Skip to content
Part 42 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

AHMAD

A daidai wannan lokacin kuma Ahmad ne ya fito sanye cikin wata dakakkar shadda gambari blue, amma ba dark ba. Wacce aka yi wa din kin babbar riga. Kallo daya za ka yi wa shaddar da dinkin ka san ba kudi kadan aka kashe wajen saye da kuma dinka ta ba.

Kafarshi bakin takalmi na cover ya sha mai sai walkiya yake yi. Yayin da kanshi ke sanye da jar dara. Kamshi mai dadi yana fita a ko wane lungu da sako na jikin shi.

Ya yi sallama a falon Hajiyar daga Asad har Hajiya suka dago idanunsu zuwa kanshi, Sai ya fuske kamar bai ga suna kallon na shi ba.

Sai ma zama da ya yi yana kallon Asad wanda shi ma shaddar ce Gezna a jikin shi. Sai dai sabanin ta Ahmad shi babu babbar riga, amma dinki ne sosai da ya samu kwararren tela.

Hajiya ta kasa hakuri har sai da ta ce “Me ake yi  a Maƙera din nan haka mai muhimmanci da har ya sanya ka sanya manya kaya yau?”

Komai bai ce ba, Sai dai ya dan murmusa kadan.

“Ka yi kyau kuma mutumina” cewar Asad cikin tsokana

Hajiya ta dora da “Sosai fa ya yi kyau, ganewa ne bai yi ba, amma shigar manyan kaya tana yi mishi kyau”

“Idan ba damuwa za mu iya tafiya” cewar Ahmad yana kallon agogon da ke daure a hannunshi, wanda ya nuna sha daya saura.

Asad ya mike tsaye yayin da Hajiya ke ta rakasu da addu’ar zuwa lafiya da kuma dawo lafiya.

Asad ne ke tuƙin, yayin da suke hira sosai irin dai ta aminan nan da suka jima tare, bangare daya kuma Ahmad yana kallon yadda mutane ke ta aiki a gonakinsu don kawar da abubuwan da suka noma.

Bayan da suka fara shigowa cikin garin Maƙera ne Asad ya ce “Garin nan fa yana ta samun ci gaba, ga shi an yi musu titi, ga makaranta har da asibiti, kuma ka ga ana ja musu Nepa ma”.

Asad ya juya ganin shi side din da makarantar take ya ce “Kuma makaranta katuwa, shi kanshi asibitin yana da girma”.

“Ba laifi, kuma ana yo musu posting din manyan likitoci babu laifi”cewar Asad, kafin Ahmad ya ce wani abu ya kuma cewa” Ina muka nufa ne?”

“Gidan maigari” Ahmad ya amsa gabanshi na ci gaba da faduwa, saboda tun da suka tunkari garin gabanshi ke faduwa kamar wanda zai kai kanshi a yanke mishi hukuncin kisa.

Asad ya tsaya daidai tsakiyar kasuwar hade da yafito wani da hannunshi alamun kira.

Dama da yawan hankulan mutanen ya dawo kan motar, rabonsu da suka ga irin wannan motar mai kyau da tsada tun ranar da aka yi bikin yaye daliban makarantar garin.

“Gidan Maigari don Allah?” Asad ya tambaya

“Ai kun iso yallaboi, ga shi can mai bushiyar bedin can, mai baranda”.

Kai Asad ya shiga jinjinawa alamar ya fahimta, yayin da Ahmad ya zaro yan dubu-dubu guda biyar ya mikawa mutumin, saboda kammaninshi kadai sun isa su nuna yana bukatar taimako, ba sai ya bude baki ya fada ba.

Kofar gidan Maigarin suka parker motar sannan suka fito zuwa cikin wani zaure, wanda suka tabbatar shi ne fadar.

Da sallama suka shiga, yayin da suka ci  karo da Maigarin a kan kujera ga fadawa zagay da shi. Ganin su Ahmad ya sanya su mikewa suka rika mika gaisuwa, duk kuwa da basu san ko su waye ba, amma shigarsu ta isa ta nuna su din ba ƙananun mutane ba ne. Saboda kamshin turarensu ma kadai da ya cika fadar ya ishe su yanke hukunci.

Saman tabarmar suka zauna hade da gaishe da Maigari, ya amsa yana kare musu kallo da tunanin ina ya sansu.

“Ban shaida ku ba” cewar Maigari ganin duk sun yi shiru.

Asad ne ya ce “Daga Dawuri muke, sunana Asad, dan gidan magajin gari, wannan kuma Ahmad yaro Galadima”.

