Skip to content
Part 18 of 19 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

“Me kike tunani?” ya katse mata tunanin

“Ina tuna kai mutumin kirki ne, da ko wace mace za ta so ya zamo miji a gare ta. Wannan ya sa nake ganin ni din nan ban dace da kai ba”

Kallon ta yake sosai kafin ya ce “Me ya sa ba ki dace da ni ba?”

“Saboda ina da ciki.” kai tsaye ta amsa mishi tambayar, yayin da idanunta ke shimfide a kan fuskarshi, a kokarinta na nazartar yanayin shi.

“Kina da ciki!” ya fada a hankali kamar mai raɗa, lokaci daya kuma yana girgiza key din motar da ke hannun shi.

“Kina da aure kenan?” ya yi tambayar idanunshi a kanta

“Da dai ina da shi, amma yanzu ba ni da shi”

“kenan kin rabu da Baban yaron cikin ki?”

“Ban rabu da shi ba, na dai rabu da mijin da nake aure”

“You confused me!”

“That’s why na ce ban dace da kai ba”

Shiru ya yi kamar wanda aka umurceshi da yin hakan, har zuwa lokacin da aka fara kiran sunayen da ke cikin motar da aka siyawa Asma’u ticket.

Yana ji aka kira sunanta har ta shige bai iya motsawa ba.

Kasancewar saitin window take shi ya sa ta bude glass tana kallon shi. Har zuwa lokacin da direba ya fara warming din motar, daidai lokacin ya yi firgigit, hade da laluben inda zai ganta

Lokacin da ya samu sa’ar dora idanunshi a kan fuskarta ita ma shi din take kallo, duk yadda ya so ya isa wurinta kafafunshi sun ki ba shi haɗin kai, yana gani motarsu ta fice daga cikin tashar.

*****

RUMASA’U

Yau kam Goggonta (Mahaifiyarta) ce ta zo mata. Kafa da kafa Aibo ya tafi har ƙauyen ya faɗa mata Ruma ba ta da lafiya.

Haka nan ta cire kunyar yar fari ta zo gidan, saboda rabon da ta ga Ruman tun ranar da aka kai ta gidan miji. Kuma ƙa’ida da dokar gidan Alaramma ya aurar da yarinya ba ta zuwa gida sai ta shekera, muddin lafiya-lafiya. Sai ko idan haihuwa ta yi kafin ta cika shekarar.

Lokacin da Goggon ta shigo gidan Ruma kwance take kan tabarma a kofar kitchen tana ɗan shan hantsin safe.

Da gudu ta isa wurin Goggon hade da makale ta, cike da wata irin murna da farin ciki.

Goggon ma sai ta kasa boye murnarta da ɗokinta na ganin Ruma, a haka suka karasa ɗaki. Kafin Ruma ta gaishe ta cike da ɗoki.

Ta amsa tana kallon yadda Ruman ta ƙara wani zoƙalailai, fuskar fiyot. Cike da kulawa ta ce “Wai tun yaushe ba ki da lafiyar nan ne, na ga kin zube da yawa?”

“Bai fi sati ba, kuma na ji sauki, Yayanmu ne ya fada miki ba ni da lafiya?”

Girgiza kai ta yi hade da fadin “Mijinki ne ya je har gida ya fada min, ya kuma matsa lallai in zo in duba ki”

Ruman da ta saki baki tana kallon Goggo, ta rufe bakin cike da mamakin yadda Aibo ya canja a cikin sati daya, babu hantara babu wulakanci. Abinci da kanshi yake karbowa gidan Alaramma ya ba ta, ko ya sawo. Bayan dai wannan babu wata hira da ke shiga tsakaninsu. Yana kara linka kulawarshi a kanta, da zarar ya ga baƙi sun shigo duba ta, musamman ma fi kusanci da ita, ko wanda ya san za su iya ba Alaramma labarin abin da suka gani.

“Kina cin abinci kuwa? Ramar nan ta yi yawa?” Goggo ta katse mata tunani.

Nisawa ta yi a hankali kafin ta ce “Ina ci, ciwon ne ya buge ni sosai. Goggo yaushe za ki dawo gidanmu don Allah”

“Wani abu mara dadi yana faruwa da kannen ki ne?”

Kai ta girgiza tare da fadin “Babu komai, kawai dai na fi son in gan ki cikin gidan”

“Ni kaina ina son dawowa, Babankun ma yanzu yana son in dawo, matsalar ta Alaramma ce da Baba Malam. Bamu san yadda za su dauki abun ba”

Damuwa ta bayyana karara a fuskar Ruma, saboda ta san waye Alaramma, tauri ne da shi kamar arnan farko, idan ya ce a’a ko Baba Malam wani lokacin haƙura yake, saboda dukkansu da bazar Alaramman suke taka rawa.

