Skip to content
Part 40 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Kai Ahmad ya dago hade da sauke idanunshi a kan Ak, dalilin da ya kara sanya Ak daidaita nutsuwar shi,  ya shiga kame-kame har ya ba mutanen da ke cikin shagon dariya.

Saboda Ahmad irin mutanen nan ne masu kwarjini da kallo daya za su yi ma, ka shiga taitayinka, duk kuwa irin tsaurin idonka,  musamman idan ba ka da gaskiya.

“Za gayo nan” cewar Ahmad kamar ba ya son maganar.

Cikin shafa kanshi mai tulin suma AK ya zagaya can cikin shagon inda Ahmad yake zaune.

Sai ya tsugunna kanshi a kasa, Ahmad kuma ya gyara mishi wurin  zama amma a kan package din minerals.

Bari ya yi sai da ya nutsu sosai sannan ya ce “Ka ce ba ka san gidansu ba, kuma ba ka da lambarta?” yadda ya yi maganar idanunshi a kan wayarshi sai ka dauka ba ma shi ba ne.

“Eh wlh ranka ya dade, amma ba za a rasa lambarta cikin group din WhatsApp na makaranta ba, ko babu ma akwai inda zan samo ma”.

Kamar Ahmad ba zai ce komai ba, Sai kuma ya ce “Samo min”.

Keypad din wayar shi ya dakko hade da jujjuyata cikin yar kunya ya ce “Yallaboi sai dai in ba ka lambar ka kira, ni wayata shiru ne wallahi.”

“Ba ni lambar wayar taka” cewar Ahmad lokaci daya kuma yana taba wayarshi.

Bayan ya karanto mishi lambar sai ga airtime na 10k.

Cikin zaro ido ya ce “Kutumar bu…”Sai kuma ya kame bakin na shi, kamar zai yi kuka ya ce” Yallaboi dubu goma ka sanya min, ina ni ina katin 10k,ai da na 200 ka sanya min in ya so ko 2k ce a hannu ka ba ni”.

“Ka kira ta” cewar Ahmad yana dan kara hade fuska alamar ba wasa.

Nura dai dariya yake yi kasa-kasa, saboda yana jin duk hirar tasu.

Ak kuma ya ce “Yanzu kuwa yallaboi, hands-free ma zan sanya ka ji komai”

Ya kai karshen maganar yana kiran wata lamba.

“AK sai da bullet” daga can muryar wata mace ta fada.

Cikin salonshi ya ce “Haka ne yan mata, transformer Kuma sai da wuta Allah” suka yi dariya a tare shi da yarinyar da ya kira din.

Sai kuma ya ce “Summy turo min lambar Jhu don Allah”

“Ta samu ne, na san kai din nan ungulu ce…”

“Ke dalla ki turo min, kar ki yi min iskanci” ya katse ta

Cikin dariya Summy ta ce “Dan iska kawai, bari a turo ma”

Ko minti daya bai cika ba, Sai ga lambar ta tura

Ahmad ya duba sannan ya ce “ga lambar ƴallaboi”

Numfashi Ahmad ya sauke a hankali hade da lumshe ido ya bude su a kan AK din Sannan ya ce “Kira ta, ka tabbatar ka san yadda ka yi ka ji tana gida, da kuma address din gidan nasu”

“Wannan mai sauki ne” cewar Ak hade da kiran layin Juwairiyya.

Ba jimawa kuwa muryarta ta ratsa kunnuwan su Ahmad

“Assalamu Alaikum. Waye please?”

“Yar rainin wayau, ba kya daukar murya?”

Daga can Juwairiyya ta dan yi shiru sai kuma ta ce “Na so in dauki muryar amma ta shige min, waye don Allah?”

“Ni din ne ba ki gane ba?”

Sai, kuma Juwairiyyar ta fashe da dariya tare da fadin “Ak sai da bullet”

Da alama wannan shi ne in kiyar Ak din, cikin dariya ya ce “Yar rainin wayau, ga ni a bye pass ta ina ne lungunku, yau zumunci nake ji”

Cikin dariya ta ce “Wlh da ban dau murya ba (sai kuma ta marairaice) ka da ki gurbi, almost 3wks da na koma school”

Kafin ya ce wani abu kuma ta ce “Amma gidanmu fa ba wuyar ganewa, da ka zo masallacin Al-azhar gate 4 house No 4 by your left Shi ne gidan”

“Yan gayu” cewar Ak cikin tsokana.

