki a mace ya fice daga gidan.
Ita ma sai ta juya zuwa cikin gidan tana share ragowar hawayenta.
Ranar dai haka ta wuni kuka, musamman yadda yan gaisuwa ke ta nuna tausayinta a kan fuskarsu da muryoyinsu.
Yau kam duk abokan huddar Inna da ke kauyuka ne suke ta zuwa gaisuwa, musamman wadanda suke kular mata da gonakinta da dabbobinta
Ranar Lahadi da ta kama gobe addu’ar uku iyala Mama Halima suka zo, ciki har da Nabila wacce ta kasance sa a ga Hafsat sai kuma Juwairiyya wacce take zaman yayarsu, zuwansu ya yi wa Hafsat dadi, ba karamin kewa suka cire mata, ranar Litinin aka yi addu’ar uku, kuma a ranar duk wadanda Inna ke da kadara a gunsu, suka gabatar da jawabin kadarar, a gaban Mama da babban ɗanta Tajuddeen, Malam Ayuba sai kuma Hafsat.
Ba karamin mamaki Malam Ayuba ya yi ba jin abin da Inna ta mallaka
Shanu ashirin, tumaki talatin ban da awakinta na nan gida da kaji da zabbi.
Gonaki goma manya da kanana, ga filaye guda biyar, a ranshi ya rika jin kakarshi ta yanke saƙa, dole ya sa a raba gadon nan ran bakwai, ya kwashi rabonshi ya siyar ya yo aure. Fatan shi Kar Mama Halima ta ba shi matsala, saboda ya santa sosai ƴar tijara ce, lallabawa yake da ita su rabu lafiya, Ya nai mai wasa da macijin tsumma ƴan kallo lafiya, masu wasa lafiya.
Bayan gama lissafe-lassafen ne Hafsat ta koma daki jiki a mace, duk wani abu da ya shafi Inna idan ana tattauna shi narkar mata da zuciya yake, har yanzu wani iri take ji game da mutuwar Inna, kamar gaske, kamar ba gaske.
Tana gab da shiga daki ne muryar Yayanta Dauda ta katse ta “Ke Tatuwa, ki zo waje ana kiran ki” ya yi maganar cikin budaddar muryarshi
Saboda sai ya yi wata uku baya gida, duka shekarunshi basu fi 17-18 ba, amma garuruwan da ya taka Allah kadai ya san su sai shi, wai neman kudi yake zuwa.
Ko yanzu ma Allah ne ya kado shi gidan, har ya riski mutuwar.
Fasa shiga dakin ta yi, ta juya zuwa kofar gidan.
Ba ta yi tsammanin ganinshi ba, ta dauka Nasir ne, shi ya sa cikin sauri ta kara tattara nutsuwarta kamar yadda dai take yi a duk lokacin da take gaban shi.
“Ina wuni?” ta fada bayan ta dan rusuna alamun girmamawa.
Ya lumshe ido yana jin wani irin tausayinta na kara shiga ko wane bangare na jikin shi
“Ya kike?” ya fada cikin tattausar murya yana kallon ta
Bai jira amsawarta ba ya kuma cewa “Ya karin hak’uri?”
“An gode Allah” Ta fada a hankali tana kokarin danne hawayenta
“Jiya na dawo sai na riski labarin rasuwar, Allah Ya jikanta, Ya gafarta mata Ya Kyautata makwancinta. Ke kuma ya raya ki, Ya albarkaci rayuwarki.”
Ta lumshe ido a hankali tana mai jin dadin addu’arshi, kamar tun da aka yi rasuwar babu wanda ya yi mata addu’a mai dadin ta shi.
Hawaye suka rika gangarowa daga cikin lumsassun idanunta zuwa kan farfajiyar kyakkyawan fuskar ta.
Ba tare da ta bude idanun ba ta ce “Amin Ya Rabbb. Na gode sosai, Allah Ya saka da alkairi.”
“Amin” ya amsa a sanyaye, duk suka yi shiru, Sai sautin jan majinarta da yake fita lokaci-lokaci.
