Skip to content
Part 23 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

*****

HAFSAT

Duk wani nauyi na Hafsat din Mama ba ta jin shi, saboda ranta a, bace yake, ji take kamar ta tafi Dawuri a kasa ba tare da ta hau mota, gidan gaisuwar da ta zo don shi din ma ba ta je ba. Bakin kasuwa ta dawo hade da tare mashin ya fitar da ita bakin hanya inda za ta samu motar Dawuri kai tsaye.

Zuwa lokacin Hafsat ta farko, sai dai kallo daya za ka yi mata ka fahimci ba ta cikin hayyacinta

Hausawa suka ce wai sa a ta fi sammako, mashin na dire Mama, mota ma na tsayawa. Shi ya sa 10mns ya kai su Dawuri daga nan kuma ta tare keke napep sai asibiti.

Kasancewar tana da lambar katinsu na Health Insurance ba ta Sha Wata wahala ba, ta samu ganin likita aka kuma basu gado. Sai a lokacin ta kira mijinta da kuma yaranta, Nabila, Juwairiyya da kuma Tajuddeen ta sanar musu da abun da ya faru.

Dukkansu basu rufe 30mns ba suka hallara a asibitin. A lokacin Hafsat bacci take yi, hannunta daure da ledar ruwa.

Cike da tausayawa Alhaji Aminu miji ga Mama Halima wanda kuma aka fi sani da E.S yake kallon Hafsat kafin ya ce “Ya kamata a wannan karon ki rike yarinyar nan wajen ki gaskiya”

“Ai mahaifinta ba zai bari ba, yanzu ma da bala’i na dakko ta”

Tajuddeen ya ce “A yi kararshi mana Mama, ko ya fi karfin hukuma ne, hatta dukiyar tata ma sai an karbe ta a hannun shi wlh”

Nabila ta yi caraf tana fadin “Tun yaushe nake fadawa Mama haka amma ta ƙi”

“Ba ƙi na yi ba Nabila, mahaifinta ya fi ni iko a kanta, sannan ita shari’a sabanin hankali ce, abin da kuke tunani daban, abin da kuma zai faru daban.”

“To a gwada yi mana Mama, a ga abin da zai faru din” Cewar Juwairiyya a karon farko da ta tsoma bakinta cikin hirar tasu

“To mu bari dai ta samu lafiya tukun” cewar Mama a hankali

E.S dai bai tofa ba.

Zuwa karfe shidda na yamma Hafsat ta fara dawowa hankalinta, har ta iya bude baki ta ce “ruwa” Nabila da dama idanunta suke kan Hafsat din ita ce ta daga da sauri zuwa saitin bakinta hade da kanga kunnenta tana fadin “Me za a ba ki?”

“Ruwa!” Hafsat ta dan daga murya kadan.

Juwairiyya ta miko wa Nabila robar ruwa ta bude, Mama kuma ta daga Hafsat din, ta sha ruwan kadan.

“Za ki ci abinci?” Mama ta tambaye ta cike da kulawa

Shiru ta yi idanunta a kan Maman kamar ba ta fahimci abin da ta fada ba.

Dalilin da ya sanya Mama kara maimaita tambayarta.

Da sauri ta girgiza kai alamar a’a, kafin ta lumshe ido, a kokarinta na tuna yaushe ta zo nan

Abin da za ta iya tunawa kawai shi ne Babanta ya ce ta tashi ta ci abinci, daga nan kuma ba ta san ya aka yi ba, Sai ta bude ido ta ga kamar Mama Halima ta rungumeta da wasu mutane zazzaune kamar cikin mota. Still ba ta san yadda aka yi ba, Sai yanzu da ta farka ta tabbatarwa da kanta a asibiti take. Kuma asibitin bai yi kama da na kauyensu makera ba. Ya fi mata kama da manyan asibitocin masu kudi da ake bayar da misalansu a cikin littafan da take karantawa.

Jin ana kokarin dago ta ne ya sanya ta bude ido da sauri, Nabila ce ke kokarin tayar da ita. Ita ma sai ta taya Nabilar mikar da kanta, su biyu ita da Juwairiyya suka kama ta zuwa toilet din da ke cikin dakin da suke. Kan toilet ta zauna suka mika mata brush ta yi. Sosai sai ta ji dadin bakin nata.