“Dan rainin wayau, Allah Ya shirye ka AK”

“Tare da ke ya amsa hade da yanke kiran yana kallon Ahmad, saboda Ahmad din ya ji komai.

Sai dai yanayin da ke kan fuskar tashi bai nuna alamar ya ji komai din ba.

” Karanto min No nata”

AK ya shiga karanto lambar cike da kwarewa.

Tsaye Ahmad ya mike lokaci daya kuma yana saving lambar, sai da ya mikawa Nura hannu kafin ya ce “Idan ba damuwa ku ma dan je wurin mota”

Su biyun suka bi bayan shi, rafar kudi na dubu hamsin-hamsin ya miƙa wa ko wannensu.

Murna kam kar AK ya ji labari, saboda tun da yake ba a taba yi mishi kyautar 50k ba.

Ya rasa dalilin da ya hana shi farin ciki, bayan ya samu kaso 95 da biyar cikin dari na abin da yake nema.

Daga wurin A&A hospital ya wuce, yana son ganin Asad, ya tabbata zuciyarshi za ta ɗan saki daga damuwar da yake ji

*****

ASMA’U

Kwance take yayin da wani irin zazzabi mai zafi ya rufe ta, sakamakon yayen da ta yi.

Saukin ta daya ma da Momy ta dauki Abdallah tun jiya da aka yi yayen.

Yau dai har kuka ta yi, ta rasa abu mai sauki a cikin haihuwa, hanyar samun cikin ma ta wani bangaren akwai wahala, rainon cikin wahala, haihuwar ma haka, rainon yaron ma haka, to ashe yayeyn ma ba sauki.

Ita kam ta karbi jarabawa mai wahalar gaske, ba ta fatan irin abin da ya same ta ya samu wani.

Ana cewa amfanin zunubi romo, ita kam ta kasa gane ina wannan karin magana ta dosa, musamman ma a kanta.

Sakamakon aikata ba daidai ta hadu da abubuwa marasa daidai ba iyaka.

Sosai haushin Mk yana kama ta, musamman idan ta tuna yadda ya yi shiru dasu, yanzu ga shi jiya ba ta yi bacci ba, sabanin shi da kila ya kwana cikin nishadi rungume da matarshi.

Ya lika mata abu ya tafi ya bar ta da wahalar shi.

Yadda ta sha wuya da shiga kalubale daga haduwarsu da Mk zuwa yanzu ta tabbata shi ko rabin abin da fuskanta bai fuskanta ba.

Ta kai hannu a hankali hade da dafe nonuwanta da suka yi tantsan-tantsan sai azabar ciwo, kwanciya ko wace kala ma gagararta take yi.

Saboda ko yanzu zaune take gefen katifa, wanka take son yi, saboda zuwan AG amma ba ta san ta ya ma za ta yi wankan ba.

Haka ta ci gaba da zama har zuwa lokacin da kiran AG ya shigo wayarta, ya kuma shaida mata yana wajen gate.

Cikin dabara ta mike, hade da canja doguwar riga mara nauyi, wata irin azaba take ji a duk lokacin da rigar ta shafi kirjin nata, shi ya sa ba ta so zuwanshi ba, amma ya nace dole sai ya zo.

Hijab kawai ta zira, ta rika tafiya cikin dabara har ta isa gate din ta bude mishi.

Idanunshi zube a kanta yayin da yanayinshi ya canja zuwa tsantsar tausayinta, “I’m so sorry dear” ƴa faɗa a tausashe

Hawayen rashin dalili ta ji sun zubo mata, ta, shiga daukewa a hankali.

A kwanakin nan haka take magana kadan sai ta sanya ta kuka, wani irin kunci take ji na rashin dalili.

Yayin da sabon yanayin nata yake tasiri a zuciyar AG hade da kara narkar da sonta a cikin zuciyarshi.

Yanzu ma ji ya yi kamar ya rungumeta zuwa jikinshi, sai dai ya san yadda take jaddada mishi irin ciwon da take ji, ya tabbata ko akwai auranta a kanshi, sai dai ya lallashe ta da fatar baki.

Sannu a hankali ta juya zuwa sitroom shi ma ya bi ta a hankali kamar ba ya so.

