Skip to content
Part 33 of 36 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tana jin Baban nata yana cewa “Na je na fifita ta, ki fadawa duk wanda za ki fada mawa, sai ya zo ya yi miki maganin abun. Kuma na fada miki ke da ɗanki sai kun biya ta akuyarta biyu da ragonta daya.”

Daga haka ya fice, ya bar Inna Kuluwa na ta haushi kamar karya, duk wani abin da yake ci mata tuwo a ƙwarya ranar dai da ta bude shi. Har da yadda ya rika siyar da komai na shi a kan kara aure. Kuma wai ba a kawo mishi uwar kowa ba sai kilbibi da karuwanci

A wannan gaɓar ne amarya Murja ta saka baki. Cikin isa da nuna gadara ta ce “Ahir dinki! Hawainiyarki ta kiyayi rama ta. Ni din nan na fi karfin yinki. Tun da na zo gidan nan na taba shiga shirginki? Kuma karya kike ki ce a gidan nan ban zo da komai ba. Ki fada min na taba aron ko cokalinki? Ke kuwa kullum cikin aike kike makota a aro miki wannan, a aro miki wancan. Sana’ar ki ta banza tun da ba ta hana ki aro ba. Kuma karuwanci ai a gidan mijina nake yi. Kuma ban haifi ɓarawo dan tasha ba”

Inna Kuluwa ta yi caraf tana fadin “Amma ai kin raba miji da matanshi ko? Kuma naka na fate-fate ba ka bayar da rancen gari, tun da ƴaƴan nan ke ma kin haifa”

“Amma ban haifi ƴan iska ƴan tasha ɓarayi ba. Kuma wanda ya isa ya tumbatsa shi ke fito da na ciki ya shiga yay bake-bake. Ni din nan gidan Ayuba zama daram mai nakuda ta samu gado. Duk wani kulle-kullenku da asirinku kar nake kallon ku. Ni na ci dubu sai ceto, idan kullum a tafe kuke ni a can na kwana. Ni din nan ba irin wacce kuka sanya aka tsana ba ce. Ku ka sawo maita a kasuwa kuka lika mata. “

” Ai wanda ke abu shi ke tunanin kowa ma yi yake. Saboda kina asirin ne shi ya sa kike ganin kowa ma yi yake. Maita kuma ai bamu isa mu sanyawa mutum ita ba, Sai dai shi da kanshi ya nuna kanshi”

“Asiri kam ina yi, fadi da ihu ki kara da wayyo. Saboda na mori malami, ai mai ƙaramin ubangida ya wahala. Kuma maganar sayen maita, kina son a fada miki inda kuka je kuka sawo ta, da hanyar da kuka bi ta yi tasiri?”

Wannan ce-ce-ku-ce ya sa makota suka cika gidan, wasu ƴan rabo, wasu kuwa kwal uwar daka suka zo ji. Ana tsaka da rikicin ne Mama Halima ta shigo, yadda ta samu gidan ne ya, sanya ta yin tsaye tana sauraron yadda ake bankaɗa. Saboda Inna Luba ma ta shiga fadan.

Hafsat kam na kofar dakin kajinta fuska duk a kumbure tana ji da kuma sauraro. Sam ba ta san ma Mama Halima ta shigo ba, saboda gidan nasu a cike yake da mata gami da yara ƴan kallo.

Shi ma cikin dariya ya shiga parking space ya yi parking sannan suka shiga cikin babban wuri ne, kuma ɓangare-ɓangare. Akwai bangaren kayan kwalam da maƙulashe gami da kayan sanyi. Akwai bangaren cosmetics,

Akwai bangaren zannuwa atamfofi manya da kanana, laces,shadda, dogayen riguna. Ga bangaren jaka takalma da gyale. Ga bangaren kayan jarirai. Ga bangaren wayoyi wanda komai na waya akwai, tun daga screen guard, batir, condom na waya da sabbin wayoyi.

Cike da mamaki Hafsat ta ce “Amma mai wurin nan mugun ɗan haɗama ne Yaya Tajuddeen, kamar shi kadai ne aka yi wa garin Dawurin”

Murmushi Tajuddeen ya yi kafin ya ce “Shi ne mai jiran gadon sarautar gidan da kika baro”

Baki bude ta ce “Ɗan Galadima ne?”

Da kai Tajuddeen ya amsa mata.

