Wayarta ta janyo idanunta a kan agogon da ke jikin wayar, karfe shidda saura na yamma ya nuna mata.
Lambar Mk ta lalubo, ga mamakinta sai ta ji ta shiga.
Ido ta zuba ma wayar tana jiran ta ji waye zai daga, ba ta gama mamakin yadda wayar ta shiga ba, ta ji muryar Mk yana fadin “Hello! Waye?”
Maimakon ta yi magana sai ta yanke kiran, cike da mamakin jin muryar Mk.
Ganin ya biyo baya ya sanya ta dagawa a tausashe ta ce “Hello!”
Daga can Mk ya ce “Asma’u!” yadda ya kira sunan sai da zuciyarta ta buga, kafin ta amsa ya kuma cewa “Asma’u!”
Yanzu kam ta amsa a hankali, yayin da zuciyarta ta narke, sosai tana son Mk, duk yadda ya ba ta haushi sai ta ji ta kasa nuna mishi hakan
“Are you alright”
“I’m not”
“Me ya faru?”
“Ina da ciki.” kamar za ta yi kuka ta yi maganar.
Shi kuma cikin sauri ya ce “What, are you serious?”
“I’m serious Mk, almost 2month”
Da sauri ya mike daga kishingiden da yake, yayin da kirjinshi ke bugawa da sauri. Sai da ya waiga ko ina ya ga ba kowa sannan ya ce
“Cikin na waye?”
“Na ka ne”
“How do you know?” ya tambaye ta with confused
“Saboda lokacin da zan taho gida ina period, kuma na yi wanka da kwana biyu muka hadu da kai, time da na koma guda kuma mijina baya nan, bamu hadu ba sam.”
“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!!!” Haka rika fada cikin tashin hankali kafin ya ce “Kina ina yanzu?”
“Ina gidanmu”
“Me ya sa?”
“mun rabu da mijina sakamakon abin da ya faru”
“please Asma’u tell me you’re joking please”
“I’m not kidding you Mk, wlh ina gida yau aka kawo min kayana hade da takardar sakina”
Duk suka yi shiru, kamar ba waya suke yi ba, kowa da abin da yake tunani
Mk dai yana cikin kololuwar tashin hankali fiye da lokacin da AG ya kama shi. Ji yake ina ma mafarki yake, amma ta ina zai fara tsugunnawa ya fadawa iyayenshi wai yana da ɗa a waje, kai! Akwai sakel
“What is the solution now?” ya tambaya jiki a mace
“Babana ya hana a cire.”
“Dole a cire shi Asma’u, ba zan iya fuskantar iyayena da wannan abun kunyar ba, ta ina zan fara yi musu jawabi”
Cike da jin haushi ta ce “Ni nawa iyayen su mutu kenan ko Mk, zan rayu ko ba zan rayu ba, kai dai in cire, to ba zan cire ba gaskiya saboda ni kaina tsoro nake ji”
“OK za ki yi fadan ne? To ki gama”
Karshen maganar ta shi ta yi daidai da yanke kiran.
Fashewa ta yi da kuka, kukan da take jin shi har cikin ranta, ji take ina ma ta yi ta yin shi kar ya tsaya
Tausayin iyayenta ya kara kama ta, tana jin lallai ta yi musu ba daidai ba, Mk ma da yake namiji yana gudun abin da iyayensa za su yi, bare ita mace.
Lallai wannan babban kalubale ne a gare ta, da sauran mata ƴan’uwanta.
Ta so tambayar shi me ya faru da shi, sai kuma sawun giwa ya take na rakumi.
Jin shigowae kira ya sanya ta mayar da hankalinta kan wayar, sabuwar lamba ce, kamar ba za ta daga ba sai kuma ta daga din
“Husnah” aka kira sunanta
kasa-kasa ta amsa lokaci daya kuma tana laluben inda ta san muryar.
“Lukman ne daga Villa hotel”
Idanunta ta lumshe a hankali kafin ta ce “Barka yamma fatan kana lafiya?”
“Da sauki dai, a kan hanya ta ta komawa gida bayan na kai ki tasha na yi hatsari, shi ya sa kika ji ni shiru for 2dys”
A firgice ta ce “Subhnallah! Ya kake yanzu?”
