Skip to content
Part 29 of 48 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Shiru Alaramma ya yi kafin ya ce “Rufin bakin na gabadaya, ko mutum ne kwara daya?”

Khalid ya juya kan Mk wannan ya sa Mk ya ce “Eh to kamar dai duk wanda yake da hannu a lamarin”

“Akwai sunansu ai ko?” Alaramma ya kuma tambaya

Mk ya jinjina kai alamar eh

Littafi Alaramman ya mikawa Mk yana fadin “Rubuta min sunansu a nan” saboda shi idan ban  sunan shi, to ba ko wane suna yake iya rubutawa ba farat da garaje. Sai idan da ajmi, da boko kam, ba lallai ya iya rubutawa Shi ma rubutun sai ka rantse da Allah ɗan primary one ne ya yi shi. Amma a ido da cikar zati za ka dauka professor ne.

Mk ya karba hade da zana sunan Asma’u, Aunty Hajara, Alhaji Abdallah da kuma sunan Momy wato Maryam. Saboda idan bai manta ba, Asma’u ta sha fada mishi sunan Mamanshi daya da Mamanta. Kuma sunan Mamanshi Maryam.

Alaramma ya shiga kokarin karanta rubutun, wanda ya dauke shi ku san minti talatin kafin ya gane.

“To yanzu za ku dan kara jira don Allah, akwai rubutun da zan sanya a yi, Sai ka sha. Shan rubutun yana nufin ka shanye su, babu abin da za su iya. Sannan kuma za ku dawo nan da kwana uku ko biyu, akwai layar da zan ba ku, Sai aje a jefa ta a cikin ruwa rijiya ko rafi, amma wanda baya ƙafewa”

Khalid ya jinjina kai alamar yana fahimta.

“Sannan akwai layar da za a daga dutse a danne, a samu dutsen da aka tabbatar ba a dagawa” yanzu kam gabadaya suka jinjina kai alamar fahimta.

Bai yi magana ba, Sai waya da ya dakko ya kira Usman.

Ba jimawa Usman din ya karaso.

Alaramma ya mika mishi sunayen mutanen da Mk ya rubuta yana fadin “Ka, je ka samu Malam Razzaƙu, Bara’u, Mustapha, Gambo da kuma Hudu. Ko me suke yi su ajiye, wadannan sunayen nake so a yi wa rubutun ɗaure baki” Usman ya amsa cike da, girmamawa.

Alaramma kuma ya mike zuwa gida ya fitowa da su Mk abinci, aka canja musu wuri yayin da ya ci gaba da ganawa da, baƙin shi.

HAFSAT

Ranar Asabar ita ce ranar da ta kama za a yi taron yaye dalibai karon farko a makarantarsu Hafsat.

Kuma rana ce da malamai gami da daliban suka yi wa shiri, don ganin sun fita kunyar ma’aikatar ilmi, da nunawa jama’a suna sauke nauyin da aka dora musu.

Sun gayyato manyan mutane, musamman na karkashin hukumar ilmi. Babban baƙo kuma uban taro shi ne Muhammad Inuwa Hakimin Dawuri Galadiman jihar Tanga.

Hukumar makarantar ta tsara shirye-shirye masu ilmantarwa, fadakarwa da kuma nishadantarwa.

Don kayatar da baƙi hade da daga darajar makarantar a idon mutane.

Shi ya sa tun misalin karfe takwas na safe masu decoration suka fara gyara filin taro. Runfuna shidda aka kafa. Biyu na baki maza, biyu baki mata, daya malamai daya kuma dalibai.

An kayata wurin ta yadda ko waye kai ka zo sai ka ji wurin ya burge ka.

Wannan ya sa mutanen gari yi wa makarantar tsinke, wadanda aka gayyata dama wadanda ba a gayyata ba. Har da matan aure ba a bar su a baya ba, wajen zuwa kashe kwarkwatar idanunsu. Musamman da ba taɓa yi aka yi ba.

Misalin karfe goma makarantar ta cika maƙil, motoci kam gasu nan kala-kala. Ku san kowa da aka gayyata ya iso. Mama Halima ma da ta tawagarta sun iso kamar yadda suka yi wa Hafsat alkawari. Musamman da ya kasance mijinta na daya daga cikin wadanda aka gayyata. Hatta Galadima ma ya iso da tawagarshi. Cikin shiga ta alfarma da ke nuna shi din mai mulki ne.

