Skip to content
Part 20 of 21 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

JUMA’A  8:30AM

Duk da yadda aka sha ruwa, daren Alhamis, har zuwa wayewar garin juma’a zuwa karfe bakwai na safe ba, hakan bai hana da yawan ma’aikata zuwa wajen aikinsu ba, kamar yadda bai hana wasu ƴan makarantar zuwa makaranta ba, ciki har da Hafsat, wacce ta fito fes cikin uniform dinta, bayanta goye da katuwar school bag din ta.

Kuma sai a lokacin ne Inna Luba ke kwashe jikakkar tokar da ke cikin murhu a kokarinta na dora kokon safe domin karyawa.

“Ina kwana” cewar Hafsat lokacin da ta zo daidai rumfar girkin nasu

Inna Luba ta dago daga duken da take ta ce “Lafiya kalau” daga nan ba ta kara cewa komai ba, ita ma Hafsat din ba ta kara diga aya ba ta fice daga gidan.

Kamar yadda ta yi zato hakan ne ya faru, ta yi ta cin karo da dalibai wasu a keke wasu kuma a kafa, wasun kuma a mashin iyayensu ke kai kaisu.

Ta raba tafiyar tata tsakiya Nasir ya shiga gabanta da mashin din shi.

Ta yi saurin ja baya a tsorace, ganin waye kuma sai ta dan saki fuskarta.

“Na je gidan aka ce kin taho ai” ya yi maganar ba tare da ya amsa gaisuwar da take mishi ba

Kafin ta kara cewa wani abu ya mika mata ledar da ke hannunshi yana fadin “Na san ba ki karya ba”

Ledar ta karba, tare da fadin “Na Ci biscuit ai.”

“Biscuit da safe kuma, hau in kai ki school din sauri nake in koma gida in shirya zuwa wurin aiki”

Dire maganar tashi ta yi daidai da hawanta saman mashin din.

Shi kuma ya murza mashin din cike da kwarewa ya dauki hanyar makarantar tasu, suna taba yar hira kadan.

Bayan ya ajiye ta,kamar kullum 200 ya ba ta kudin break, ka’ida ne ko ba shi ya kawo ta ba, idan zai tafi wurin aiki sai ya tsaya ya ba ta. Idan ma aikin rana yake yi, to kafin break din zai zo school din ya ba ta.

“Yanzu ya za a yi ki yi break din, ban san shayin ya huce.”

Ta shiga waige-waige, saboda ita din ma tana jin yunwar.

“Ko staffroom za ki shiga?”

Ido ta waro kafin ta ce “Ba ruwana”

“To mu je wurin waccan bishiyar babu mutane sosai, sai ki ci a wurin”

Mashin din ta kuma hawa ya tuka su zuwa wurin bishiyar katuwar kanyar da ke bayan wasu classes.

Dutse ya dakko mata ta zauna, ta rika shan tea din ta cikin ledar kasancewar babu zafin da zai cutar.

Bayan ta gama ne ya kuma daukarta zuwa kofar class dinsu sannan ya tafi.

Lokacin da ta shiga ajin Uncle Najib ne ke bayar da darasi, jim ta ɗan yi, don jiran umurninshi, na ta shiga ko kar ta shiga, saboda ta san halin shi, idan har ya shiga aji babu mai shiga, kamar yadda yake korar mai surutu.

“Why are you coming late?” ya tambaye ta bayan ya hade fuska.

Kirjinta ya shiga bugawa, yayin da tsoron shi ya bayyana cikin idanunta.

“I’m asking you” ya katse shirun ta.

“I…”sai kuma ta yi shiru, tana kallon shi da fararen idanunta, da suka yi maiko

Bai san lokacin da ya ce” Go and seat down “

” Thank you”ta yi saurin fada, lokaci daya kuma tana nufar kujerar zamansu

Yau Na’ima ba ta zo ba, Farida ce kawai a kan kujerar.

Haka suka rika daukar darasi har zuwa lokacin da aka tashi, da misalin karfe 12pm.

Kamar kodayaushe sai da ta fara karbar abincinta wurin Maman Iyabo kafin ta wuce gida.