Su suka kuma kamo ta zuwa gadonta. Mama da ke rike da kofin shayi ta shiga ba ta a hankali har sai da ta sha da dan dama, sannan suka kwantar da ita.

Misalin karfe takwas aka kuma daura mata wani ruwan. Ba jimawa bacci ya kuma dauke ta.

Misalin tara na dare ES ya zo ya dauki Mama, Tajuddeen da Nabila, a ka bar Juwairiyya.

Misalin sha biyu na dare aka cire mata ruwan. Juwairiyya ta kuma hada mata tea mai kauri ta sha, bacci ya kuma dauke ta. Da asuba kam da kanta ta yi alwala, Sai dai sallahr a zaune ta yi, jikinta ba kwari.

Tana idar da sallahr Juwairiyya ta kuma hada mata tea ta sha hade da bread kaɗan, Sai ta dan ji karfin jikin kadan.

Saman gadon ta koma ta zauna hade da jingina bayanta tana kallon Juwairiyya da ke ta latsa wayarta cike da kwarewa.

“Aunty Ju!” Hafsat ta kira Juwairiyya da sunan da suke kiranta

Da sauri ta dago kai tana kallon Hafsat din

“Nan din ina ne?”

Murmushi Juwairiyya ta yi kafin ta ce “Asibiti ne.”

“Mama ce ta kawo ni ko?”

Kai Juwairiyya ta daga alamar Eh.

“Kin ji tana fadin Ya Nasir ya rasu?”

Yanzu kam idanu Juwairiyya ta zubawa Hafsat ba tare da ta ce komai ba

Hawaye suka shiga gangarowa Hafsat, cikin kuka ta ce “Da gaske Ya Nasir ya rasu shi ma kamar yadda Innata ta rasu. Yanzu kuma ba ni da kowa sai Mama. Ina ma Mama ba ta kawo ni asibitin nan ba, so nake in mutu ni ma”

Juwairiyya da dama ita ba ta kallon mai kuka ba ta yi ba, take ta fara hawaye, ta mike zuwa kusa da Hafsat din, cikin sigar lallashi ta ce “Ki yi hak’uri Hafsat, Allah Ya na tare da ke, ki yi musu addu’a ba kuka ba. Sha Allah suna a makwanci mai kyau”

Kai Hafsat ta shiga girgizawa, yayin da zuciyarta ke yi mata wani irin zafi. Ruwan hawaye ya ci gaba da wanke kumatunta.

“Ya Nasir rawa da yawa yake takawa a cikin rayuwa ta Aunty Ju, shi ne duk wani farin cikin la, bayan rasuwar Innata ban rasa komai ba, Sai dai kawai kewarta. Amma Y Nasir ta yi min komai. Yanzu kuma na rasa shi. Shi ya kai ni makaranta fa a ranar.” ta karasa maganar cikin kuka mai sauti

Juwairiyya ya ma sai ta kara rushewa da kukan

Cikin kukan ta ci gaba da cewa” Ya ce min in yi sauri in karya, sauri yake ya koma gida ya yi shirin tafiya wurin aiki. Ashe tafiya ba ta dawowa ba. Aunty Ju wlh ina fatan mutuwa. Ni kadai na san yadda nake ji. Gani nake yi kamar babu sauran wani jin dadi da ya rage min”

“Ki bar fadin haka, in Sha Allah za ki yi farin ciki nan gaba, jikina yana ba ni haka” cewar Juwairiyya a lokacin da ta rungumota sosai zuwa jikinta

Haka suka yi ta kuka har Juwairiyya ta yi shiru, Hafsat kam da ta dan fara yin shiru sai ta kuma rushewa da kuka, har sai da nurse din da ke kula da ita ta shigo duba ta, sannan ta dan tsagaita da kukan.

Bayan fitar nurse din ne ba da jimawa ba Nabila ta shigo hannunta rike da basket.

Bayan ta yi wa Hafsat sannu ne hade da yi mata fadan yawan kukan da take yi ne, ta hada mata tea gami da sanya mata pepesoup na kayan ciki ta kuma mika mata bread

Nabila ta kalli Juwairiyya da take kurbar tea ta ce “Aunty Ju kin san wani abu kuwa?”

Ba iya Juwairiyya ce ta dakata da sipping tea din da ke yi ba, har da Hafsat.

Zama Nabila ta gyara kafin ta ce “Muna shirin tahowa asibiti kawai sai ga police wai an yi karar Mama”

Da sauri Juwairiyya ta aje kofin tean da take sha a kasa tana fadin “Waye ya yi karar ta?”