“wlh na dauka wurin na mace ne, da na ga AMI, ca nake ko Amina. Shi ne aka gutsire sunan”

Cikin dariya Tajuddeen ya ce “Ahmad Muhammad Inuwa yake nufi”

Kai ta langabar gefe alamar ta fahimta.

Daga nan suka fito, zuwa cikin daya ginin wanda aka rubuta *AMI RESTUARANT*

Uniform din ma’aikata wurin ne ya fi burge Hafsat. Nan ma suka zagaya sannan suka fito, Hafsat zuciyarta fal da mamakin yadda wasu suka iya neman kudi.

Har sai ta yi wa kanta sha’awar irin wannan kasuwancin.

Suna kan hanyar komawa gida aka kira sallahr magriba.

Yau kam hirar Hafsat da Mama kaf din ta a kan gidan Hakimi ne da AMI SHOPPING COMPLEX.

*****

MK

Mk dai wani bangare na zuciyarshi ya fara samun nutsuwa, saboda a yau ne magabatanshi suka je Malamawa nema mishi auran Ruma, kuwa tabbatar mishi da an ba shi. Har an sanya lokacin daurin aure.

Bangaren Ruma abun ya fi zo mata da mamaki, za ta auri miji, saurayi, dan gayu, mai ilmin boko, da birni ba kauye ba.

Karon farko da Mk ya zo wurin ta a matsayin mai son auranta, ga ni ta yi kamar wasa. Yanzu kuma da aka kara tabbatar mata ta hanyar zuwan magabatanshi sai take jin ta farin ciki.

Haka nan ma sai ta kama tsalle a daki tana celebrating za ta auri miji dan birni kuma dan boko.

Su Alaramma kara bude wuta su kai wurin ganin sun rufe duk wata kofa da za ta basu matsala. Duk wani ko wata da suka san Ruma za ta iya fuskantar matsala a wajensu sai suka rubuce mata shi ta shanye.

Shiga irin wannan gidan ba  abu mai sauki ba ne. Musamman a wurinta da ba ta yi karatun boko ba. Ya kuma san yadda ahlin wannan gida suka kwankwadi madarar boko.

Shi ya sa ya yi wa Malama Aisha magana wai Ruma za ta rika zuwa tana koya mata A,I,O,U,E. Wai ko karatun Hausa ta iya kafin lokacin auran.

*****

HAFSAT

Hausawa sun ce wai laifin dadi karewa, Hafsat hutu ya kare sai shirin komawa, dalilin da ya sanya su Juwairiyya da Nabila zuwa gida.

Ranar Asabar da ta kama saura kwana daya Hafsat ta koma suka tafi saloon, basu dawo ba sai karfe biyu na rana, sakamakon ruwan sama da aka makaka tun daga lokacin da suka tafi ba jimawa har zuwa karfe biyun.

Kasancewar sun yi sallah a wurin, suna shigowa gida abinci suka nufa. Hafsat dai kadan ta ci. Saboda wani irin zazzabi take ji, ita ta tsani a taba mata kai. Bare yau din nan ba karamar wahala ta ci ba. Har da stretching aka yi mata.

Cikin tsokana Nabila ta ce “Mama yarinyarki kuwa anya ba ta da aljanu. Saboda yau saura kadan su tashi a shagon saloon”

Yadda Mama ke kallon ta ne ya sa ta ce “Mama kin ga yadda take cuda min kai kamar tana wanke shuwaka. Sannan ta zo, ta yi ta jan shi da wani abu. Wlh duk ban lafiya ma nake ji na. Taba jikina ki ji” ta kai karshen maganar hade da janyo hannun Mama ta dora saman wuyanta

“Amma kuma kin yi kyau sosai, kar ki so ki ga yadda gashinki ya kara tsawo, ga baƙi ya yi sai sheki yake yi” cewar Mama lokaci daya tana shafa kan

“Bari Ya Tajuddeen ya zo ya biya kudi wlh” cewar Juwairiyya cikin dariya

“Gaskiya kam yau an fito mishi da masoyiyarshi fes”

Duk suka yi dariya har da Hafsat, cikin dariya Mama ta ce “ku yi wanka don Allah ku je gidan mai dinkin nan, idan ma ba ta karasa ba, ganin idonku ta karasa shi”

“Ni dai ba zan yi wanka ba” cikin sauri Hafsat ta fada.