Wanka ta fara yi, ta ci abinci, sannan ta yi sallah, daga nan kuma ta haye gadon ta bacci mai dadi ya dauke ta.

A cikin baccin ne ta rika jin wani mummunan sako na shiga kunnen ta, dalilin da ya sanya ta tashi a firgice hade da fitowa tsakar gidan don tantance abin da ta ji a cikin baccinta.

“Musa me ya faru?” ta tambayi kanin nata da sauri saboda shi ne ya kawo rahoton.

A rude ya ce “Wlh Malam Nasiru mai Chemist aka kawo cikin motar ƴan sanda ya yi hatsari, Sai jini ke zuba, kuma an ce ya mutu, wai mota ce ta taka mishi kai”

Yadda mutanen gidan suka yi shiru, haka Hafsat ta yi shiru a kofar daki, ba ta san ko minti nawa ta dauka a tsaye ba, ba kuma za ta ce ga abin da ta tuna ba, abin da ta sani kawai shi ne maganganun Musa kanenta suna ta mata yawo a cikin kwakwalwa, sune kadai abin da ke mata amsa-kuwa.

Kamar jikakken tsumma haka ta ja kafafunta zuwa cikin daki, ta yi tsaye kafin daga bisani ta fada saman gado hade da fashewa da kuka, kuka take kamar shi ne aikin da aka ba ta yau, zuwa can kuma sai ta mike da sauri ta zira hajabinta zuwa waje.

Tafiya take kamar za ta tashi sama, so take ta tabbatar da abin da Musa ya fada mata, fatanta Allah Ya sa ba gaskiya ba ne, idan ma gaskiyar ne Allah Ya sa iya hatsarin ne bai mutu ba.

Tun da ta ɓulla santar da za ta sada ta da gidansu Nasir take cin karo da mutane fuska babu annuri, wannan ya sa kara sanyaya mata jiki, ruwan hawayen ya shiga bulbulo mata da sauri. Yayin da ta kara daga kafafunta a kokarinta na shiga kwanar gidansu Nasir din.

Turus! Ta yi, lokacin da ta shiga kwanar, saboda yadda ta ga mutane jimgim a kofar gidan, hakan ya sa ta gasgata lallai Nasir ya rasu.

Wata falwaya ta rungume ta shiga rera kukanta da dukkan zuciyarta, tana tsaye a wurin har aka fito da gawar Nasir aka sallace ta, sannan aka dauke ta don kai shi makwancinshi na karshe.

Lokacin da aka daga gawarshi sama, Daga inda take tsaye, ta hango yadda jini ya ɓata likafanin da aka lullubeshi da shi.

Haka ta rika bin gawar da idanu tana kuka har suka bacewa ganinta.

Kafin ta rarrafo zuwa gida, daki ta shige hade da fadawa saman gado, ta shiga kukanta with different styles, ta yi murya a bude, ta sharɓe, ta yi mai buge-buge. Duk wani style din kuka da ta canja ba ta mantawa da yi wa Nasir Addu’a

Ta yarda sai da nutsuwa da kwanciyar hankali ake ibada, ita dai yau daga sallar asuba da azhur da ta yi ba ta kara yin wata sallah ba.

Hausawa sun ce wai bacci ɓarawo ne, to ita dai ko sau daya bai gwada satarta ba, haka ta kwana kuka har asuba. Kuka ne guda biyu ta hade su wuri daya take yi,na mutuwar Nasir da kuma na tunawa da Innarta.

Ba karamin kokari ta yi ba, da har ta idar da sallahr asubar ba ta yi kuka ba. Sai dai tana sallamewa ta kifa kanta a wurin ta shiga rera wani sabon kukan

Wunin ranar dai ko ruwa bai shiga bakinta ba sai na alwala.

Kuma da alama ƴan gidan a wannan karon sun tausaya mata saboda har abinci suka rika kawo mata

Sai dai ko daya ba ta ɗandana ba, ita yanzu babu abin da take so irin ta mutu, cin abinci kuwa yana daya daga cik abin da zai iya yi mata shamaki da abin da take fata

Zuwa dare zazzabi mai zafi ya rufe ta, ga amai na rashin cin abinci. Maimakon ta damu da ciwon sai ta rika jin dadi hade da addu’ar Allah Ya sa ta mutu kafin safiya.

