Skip to content
Part 19 of 48 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Sakwarar ta ture kafin ta ce” Wannan zan ci”

Duk suka yi dariya ita da Mama. Sannan Maman ta ce “Ba laifi kin yi kyau. Amma har yanzu na kasa yadda kina zaune a gidan nan cikin kwanciyar hankali.”

Kamar ba za ta cewa Mama komai ba, Sai kuma ta fadi abin da ke damunta, na maganar auran Babanta, was Saboda ko jiya ta ji su Inna Kulawa na hirar, har suna cewa wai Malam Ayuba ya siyar da gonar shi da ka aka ba shi na gado, ya kuma bayar da jinginar wasu duk don saboda ya yi auran

A sanyaye ta ce “Ba na fuskantar komai, Sai dai Babana wai aure zai yi, kuma a wannan dakin zai sanya matar, kuma ni ba na son zama a dakin su Inna Kuluwa”

Shiru Mama ta yi cikin nazari kafin ta ce “Shi Ayuban aure zai yi? To Allah Ya bayar da sa a. Kar ki damu, idan maganar auran ta tashi da gaske, zan zo gidan, idan ba zai ba ni ke ba, Sai ya ba ni damar gina miki daki madaidaici ki koma, tun fili ne dai ga shi nan a gidan kamar za a raba kwallo.”

Maganar ta yi wa Hafsat dadi sosai, saboda da abun take kwana take tashi.

Ita kam ba za ta iya rayuwa a dakunan matan Babannata ba, tana da kyankyami musamman yanzu da damuna ke karatowa. Ta san ba karamar wahala za ta ci ba.

” Mun yi magana da Nasir a kan gonar Innaki ta nan bayan gari wacce a ka ba ki, ya fada min Babanki yana neman wanda zai ba aronta, shi ya sa na zo ni in noma ta, tun kafin ya bayar da aron”

Hafsat ta yi sagale da spoon din da ke hannunta, yayin da maganar ta zo mata a bazata, ba ta san ma shirin Baban nata ba sai yanzu.

Dama ita kadai take shawara da zuciyarta, a kan za ta je ko sari shuka ne ta yi ma gonar. Yana matukar son gonar, ko yanzu idan kewar Innarta ta dame ta, sai ta saka hijabinta ta je gonar ta zauna.

Saboda yawon Inna ba ya wuce gonar, masara da farin wake take yi a gonar, wani lokaci kuma sai ta raba ta biyu, kasancewar tana da girma sosai, bangare daya ta sanya masara da farin wake, bangare daya kuma ta shuka gyada da dawa. Har kubewa ta na watsawa jefi-jefi.

Ga in yadda ta yi shiru ne Mama ta ce “Ba zan bar komai na ki ya lalace ba Hafsat, duk wata dukiya da aka ce ta ki ce, ina nan ina bibiyarta.

RUMASA’U

Tun bayan da Aibo ya tafi ba ta kara isassar lafiya, yau ciwo gobe sauki, ku san ko wane lokaci ba ta da lafiya.

Abin da kowa yake dauka ciki ne, musamman yadda wadanda aka aurar dasu tare suke ta faman laulayi. Sai dai nasu laulayin bai yi yawan nata ba.

Shi ya sa kullum ake cikin kawo mata jike-jike da rubutu.

Wani lokaci idan ta sha sai ta ci uban amai kamar za ta amayar da ƴan cikinta, dalilin da ke kara sanyawa su amince da hasashensu na ciki ne da ita.

Kamar yanzu ma aman ta gama, wanda ya jigatata, shi ya sa take kwance a wurin da ta yi aman tana mayar da numfashi.

Daga kwancen da take ta amsa sallamar da aka yi a hankali.

Malam Aisha ta shigo gidan sosai kafadarta sagale da akwatin digo na polio. Cike da tausayi take kallon Ruma da ke kwance ta ce “Ba lafiya ne?”

Kai ta daga alamar eh

“Subhnallah! Sannu Allah Ya ba ki lafiya” ta yi maganar lokaci daya tana sauke box din da ke kafadarta hade da kama Ruman ta kai ta cikin daki.

“Kin sha magani ne?”