Bayan ya zauna ne ta kare mishi kallo, sanye yake cikin blue black din wani hadadden boyel da ya samu dinki mai kyau

Idan dai kwalliya AG ya iya ta, irin wacce take boye shekarunshi ta fito da cikar zatinshi.

Yadda ta kafe shi da ido ne ya sanya shi mikewa zuba kusa da ita ya zauna, duk kuwa da wurin ya matse.

Daidai kunnen ta ya ce “What are you looking? Ko na yi kyau ne?”

Cikin alamun jin kunya ta kawar da kanta gefe, yayin da jikinta ke karbar sakon da jikinshi ke tura mata a hankali.

A hankali ta yunkura da niyyar tashi, ya yi saurin mayar da ita, wannan ya sa ya fama mata ciwonta, har ba ta san lokacin da ta saki kara ba, hade da fadawa jikinshi cikin tsananin azaba.

“Oh my God!” ya fada da sauri kafin ya ce “Na zo jinya kuma na fama. I’m sorry, ban yi da niyya ba.”

Sai kuma ya daga ta a hankali daga jikin nashi zuwa wurin da ta tashi, kafin ya ce “Bari in koma wurina, dama na zo tonon fada ne, na tabbata sai kin tashi” Ya, karasa maganar hade da kissing din bayan hannunta.

Baki ta tura kawai ba tare da ta ce komai ba.

“Ina Baban?”

“Yana wurin Momy” ta yi maganar har zuwa lokacin tana kumbura baki

Siririn murmushi ya yi kafin ya ce “Rigima”

Sai ta kara tura bakin, ba tare da ta ce komai ba

“Za mu je asibiti ne?”

“Ai na je, sun ce zai sauka daga yau zuwa gobe”

“Shi ma a shagwaɓen ya ce, ni kuma ba na son su sauka, da ace akwai abin da za a yi su zauna a haka ba ciwo da an yi, ko, nawa ne zan biya”

Hararar da take aika mishi ne ya sa cikin dariya ya ce “Na ce kar su yi ciwo”

Ta janye idon hade da mikewa don kawo mishi abun taɓawa

“Ina za ki je? Kar ki sake ki ce za ki kawo min wani abu, ki yi zaman ki, ni ganinki ma ya wadatar.”

Sai ko ta zauna din, saboda idan akwai abin da take jin tsoro a yanzu shi ne yin abin da zai fama ta

“Ban ji motsin Aunty ba”

“Ta je wurin Momy ganin little”

“OK” ya yi maganar hade da tattare hankalinshi a kanta sannan ya ce “Asma’u, idan har da gaske kina son aurena, ina bukatar hakan nan da watanni biyu”

Idanunta ta narke a kanshi ba tare da ta ce komai ba, ba ta san me ya sa ba, ita har yanzu ba ta jin son shi cikin zuciyarta, kawai tana mishi wasu abubuwan ne saboda alkairinshi gare ta

“Me kika ce?”

Shiru ta yi kamar ba za ta ce komai ba, Sai kuma ta ce “Ka je ku yi magana da Dady to”

Kila bai yi tsammaci haka daga gare ta ba, shi ya sa ya yi mutuwar zaune, abin da bai sani ba a yanzu ba ta da wani zabi. Zabin ta mutum daya ne kuma ta san ya yi mata nisa. Shi kuma AG rufin asirinta ne, ya san komai, a kan idonshi aka fara komai kuma a kan idon shi aka gama, so babu wani abu da za ta boye mishi.

“Na gode sosai da jin wannan amsar ban yi tunanin jin ta ba. I promised you Asma’u za ki yi farin ciki a gidana, sonki nake yi daga can cikin zuciyata. In Sha Allah zan ɗebi miki shakkarki a kaina.

Bari ki ga, yanzu zan je in nemi Dady, saboda gobe jirgin 10am zan bi”

Ya yi maganar hade da mikewa, cike da mamaki ta ce “Wai haka da sauri”

Ido ya waro kafin ya ce “Ke! A bari ya huce ai shi ke kawo rabon wani. Zan sanar miki da yadda mu ka yi.” ya kai karshen maganar hade da dago ta a hankali, murya ya sassauta yana fadin “Ba a a yi min rakiya ba”

Kai ta sunne dab kirjinshi alamun kunya, Sai ya karasa kwantar da kan nata a hankali. Yayin da ta rika jin fitar da numfashinshi da sauri.

