Skip to content
Part 4 of 19 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Lokacin da su Baba Malam suka isa gidan ba kowa sai Yaya da ke zaune gindin murhu tana tafasa  ruwan dama koko, ba sai ka tambaya ba, yanayin da ke kan fuskarta kadai ya isa ya shaida ma zuciyarta a lalace take.

Shigowarsu Baba Alaramma ba karamin kara tayar mata da hankali ya yi ba, jikinta ya shiga rawa , tamkar ita ce Ruma da ta haihu ba tare da aure ba.

Jiki na rawa ta mike tsaye, sai kuma ta koma ta tsugunna lokacin da ta ga Baba Malam ya kunno kai ya shigo. Cikin tsananin biyayya ta shiga gaishe shi, ya amsa a sake ba tare da ya kalli inda take ba.

Baba Malam Nura ne ya ce “Ina abun da Ruma ta haifa din?”

“Yana nan daki” Inna ta amsa da alamun tsoro. Lokaci daya kuma ta nufi dakin ta dakko baby ta mikawa Malam Nura

Shi kuma ya mikawa Baba Malam cikin girmamawa.

Baba Malam ya tsurawa yarinyar ido kafin ya janye a hankali zuwa kan Baban ɗanshi Malam Balarabe yana fadin “Duba min yarinyar nan tana da rai ?”

Da sauri Malam Balarabe ya karbi Babyn ya shiga bincikar numfashinta.

“Ba ta numfashi.” ya fada a firgice.

Duk sai suka rufu kan yarinyar idan ka dauke Malam Yunusa mahaifin Ruma wanda ya jingina da katanga cikin halin damuwa.

“Ba dai kashe yarinyar nan kuka yi ba Yaya?” cewar Alaramma yana kallon Yaya wacce ke kofar dakinta tsaye.

Cikin kidima ta shiga fadin “Ni! Wlh ban kashe ta ba. Ta ya zan kashe rai? Lokacin da ta haihu na rude ashe zaren cibi ya shake mata wuya ban lura ba, Sai daga baya na lura ban sani ba ko shi ne ya yi…” sai kuma ta yi shiru tana kallon mijinta wanda shi ma din ita yake kallo

Duk suka yi shiru alamun kowa da abin da yake tunani.

Baba Malam ne ya katse musu shirun da fadin” A je gidan Nura tun da akwai fili sosai a yi mata sallah sannan a haƙa rami a binne ta.”

Duk da basu ce komai ba, amma hakan bai hana shi fahimtar cewa sun ji abin da ya fada ba.

Ya juya zuwa kan Malam Balarabe ya ce” Ina son yadda za a binne yarinyar nan, a binne maganar nan, a rufe min bakin kowa har da na Angon ba na son wani ya kara daga maganar nan”

Daga haka ya juya zuwa kofar fita daga gidan.

“Ina Goggon (mahaifiyar Ruma)” Alaramma ya tambayi Yaya cike da bacin rai.

“Tana can kauyensu suna” Yaya ta amsa shi jiki a mace

“Amma Yaya kun san yarinyar nan tana da ciki shi ne ba za ku fada tun wuri ba, Sai da aka kai wannan matakin, kuna son makiyanmu su yi mana dariya, kun kyauta mana kenan. Kun zubar mana da kima da darajar gida?”

Kamar za ta yi kuka Yaya ta ce “Wlh! Wlh!! Wlh!!!  ka ji sau uku kenan, ban san Ruma na da ciki ba…”

“Kina macen za ki ce ba ki san tana da ciki ba, har cikin ya girma ya isa haihuwa amma ba ki sani ba, a ina yarinyar ke dab-dala ba a ɗakinki ba? .” Alaramma ya katse ta kamar zai buge ta

“Wlh ni dai ban sani ba, idan na san tana da ciki ranar nan ta fadi a bakin raina” Yaya ta kuma saɓa ranta a kokarinta na kare kaina

“To ai abun tambayar ma shi ne, ta ya aka yi cikin a ina? Yarinyar da ba fita take yi ba” Malama Balarabe ya fada a tausashe

“Su, su biyun nan sun san a ina aka yi shi da yadda aka yi shi, kuma wlh tlh duk wanda na gano akwai hannunshi a faruwar wannan abun sai ranshi ya yi mugun baci, ba za  ku bata mana zuriya ba. Duk irin tsaro da matakin da muke dauka wajen tarbiyar yaran nan ace sai da kuka bayar da kofar da mutumci da kimarmu zasu zube.”