Ruma da ke kwance ta yi nuni da kalolin jikakkun magunguna da ke gaban sif dinta.

Cike da kyankyami Malama Aisha ke kallon magungunan kafin ta ce “Ba ku je asibiti ba?”

Kai Ruma ta daga a hankali, ba tare da ta ce komai ba.

“Bari in samu Alaramman” cewar Malama Aisha a lokacin da take kokarin fita, ita kaɗai ce take iya zuwa gidan na shi don yin rigakafin digon polio, duk da bai taba bari an digawa yaran ba, amma hakan bai hana ta zuwa ba duk lokacin da ake polion, a matsayinta na focal person.

Kamar ko wane lokaci kofar gidan na shi akwai mashina, kekuna har da motoci, na mutanen da suka neman taimako.

Sai kuma dalibanshi da suke ta hidimominsu tsakanin, masallacin kofar gidan, makarantarsu, rijiya da kuma wuraran kwanansu.

A kofa ta tsaya tare da aika yaro don yo mata magana da shi. Ba jimawa kuwa ya fito ganin ta ya sanya shi dariya yana fadin “Ba ki gajiya ko Malama, sau nawa zan fada miki yaran rukuninnan ba a yi musu allurar nan. Babu zuwa asibiti, muna da magungunanmu na gargajiya”

Ita ma dariyar ta yi kafin ta ce “Haƙƙina ne yin hakan, koda ba za ka bayar ba, kuma na sani ko canja ra’ayi”

Cike da mamakin maganarta ya shiga girgiza kai yana fadin “Ai ra’ayina a nan ɓangaren ba zai canja ba, kamar yadda na ki ma ba zai canja ba, kin ga duk wadannan tsarabe-tsaraben da boko ya zo da shi ba da ni ba. Idan ba shiga gonar Allah ba, ta ya za ace wai an san abun da mace za ta haifa tun a ciki da kuma ranar da za ta haife shi”

Malama Aisha ta yi dariya, saboda yadda ta ga ya jahilcin abun, kafin ta ce wani abu ya dora da “Shi ya ma ni ba ni ba karatun bokon nan, da zarar an yi nisa cikin shi sai a kafurce.

Wata dariyar ta kuma ka yi kafin ta ce”A bar wa lokaci, shi ne alkali. Sannan akan hanyata ta zuwa nan, na shiga gidan Ruma na samu ba ta da lafiya.”

“Wlh ba ta jin dadi, iyayenta mata sun ce ciki ne.”

“Ya aka yi a ka san ciki ne, bayan ba aje asibiti ba?”

“To su cikin bakonsu ne, ko, kallon mace su ka yi muddin tana da ciki ai suna ganewa, bare sun ce duk wani alomomin cikin sun bayyana a jikinta”

Malama Aisha ta jinjina kai alamar tana fahimta kafin ta ce “Ba na jin akwai ciki a jikin yarinyar nan, Sai dai ko typhoid”

“To shi kenan a debo mata ganyen gwanda, shi ne kat a maganin typhoid”

Kai ta kuma jinjinawa, lokaci daya kuma suka yi sallama.

Bayan tafiyar ta ne ya juya kan Bara’u wanda ke zaune kan dakali yana rubutu

“Kai Bara’u zo nan”

Cikin hanzari ya taso zuwa gabanshi ya duka

“abokinku Aibo zai kai kwana nawa da tafiya”

Shiru Bara’u ya yi alamar tunani kafin ya ce “zai yi wata biyu”

“Ina son ya dawo gida nan da kwana uku, sannan a kafe shi, ban son ya kara fita.”

“An gama Malam” cewar Bara’u cikin girmamawa. Daga haka ya juya zuwa cikin gida.

*****

ASMA’U

Falon ya kasance shiru tsawon lokaci kafin Dady ya yanke shirun nasu da tambayar “Yanzu can gidansu Ahmad din, sun san abin da ya faru?”

Aunty Hajara ta yi saurin cewa “Kuskuren da ta yi kenan, ta ri ga ta sanar musu tana da ciki.”