RUMASA’U

Tun asuba da ta yi sallah ba ta samu damar komawa ba, saboda wankin da ta dauki tsawon lokaci tana yi jiya, shi ruwan sama ya bata. Sam ba ta san an yi ruwan ba, Sai da ta fito sallahr asuba ta ga waje a jike.

Wasu kayan duk sun fado, Sai misalin karfe bakwai na safe ta gama wanke kayan da ruwan ya bata ta kuma shanya.

Kafin ta shiga neman abin da za ta ci, koko ta dama ta hada da kuli ta karya.

Duk Aibo bai san abin da ake yi ba yana ta bacci kamar ya mutu.

Sai misalin karfe tara ya tashi, ya yi sallah sannan ya sawo beridi da shayi ya sha abun shi a gabanta

Bayan ya gama ne ya ce “Tashi mu tafi asibiti, muddin aka gwada ki aka ga kina da ciki wlh sakinki zan yi, koda kuwa za a mayar da ni kuli-kulin kubra.”

Ita dai komai ba ta ce ba, ta dauki hijabinta ta saka, suka fice gidan yana gaba tana bin shi a baya.

Koda suka je asibitin ma shi ne ya yi bayanin abin yake so a yi mata, bayan fitsari gami da jininta suka karba.

Cikin 30mns sakamako ya fito inda ya nuna Ruman ba ta dauke da ciki.

Ita dai ba za ta ce ga abin da ta ji ba, farin ciki ko akasinshi, ita fa har yanzu ma ba ta fahimci komai na rayuwar da shi yake tunanin ta fahimta ba.

Yanzu kam ita ce a gaba, shi kuma yana bayanta, bakinshi bai yi shiru na aiko mata da baƙaƙen maganganu ba.

 “Wlh ki godewa Allah ba ki da cikin nan, idan kuma zubar da shi aka kara yi Allah Ya isa. Tun da ai ko shi Auwalun ya ce ba shi ne ya yi miki ciki ba, kawai lika mishi aka yi, saboda Alaramma ba ya son Yayarshi.”

Ita dai ba ta ce komai ba.

“Ya fada min su Tsohon da su Malam Mustapha sune suka miki ciki, kuma ba shi ne karon farko da suka miki cikin ba, zubarwa ake yi, wancan ne dai ya gagara.”

“Kai!!!” Ruma ta fada da alamun mamaki, kafin ta ce “Wlh karya yake yi, babu ruwan Ya Mustapha da Ya Tsoho, kuma Allah Ya isa” ta kai karshen maganar cikin zumbura baki.

Aibo ya juyo a fusace yana fadin “Ubanwa kike wa Allah Ya isar, kenan ma dai kin san kin yi cikin, yar iska watsastsiya, ai ni ne zan yi muku Allah Ya isa.”

Baki kawai ta tura hade da ja baya kadan don kar ya kawo mata duka, daga nan kuma ba ta kara tofa komai ba. Illa sauraronshi kawai da take yi, yana ta haushinshi shi kadai kamar karya

Bularsu kwanar rukunin gidajen nasu ke da wuya, suka yi kicibis da Alaramma zaune a kan rijiya, hannunshi rike da wata katuwar gora.

Hantar cikinta ta kada, musamman da ta jefa kwayar idanunta cikin ta Alaramma. Duk sai suka yi burki, ana kallon-kallo, wai Akuya kallon kura.

“Kai! Wato ka girma ka fara gaban kanka ko Aibo, da ranar Allah za ka tasa matarka zuwa asibiti wani kato ya lallatseta, sakarai mara kishi” cewar Alaramma a fusace lokaci daya kuma yana tashi tsaye daga kan rijiyar.

“Ku zo nan!” ya fada a harzuke hade da nuna su da hannu.

Ruma ba ta jira bin ba’asi ba, ta nade hajabinta hade da zurawa da gudu. Saboda ta san karamin aiki ne a wurinshi ya aje mata waccan gorar ta hannunshi.

Dukan da ta san zai iya sauke mata allon kafada.

A tsorace Aibo ya taka kadan zuwa wurin Alaramman, bayan ya dauke idanunshi a kan Ruma wacce ta tsilla da gudu kamar barewa.