Kai karshen maganar Asad ta yi daidai da fadowar Maigari daga saman kujera yana fadin “Ayi min afuwa Ranku ya dade, wlh ban gane ku ba, tuba nake Allah Ya ja da ran Galadiman Tunga Hakimin Dawuri. Allah Ya ja kwanan Magajin Garin Dawuri. Allah Ya kara musu lafiya, Allah Ya kiyaye gabansu da bayansu”.

Fadawa na amsawa da “Amin Ranka ya dade! Allah Ya ja kwanan Hajiya Babba, Allah Ya kara mata lafiya…”

Wannan hayaniya ba karamin ɓata ran Ahmad ta yi ba, shi ya sa ya yi kicin-kicin da fuska. Har sai da Asad ya lura ya dakatar da su, hade da umurtar Maigari ya koma kujerarshi.

“Wane ni Ranka Ya dade, ina sama kuna ƙasa.”

“Haka ne yallaboi! “fadawan suka amshe.

Siririn tsoki Ahmad ya ja, wanda Asad ne kadai ya iya jin shi.” Mun zo neman wani”cewar Ahmad cikin murya mai dan kauri.

“Allah Ya ja da ran Galadimanmu na gobe, waye shi a cikin garin nan, yanzu nan a binciko ma shi?” cewar Maigari.

Kamar Ahmad ba zai tanka ba, Sai kuma ya ce “Malam Ayuba mai kayan miya”.

Ba iya ƴan fadar ne kadai suka shiga mamaki ba, har da Asad, saboda shi bai san me ya kawo su garin ba. Yanzu kuma da Ahmad ya fadi wanda suka zo nema, Sai ya ji ya kosa a kira shi ko don ya ji dalilin Ahmad din na neman shi.

“To ko Malam Ayuba kanen Malam Bawa can gudan marigayi Malam Dauda yake nufi?” cewar wani Bafade.

“Eh, ni ma dai ina jin kamar shi din yake nufi” wani ma ya fada.

Maigari ya tada kai yana kallon Ahmad sannan ya ce “Shi din kake nufi Ranka ya dade?”

“Yana da yarinya Hafsah dai” Cewar Ahmad.

Maigari ya juya kan fadawanshi don neman karin bayani.

Wanda ya yi magana farko, ya kuma cewa “Shi ne dai, yarinyar ai ita ce wacce mahaifiyarta ta rasu, ko ba wata fara ba?” Bafaden ya juya yana kallon Ahmad don tabbatarwa.

Kai ya daga alamar eh.

“To aje a zo da Malam Ayuba yanzun nan sarki fada. A rarrabu, wasu kasuwa wasu gidanshi kai har da gonarshi ma” cewar Maigari cikin bayar da umurni.

Kafin 30sec sun fice daga fadar, fitarsu da mintuna talatin sai gasu sun taso keyar Malam Ayuba, wanda kallo daya za ka yi mishi ka fahimci a kidime yake a kuma rude.

Sauri yake yi kamar zai kifa, tun daga zauren ya watsar da silifas din shi, daga nesa ya fadi ya shiga kwasar gaisuwa.

“To ga shi nan Ranka ya dade, shi ne wannan?”

Kai Ahmad ya daga yana karewa Malam Ayuba kallo, duk da ba wani sanin Hafsat ya yi ba, amma bai ga ta ina ya yi kama da Hafsat din ba.

Ya janye idanunshi daga kan Malam Ayuba zuwa kasa komai bai ce ba.

Wannan ya sa Maigari ya ce” ko ba shi ba ne ranka ya dade?”

A hankali ya motsa bakin shi yana fadin” Shi ne “shi kanshi ya fadi hakan ne ba don yana da tabbas ba.

Maigari ya nuna su Ahmad yana fadin” ka ga masu neman ka nan Malam Ayuba, daga can Dawuri suke, wannan (ya nuna Ahmad) ɗanɗan mai girma Galadima ne, shi kuma wannan (ya nuna Asad) ɗanɗan Magajin Gari ne”

Take Malam Ayuba ya kuma rudewa, shi da ko kofar gidan Galadima bai taba zuwa ba, to me ya hada shi da ƴaƴan gidan. Shi Galadiman ma sau daya kacal ya taba ganinshi ranar da aka yi taron graduation. Hannayenshi ya daga du biyun alamar gaisuwa yana fadin “Sannunku Ƴallaɓoɓi!”  shi da kanshi ya ji bai yi daidai ba, Sai kuma ya ce “Sannunku Ranku ya dade!” Asad kam har sai da ya yi guntuwar dariya, yadda Malam Ayuba ya kidime gami da tsoracewa ba karamin dariya ya ba shi ba.