“An ga Auwalun kuwa?” Goggon ta kuma katse mata  tunani

Hannayenta ta watsa kafin ta ce “Ban sani ba, ni ban ƙara jin wani ya yi batunshi ba”

Cike da takaici Goggo ta ce “Ai tsakanina da yaron nan Allah Ya isa, in Sha Allah sai ya gani a ƙwaryar shanshi”

Kafin Ruma ta ce wani abu suka ji sallamar Aibo.

Cike da girmamawa ya gaishe da Goggo, sannan ya dauki babban kwanon samira ya je ya siyo mata abinci.

Yayin da kannen Ruma wanda Goggo ta haifa da ma na Yaya suka yi wa gidan Ruma tsinke. Lokacin gama abincin rana Yaya da kanta ta kifo zane ta zo gidan Ruma ta kawo, suka sha hirarsu sosai da Goggo kamar ba kishiyoyi ba.

Sai da ta yi sallahr la’asar kafin Usman ya dauke ta a kan mashin ya kai ta gida.

Sosai Ruma ta warware, sai dai ramar da ta yi, wacce take sanyawa duk wanda ya kalle ta ya san ta yi ciwo.

A satin kuma Aibo ya fara shirin tafiya, yar ragowar masararta ya tsiyaye kaf ya siyar, wai ya kashe mata duk kudin motarshi a lokacin da ba ta da lafiya. Haka ya tafi bai bar ta da ko kwaya a cikin ɗaki ba bare kudi.

Ranar dai haka ta wuni da yunwa kuma ta kwana da ita, Sai da ta ji uwar bari ne da safe ta aika gida aka karɓo mata koko.

Ganin tana kokarin wuni da wata yunwar kamar jiya ya sa ta samu almajiri ya kira mata Yayanta Usman.

A tare suka taho da ɗan aiken, cikin zaure ya tsaya ita kuma ta saka hijab zuwa zauren, bayan sun gaisa ne ya ce “Aka ce kina kirana, ba dai jikin ba ko?”

Hawayen da take ta kokarin ɓoyewa suka ziraro mata. Cikin kukan ta ce “Dama…” Sai kuma ta yi shiru tana jan majina

“Dama me?” ya tambaye ta cike da kulawa

“Ya tafi ne, kuma babu abinci.” ta fada cikin muryar kuka.

“Komai ba ki da shi?”

Kai ta daga alamar eh.

“To shi kenan, za a kawo miki”

Ganin ya juya zai tafi ne ya sa ta ce “Ya Usman don Allah kar ka bari su Baba Alaramma su ji”

“Ba zan fada musu ba” daga haka ya fice daga gidan

Ba jimawa kuwa sai ga shi tare da almajirai dauke da masara kwano ashirin. Ya ba ta dubu daya ya ce zuwa gobe za a yo mata sauran cefanen.

Godiya sosai ta yi mishi, ko bai kawo mata komai ba, masarar ma ta ishe ta, ballantana ta san zuwa jibi har shinkafa za ta gani, saboda suna nomanta sosai. Shi kan shi Ya Usman din ya noma sama da buhu ashirin.

*****

ASMA’U

Misalin karfe 6:30pm suka sauka a babbar tashar jama’a.

Wani sanyin dadi ya rika ratsata, Sai take jin kamar an sauke mata kaya, amma daga lokacin da ta farka zuwa lokacin da take kan hanya sam hankalinta ba ya jikinta, ji take kamar ta fito daga cikin motar ta sanya kafafunta za ta fi sauri.

Keke ta dauka drop zuwa gidan Aunty Hajara, wacce ta kasance kanwa a wurin mahaifinta, haka nan ta ji ta fi samun nutsuwa da zuwa gidan fiye da gidansu.

Bayan mai mashin din ya aje ta ne ta nufi gate din hade da kwankwasawa, wajen mintuna goma sannan ta ji ana taɓa kofar, yayin da Aunty Hajaran ke fadin “Don Allah ko waye ya yi hak’uri wlh sallah nake…”

Daidai lokacin da bude gate din, ganin Asma’u tsaye kuma sai ta fasa karasa maganar take, ta yi tsaye baki bude tana kallon ta.

Bakin ta rufe haɗe da fadin “Asma’u lafiya? Daga ina kike?”