“Ba ta da lafiya ne…” sai kuma ya yi shiru, ya kasa karasawa.

Saboda ya san dokar gidan Alaramma, ba a zuwa asibiti, magungunan gargajiya, rubutu da kuma na Islamic su ake amfani dasu. Sannan baya barin mata fita da rana tsaka, koma menene sai dai mace ta bari sai dare ya yi.

Kamar kuma su da suke karkashin shi, kafin su aiwatar da komai sai sun zo wajen shi sun nemi shawara.

“Wato kai idanunka sun bude ko, nema kake ka yi min rashin kunya, idan ka sanya kai ka tafi kamar tunkiya sai an nemo ka, ba ka bar ma yarinya abinci, duk fa abin da kake yi ina sane. Ni za ka nunawa ban isa ba?” ya kai karshen maganar hade da shirga mishi katuwar gorar a gadon baya.

Da sauri Aibo ya rike gorar yana fadin” Don Allah Malam ka yi hakuri, wlh ba zan kara ba”

“Karya kake za ka kara don ubanka” cewar Alaramma hade da fisge gorar ya aza mishi ita a karo na biyu.

Haka Aibo ya rika magiya Alaramma na shirgarshi har sai da su Malam Balarabe suka shiga maganar.

Tun da ta fito daga gidan Uncle Najib ya zuba mata ido, bai dauke ba har sai da ta kara so da da shi.

Ya janye idanunna shi a kanta lokaci daya kuma yana amsa sallamar ta hade da gaisuwa da take mika mishi

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya ce “Me ya sa yau ba ki je makaranta ba?”

Cikin sanyinta ta ce “Ban da lafiya ne”

“Me ya sa ba ki aiko ba?”

Shiru ta dan yi kamar ba za ta ce komai ba, Sai kuma ta ce “Tsakaninmu da Faridan akwai nisa kuma ba zan iya zuwa ba”

“Me yake damun ki?”

“Zazzabi ne, amma na ji sauki yanzu”

Ya zubawa fuskarta ido wacce ta nuna kamar ta yi kuka ta gaji.

Tun da yake a duniya, bai taba jin yana tausayin wata halitta ba, kamar yadda yake tausayin Hafsat, dama ga ta da zubin abun tausayi. Ji yake kamar idan ya kare service din shi ya tafi da ita. Sam ba ya son ganin ta cikin damuwa.

“Za ki iya zuwa gobe ko?” ya yanke shirun da ke tsakaninsu.

Kai ta daga alamar eh.

Daga haka ya ce ta je gida, Sai da ya ga shigewarta cikin gidan kafin ya tafi.

ASMA’U

Yau kwana biyu da dawowarta gida, idan ta ce ba ta taba shiga kunci da tashin hankali da ta shiga a kwanaki biyun nan ba, ba ta yi karya ba.

Ko lokacin da ta fahimci tana da ciki ba na Ahmad ba ta shiga tashin hankali irin na kwanaki biyun nan ba. Duk yadda take son cin abinci yanzu kam ba ta iyawa, tana ganin shi take kyale shi.

Tun zuwanta hankali mutanen ukun nan bai kwanta ba, Aunty Hajara, Momynta, da kuma Dadynta. Kullum Momy sai ta zo gidan Aun Hajara ta sha kukanta sannan ta tafi, yayin da Dady har asibitin cikin barrack ya kwanta. Aunty Hajara da take tare da Asma’un ma kullum cikin jimami take, musamman yadda Dady ya saba ranshi a kan kar komai ya samu cikin Asma’u, duk wanda ya sake ya yi wa cikin wani abu bai yafe ba.

Ko bai ce ba ma, ba ta jin za ta cire cikin, tsoro take ji sosai, shi ya sa ita ma ba ta goyon baya.

Hankalin kowa ya fi tashi ne a yau, inda kayan ɗakinta suka iso tare da takardar sakinta saki ɗaya.

Yau kam ta yi kuka mai tarin yawa, ta ji ta tsani Mk, wanda ya yi sanadiyyar raba ta da nagartaccen mutum irin Ahmad.

<< Abinda Ka Shuka 19Abinda Ka Shuka 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×