Daidai lokacin kuma Mc ya fara announcing cewa za a fara abin da ya tara mutane

Limamin garin makera shi ne ya fara bude taro da addu’a.

Sai bayanin maraba daga shugaban makaranta. Sannan bayanin muhimmancin ilmi, da kuma yadda tsarin ilmi yake, da irin yadda hukumar ilmi ta tsara yadda za a bayar da shi. Matakan da Malamai ya kamata su bi wajen bayar da shi din daga nakin ES Alhaji Aminu mijin Mama Halima. Daga nan jawabin Chairman na karamar hukuma kan irin gudunmuwar da suke bawa makaranta, da irin rawar suke takawa.

Sai kuma jawabi, babban baƙo kuma uban taro Alhaji Inuwa Galadiman Tunga.

Bayan gama duk wadannan jawabai aka tafi kan agenda ta gaba. Wanda speech ne daga bakin head girls na godiya ga Allah SWT da ya kawo lokacin gama makaranta lafiya, Sai godiya ga iyaye da malamai kan irin gudunmuwar da suka basu. Duk jawabin da harshen turanci take yi. Bayan ta kammala kuma aka shiga agenda ta gaba. Inda dalibai na English club suka shigo da welcoming song, wakar da ta burge kowa aka rika yi musu liki kamar ana biki.

Bayansu, Sai kuma debate, turn din su Hafsat Kenan. Haka aka shigo da seat na zama guda biyu, opposing side da Kuma supporting.

Bayan daliban sun zauna, Mc ya gabatar da topic din debate “Wadannan dalibai za su yi muhawara ne a kan iyaye ne ya kamata su zabawa yara abin da ya kamata su karanta a makarantar gaba da secondary, ko yaran ne ya kamata su zabi abin da suke so su karanta a makarantar gaba da secondary”

Hafsat ce 1st speaker from supporting side, ta fito calmly cikin gogaggun uniform dinta da suka kara fito da ita a matsayin cikakkar daliba.

Bayan ta gabatar da sunanta ta shiga zazzago ruwan hujjoji cikin harshen turanci, yayin da tafi ke tashi raf-raf-raf.

Malam Ayuba sai dashe baki yake yi, duk da bai san me take cewa ba. Amma jin shi yake ya yi sama. Musamman yadda mutane ke ta danganta shi da Hafsat din, ana cewa ƴarshi ce.

Bayan gama debate still welcoming song from Hausa club su ma suka shigo. Liki kam har da mutanen gari ba a bar su a baya. Kila don a wannan karon suna jin abin da ake fada ne. (ni ce na ɗan dara, kada a rika yin abu ba wasa ba dariya)

Bayan fitar yan Hausa club, Sai kuma aka kara juyowa kan su Hafsat inda za su gabatar da quiz tsakaninsu da masu fita.

Duk da mafi yawan ƴan kauyen basu san me ake tambaya ba, me kuma ake bayar da amsa sosai Hafsat ta Farida suka burgesu, Farida bangaren Math’s take mai karanta questions na dire tambayar shi take fadin amsa, yayin da Hafsat take bangaren English, biology, chemistry da Kuma agriculture. Abubakar Kuma aka bar mishi physics da geography.

Quiz din har sai ya fi debate din kayatarwa, musamman ga wadanda suke jin tambaya da kuma amsar. Tafi kawai kake ji raf-raf-raf ko ta ina. Kowa ka kalli fuskarshi akwai Nishadi, musamman shugaban makaranta gami da malamanshi.

Bayan fitarsu Hafsat kuma aka tafi career day.  Daliban da suke wakiltar malaman makaranta sune suka fara fitowa mace daya da kuma namiji daya, cikin shiga ta malamai, suka fadi waye malamin makaranta, me ye aikinshi da kuma muhimmancinshi ga al’umma.

Bayan fitarsu sai manoma, nan mace daya namiji daya, su ma da shigar manoman, yar shara da fatanya.

Daga nan sai likitoci Hafsat ce ita da wani yaro Yusuf Muhammad.