“ki je gida, daga nan ki yi min magana da Baba zan yi mishi gaisuwa”
Komai ba ta ce ba, ta juya zuwa cikin gidan da ragowar hawayenta.
RUMASA’U POV
Aibo ya zame mata tauraruwa mai wutsiya ganinta ba alkairi ba, tsawon sati da zuwan shi, ba ta kara farin ciki ba, kullum cikin fargaba take.
Ba ta taɓa tunanin ya iya mugunta irin haka ba, ya tsame hannu daga hidimar gidan gabadaya ya bar mata, iya ka ci kawai ta yi ya ci. Idan ya ji ba shi da kudi ya gwaji masara ko shinkafar gararta ya siyar ya saka kudin aljihu, sulaibiyar baya ba ta.
Idan dai bakinsu ya hadu to baƙaƙen maganganu gami da gori zai yi mata.
Yanzu ma rakuɓe take kan kujera tana kallon yadda yake auna masara cikin buhu, bayan ya gama ya nade buhun hade da saba shi a kan kafada ya nufi kofa.
Ta tattara duk wani karfin halinta wuri daya ta ce “Yau ba kudin kayan miya”
Ya fasa fitar da ya yi niyya ya juyo fuska a hade yana yi mata wani kallo, kallon da ya sanyata shiga taitaiyinta.
Ya nufo inda take, hakan ya sa ta yi saurin mikewa ta nufi dan sirdaden da ke tsakanin gado da sif din ta ta makale. Sosai tsoron shi take ji
Ya tare hanyar da za ta fita yana kara aika mata da mugun kallo sannan ya ce “Ke! Ni ne zan ba ki kudin kayan miya? Me ye tsakanina da ke da zan ba ki kudin kayan miya, da can ni ne nake ba ki?”
Yadda ya tsare ta da ido ne ya sa ta shiga girgiza kai a tsoroce.
“To sai na faffasa miki wannan dogon bakin naki duk ranar da kika kara tambaya ta kudin kayan miya. Ni kin ganni nan, karfina aka fi aka jogana min ke, sulaibiyar dita ban kashe ba, kuma zan kashe ta a ragowar wasu katti ba, wanda dai ya sargafa min ke, Sai ya karasa ladan shi, ni nan ba da jimawa ba zan yi aure, amma ke ba matata ba ce. “ya kai karshen maganar hade da juya ya nufi kofar fita, har ya kai bakin kofar kuma sai ya juya ya kallon yadda ta rukube ya ce” Kuma wlh na dawo ban samu abinci ba, (ya yi kwafa sannan ya ci gaba) ba sai na fada miki sakamakon ba”daga haka ya juya ya fice.
Ta sauke bayyanannar ajiyar zuciya hade da zama gefen gadon jiki a mace kamar an tsoma biredi a cikin ruwan zafi.
Ji take kamar ta rufa gyalenta ta tafi gida ta fadawa Baba Alaramma duk gorin da yake mata, Sai dai kuma tana jin tsoro.
Musamman yadda mahaifiyarta tai ta nanata mata kalmar” ki yi hakuri, kar ki sake ki baro gidan mijinki, shi ne rufin asirinki, kina dai ganin da yadda aka yi auran nan” ba ita kadai ba, kowa ma fadan da ya rika yi mata kenan.
Ta mike zuwa tsakiyar dakin ta yi tsaye tana karewa komai na dakin kallo, kamar yau ta fara ganinsu, ta shiga bude samirun saman sif, wai ko ta manta da wasu kudin, ta gama bude su kaf babu komai.
Ta yi tsaye cikin rashin sanin abun yi, can kuma sai dabarar dafa fara da mai ta fado mata.
Ba ta jima ba, ta kammala girkin, duk yadda ta so, ta ci abincin sai ta kasa, ta rika juya shi cikin kwanon da ta zuba.
Tun da Aibo ya zo, ba ta kara samun nutsuwar cin abinci ba, duk wani abinci idan ta yi shi, Sai ta rika jin shi kamar kasa very testless.
