Skip to content
Part 34 of 48 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Abun mamaki kuma sai ga shi sun kara haduwa da su Asad din a wani layi daban.

Ganinsu ya sa Nabila kara tuntsirewa da dariya, yayin da Hafsat ta hade fuska kamar za ta kama da wuta.

Ba Asad ba, hatta Ahmad sai da ya fahimci suna tsokanar Hafsat din ne, sai da suka iso gab Hafsat cikin murmushi ya ce “Matsoraciya ba ki ci ciwo ba?”

Maganar tashi ta sanya Juwairiyya da Nabila gajeriyar dariya. Ita kuma ta tamke fuska.

“Kuna tsokanarta ko?” cewar Asad daidai lokacin da suka gota su Hafsat.

Yau kam labarin saloon da faduwar Hafsat shi ne ya zama topic a gidan. Tun Hafsat na hade fuska har ta fara dariya. Musamman yadda kowa ke bayar da labarin abin da ya taba razana shi.

Ku jira in je muku gulma, wurin Asad da Ahmad…

*****

DAWURI

A karo na ba adadi Ahmad ya yi juyi bisa lallausan gadonshi, cike da jin haushin abin da ya hana shi bacci.

Wani dogon tsokin ya ja hade da mikewa zaune, lokaci daya kuma yana shafa kwatancen bakin gashin kanshi.

Wayarshi ya dakko da ke kan bed side drower karfe daya na dare cif-cif ta nuna mishi. Wannan yana nufin ya kwashe tsawon awa biyu kwance kenan.

Tun daga lokacin da baccin ya gagara daukar shi yake laluben abin da ya hana shi baccin amma bai lalubo komai ba. Duk bangaren da ya juya zai ga komai yana lafiya.

Dogayen kafafunshi ya diro daga saman gadon a hankali zuwa falon. Nan ma tsaye ya yi cikin rashin abun yi. Bai san ko mintuna nawa ya kwashe a tsayen ba, kafin ya koma saman kujera ya zauna.

Kanshi ya kwanta hade da lumshe idanunshi. Baƙi sidik din gashin Hafsat da ya sauka har saman kafadarta ya fara mishi gizo.

Ya yi saurin bude idanun da sauri, tun daga lokacin da ya dora kwayar idanunshi a kan gashin Hafsat har yanzu bai huta ba. Duk abin da yake yi sai ya rika ganin gashin ko fararen kafafunta masu lalle.

“Kodai aljana ce?” ya tambayi kanshi a bayyane.

Kuma har a lokacin gashin Hafsat din ne ke yi mishi gizo

“Oh my God! What’s all that mean?” Cike da bacin rai ya yi tambayar kamar Hafsat din ce a gaban shi

Kanshi ya dafe da hannayenshi biyu cike da takaicin idanunshi, saboda yadda har zuwa lokacin basu daina nuna mishi hoton kan Hafsat ba.

Abu kamar wasa sai ga shi har karfe uku yana zaune a falo, jikinshi duk a mace, dakyar ya mike zuwa toilet ya dauro alwala, ya shiga jera salloli, har aka kira sallahr farko, wani irin bacci ne a idanunshi shi ya sa yana dawowa daga masallaci ya haye gado, bakin dauke da addu’ar Allah Ya kawo mishi bacci.

Cikin sa a kuwa baccin ya dauke shi.

Har 11am bacci yake yi, dalilin da ya sanya Hajiya shigowa sashen na shi ranta babu dadi.

Wani bangare na zuciyarta yana fada mata ko a kan maganar Zaitun ne ya ki zuwa gaishe ta

Wani bangaren kuma cikin fargaba take, Ahmad baya irin wannan halin, wai don an yi mishi fada ya kauce daga wata turba mai kyau da yake kai.

Yadda ta hango shi saman gado luf ko jallabiyar da ya je masallaci bai cire ba, Sai gabanta ya kara tsananta faduwa.

Bayan ta iso dab da shi idanu ta tsira mishi, Sai da ta tabbatar yana numfashi kafin ta fara kiran sunan shi a hankali.

A hankalin ya bude idanunshi masu cike da bacci ya zuba a kan Hajiyar, Sai kuma ya mayar dasu ya lumshe

“Lafiya kake Ahmad, har 12 na neman yi kana kwance, ba ka ce jirgin karfe daya za ka bi ba, ko ka fasa komawa yau din ne?”

Cikin muryar bacci ya ce “Na sa an yi cancel din flight din, an mayar karfe 5pm”

“Ba ka jin dadi ne?”

Kai ya girgiza alamar a’a, Sai, kuma ya mike zaune a tsakiyar gadon.

“Ahmad!” Hajiya ta kira sunan shi cike da kulawa.