Runtse idanunta ta yi kam domin kuwa ta san wannan ita ce tambayar da duk wanda ya ganta a yanzu zai yi mata. Sannan amsar da za ta ba shi ita ce abu ma fi tayar da hankali fiye da ganintan.

Tuni ta ci alwashin ba za ta tsaya wahalar da shari’a ba, kai tsaye za ta fadi abin da ya faru, saboda ba ta ga amfanin ɓoye-ɓoyen ba.

“Kin yi shiru lafiya wai?” Aunty Hajara ta katse mata tunani

“Amma ba lau ba” cewar Asma’u a hankali.

Wannan ya ƙara sanyaya jikin Aunty Hajara, jiki a mace ta janye daga kofar Asma’u ta raɓata suka jera zuwa cikin falon.

Tsakanin zamansu da kuma tambayar da Aunty ta ƙara jefo mata ba a san wanne ya riga wani ba

“Ba dai sakinki ya yi ba ko?”

“To ga shi nan dai Aunty.”

“Me ya faru?” cikin zaƙuwa Aunty Hajara ta kuma tambaya, yayin da tashin hankali da damuwa suka bayyana a fuskarta.

Jakarta da ta dora bisa cinya ta sauke zuwa kasa lokaci daya kuma tana gyara zamanta kan kujerar, yayin da zuciyarta ke lalubo mata hanyar da za ta fadawa Aunty Ainihin abin da ke faruwa.

“Ina jin ki Asma’u, kin san dai halina, ban iya tashin hankali ba.” yadda Aunty Hajara ta yi maganar jiki a matukar sanyaye sai ya kara kashewa Asma’u jiki, take jin lallai ta aikata babban kuskuren, sannan ba ta kyautawa ahalinta ba.

“Aunty ban san ta ya zan fara fada ba, ban kuma san ta ya za ku kalli abun ba, amma maganar gaskiya ina cikin tashin hankali gami da nadamar da duk yadda zan kwatanta abun ya yi kadan. Don Allah ku yi hakuri ku yafe min kaddara ce. Kafin yanzu aka ce zan aikata wannan lallai zan ce karya ne, ina daya daga cikin wadanda nake kyara tare aibata masu irin aikata wannan abun ma, sai ga shi na tsinci kaina dumu-dumu a ciki. Shi ya sa aka ce ba ka yaɗa zunubin wani, kai ma sai Allah Ya jarabe ka da irin shi ga kam Allah Ya jaraba ni”

“Don Allah ki fada min”

“Aunty ina da ciki ne” Asma’u ta fada kai tsaye.

Cikin haske da ya haska falon Aunty Hajara ta aikawa da Asma’u wata irin harara kafin ta ce “Don ubanki don kina da ciki shi ne za ki baro gidan mijinki ki zo nan ki tayar mana da hankali.”a harzuƙe ta yi maganar

Kafin Asma’un ta ce wani abu Aunty Hajara ta ɗora” Wlh na kusa yi miki Allah Ya isa. Yar banzar yarinya kin zo kin daga mini hankali. Sai ka ce wacce ta yi cikin shege. Me ye abun tayar da hankali ciki da mai shi. Mtswww “ta karasa maganar hade da jan wani dogon tsoki

” Aunty idan cikin nan na Ya Ahmad me zai sa in taho gida? “cewar Asma’u tana kallon idanun Aunty Hajara

” Me kike nufi? Cikin ba na shi ba ne, to na waye? “

A kidime  Aunty Hajara ta jero tambayoyin.

Shiru Asma’u ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Wannan ya sa Aunty Hajara ta ce” Cikin ba na shi ba ne? “

Kai Asma’u ta daga alamar eh

” How do you know? “

” Saboda lokacin da na baro can period nake yi, kuma da na zo nan ma na yi, sannan da na koma ban same shi a gidan ba ma. “

” Asma’u! “Aunty Hajara ta kira ta with confused, kafin ta ce” Kin san me kike fada kuwa?”

Karon farko da hawaye ya ziraro daga idanunta, cikin muryar kuka ta ce” Wlh Aunty cikin nan ba na Ya Ahmad ba ne, ni ba zan dauki alhakinshi wajen renon jinin wani ba. Ya Ahmad mutumin kirki ne. “

Aunty Hajara ta shiga jijjiga kai cike da tashin hankali, kafin ta ce” Eh lallai abun kuka ya same mu. Asma’u kin kashe mu da ranmu. Yaushe nan mu ka gama gulmar yar makociyarmu da ta rasu wajen zubar da ciki. Ashe ni ma nawa abun gulmar na kan hanya. Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un ni. Hajara!”