Duk suka yi dariya, yayin da Nabila ta mike don fara shiga wankan.

(Tun da duk muna cikin garin Dawuri ne, bari mu leka gidan mai girma Galadima, kafin su Hafsat su fito)

Wurin da aka tanada don parking Asad ya yi parking, kai tsaye kuma part din Ahmad ya dosa.

Har cikin bedroom din Ahmad din ya isa.

Zaune yake a gefen gado, yau jini ya motsa shigar sarauta ya yi, amma mara alkyabba, irin dinkin nan mai falmara da ake dorawa a sama.

Yanzu ma takalminshi yake sanyawa black, masu zubin Sarautar.

Duk da kyan da ya yi hakan bai hana bacin rai da damuwa bayyana a kan fuskarshi ba.

A ciki-ciki ya amsa sallamar Asad har ya zauna gefen gadon bai dago ba, Sai da ya gama sanya takalmin sannan Asad ya ce “Inyeee! Yau ka fito a prince dinka”

Komai bai ce ba, ya mike zuwa kan mirror ya shiga fesa kalolin tura masu taushin kamshi.

Zama Asad ya gyara yana fadin “Wai duk a kan maganar Hajiyar ne kake ta ɓata rai”

Fuska ya kuma tsukewa sannan ya ce “Ta matsa a kan yarinyar nan, ni Zaitun ta yi min yarinya. Haba Asad can you imagine in haɗa shimfida da wannan yarinyar, don Allah ban zubar da ajina ba. Karamar yarinya just 19-20 years haba”

“To kai yar shekara nawa kake so?”

“Ina laifin 25 years, ta san komai.”

Asad ya murmusa kadan kafin ya ce “To ka hakura kawai da Mamin, don ni kaina ban ga wata matsala a Mami ba”

“Ni fa kawai ba ta min ba”

Jinjina kai Asad ya yi kafin ya ce “To yanzu wurin Zaitun din za mu je?”

Hararar da Ahmad ke aika mishi ne ya sanya shi kwashewa da dariya har yana kwanciya bisa gadon.

Komai Ahmad bai ce mar ba ya nufi kofar fita, shi ma sai ya bi bayan shi cikin dariya kasa-kasa.

Wajen dawakai ya samu Ahmad din tsaye, yayin da wani dogari ke kwanto mishi farin dokin shi.

Bayan dogarin ya kawo dokin gaban Ahmad ne ya koma ciki hade da kwanto na Asad. Saboda ko basu fada mishi ba ya san tare zasu fita.

Cike da kwarewa Ahmad ya haye saman dokin, Sai ya kara kwarjini gami da cikar zati.

A tare suka fito daga gidan kai tsaye kuma suka mike titin bayan gidan wanda zai kaisu unguwar Bye pass.

Duk lokacin da ranshi yake cunkushe babu dadi, ranar ne yake son fita rangadi.

Musamman yau da garin ya kasance an yi ruwa sosai, yammacin sai ya yi dadi gami da saka Nishadi.

Kadan suke taɓa yar hira, lokaci daya kuma Ahmad na karewa mutanen da suke wucewa kallo, wasu su ba shi tausayi, wasu kuma su burge shi.

Abubuwan sha’awa na farkon shigowar kaka gasu nan birjik a gefe titi, irin ɗata, gauta, yalo, gyada, Masara dafaffa da gasassa, gujiya, rake rogo, Dankali ga kuma awara da yan mata ke ta suya a gefen titi.

A hankali suka nausa cikin unguwar Bye pass, suka fara wuce manyan gine-gine da tituna masu kyau hade da tsabta, rashin hayaniyar unguwar da rashin yalwar mutane ya sa suka saki linzamin dokin cike da nishadi.

A daidai wannan lokacin ne kuma su Hafsat suka fito don zuwa gidan mai dinki, a jere suke su ukun yayin da suka sanya Hafsat a tsakiyarsu.

Daidai za su shiga kwanar gidan mai dinkin su Asad kuma suka fito daga kwanar a sukwane.

A matukar kidime kuma a tsorace suka fasa kara a tare yayin da Juwairiyya ta yi bangaren gefenta da gudu haka ma Nabila. Hafsat da ke tsakiya ta fi dukkansu shiga tashin hankali, saboda dokin Asad a daidai saitinta yake.