“To me ye kuskuren a nan?” shi ma ya yi saurin tambayar

“Da ba sai ta koma dakin mijinta ba, mu kama bakinmu mu yi shiru, shi Ahmad din ya isa ya ce cikin ba na shi ba ne? Ina mai tabbatar maka murna zai yi, saboda yadda daman yake neman haihuwar nan ido rufe”

“kina nufin ya raini cikin da ba na shi ba Hajara, this will not happen, ba zan bari ba. Ahmad kam bai cancanci haka ba”

“To sai a cire ta koma.”

Ya kalli Momy da ta yi maganar kafin ya ce “A cire me? Babu wannan maganar, ba za a cire cikin nan ba.”

Cikin kuka Momy ta ce “Ban gane ba za a cire shi ba? Ko ba za ta koma ba ai, dole a cire shi, kana nufin za ta haife shi ne?”

“Kwarai kuwa, sannan a kaiwa mai shi, idan kuma babu mai shi din sai ta raini abun ta, amma wlh blh babu wani abu da za a yi wa cikin nan. Kuma ta bari wani abu ya faru a bayan idona ban yafe mata ba”

Cikin sauri Aunty Hajara ta ce “Gaskiya Baban Dady ka yi saurin rantsewa, ta ya za a bar cikin nan, wannan ba abun kunya da magana ba ne a wurinmu”

“Annabi ya yi gaskiya, dama ya ce *KAMATUDDEEN TUDAAN* Duk abin da ka yi ma wani kai ma sai an yi maka. Kuma ba kun iya surutu irin wannan ba. Yanzu ke yaushe mu ka gama magana a kan matar Auduu, kuka ce cikin jikinta ba na shi ba ne saboda bai haihuwa, amma ita daga zuwanta ta yi ciki. Saura kadan ku ja mana zuwa kotu, to yanzu ga shi a gidanki sai ki yi ta magana har ki gaji.” Ya kai karshen maganar idanunnshi a kan Momy. Lokaci daya kuma ya kanga wayar shi a kunne. Ba jimawa muryar Hakimi ta bayyana

Gaisawa suka fara yi kafin Dady ya ce” Sai ga Asma’u ta dawo gida”

Daga can bangaren Hakimi ya ce “Alhamdulillah! Na yi farin ciki, saboda a nan muna cikin tashin hankali da fargaba, musamman mijinta.”

“Allah sarki ai ta iso gida lafiya” Cewar Dady

“To Alhamdulillah Ma Sha Allah”

Duk suka yi shiru, wannan ya sa Dady ya ce “Ta fada mana duk abin da ya faru, don Allah ku yi hakuri ka haifi yaro ne ba ka haifi halin shi, yaran zamani sai addu’a, wlh…”

Hakimi ya yi saurin katse da fadin “Haba! Haba Alhaji Audu, wannan shi ake kira da kaddara, yarinyar nan ba ta yi kama da wacce ta taso gidan da ba tarbiya ba. Mun yi imanin kaddara ce ta fada mata. Mu da kai duk abu daya ne, abin da ya same ta mu ya sama. Allah ubangiji ya kyauta gaba.”

Wani irin daci da kunci ya baibaye zuciyar Dady, ji yake kamar ya rufe Asma’u da duka, ta tozarta shi, ta zubar mishi da mutumci.

“Shi kenan Ranka-shi-dade, mun gode Allah Ya kara girma” ya fada muryarsa cike da rashin jin dadin abun da ya faru

Daga can Galadima ya ce “Babu komai, sannan wannan abu zai tsaya a tsakaninmu ne, mu rufawa juna asiri don Allah. Hatta ƴan’uwan Ahmad basu san da faruwar wannan ba, kuma sha Allah ba za, su sani din ba.”

“Mun gode” cewar Dady yana kara jinjina dattako irin na Galadima.

Daga haka suka yi sallama, Dady ya sauke wayar a fusace yana kallon Asma’u da ta rabe jikin kofa ya ce “Wlh ki cutar da ni Asma’u, kin zubar min da mutumci gami da kima ta. Kin tozarta ni. Yau ji na nake yi kamar tsirara a bainar jama’a. Kin samu miji dan gidan mutumci wanda ya san darajar mutane, mutumin kirki, ga shi za ki rasa shi saboda son zuciyarki.” Daga haka ya fice daga falon, zuciyarsa na matukar suya, Momy kam da Asma’u kuka kawai suke yi. Aunty Hajara ce ta zauna shiru, kamar hoto. Abun duniya ya ishe ta ya dame ta, ba ta taba tsammanin wannan abun kunyar cikin zuriyarsu ba. Sai ga shi a kusa da ita ma fi kusanci.