Yaya dai shiru ta yi, wannan ya ba Alaramma damar yin fadan da bai yi ba a gidan Baba Malam, inda yake shiga ba nan yake fita ba. Alwashi kala-kala yake ci marasa dadi a kan Auwalu.

Cikin fadan ne ya ce Yaya ta nemo wanda zai je ya dakko Goggo a kauye daga nan ya fice, yayin da sauran ƴan’uwanshi biyu suka rufa mishi baya, ban da Malam Yunusa da tun da abun nan ya faru ya zama kurma, ba ya uum bare – uh-uh.

Wannan  kenan.

*****

GARIN MAƘERA

Matsakaiciyar hanyar ce, wacce ta mike ɗoɗor har zuwa cikin garin maƙera, cike take da ƴan makarantar gaba da primary sanye cikin uniform din masu kalar fari da maroon din hijab, Mazan kuma maroon din hula.

Duk da karfe biyu na rana ne yunwar cikinsu da ranar da ake kwallawa ba ta hana wasunsu guje-guje da tsokanar fada ba.

Haka suka riƙa wucewa gungu-gungu.

Hafsat ce kaɗai ware can gefen hanya take tafiya ita kaɗai  nutse, duk yawan daliban ita ba ta da abokin tafiya kamar yadda ba ta da abokin magana.

Basu fara nisa a tafiyar ba, suka zo inda hanyar ta rabu uku, daya dama, daya hagu sai kuma daya da ta mike (wacce suke kai tun farko)

Daidai nan yawan daliban ya fara raguwa, wasu suka bi hanyar da ta yi dama wasu kuma suka bi hagu, yayin da wasu suka mike ciki har da Hafsat da sam ba ta da kuzari.

Saboda tsokanar da daliban suka yi mata lokacin da suke kokarin bin hanyar gidajensu.

Har ta gaji da kai kararsu, saboda ka’ida ne kamar hanyar ɗaka, duk lokacin da za ta fito kasuwa ko makaranta, cikin aji ko wajen aji sai an samu masu tsokanarta duk da yadda take keɓe kanta ba ta shiga harkar kowa.

Lokacin da suka iso tsakiyar kasuwar ne yawan daliban ya kuma raguwa sosai, sai kadan da suka kuma miƙewa ciki har da Hafsat.

Tun daga nesa ta hango kofar gidan maigari cike da jama’a, yara da manya har da matan aure.

Wannan ya tabbatar mata akwai abin da ke faruwa, kodai an kama ɓarawo ko kuma an yi fada ne, ko an yi wasu baƙi masu ban mamaki.

Da ace akwai wata hanyar da za ta kai ta gida, da ta canja zuwa ita. Sai dai ba ta da wani zaɓi da ya wuce bi ta cikin mutanen.

Haka ta rika kutsawa cikin mutanen a kokarinta na neman hanya.

Wasu kuma idan suka gan ta, da kansu ma suke darewa suna ba ta hanyar.

Wannan ba sabon abu ba ne  a wajen ta, saboda idan har za ta tunkari taron jama’a musamman mata da kananan yara, zasu dare kowa yay ta kansa.

Lokacin da ta isa tsakiyar taron ne numfashinta ya nemi daukewa, idanuwanta suka rika yi mata bishi-bishi saboda mugun ganin da suka yi.

Mahaifiyarta ce tsirara a bainan nasi yayin da wasu matasa suka zagaye ta da bulali, sai kuma wata mata da ke shimfide a kasa kamar gawa.

Ba ta san tana da jarumta ba, ba ta san son da take yi wa mahaifiyarta ya kai hakan ba sai a ranar.

Saboda aguje a kuma kiɗime cike da tashin hankali ta ratsa cikin tsirarun mutanen da suka zagaye mahaifiyar tata,

Cikin zafin nama ta cire dogon hijab din ta hade da saka mata a jikinta lokaci daya kuma ta rungume ta, wannan ya faru ne cikin sakanni da basu wuce talatin ba.

Wurin ya dauki ihu, yayin da matasan ke kokarin raba Hafsat da mahaifiyarta abin da suka kasa samun nasara.

Wurin sai ya rabu biyu, da masu tausaya Hafsat da mahaifiyarta, da kuma masu ganin an ci gaba da tozarta Hafsat da mahaifiyarta.

Kuka Hafsat ke yi sosai kamar ranta zai fita, kuma ta hana kowa ya iso inda mahaifiyarta take, ba tare da ta jira umarmin maigarin ba, ta rika jan hannun mahaifiyarta suna fita daga taron mutanen.