“Alhamdulillah ina samun sauki, kaina ne ya bugu sai da aka yi min dinki, amma ina samun sauki, fatan kin isa gida lafiya”
“Alhamdulillah na isa lafiya, na gode da taimakonka, Allah kuma ya ba ka lafiya, Ya kiyaye gaba”
Numfashi ya sauke a hankali kafin ya ce “Amin na gode. Za mu yi magana.”
“To na gode ni ma” ta amsa lokaci daya tana kallon fuskar wayar, yayin da zuciyarta ta rika dakko mata hoton Lukman, Matashin saurayi ɗan gayu mai jini a jiki, tsabta da kuma nutsuwa.
Da ace kaddara ba ta hau kanta ba, tabbas da ta ba shi dama, shi kadai namijin da bai nuna mata maitarshi a fili ba.
AG
Bayan ya gama hada kayanshi tsab ciki jakar ya rufe. Sai ya juyo da kallon shi kan matarshi wacce ke zaune gefen gado tana kallon duk abin da yake yi.
Ji ya yi tausayinta ya kama shi, Laɗifa mace ce mai, hak’uri sosai da kawar da kai, ba a komai ne take magana ba. Wannan dalilin ne ya sa ko ya yi niyyar shuka mata rashin mutunci sai ya fasa, saboda hak’urinta.
Tun jiya yake dauki tafiyar, ya ji daren ya yi tsawo, yanzu kuma da ya shirya tsab don tunkarar abin da ke gaban shi, yanayin Laɗifar sai ya cire mishi kaso hamsin cikin dokin da yake yi.
Wannan ya sa ya zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinshi ya ce “Ummanmu (haka yake kiranta wani lokaci” kafin ta amsa ya ce “I’m sorry, kamar yadda na fada miki tafiyar nan ta gaggawa ce, ni kaina ban san da ita, but ba zan wuce 3dz ba kamar yadda na fada”
Jikinta ta zare daga na shi a hankali kafin ta ce “Ai ban ce komai ba”
“I know, but yanayinki ya kashe min jiki”
Murmushin karfin hali ta yi kafin ta ce”Kar ka damu, ai ka san haka nake, fatana aje lafiya a dawo lafiya “
Tsaye ya mike hade da ciro wasu kudin cikin aljihunshi ba tare da ya san ko nawa ba ne, Ya dora mata a kan kudin da ya ba ta tun farko.” Take good care of yourself and my kids please. You know how much I love you all. “
Kai ta jinjina hade da murmushi, ita ma sai ta mike hade da kwashe kudin ta matse su a hannunta, suka jera har gate, inda suka kara sallama ya fice. Saboda jirgin karfe tara na safe zai hau zuwa garin Jama’a.
Tun daga ranar da ya dora idanunshi a kan Asma’u, yau ce rana ta farko da kaso ashirin cikin dari na damuwar da yake ciki ya fara raguwa.
Shi kanshi ya san Allah Ya yanka mishi kazar wahala, ga shi nan kuma yana ta figarta
Idan ba jarabawa ba, ta ya zai ga an dakko mace zuwa hotel, kuma ya ji ya kamu da son ta. Kodai irin abun da Hausawa ke cewa abin da ka yi kai ma za a yi ma ka.
Idan haka ne ai shi bai taba zina ba, idan ba dai ko don ya bude inda ake zinar ba ne za a hukunta shi. Tabbas yana son Asma’u so kuma na aure, a shirye yake ya batar da ko nawa idan har zai same ta. Yanzu haka a fitowar da ya yi, ya daukar ma kanshi alkawari ba zai dawo gida ba sai da labari mai dadi wa zuciyarshi.
Karfe tara da ƴan mintuna jirginsu ya daga, zuwa karfe shadaya na safe ya sauka a babban tashar jirgin sama da ke Jama’a.
Tun daga airport din ya fahimci Jama’a gari ne mai kyau da tsari, jami’ansu cikin uniform masu kyau gwanin sha’awa.
Kai tsaye hotel din da ya yi browsing ya nufa. Sai da ya yi wanka ya canja kaya zuwa marasa nauyi sannan ya kira Laɗifa. Suka gaisa ya shaida mata saukar shi lafiya kafin ya kwanta bacci mai cike da mafarkai kala-kala ya dauke shi.
Misalin karfe biyu ya farka, ya kuma yin wanka hade da alwala. Bayan ya idar da sallah ya canja kaya zuwa manya, I’d card nashi ATM ya zuba aljihu, ya fice daga dakin bayan ya rufe kofar.