Bai amsa ba, amma ya dago idanunshi ya zuba mata

“Akan maganar Zaitun din ne?”

Kai ya girgiza alamar a’a

Gefen gadon ta zauna cikin kulawa ta ce “To me ye matsalar? Ba na son ganinka cikin yanayin damuwa, wane irin bacci ne tun asuba har sha biyu, kuma har yanzu din ma bai ishe ka ba. Wannan yana nufin jiya ba ka yi bacci ba”

Hamma ya yi hade da siririyar mika, yayin da idanunshi ke dakko mishi hoton Hafsat zaune cikin wannan korayen ciyayi, fararen idanunta da suka tara hawaye zube a kan Asad.

Da sauri ya girgiza kanshi hade da murza idon, cikin takaicin yadda ya kasa mantawa da abun.

“Ka zo ka yi break” cewar Hajiya hade da mikewa a sanyaye ta bar dakin.

Duk wasu hidimomi da ya yi a cikin dakin zuciyarshi na makale da hoton Hafsat, a lokacin ne ya fahimci babu wani abu da idanunshi ya rage a jikin Hafsat bai dakko mishi hoton shi ba.

Saboda yanzu kam har hoton yadda ta mike tsaye kyakkyawan dirinta ya bayyana yana kallo.

A haka ya je ya yi break, duk sai ya zama sukuku.

Lokacin da Asad ya zo kan, batun tafiyarshi shiru ya yi ko ya ji Asad ya yi batun Hafsat sai dai har su ka gama maganarsu Asad din ya tafi bai yi maganarta ba.

“Me ya sa ni? Kodai Aljana ce, saboda Asad ya yi mata kirki shi ya sa ba ta yi mishi gizo?”

Tambayar da ya ta yi wa kanshi kenan fiye da kafa saba’in, kuma ko sau daya bai samu amsarta ba.

Misalin karfe uku ya bar garin Dawuri zuwa garin Nasara, inda a can ne zai hau jirgi zuwa jihar da yake aiki.

Bangaren Hafsat kam, ko kadan zuciyarta ba ta dau hoton komai da niyyar hana ta, sakewa ba, Sai dai kawai idan ta tuna ta kan yi dariya ko ita kadai ce.

Ita dai ba ta bar Dawuri ba sai karfe 5pm,cike da tsaraba, irin kayan sanyawa, cosmetics da kuma abinci. Misali garin kwaki, biscuits kala-kala.

Jama’a bari in leka muku Mk da masoyiyarshi Rumasa’u

*****

MALAMAWA

Yau kam kauyen Malamawa cike yake da al’umma, da manyan motoci sakamakon daurin auran Rumasa’u da aka daura da Mk.

Bangaren Mk baki ya ki rufuwa, da ka gan shi ka ga sabon ango da yake farin ciki da cikar burin shi

Alaramma ya shige cikin manyan mutane, idan ka ganshi ka dauka wani gwamna ne ya zo daurin aure, ya sha dakakkiyar farar shadda gambari. Shaddar da ta kara mishi kwarjini, abinci kam ga shi nan, ranar dai almajirai kakarsu yanke saƙa ta yi.

Misalin karfe biyar na yamma zugar anguna ta daga da amarya Rumasa’u.

Wacce ta yi la’asar, saboda wannan ita ce ranar farko da ta yi nisa

da garinsu. Duk yawonta ba ya wuce kauyensu Goggonta, shi kuma har da kafa zuwa ake yi. Ba ta taba tafiya unguwa mai nisa cikin mota ba.

Duk da idanunta a lullube suke, lokacin da suka isa gidanta tana jin yadda mutane ke ya ba kyawun gidan, ana ta cewa Allah Ya yi mata canji ma fi alkairi.

Abu ya samu ma’iya wai kukan aure da sallallami, ai ranar dai bacci sai ɓarawo, amma ƴan kawo amarya kam sun kashe kwarkwatar idon su, ga kayan kallo wuta ba, daukewa, ga bayi mai madubi (tiles) haka suke cewa.

Washegari misalin karfe goma motoci suka kwaso ƴan kai amarya zuwa Malamawa. Aka bar amarya da ango da halinsu”

Bari mu leka Asma’u mu ji ko ta samu labarin auran Mk.

ASMA’U

Kamar ko wane lokaci yau ma zaune take gefen katuwar katifarta tana kallon Abdallah da ke koyon tsayuwa, da ya mike sai ya zauna, hakan ba karamin nishadi ya sanyata ba.

Wayarta da ke kan cinya ta dauka ta shiga yi mishi bidiyo. Sai da ya, gaji sannan ta bude data ta shiga Facebook.