 Fitarsu ke da wuya yara suka dafa musu baya suna ihu har sai da suka shige gida.

A tsakar gidan kishiyoyin mahaifiyar Hafsat ne tsaye gaban turmi hannayensu rike da taɓare suna kallon kofar shigowa.

Suka zubawa su Hafsat ido lokacin da suka shigo, kamar ba zasu ce wani abu ba, Sai kuma suka saki shewa hade da tafa hannu a lokacin da su Hafsat suka shiga daki, sannan suka jefa taɓarensu cikin turmi suka shiga daka har da na gayya.

Hafsat gado ta fada tare da sake wani kuka mai cin zuciya, Inna kuma kasa ta zauna ba tare da ta nemi zane ta daura ko ta cire hijabin da Hafsat ta sanya mata ba, dukkansu kuka suke mai cin zuciya gami da daci, babu mai lallashin wani.

Haka su kai ta kuka har zuwa karfe biyar na yamma, a lokacin Hafsat ta fito tsakar gida don yin alwala, bayan ta idar da sallahr ne ta kuma fitowa ta, zubawa Inna ruwan alwala ta kamo ta zuwa tsakar gidan, ba ta damu da habaice-habaicen matan gidan ba, idan da sabo daga ita har Inna sun saba.

Bayan ta gama alwalar ta kuma kama ta zuwa daki.

Inna a sallahrta ma kuka take ji take ina ma Allah Ya dauki ranta a yau din nan ta huta, da ace ta fuskanci abin da zai faru bayan tozarcin da aka yi mata yau.

Bayan ta sallame sallahr ne ta daga hannayenta biyu sama cikin kuka ta ce “Allah ka dauki raina yau, Allah don Allah ka kashe ni yau, ba na bukatar rayuwa na gaji haka nan”

Hafsat da ke gefen gado zaune ta yi saurin sakkowa hade da dankwafar da hannun Inna, cikin na ta kukan ta ce “A’a Allah! Don Allah, Allah a’a, Allah kar ka amshi addu’arta, Allah tawa za ka amsa, ina bukatarta a raye, idan kuma za ka kashe ta, Allah ka dauki rayuwarmu tare, ni ba na bukatar rayuwa idan ba ta. Ina rayuwa ne kawai saboda ita. Allah don Allah kar ka karbi addu’arta” ta karasa maganar hade da fadawa kan Inna ta fashe da wani sabon kukan.

Inna ma sai ta fashe da kukan, cikin kuka ta ce “Hafsat gara in mutu, idan ba ni za ki rayu cikin farin ciki. Da ace tun lokacin da na haife ki na mutu, da yanzu ba ki rayuwa cikin tsangwama da hantara ba, da yanzu ba ki yi karo da wannan baƙar ranar ba. Ya fi in mutu ko kin samu ki rayu cikin salama.”

Cikin kuka Hafsat ta ce “Inna ai ke ce duk wani farin cikina, komai zan samu idan ba ki a duniya a lami ne, duk wani farin ciki nawa yana cika ne saboda kina raye. Don Allah ki daina yi wa kanki fatan mutuwa”

Shiru Inna ta yi saboda wani ƙullutun baƙin ciki da ya taso mata ya tsaya mata a zuciya, bangare daya kuma tana sauraron sautin kukan Hafsat mai ban tausayi.

Haka suka kuma bude wani sabon shafin kukan baƙin ciki.

Sallahr magriba ce ta tashe su, zuwa lokacin tuni kamanninsu sun canja, ido ya yi jazur haka ma fuska, musamman ta Hafsat da ta kasance fara tas, kodayake Innar ma tana da haske,  irin mai yellown nan.

Habaici kam sun sha shi har sun gaji, Hafsat ce dama mai damuwa da habaicin wani lokaci, yau kam damuwar da take ciki ta fi karfin wancan habaicin na su Kuluwa da Asabe.

Zuwa isha’i zazzabi sosai ya rufe Inna, duk da ita ma Hafsat din tana jin zazzabin, amma na Inna din ya fi damunta.

Bayan sallahr isha’i ta nufi Chemist din Malam Nasiru, shi kadai dama yake siyar mata da magani yake kuma dubasu idan daya daga cikinsu ba shi da lafiya.

Lokacin da ta isa kofar Chemist din matasa ne sa’ar Nasiru zaune suna hira.

Zuwan ta wurin duk sai suka yi shiru bayan sun amsa sallamarta.

Nasiru ya mike ya shiga Chemist din ita kuma ta bi shi baya.

Idanunshi zube a kanta ya ce “Me ya faru Hafsat?”