“Babansu Hafsat. Wai ta je har gida ta dauke mishi diya. Yanzu haka dai suna police station.”

Juwairiyya ta yi shiru cike da jin haushi, tana son fadin magana mara dadi a kan Malam Ayuba kuma tana jin nauyin Hafsat.

Ita ma Hafsat din shiru ta yi, cike da jimamin abin da ya faru.

Ba tun yanzu ba ta san Mama Halima ba ta shan inuwa daya da kowa a gidansu. Zai wahala ta je garin ta baro shi ƙalau ba a yi fada ba

Ita ba ta da hak’uri ko kadan, ba ta iya dannewa idan ta ga an yi wa yar’uwarta rashin adalci.

Da a ce ana karar mutanen gari gabadaya, tabbas da Mama Halima ta yi karar mutanen garin Maƙera gabadayansu. Saboda kazafin da suka yi wa ƴar’uwarta.

Sai ɗakin ya koma shiru. Hafsat dai komawa ta yi ta kwanta lamo kamar mai bacci. Su Nabila kuma hankalinsu ya fi karkata a kan kiran waya suna tambayar ya ake ciki, me ke faruwa?

AG&ASMA’U

Nutsuwa ya yi sosai yana kallon duk inda suke wucewa, yayin da zuciyarshi ke cike da fargaba gami da abun da zai je ya taras.

Jikinshi yana ba shi akwai wani abu ba daidai ba gami da Asma’u. Musamman yadda mahaifinta ya tambaye shi ko shi ne ya kama mata daki a hotel. Ta ya mahaifinta zai san an kama mata daki a hotel?

Da wannan tunanin suka isa kofar wani gida.

Alhaji Abdullahi ya yi parking suka fito tare. Lokaci daya kuma ya kanga wayar da ke hannunshi zuwa kunnen shi yana fadin “Zo ki bude kofar”

Bayan ya sauke wayar ne ya kalli AG wanda ya yi tsum ya ce “Gidan kanwata ne, mijinta ya rasu shekera daya baya. Shi ma soja ne, amma land army”

“Allah Sarki, Allah Ya jikanshi, Ya gafarta mishi” Cewar AG a sanyaye

“Amin” Alhaji Abdullahi ya amsa lokaci daya kuma yana nufar kofar da Aunty Hajara ta bude

Suka jera su biyun Alhaji Abdullahi yana kara yi mata bayanin AG, yayin da AG kuma ke bin su a baya, jiki babu kwari.

Har babban falon gidan suka isa, Alhaji Abdullahi ya yi mazauni a daya daga cikin kujerun da ke falon

 AG kuwa kasa ya zauna hade da mikawa Aunty Hajara gaisuwa cike da girmamawa sannan ya mayar da kanshi kasa ya soke.

“Kira Asma’un ina sauri ne, na baro aiki a office, kuma Ina da baƙi”

“To” ta amsa hade da juyawa, ba jimawa suka dawo tare da Asma’u, wacce a lokacin Auntyn ta tashe ta a bacci

Daga can nesa ta duka hade da gaishe da Baban nata, ya amsa ba yabo fallasa, kafin ya ce “Kin san wannan?” ya yi maganar hade da nuna AG da yatsa

Ta juyar da akalar ganinta kan AG, daidai lokacin shi ma ya dago, kwayoyin idanunsu suka hadu.

Da sauri ta bude baki alamun mamaki, ta yi saurin dauke idanunta zuwa kan Alhaji Abdullahi wanda dama ita yake kallo.

Ta sake dora su kan AG, yanzu kam tsoro ma abun yake ba ta, Anya ba aljani ba ne, ta fada a zuciyarta

“Kin san shi?” Alhaji Abdullahi ya kuma tambaya

Girgiza kai ta yi hade kuma da daga kan, wanda ke nuna alamar eh da kuma a’a

“Be specific!” Yanzu kam cikin tsawa Alhaji Abdullahi ya yi maganar.

“Ni sau daya na taba ganin shi” ta amsa a firgice

“Yana da alaka da abin da ke jikin ki” kai ta girgiza alamar a’a

“Tashi ki je”

Da sauri ta mike zuwa inda ta fito, har zuwa lokacin a rude Kuma a kidime take.