Ko wannensu cikin shigar likitoci. Shigar da ta yi wa Hafsat kyau sosai, kamar wata mai koyan sanin makamar aiki a asibiti. Su ma suka yi nasu gwanin sha’awa suka fita. Malam Ayuba fa baki har kunne, mamaki yake wai Hafsat ce haka. Bai taba tsammanin makarantar nan ana koyi har haka ba. Kodayake ba shi kadai ba, duk mutanen kauyen wannan taro ba karamin tada musu tsumin kara jajircewa a kan yaransu.

A nan ne manyan baki suka rika yiwa daliban da suka yi carrier day kyauta, duk wanda aka ambaci sashenshi sai da ya yi kyauta.

Wani kuma sashen da ya burge shi yake yi wa kyauta.

After career day Sai aka shiga cultural day representing.

Da Hausawa aka fara, inda Ni’ima ce ta yi representing Hausawa

Daga nan sai Fulani, nan kuma Hafsat ce ta wakilta. Tun da ta shigo filin ake tafi. Complete ta yi shigar Fulani babu abin da ta rage. Dama ga ta fara, ga kitson Fulanin an yi mata gashin nan na gaba har kan kirjinta kamar an yi mata kari, ga Daagaa ta kafa da hannu ta sanya, ga ta wuya da saman goshi. Sai ta fito kamar dai ba fillatanar. A ranar ƴan kauyen suka tabbatar da Hafsat mai kyau ce, a wannan karnin za su iya cewa kaf garin babu mai kyanta. Kamar ba Malam Ayuba ne ya haife ta ba. Wanda ya zama Cele a wurin taron ta dalilin Hafsat kowa son ganinshi yake. Shi ya sa sai dargaje baki yake yi.

Cikin harshen Fulatanci ta gabatar da kanta, yadda take fitar da yaren ka rantse da Allah dama can bafillatanar ce. Ta fadi su waye Fulani, ya suke, wace gudunmuwa suke bayarwa ga al’umma. Sannan cikin kwarewa ta shiga dama furar da aka sanya mata a cikin ƙwarya hade da lafiyayyen nono mara gauraye, saboda yau ɗin nan ma da safe Bammi mai kiwon shanun Innarta ya ba Tukuro ya kawo mata shi.

Bayan ta gama dama furar ta daga ta ludayin ta yadda kowa zai gani. Duk wanda idanunshi ya sauka a kan furar kuwa sai da ta ba shi sha’awa. , sannan ta kira ta a matsayin babban abinci ga Fulani.

 Wurin Galadima ta nufa hade da  durkusawa ta mika mishi furar, Sai ko ya kama ludayin ya debo kadan ya kurba.

Take wurin aka hau sowa mata har da guɗa.

Haka ta riƙa bin ƴan high table din tana mika musu furar a matsayin su ɗanɗana abincin Fulani. Abun mamaki kowa sai ya dan diba ya sha. Kila ko don ganin Galadima ya sha.

Nan ma haka aka rinka yi mata liki, hotuna gami da video.

Bayan fitar Hafsat sauran cultures din ma suka shigo, ko wanne gwanin burgewa.

Bayan gama culture representing, sai Kuma aka shiga cultural dance. Nan Kam babu Hafsat, saboda shugaban tsara cultural dance din Uncle Najib bai sanya sunanta ba.

Yadda cultural dance din ya bayar da cittah sai ta ji Ina ma ace tana ciki, ita kadai sai washe baki take yi.

Bayan cultural dance Sai aka shiga bayar da kyaututuka ga dalibai, har da malamai masu kwazo. Hafsat dai ta samu kyautar first position, ajin nasu ba a bayar da kyautar overaller ba. Saboda yadda Abubakar ya karya mata record, sakamakon yin First position da ya yi first term.

Hafta din ta kara samun kyautar dalibar da ta fi ko wace daliba biyayya.

Sai kuma aka ba ta best in English language, Chemistry and Biology. Kenan kyauta biyar ta karba. A ranar ne kuma aka basu prefect inda ta samu mukami biyu Sp da kuma Health prefect.

Wannan rana duk wani masoyin Hafsat yana cikin farin ciki hade da alfaharin kasancewarta ƴar’uwarshi. Wadanda kuma ranar suka fara sanin ta, ta yi matukar burgesu. Musamman yadda Allah Ya hada mata abubuwa da yawa, ga kyawu ga kuma ilmi.