Sunan Mk ta yi searching kasancewar baya cikin friends dinta, idan dai ta so sanin wani abu dangane da shi, ta kan yi searching sunanshi ta shiga wall nashi ta gama kalle-kallenta ta fito.

Hoton farko da ta ci karo da shi, shi ne ya fara tsaida mata da numfashinta, haka ta rika scrolling tana cin karo da hotunan auran Mk din kala-kala. Kallo daya za ka yi mishi ka fahimci yana cikin farin ciki.

Kirjinta ya rika wani bugu dumu-dum, jikinta har rawa yake yi, ta fita daga Facebook din kai tsaye kuma ta kira Mk.

“Da gaske ka yi aure?” shi ne tambayar da ta fara jeho mishi, duk yadda ta so saita kanta kuma ba ta iya yin hakan ba. Sai da ya fahimci hankalinta a tashe yake.

“Waye ya fada miki?”

“Ga abu na gani” a fusace ta yi maganar

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce “Look Asma’u, please take it easy, Ina sonki ke kanki kin…”

“Hold it Mk” ta yi saurin katse shi a fadace

“Amma na nemi mu yi aure Asma’u”

“Yaushe ka nema? Yaushe ka nema Mk?”

Calmly ya ce “Ban taba ce miki mu yi aure ba?”

“Amma yaushe? Yaushe rabon da ka kira wayata, ko a chat ma yaushe rabon da ka tambayi lafiyata bare ta Abdallah. Wato ka samu abin da kake so a wurina Mk, ka bar ni da wahala da yaronka, kai kuma ka yi aure, za ka rayu da matarka cikin jin dadi. Bayan ni ka raba ni da nawa mijin. Ina son Ahmad Mk, ban san ina son shi ba sai yanzu da ba ya gefena, amma ka raba ni da shi. “cikin kukan da ke nuna tashin hankali gami bakin cikin da take ciki ta karasa maganar.

Jikin Mk ya yi lakwas idan akwai abin da ke daga mishi hankali har gobe to bai wuce ya ji Asma’u cikin damuwa ba. Kukan da take yi yanzu sai yake jin kamar ana mai feshin wuta cikin zuciyarshi.

Komai ya kasa furtawa yayin da Asma’u ke kuka kamar dai an aiko mata da sakon mutuwa.

Ita ce ta yanke kiran hade da wurgi da wayar, kafin ta fada saman katifar ta saki wani sabon kukan.

Abdallah da bai saba ganin haka ba, shi ma sai ya kyakyace da kuka.

Tana jin Aunty na tambayar Asma’u lafiya Abdallah ke wannan kukan.

Dole ta janyo shi hade da tura mishi nono, har zuwa lokacin kuma kuka take yi. Tana jin kira na ta shigowa gami da sakonni amma ko sau daya ba ta yi alamar zuwa inda wayar take ba, saboda ta san ba kowa ba ne face Mk

Sai kuma ta ji takun Aunty Hajara zuwa cikin dakin da take. Da, sauri ta yi kasa da kanta, saboda babu lokacin da za ta goge kwallanta, don tuni Aunty Hajarar ta iso.

“Wai Abdallah faduwa ya yi ne?”

Kanta a kasa ta ce “Eh, faduwa ya yi”

“Haba,, shi ya sa na ji kuka kamar ana zare mai rai. Raggon maza kawai”

Kafin Asma’u ta ce wani abu Aunty Hajara ta dora da “Abubakar ne ya kira wayata wai ya kira ba ki dauka ba. Don Allah Asma’u ki daina wahalar da bawan Allahn nan, haba don Allah. Kalli yadda yake dawainiya da ke, da kuma yaronki. Dawainiyar da ko uban yaron ma ba ya yin ta, to waye ma ya san shi. Ina wayar take kira shi”

Ta shiga raba idanunta cikin dakin, har ta yi nasarar hango inda ta jefa wayar.

Aunty Hajarar ce ta mika mata wayar, ta kuma yi tsaye a kanta sai da ta ji muryar AG yana fadin “Hello!” sannan ta fice daga dakin.

Maimakon Asma’u ta yi magana sai kawai ta ci gaba da shesshekar kuka. Abin da ya yi matukar tadawa AG hankali, shi kadai ya san yadda yake jin ta a kirjinshi. Daidai da sakan daya sonta bai taba ragewa ba a kirjinshi.

Cikin tashin hankali ya rika tambayar “Masoyiya me ya faru? Little ne ba lafiya? Ke ce ba ki da lafiya?” haka ya rika jero mata tambayoyi amma ko daya ba ta amsa mishi ba, sai kuka da take yi.

Dole ya yanke kiran, lokaci daya kuma ya tafi online  domin yin booking din flight zuwa Jama’a.

<< Abinda Ka Shuka 33Abinda Ka Shuka 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×