” Asma’u me ya sa kika aikata haka? “yanzu kam Aunty Hajara cikin kuka ta fadi haka

” Ƙaddara Aunty, wlh kaddara, tun da nake sau daya na taba aikatawa, ranar da na bar garin nan zuwa gida, shi ne da na yi yamma na kira wani da muka hadu a Facebook na fada mishi ina son daki a hotel mai kyau, shi ne ya kama min ya zo ya tafi da ni, daga nan kuma ni ban san yadda aka yi ba” Asma’u ta gillo karya.

“oh ni Hajara, idan maganar nan ta fasu ina zan sanya kaina. Ke kuma don ubanki da ba sai ki yi zamanki a dakinki ba. Ai ana samun mata masu ciki kuma suna haila”

“Aunty zunubin sai ya y min yawa ai. Kin fa san waye Ahmad. In cuce shi har sau nawa kenan? Wlh ina jin tausayinshi.” cikin kukan da ke nuna alamar tausayin ta yi maganar.

Shiru Aunty Hajara ta yi kamar ba za ta sake cewa komai ba, Sai kuma ta ce “Kuma kin fi ni gaskiya. Ni kaina haka nan tausayi yake ba ni. Baya da hayaniya. Irinsu idan ka cucesu Allah ke rama musu da gaggawa”

“To kin gani” cewar Asma’u a sanyaye.

Duk suka kuma yin shiru, kafin Aunty Hajara ta mike zuwa inda wayarta take lokaci daya tana kokarin kiran wata lamba.

Ba jimawa kiran ya shiga Asma’u ta zuba mata ido tana kallon ta har zuwa lokacin da Aunty Hajarar ta ce “Baban Dady kana gida ne?”

Daga can daya bangaren Baban Dadyn ya ce “Ina kan hanyar komawa gidan dai. Lafiya ko?”

“Lafiya ƙalau, bari in karaso”

Daga haka ta yanke kiran idanunta a kan Asma’u da ta zuru-zuru tana kallon ta.

“Gara kawai a yi mai gabadaya haihuwa da mahaifa. Tashi mu tafi can gidan wurin Baban naki”

Narkewa Asma’u ta kuma yi kafin ta ce”Na shiga uku Aunty Babanmu kam zai kashe ni. Wlh ba da son raina na aikata ba”

“Don Allah ta shi mu tafi” cewar Aunty Hajara a, lokacin da take fita kofa. Sam hankalinta baya jikinta. Jin abun take yi kamar mafarki ko kuma a film. Har yanzu ta kasa gasgata abin da ta ji daga Asma’u.

Idan ban da abun yaran zamani ma, ta ya za ka kira mutum ba ka san shi ba, haduwa social media kawai, ka ce wai ya kama ma daki a hotel ka yi dare. Yanzu ba ga shi nan ba ya diga musu jaraba ba.

Haka suka rika tafiya shiru kowa da abun da yake tunani, basu jima a bakin hanya ba suka samu keke Napep. Mintuna goma ya kai su sabuwar unguwa.

Har kofar gida mai keken ya ajiye su, basu jima a kofar ba bayan sun kwankwasa Nabila kanwar Asma’u ta bude masu

Ita kanta baki bude take kallon yayar tata, yayin da mamaki karara ya bayyana a kan fuskarta,kila shi ya sa ta kasa magana sai gaba da ta yi a guje, da alama za ta kai rahoto ne.

Shigarsu corridorn ke da wuya kuwa suka ci karo da kannen Asma’un guda biyu maza Yusuf da Muhammad. Maimakon su makale ta kamar yadda suka saba idan sun ganta sai suka yi tsaye suna kallon ta sake da baki. Kila sun ɗauka da farko Nabila wasa take yi musu.

Daidai lokacin Momy tare da Dady suka fito. Cike da maɗaukakin mamaki suke kallon Asma’u.

Momy ta yi karfin halin cewa “Lafiya?”

Shiru Asma’u ta yi takure jikin pillar, saboda tun da ta su Momy suka fito ta ƙi gaba bare baya.

“Lafiya?” Dady ya juya tambaya kan Aunty Hajara.

“Ku mu je dai ciki” ta yi maganar lokacin da take nufar kofar da za ta sada ta da ɗakin Momy.

Gaf za ta shiga dakin ta juyo da kallon ta zuwa kan Asma’u tare da faɗin “A nan za ki zauna ke?”

Jiki a mace ta janyo kafafun haɗe da bin bayansu.

<< Abinda Ka Shuka 17Abinda Ka Shuka 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×