Ita kanta ba za ta iya shaida mai ta gani ba tsabar kidimewa, kawai dai taga wani abu Kato baƙi a gabanta, daga nan kuma ta shiga kokarin ceton ranta.

Cikin ciyayin da ke gefen hanyar ta fada, duk da faduwar da ta yi ba ta hak’ura ta shiga rarrafawa da sauri.

Duk yadda Asad ke sanar da ita ta dakata hakan bai sai ta tsaya ba, sai da ta yi dan nesa dasu, sannan ta yi zaune cikin ciyawar tana kallon Asad wanda ke kokarin sauka daga kan dokin.

Sai kuma a lokacin ne ma ta san doki ne, Ahmad dai tsaye ya yi kamar an zana shi yana kallon Asad da ke tattare takalman Hafsat da ta watsar.

A, gabanta ya ajiye takalman yana fadin “I’m so sorry please, ba mu san kun taho ba. Ba ki ji ciwo ba dai ko?”

Komai ba ta ce ba, sai kokarin dauke hawayen tsoron da ke zubo mata take yi.

Ya juya kan su Juwairiyya da ko waccensu ke gefen ta, a darare don su kansu har zuwa lokacin basu dawo daidai ba.

” Zo ku kama ta mana”

Cewar Asad yana kallon su

Juwairiyya ce ta yi karfin halin takowa har inda Hafsat din take, sai a lokacin kuma Hafsat ta shiga kokarin mayar da hijabs din saman kanta, wacce ta sabule sakamakon firgicin da ta shiga.

Da kanta ta mike hade da saka takalminta, har zuwa bakin Asad bai mutu ba wajen basu hak’uri, hade da tambayar Hafsat ba ta ji ciwo ba, duk kuwa da ko A ba ta furta ba.

Sai da su Hafsat suka shige kwanar, sannan Asad ya kama dokin ya hau, cike da rashin jin dadi.

Ahmad ya ce “Mata sun faye tsoro, kalle ta fa, za ta ji wa kanta ciwon da dokin ma bai ji mata ba”

“Haka suke, kwanaki Maman Zarah, saboda kyankyaso kar ka so ka ga faduwar da ta yi a bayan gida, ban da Allah Ya tsare da ta goce Kwankwaso”

“Subhnallah!” cewar Ahmad.

Asad ya ce “But did you notice…”

Yadda Ahmad din ya kalle shi ne ya sanya shi dakatawa yana siririyar dariya. Sai kuma ya ce “Wlh yarinyar can kyakkyawa ce”

“Wacce?” cikin ko in kula Ahmad ya fada

“Wacce ta fadin, ka ga wani hasken fata malam mara algus”

Murmusawa Ahmad ya yi kamar ba ya so.

Saboda shi kanshi da  karewa mutane kallo bai dame shi ba, ya hango duk abin da Asad ya fada a kan yarinyar.

Musamman gashin kanta, shi ne ya fi kashe mishi ido fiye da komai.

Sai jan lalle gami da baƙin da ya kara haska madaidaitan fararen kafafunta.

Bangaren su Hafsat kam suna shiga kwanar Nabila ta ƙasa hade da kwashewa da dariya. Cikin dariyar ta ce “Wlh, Hafsat kin ba ni dariya kuma kin bani tausayi”

Juwairiyya ma dariya ta fashe da ita tana fadin “Allah ko ni ta ba ni dariya”

A haka suka shiga gidan mai dinkin suna dariya.

Zabba’u mai dinki ta rika bin su da kallo har suka zauna saman kujerun da ke falon kafin ta ce “Wai me ya faru?”

Cikin dariya Nabila ta ba Zabba’u labari, duk sai suka kuma kwashewa dariya. Ba tare da ta Juwairiyya ta tsaya da dariyar ba ta ce “Yauwa Hafsat, ke ce ke son ganin Dr Asad, wanda ya dakko miki takalma ya aje a gabanki ai shi ne Dr Asad din”

Fuska a daure Hafsat ta ce “To ni ina ruwana, kuma in Sha Allahu sai sun fadi”

Wata sabuwar dariyar Nabila ta fashe da ita kafin ta ce “Ayyah Hafsat! Ai sun ba ki hak’uri”

“Koma menene ni dai in Sha Allahu sai sun fadi”

Haka suka yi ta tsokanarta har suka baro gidan dinkin.

<< Abinda Ka Shuka 32Abinda Ka Shuka 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×