Sakwarar ta ture kafin ta ce" Wannan zan ci"
Duk suka yi dariya ita da Mama. Sannan Maman ta ce "Ba laifi kin yi kyau. Amma har yanzu na kasa yadda kina zaune a gidan nan cikin kwanciyar hankali."
Kamar ba za ta cewa Mama komai ba, Sai kuma ta fadi abin da ke damunta, na maganar auran Babanta, was Saboda ko jiya ta ji su Inna Kulawa na hirar, har suna cewa wai Malam Ayuba ya siyar da gonar shi da ka aka ba shi na gado, ya kuma bayar da jinginar wasu duk don saboda ya yi auran. . .