Ƴan garin maƙera kuma sai Hafsat din ta ƙara kima da daraja a idanunsu. Su da kansu suke jin a yanzu fa kamar ta fi karfinsu. Musamman yadda suka ga manyan mutane na yi mata kyauta, ana daukarta hotuna kamar ita ce Gimbiyar jihar Tanga.

Farin ciki wurin Mama Halima da iyalanta ba a magana, har da kuka, ba sau daya ko biyu ta shigo filin idan Hafsat na gabatar da wani abu ba ta zuba mata kudi hade da rungume ta alamun dai tana cike da farin ciki.

Ana kiran sallahr la’asar taro ya tashi, sai a lokacin ne Uncle Najib ya samu ganinta ya hada ta da yan gidansu suka gaisa cike girmamawa, ita ma sai ta hada shi da Mama Halima suka gaisa. Ya mika mata leda mai kyau yana fadin gift dinshi zuwa gare ta.

Duk yadda ya so su yi sallama a nutse abun ya faskara, shi ana jiranshi ita ma ana jiran ta

Ita kam ma ba ta san ranar zai tafi ba, ta dauka zai dan kara kwana ko biyu haka. Shi ya sa sam ba ta damu ba. Ta nufi su Juwairiyya da suke jiranta.

A cikin boot din motor ES aka zuba duk wasu kyaututuka da ta samu, ƴan gari kam sun zagaye ta sai kallo suke yau ta zama kamar wata tauraruwa a wajensu. Kila mamaki suke yi Hafsat dai yar gidan Hinde da Malam Ayuba yau ita ce ta zama tsakiyar manyan mutane. Ita ce take turanci kamar ba ta iya Hausa ba. Ita ce kuma ta juya Fulatanci kamar ba ta san wani yare ba. Ita ce ta dama fura Galadima ya sha. Ita ce wacce Mc ya fi kiran sunanta a taron.

Bayan sun gama zuba kayan Tajuddeen ya ja su zuwa gidan Malam Ayuba. Yayin da ES ya tsaya don ganin an sallami kowa cikin aminci. Da kuma kasafta kyaututukan da aka samu daga manyan baki da ma ƙananan. Musamman kudi.

Yau kam Malam Ayuba kamar sallarshi, farin cikin shi ya kasa boyuwa, labari ya rasa wanne zai bayar, tun su Inna Kuluwa na jin dadin labari game da biye shi har suka yi shiru suka bar mishi. Mama Halima da su Juwairiyya ne kawai ke dariyarshi wani lokaci. Aka baje kyaututtukan da Hafsat ta samu, kudi ne, littattafai da tarkacen kayan karatu a har da su biscuit, turaruka masu kamshi. Da kuma kudi dubu hamsin a cikin envelope.

Mama Halima ta kasafta komai, kowa ya dangwali arziki.

Sai karfe shidda na yamma Mama Halima suka bar ƙauyen maƙera, cike da jin dadi gami da alfahari da Hafsat.

Hafsat kam sai da ta nutsu da dare sannan ta bude ledar da Uncle Najib ya ba ta.

Wani kwali mai kyau ta fitar wanda rubuta sunanta a samanshi da salon rubutu mai kyau.

Ta cire kwalin saman da ya kasance kamar murfi ga babban kwalin. Sallaya ja ta fara cirowa wacce aka rubuta sunanta da farin wani abu mai kyau.

Sai alkur’ani hizif sittin shi ma ja da sunanta a jiki, akwai turare shi ma jar kwalba da sunanta a jiki. Sai hijab dogo ja. Counter da kuma casbaha.

Can kasa kuma littattafai ne na English na karatu da kuma na labarai. Sai kuma waya karama, gefen ta envelope mai kyau. Da sauri ta yage envelope din, Sai ga kudi sabbi fil sun zubo, ta tattare su zuwa gefe daya. Ta dauki ƴar ƙaramar ta kardar ta fara karantawa kamar haka

“Hafsat!”

Abin da kawai aka rubuta kenan.

Ta kurawa takardar ido, a, kokarinta na gano abin da sakon ke nufi. Sai kuma wayar da ke kan cinyarta ta shiga kara alamun kira. Wannan ya tuno mata da Ya, Nasir saboda a wayar shi ta koyi yadda ake amsa kira da kuma yadda ake kiran…

<< Abinda Ka Shuka 28Abinda Ka Shuka 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×