Daidai saitin kunnenta ya ce “I love you so much dear”

Ita kanta ba ta san lokacin da ta lumshe idanunta ba, yayin da hancinta ke shakar daddaɗan kamshin turarenshi.

Kanta ta ta kasa janye, shi ne ya janye ta, hade da rike hannunta suka fice daga sitroom din. Zuciyar AG fes, ya yarda karin maganar nan ta Hausawa da suke cewa mai nema yana tare da samu.

*****

AHMAD

Bayan ya yi parking motarshi a private parking space na asibitin ne, ba tare da ya fito ba ya kira lambar Juwairiyya, sai dai har ta yanke ba a daga ba.

Abin da ya sanya shi mayar da wayar aljihu, hade da fita daga cikin motar zuwa office din Asad.

Basu baro asibitin ba sai da suka yi sallahr magriba a cikin masallacin asibitin sannan suka nufo gida.

Asad dai gidanshi ya wuce kai tsaye, yayin da Ahmad ma ya nufo nasu gidan.

Bai shiga gidan ba sai da aka yi sallahr isha’i, Sai suka shiga tare da Hakimi.

Ya jima a sashen Hakimin suna tattaunawa, har sai da Hajiya ta shigo, ya gaishe ta sannan ya fita zuwa sashen shi.

Bangaren Juwairiyya kuwa lokacin da Ahmad ya kira ta tana library, sannan wayar tana a silent, Kuma tana fitowa ta wuce masallaci sallahr magariba. Sai da ta dawo hostel ne ta ga kiran bayan da ta ciro wayar daga cikin jaka. Ta bi kiran kuma ba a daga ba.

Sai dai a lokacin da ta kira Ahmad yana tuki, shi ma kuma wayar na a, silent, sannan bai duba ta ba sai yanzu da ya dawo sashen shi, ya gama duk wani abu na al’adar kwanciyarshi sannan ya dauki wayar, ganin missed called din Juwairiyya sai ya bi.

“Kalli special no nan ta kara kirana Nabila” cewar Juwairiyya tana dagawa Nabila fuskar wayar.

“Ki daga” cewar Nabila.

“Tsoro nake ji, mai ya sa sai yanzu za a kira.”

Ganin kiran zai yanke ya sa Nabila saurin karbe wayar ta amsa kiran, sannan ta saka ta a hands-free komai ba ta ce ba.

Kamar yadda Ahmad ma ya yi shiru bai ce komai ba.

Har sai da Nabilan ta gaji don kanta ta ce” Assalamu Alaikum!”

“Wa’alaikissalam “Ahmad ya amsa kamar dam jiran hakan yake yi.

Suka kalli juna ita da Juwairiyya alamun mamaki kafin Nabila ta ce” Waye?”

Maimakon ya amsa mata sai ya ce” Juwairiyya ce”

Baki suka bude dukkansu alamun mamaki, sannan Nabila ta ce “Eh”

“Ki ba ta wayar” wannan ya tabbatar musu da ya fahimci ba muryar Juwairiyyar ba ce.

Cike da wani mamakin Nabila ta mika mata wayar “Ina jin ka” ta fada bayan ta amsa

“Sunana Ahmad, daga nan Dawuri, ko zan iya samun ki a gida gobe?”

“A’a gaskiya ina makaranta”

“Wace School”

“Health and Technology Nasara”

“Good!” ya fada cikin muryar shi mai dadin sauraro

“Zan iya zuwa makarantar gobe?”

Suka kuma kallon juna ita da Nabila, Sai Nabila ta daga mata kai alamun ta ce eh

Sai ko ta ce “Eh”

“Na gode, Sai na shigo din” bai jira cewarta ba ya yanke kiran.

Bayan yanke kiran ne Juwairiyya da Nabila suka zubawa juna ido, Sai kuma suka tuntsire da dariya suna fadin “Ikon Allah!”

Juwairiyya ta ce “Ji, kuma wani sarkin iko ne, ke kin rantse da Allah ni ce na ce ya kira ni”

Cikin dariya Nabila ta ce “Ahmad gadara kenan”

Tare suka kuma fashewa da dariya hade da tafawa irin ta shakiyancin nan”

Bangaren Ahmad kam, kwanciya ya yi hade da yin addu’a, saboda a gajiye yake.

<< Abinda Ka Shuka 39Abinda Ka Shuka 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×