Ana idar da sallahr la’asar ya dawo gidan, da, wasu manyan itace, ya zube su a tsakar gidan.
Ruma dai tana zaune a kan tabarma tana kallon shi, ya wuce daki ba tare da ya ce mata komai ba.
“Ina abincin?” ya yi tambayar daidai zai shiga dakin.
Ta amsa mishi da “Yana nan cikin dakin”
Ko ya yi magana ma ba ta ji ba, saboda ya riga ya shiga dakin sosai.
Bayan ya gama cin abincin ne, ya fito ya fara faskare, duk Ruma na zaune na kallon shi, har faskara kasu uku cikin biyar din iccen, kafin ya mike yana haki, ya juya inda Ruma take ya ce “Ke zo ki karasa fasa itacen nan”
Ta mike da sauri zuwa inda yake ta karɓi gatarin, shi kuma ya kuma ficewa.
Haka tai ta sarar itacen nan, ta babbantali wanda za ta iya sauran kuma ta bari.
A kauye dai ta taso, amma ba ta san irin wannan wahalar ba.
Kamar kullum bai shigo gidan ba sai 11pm, a lokacin bacci take yi sosai.
“Ke! Ke!! Ke!!!” cikin bacci ta rika jin muryar shi cikin fada.
Ta yi sauri ta mike zaune daga kan doguwar kujerar da take kai.
“ubanwa ya ce ki kacaccala min icce haka, kin san wahalar da na yi na samo shi. Shi ne za ki cakalkala shi ki zo ki kwanta.”
A tsorace ta ce “Wlh ban iya ba”
“Ba ki iya ba, to yau za ki koya, ai kin san dai iyayenki na gida suna faskare ko? To tashi ki je ki faskara shi.”
Ta mike da sauri, ya tasa ta zuwa tsakiyar gidan, iska mai dadi tana kadawa saboda yanayin shigowar damuna, a hada hadari ya watse, ko dazu ma hadarin aka hada ya watse.
Gatarin ya mika mata tare da fadin” Ci gaba”
Ganin yana kallon ta, ta shiga buga iccen iya karfinta, haka ta rika yi har ta samu ta gama, yayin da baƙaƙen maganganunshi suka taya ta hira.
Cikin dare tana bacci ta kuma jin yana tashin ta, wai ta je ta kwashe itacen da suka faskara ga hadari nan ya taso.
Ta mike kamar za ta fasa kuka, ta shiga kwashe itacen tana shigarwa dakin girki, ga wata irin iska mai hade da kasa na cika mata idanu, Allah Ya taimake ta, ruwan bai sakko da yawa ba, Sai dai yayyafi shi ya sa ba ta nike sosai ba, bayan ta gama kwashewar ta koma daki ta kwanta a kan 3sitter tana hawayen bakin cikinsa.
*****
ASMA’U POV
A zuciyarta ta kudurta duk garin da ta ji an fara ambatar sunanshi a tasha can za ta nufa, wala ƙauye ko birni.
Mai keken na ajiye ta wani ɗan union ya ce “Hajiya Yari ne” ta daga kai alamar eh.
“Dama mutum daya ake nema, za ki zauna a gaba?” ta kuma daga kai kamar kurma hade da bin bayan shi.
Ya bude mata motor ta zauna, kafin suka shiga tattara kudin mota.
Har motar ta tashi bakinta bai hadu da na kowa ba.
Ta juya kanta zuwa gefe tana kallon bishiyoyin da suke wucewa, yayin da zuciyarta take can wani wuri daban
Abubuwa sun yi mata yawa, ga cikin Kb, ga fitowarta ba tare da sanin inda za ta je ba, ga bacewar kb, ga fargabar abin da zai same ta nan gaba, sune suka hana mata ganin nisan tafiyar da suka yi.
Sai dai ta ji wasu daga cikin motar suna kwatantawa direba in da zai ajiye su.