HAFSAT

Wunin ranar Hafsat cikin farin ciki ta yi shi, ji take kamar kada Mama ta tafi.

Da safe kin zuwa makaranta ta yi, ta bi Mama zuwa gona, duk wani tsare-tsare da Mama da kuma Ya Nasir ke gami da yadda aikin zai kasance a gabanta a ka yi shi. Sai wajen sha daya na safe suka baro gonar zuwa gida.

Duk da ba wani sakewa Mama take yi da su Inna kuluwa ba, amma tana yi musu faran-faran.

Ba ta bar kauyen ba sai wajen karfe biyar na yamma, duk da irin jarumtar Hafsat ta aro don kar ta yi kuka hakan bai hana ta yin kukan riris ba.

Yanzu kwance take a cikin daki, lokaci zuwa lokaci hawaye na gangaro mata, saboda duk ji take babu dadi. Kewar innarta ta taso mata kamar yau aka ce ta rasu.

A can bangare daya kuma tana jin hirar su Inna Luba, duk da kasa-kasa suke yi hakan bai hana kunnenta dakko mata sautin ba, da inda hirar tasu ta dosa, hira suke a kan gobe za su je kauyen Malamawa a yi wa Malam Ayuba sha-sha-tau, a mantar da shi maganar aure. Ita ta fi kowa farin ciki da wannan abun, fatan Allah Ya sa aikin ya yi kyau, saboda ba ta son abin da zai raba ta da dakin Innarta.

Sallamar da yaro ya yi ne ta katse musu hirar.

“Wai an ce Hafsat ta zo.” cewar yaron bayan sun amsa mishi sallamar.

Tsakar gidan ya yi tsit, aya basu digawa yaron ba, har ya gaji da tsayuwa ya juya. Hafsat kuma ta fito daga daki, don ganin wanda ke kiran ta.

Bayan fitar Hafsat din ne, Inna Luba ta ce” Wai ita wannan yarinyar samari ne ke zuwa wurin ta ko me? “

Ba ki Inna Kuluwa ta tabe kafin ta ce” Oho mata.”

“Aiko idan samari ne da na yi mamaki, duk irin abun kunyar da ya faru da uwarta”

“Kina mamakin maza, to ai su da sun ga fari shi kenan. Ba ki ji har cewa suke fara ko mayya ce ba.” cewar Inna Kuluwa, kafin Inna Luba ta ce wani abu ta dora da

“Ke dai na ki ido, shi ma wannan Nasirun ba ki ga sai rawar kafa yake yi ba, babu abin da ba ya sai mata, ai kar nake kallon su.”

“Ashe ba ni kadai ba, kina ga kullum ya fita tana da kullin ledarta kamar wata matarshi, idan ba ta da lafiya ya yi ta rawar duwawu kenan”

Cikin salon gulma Inna Kuluwa ta ce”Abin da ya sa kika ga ban ja musu layi ba, waye bai san Nasiru dan iska ba ne a garin nan. Ko allura kika je sai ya gama mammatse miki mazaunai sannan ya tsira miki ita. Shi ya sa kika ga na ba banza ajiyarsu, ranar da ya dura mata ciki, Sai in ankarar da ubanta”

Inna Luba ta yi shewa alamun abun ya yi mata dadi sannan ta ce “Ai an ce abin da ya sa ma aka kore shi a asibitin garin nan kenan, latse matan mutane yake yi”

“Kwarai, ai Allah ne kawai ke rufa mishi asiri da ba a taba kama shi turmi da ta taɓarya ba.”

“To Allah Ya kyauta”

“na gaba”

Haka suka ci da gaba da gulmarsu, hade da mummunar fata wa Hafsat din.

HAFSAT

<< Abinda Ka Shuka 18Abinda Ka Shuka 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×