Maimakon ta amsa shi sai ta fashe da kuka, yayin da shesshekar kukan nata ya rika fita a hankali yana dukan zuciyarshi.

Ya sauke ajiyar zuciya a hankali, ji yake kamar ya janyo ta jikinshi ya kuma lallashe ta hade da fada mata maganganu masu dadi.

Ta zube kudin da ke hannunta a kan kanta cikin muryar kuka ta ce “Magani za a ba ni”

“Wa ye ba lafiya?”

Cikin kukan ta ce “Innata ce”

Ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, saboda yana da labarin abin da ya faru, kuma da ace yana nan tabbas ba zai bar wannan ya faru ba. Kuma da ace yana da wasu manyan kudi da ya maka duk wanda yake da hannu a faruwar hakan kotu. Sai dai yanzu shari’a sai da kudi, shi kuma yanzu yake nemansu.

“Me ya same ta?” ya kuma tambaya a hankali yayin da tausayinta ya bayyana a kan fuskarshi ƙarara

“Zazzabi ne da kuma ciwon jiki” cewar Hafsat a lokacin da take sharce hawayenta.

Bai yi magana ba ya juya ya haɗo mata magungunan da duk ya san Inna za ta bukata ya mikawa Hafsat hade da kudin da ta ajiye mishi. Sosai tausayinta yake ji.

“Na gode” ta fada a lokacin da take juyawa don barin cikin shagon.

Bayan tafiyarta ne Shafi’u ya ce “Wato Allah Ya yi kara ba na kadar ka ya ba. Waccan zukekiyar yarinyar ban da tana da guntun kashi ai da matar manya ce.”

Gaddafi ya cafe da “Sosai fa. Duk gidan babu mai kyan yarinyar nan, ita kadai ce ma fara, wlh ban da bakin halin uwarta da ba karamin kasuwa ta yi ba”

Lawwali ma ya ce ” Ka gano inda bakin zaren yake Gaddafi, wancan kyan dan maciji ne da ita, kana rabarta za a yi ba ka”

Nasir da ya fito daga cikin shagon ya ce “Wlh ba kwa yi wa yarinyar nan da uwarta adalci, ku ji tsoron ranar da za ku tsaya a gaban Allah don kare kanku a kan kazafin da kuka yi mata”

“Wane kazafi aka yi mata? Ga abu zahiri. Ko dazu fa sai da aka sanyata ta tsallaka matar malam Mubara, sannan wannan yarinyar yar gidan Lito waye ya yi sanadiyyar mutuwarta ba ita ba, daga fa yarinyar nan ta je gidan sayen albasa shi kenan. Tana dawowa sai ciwo kwana biyu ta mutu “

Nasiru ya kalli Inusa da yake maganar kafin ya ce” Yarinyar nan ni ne nan na duba ta, typhoid ne ya yi mata mugun kamu har ya taba hanjinta.”

Inusa ya janyo ashar ya maka sannan ya ce” ka ji baƙar karya, gidan ubanwa ka taba ganin hanji mutum ya ruɓe Nasiru saboda typhoid? “

Nasiru ya shiga yi wa Inusa bayanin yadda cutar typhoid take da yadda take taba hanji

Amma fau-fau Inusa da sauran abokanshi suka ki yarda.

Inda su ma suka rika lissafo mutanen da suka rasu, suna dora alhakin mutuwarsu a kan mahaifiyar Hafsat. Yayin da Nasiru ke ta kokarin kare ta.

Hafsat kam lokacin da ta isa gida matan gidan ne da yaransu gami da maigidan suke ta hirarsu cikin jin dadi. Babu wanda ya damu da halin da mahaifiyarta take ciki.

Haka nan ta yi sallama ba don tana sanya ran zasu amsa mata ba.

Inna kwance tana mayar da numfashi da kyar.

“Sannu Inna!”

“Yauwa Hafsat” Inna ta amsa cikin karfin hali

Gefen gado ta koma ta zauna, tana sauraron yadda kannenta ke ba Babanta labarin irin tozarcin da aka yi wa Innarta.

Amma ko da wasa bai tsayar dasu ba, a nan ne Hafsat ta rika jin sunayen wadanda suka sanya mahaifiyarta ta yi tsirara da kuma wadanda suka doke ta.

Sai da gidan ya koma shiru, sannan Hafsat ta fito zuwa dakin girki, ta zubowa Inna tuwo.

Dakyar ta lallaba Inna ta ci tuwon ta kuma Sha maganin.

<< Abinda Ka Shuka 3Abinda Ka Shuka 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×