A lokacin ne hankalinta ya dawo jikinta ta rika karewa jihar ta Yari kallo, ba ta taba zuwa ba, amma ta san yadda garin ya yi suna a bakunan mutane haduwar garin zai iya wuce haka.
Yadda ta ga da yawan mutanen da ke cikin motar suna sauka, ita ma sai ta ce nan za ta sauka.
Bayan fitar ta, can gefen wani shago ta zauna tana kallon yadda ababen hawa ke ta zirga-zirga a kan babbar hanyar, yayin da wasu kuma suke sallar la’asar a masallatan da ke gefen hanya.
Ba ta san ta jima a wurin ba, sai da ta ga duhun yamma ta fara shigowa, sannan ta mike zuwa shagon da ke kusa da ita, ta sayi sabon layi, aka yi mata register ta ɗura mishi data ta kuma komawa gefe ta shiga goggle.
Searching din hotels din da ke garin ta rika yi, suka rika watso mata sunayensu kala-kala
Villa shi ne hotel din da ya fi kama hankalinta, don haka shi ta yi booking ta online, ta biya kudi, suka turo mata lambar wayar da za ta tuntuba
Kafin ta mike ta tare mai keke Napep lokaci daya kuma tana kiran lambar da aka turo mata.
Yana dagawa ta ce “Ga, me Napep ka kwanta mishi wurin.” ta kai karshen maganar hade da mikawa mai keke Napep din wayar
Ta shiga sauraron yadda ake ta mishi kwatance har ya gane, ya mika mata wayar tare da fadin “Shiga mu je Hajiya”
“Nawa ne kudin?” ta tambaya daidai tana zama
“Kar ki damu Hajiya, bari dai mu isa.”
Ba ta amsa shi ba, shi kuma ba dai na janta da hira ba, hirar da ba fahimtar komai take yi ba, ba ta san ma amsar da take ba shi ba.
Tun suna wuce wajen jama’a har suka fara shiga unguwanni da ke mata kama da quarters, manyan gidaje wannan na wane wannan
Sai kuma tsoro ya kamata kar dai mai keken nan canja hanya ya yi saboda ba ta san waje ba.
Ya kamata ta latsa shi, don haka ta ce “Ya na ga ka shigo nan wajen, ni ba ta nan na saba shiga ba”
Tun da ta shiga keken sai yanzu ne ya kuma jin sautin muryarta.
“Haba Hajiya, ni fa dan gari ne, ba zan batar da ke ba, na biyo hanya mai sauki ne, duk hotels din da ke wajen nan na san su, ya shiga nuna mata duk wani hotels da suka wucewa, wasu ta ga sunayensu a online wasu kuma ba ta gani ba.
Wannan ya sa ta dan ji sanyi kadan.
“Don Allah ko za ka tsaya in sayi masarar can?” ta yi maganar hade da nuna masarar da ake gasawa a gefen hanya.
“Me zai hana Hajiya, ko cewa kika yi in koma in siyo miki masara ai zan yi hakan cikin gaggawa”
Ita dai ba ta ce komai ba ta mika mishi dubu daya “Guda biyu masu laushi, kuma wadanda basu huce ba”
“To ranki-ya-dade”
Bai jima ba ya dawo da masarar hade da canjin ya mika mata
“Na gode”
Duk surutun da yake ba ta ce komai ba, saboda ta gane take-taken shi.
Bayan ya yi parking a kofar hotel din ne, ya juyo yana kallon yadda take kokarin fita ya ce “Hajiya a taimaka min da lamba mana”
Shi da wayar ta kalla, ta ja dogon tsoki, ranta yana mai ƙara baci, yau ita mai Keke Napep yake cewa yana so. Keken da taurin kanta ne kawai ya sa take hawan shi a gidan Ahmad.
Ya biyo ta yana magiya a kan ta ba shi lamba, ganin ta kusa shigewa ne ya sa ta waigo, ta aje mishi dubu biyu a kasa tana fadin “Don Allah kar ka shigo, ni matar aure ce, ga hakkinka nan ka dauka” .