RUMA
ALHAMIS 5:30PM
A kofar ɗaki take zaune kan tabarma ta manna bayanta da katanga, lokaci daya kuma tana kallon almajiran da suke ta kokawa a tsakar gidan nata, wasu kuma suna shirya itacen da suka yo, don zuwa su sayar.
Kamar fadowar gini haka Aibo ya shigo gidan, dama shi ba sallama yake yi ba.
Wani bugu gaban Ruma ya shiga yi, kanta ya sara, dama yau ne ta fara samun sauki sosai, sakamakon shan magungunan da Malama Aisha ta kawo mata a boye. Yau kuma ga sabuwar matsalarta ya dira kamar daga sama.
Ba ta taba tsammanin ganin shi a wannan lokacin ba, saboda ba ta jin ko wata biyu ya rufa.
Almajiran da ke tsakar gidan suka rika sabewa daya bayan daya, har ya rage daga ita sai shi a tsakar gidan.
“Wato haka kike tara min katti a gida ba na nan ko?” ya yi maganar idanunshi a kanta
Ba ta ce komai ba, saboda yaran da yake magana a kansu akwai wanda ko shekara goma ma bai kai ba, ta san kawai neman bala’i ne irin na shi.
Dakin ya shige yana fadin “Ni dai Allah ya isa an cuce ni wlh, Sai da yarinya ta gama lalacewa aka hada ni da ita. Ban yafe ba gaskiya”
Duk abin da yake fada tana ji, saboda da karfi yake yi, kuma idan da sabo ta saba, hannun hagu ba bakon kazanta ba ne.
Tana jin shi yana ta fada da samirun da ke cikin dakin, motsin kirki ba ta yi ba.
Har ya gaji ya fito, ya zuba mata kananun idanunshi yana fadin “An ce min ba ki lafiya komai kika ci amai kike yi, amma kin san idan ciki gare ki ba nawa ba ne ko?”
Har ga Allah ba ta fahimci maganarshi ba, shi ya sa take ta kallon shi, tsawar da ya daka mata ce yana fadin “Ko ba ki ji ba?”
“Na ji” ta yi saurin fada a tsora ce
“To da ubanwa da ubanwa ke zuwa gidan nan bayan ba na nan”
Yadda ya tsare ta da idanune ya, sa ta ce “Ba, kowa, Sai Ya Usman.”
“Kenan cikin na shi ne?”
Ta kasa amsa mishi tambayar sai kallon shi da take yi
“Ba ki ji ba?” a, tsawace ya kuma fada
Kai ta girgiza alamar a’a, duk da ba ta san ma me a’a din nata ke nufi ba.
“Ai, gobe asibiti za mu je, idan har aka ce kina da ciki to wlh sakinki zan yi. Munafuka kawai yar iska.”
Zagin da ya yi mata ya fi ɓata rai saboda shi ta fi fahimta. Shi ya sa ta hade fuska tare da turo baki, alamun ba ta ji dadi ba.
Shi kuma ya fice bayan ya kwaso kayan dattinshi ya ce ta wanke mishi su kafin ya dawo
Ta bi kofar da ya bi da kallo cike da takaici, ta tsani yadda yake zaginta kamar wata ƴarshi.
Abin da ta fahimta duk wata daraja, kima, ilmi da kuma mutumci mace to gabadaya ya tattara ne a matacinta, da zarar ta rasa wancan abun da ko wane namiji yake hankoro to shi kenan, duk wadancan abubuwan sun tashi a banza, Sai ta zama a bar wulakantawa.
Kanta ya ishe ta misali, dubi daraja, kima da kwarjini irin na Alaramma, amma sai da laifin ta ya shafe shi, laifinta ya karya duk wata daraja da kwarjini na gidansu a idanune wadanda suka san abin da ya faru. Musamman Aibo.
Idan da haka nan ne Aibo ya yi kadan ya ci mata fuska kamar yadda yake ci mata yanzu.
Amma yanzu har Alaramma Aibo ba ya jin shakkar dankara mishi zagi a gabanta.
Hawayenta ta dauke a hankali, dakyar ta mike zuwa wurin tulin wankin da Aibon ya tule mata.
JAMA’A
Bayan AG ya fito daga hotel restaurant ya nufa, ya ci abinci, daga nan kai tsaye ya tare mai keke nape ya ce ya kai Airforce barrack.