Alhaji Abdullahi ya juya kan AG yana fadin “Ita ce Asma’un da kake nema?”

Kai ya jijjiga alamar eh.

“Me ya sa kake neman ta?”

Kanshi a kasa ya ce “Har ga Allah auranta nake son yi.”

Shiru Alhaji Abdullahi ya yi, kamar ba zai ce komai ba, Sai kuma ya ce “A lokacin da ka ganta tana da aure, amma zuwa yanzu babu auran, Sai dai ba ta yi idda ba, saboda tana da ƙaramin ciki.”

Kai AG ya jinjina alamar gamsuwa da bayanin Alhaji Abdullahi.

“Tun da ka ga wuri, idan kana da bukatar auran nata har nan gaba, za ka iya dawowa, mun kuma gode sosai”

“Ni ma na gode” cewar AG a hankali.

Alhaji Abdullahi ya mike tsaye yana fadin “Idan ba damuwa za mu iya tafiya, akwai masu jirana a office”

Jiki ba kwari AG ya mike tsaye, ya so ace an ba shi damar keɓancewa da Asma’u, akwai maganganun da yake son su yi. Kila an hana shi damar ne saboda ba ta gama idda ba.

Kamar yadda suka taho shiru, yanzu ma haka suka juya shiru, har Alhaji Abdullahi ya aje shi a bakin din barrack, suka yi sallama inda AG ya karbi lambar Alhaji Abdullahi a kan z su rika gaisawa.

*****

RUMASA’U

Tun safe take neman wayarta, wacce take taya ta hira, ta hanyar jin Waka, wa’azi ko kallon film, amma har yanzu da aka fito sallahr la’asar a masallacin gidan Alaramma ba ta ga wayar ba.

Wannan ya kara tsananta bacin ranta, ta yi zaune a gefe gado cike da takaici.

Kaf dakin babu inda ba ta bincike ba ba ta ga wayar ba.

Kuma da za ta kwanta bacci a kasan pillow ta aje ta kamar yadda ta saba.

Tana daga zaunen ta ji dawowar Aibo. Ko motsi ba ta yi ba har ya shigo dakin, hannun shi rike da tsumman da ya yo gammo.

Ya zuba mata ido, ganin yadda take ta kumburi.

“Ke ni kike harara?” ya yi tambayar cikin fada

Ba ta amsa ba, har sai da ya kara maimaita tambayar tare da matsowa kusa da ita

Ta yi saurin mikewa tsaye tare da fadin “Ba wayata ce ban gani ba.” cikin kuka ta karasa maganar.

Sai a lokacin ya tuna ma ya daukar mata waya, ya yi tsammanin ma ko don bai ba ta 200 abinci ba ne, ya sa take fushi

“Mtswww!” ya ja tsoki tare da fadin “Da Allah can ni je ki kasa min icce, kuma ki fasa manyan nan.”

Gefen shi ta bi ranta a matukar bace, ko yunwar da take ji ba ta dame ta ba irin batan wayarta. Haka ta rika fasa itacen tana kuka. Kukan bacewar wayarta.

Shi kuma ya fita, ba jima ya dawo rike da roba, wacce ya dawo shinkafa da miya da wake.

Kan dankarin kofar kitchen ya zauna ya cinye tsaf ya sha ruwa ya kuma ficewa daga gidan.

Ba ta wani damu ba, baƙin cikin da take ciki ya fi na karfin kwalelen da ya yi mata tun da ba yau ya fara ba.

Sai dare wani almajiri ya shigo ta aike shi a sace ya karbo mata tuwo gida ta ci.

Haka ta kwanta babu dadi ranta, haka kuma ta tashi da kunci. Ba ta san haka ɓatan waya yake da zafi ba, sai da ya zo kanta.

Tana zaune a kan kujera da safe rai a bace, Aibo ya shigo ko bai fada mata ba, ta san karyawa ya je ya yi, ita kuma tun jiya ko sulaibiyar ba ta hada su da ita ba. Sai wahalar kasa mishi itace.

Yadda bai yi sallama ba, haka ita ma ko kai ba ta daga ta kalle shi ba, sai da ya fara sauke mata samiru ne ta ce “Me kake nema?”

“Ban sani ba.” ya amsa mata kai tsaye.

Saiti biyu na Samirun ya hada wuri daya ya fice da su zuwa waje.

*****

<< Abinda Ka Shuka 22Abinda Ka Shuka 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×