Daidai inda doka ta nasu damar tsayawa nan mai keken ya ajiye shi.
Tsaye ya yi yana kallon kofar barrack din, wacce kafin ya isa wurinta sai ya wuce akalla gate goma na sojoji, wadanda suke shirye cikin shirin ko ta kwana, ga wasu motoci guda biyar wadanda aka daurawa bindiga, suna jiran mai tsautsayi. Fuskokin sojojin kadai ya isa ya razana mai laifi.
Ya kai awa daya a wurin yana ta lissafin ta ina zai fara, kafin daga bisani ya yanke hukuncin tunkarar gate din farko na sojojin kamar yadda ya ga masu shiga suna yi.
A ladabce ya gaishe su, kafin ya fitar da duk wasu ID cards na Shi ya nuna masu, sannan ya ce don Allah tambaya yake son yi.
Guda daga cikin sojojin ya ce “Wace irin tambaya.?”
“Ni sunana Abubakar Garba, na zo neman wata yarinya ne Asma’u Abdullahi , an tabbatar min mahaifinta Airforce ne.”
“Me ye sunan mahaifin nata ?” wani sojan ya tambaye shi
Ya dan yi shiru kafin ya ce “Ina expecting sunanshi Abdullahin, amma ban san second name din ba.”
“To ka san rank din Shi ko block nasu?” suka kuma tambayarshi
Ya shiga girgiza kai cike da sarewa, Sai kuma ya tuna Mk ya fada mishi sun bar barrack. Cike da kwarin gwiwa ya ce “An ce sun bar barrack zuwa cikin gari saboda mahaifinsu ya yi gini”
Sojojin suka yi shiru alamun nazari, wanda ya fi mayar da hankalinshi a kan AG din ya ce gaskiya akwai matukar wahala gano wacce kake nema. Wadanda suke barin barrack zuwa cikin gari suna da yawa, dama ace ka san sunan block din da suka zauna kafisu tashi abun zai zo da sauki. “
AG ya yi shiru zuciyarshi kunshe da damuwa, bai dauka abun zai zo mishi haka ba, ya dauka wannan gaɓar za ta fi ko wace gaɓar sauki sai dai ga shi tana neman fin ko wace gaɓa wahala. Saboda wurin da yake ba, wuri ne na shigar kowa ba, bare ya baza mutane su binciko mishi.
Numfashi ya sauke a hankali, yayin da fuskar shi ke bayyana damuwarshi, murya cike da rauni ya kalli sojan ya ce “Yallaboi ko zamu ɗan matsa can gefe kadan idan babu damuwa?”
Sojan ya kalli abokan aikinshi guda hudu, wadanda hankulansu ma ba a kansu yake ba.
Wannan ya sa ya dan yi gefe kadan, AG kuma ya bi bayan shi a kasalance.
Bayan sun ware din ne AG ya ce “Ni daga garin Nasara nake, kuma na zo garin nan ne kawai don yarinyar nan, ban san kowa ba, kowa kuma bai sanni ba. Iya dan abin da na fada ma shi kawai na sani gami da yarinyar nan. Shi ne nake son don Allah ka taimaka min, ka binciko min yarinyar nan, zan biya ka 100k”
Cike da mamaki sojan yake kallon AG, bai taba jin irin wannan abun ba, lallai So yana zautar da mutum, akwai tambayoyin da yake son yi mishi, amma dai baya son zurfafawa, da ya tambaye shi a ina ya santa? Ita din ta san shi? Me ya zai ba kanshi wahala haka, bayan bai da yakinin yarinyar ma za ta so shi ko a’a.
“Ya yarinyar take?” Sojan ya tambaya
AG ya gyara tsayuwarshi tare da fadin “Doguwa ce, tsawo fa mai kyau (Murmushi sojan ya yi, kafin AG ya ci gaba) tana da ɗan fadin fuska, kuma ita ba baka ce can ba, kuma ba fara ba”
Kai sojan ya jinjina kafin ya ce “Sha Allah zan yi ma kokari, Asma’u Abdullahi ko? Ka ce sun tashi daga barrack, so sanya min lambarka”
Lambar AG ya sanya mishi, sannan ya mika mishi 20k yana fadin “Na gode”
Haka suka yi sallama, Sai lokacin AG ya dan samu nutsuwa, fatanshi Allah Ya sa kwalliya ta biya kudin sabulu.
Muma muna yi mishi wannan addu’ar.