Ahmad bai yi magana ba, har sai da ya fahimci, Malam Ayuba ya dan fara nutsuwa kafin ya ce “Kana da yarinya Hafsat?” duk da a hankali kuma a nutse ya yi maganar ha kan bai hana kowa jin amon sautin muryar ta shi

“Eh Ranka ya dade, ina da ita, ita ce ƴata ma ta biyu, Allah Ya sa ba wani abun ta yi ba” yadda Malam Ayuba ya karashe maganar a marairaice sai da hakan ya daki Ahmad. Sai ya ji ya ba shi tausayi. Da alama yana sonta ko kuma dai yana jin tausayinta. Kila kuma kanshi yake tausaya mawa, saboda duk abin da ta jawo kanshi zai kare.

Kowa ya fitar da ran Ahmad zai kara cewa wani abu, Sai kuma suka ji muryarshi ya ce “An yi mata miji ne?”

Cikin sauri Malam Ayuba ya shiga girgiza kai tare da fadin “A’a wlh, ba a yi mata miji ba. Ai ba na jin ma akwai mai zuwa wurin ta”

Idanu Ahmad ya lumshe cikin dabara ya rika daidaita numfashinshi da yake gwamewa.

Asad jam kunnuwanshi kaf ya bude ya ji Ina ne karshen zancen.

Ahmad kuwa lalubo yadda zai fadi magana ta gaba yake yi, sai yanzu yake jin haushin da bai ba Asad labari ba, da yanzu an zo karshen maganar.

Wata dabara ce ta fado mishi, wayar shi ya fitar hade da rubuta text ya mikawa Asad.

Baki bude alamun mamaki Asad ke kallon rubutun, har sai da Ahmad din ya dan zungure shi sannan ya ce “To dama mun zo neman auranta ne idan ba a yi mata mijin ba”

Wannan magana ba karamin girgiza duk mutanen wurin ta yi ba, har da shi kanshi wanda ya fadi maganar, saboda jin abun yake kamar almara.

Da alama shock din da kowa ya shiga, ya hana su ga dadewar Malam Ayuba wajen bayar da amsar maganar Asad. Har shi kanshi Asad din bai ga dadewar ba.

“Ban yi mata miji ba, idan kuma Kune kuke neman auranta, kowa ya shaida na ba ku, ai babu mai gudun hada zuriya da manyan mutane irin mai girma Galadima, mutum mai dattako”

Malam Ayuba ya yi saurin yanke wannan hukuncin ne don ma kar ya ja su ce sun fasa, shi din nan ace yaran Galadima sun zo neman auran yar shi, a shi kam Allah Ya sallame shi, yaushe zai bari kanshi a kulle a je a samu matsala.

Fadawan wurin suka hada baki wajen fadin “Mai girma Galadimanmu na gobe ya karba, kuma ya gode, Allah Ya tabbatar da alkairi”

Ahmad dai kanshi na a, kasa, yayin da fadar ta rude da hayaniyar abin da ya farun.

A hankali Ahmad ya zare jikinshi ya fice daga fadar hatta takalmanshi a hannu ya riko sai da ya zo kofar waje ya sanya, sannan ya bude mota ya shige, yana, sauke wani irin numfashi mai kama da na wanda ya samu ƴanci

Tuna wani abu ya sanya tashi zaune hade da dakko wayar shi ya shiga turawa Asad text kamar haka

“_Ka karɓi lambar wani a cikin wurin, musamman Baban yarinyar, sannan ka shaida musu gobe za a kawo kayan baiko, a tsayar da lokacin bikin_”

Kanshi ya  kwantar jikin kujerar hade da lumshe idanu, bayan ya tabbatar da tafiyar sakon, zuciyarshi ba kuka ba guɗa, amma dai yana jin wani irin shauki gami da farin ciki na taso mishi a duk bayan daƙiƙa daya.

Yana a cikin motar Fadawa suka yo wa Asad rakiya, suna zabga mishi kirari, ko motsi  bai yi ba, bare ya bude idanunshi, Asad ne ya yi duk abin da ya dace.

Bai bude idanun ba har sai da ya tabbatar sun fara fita daga cik garin sannan ya mike zaune sosai hade da gyara zaman shi, ya juya da idanunshi wani gefen ya ki kallon Asad.

Ganin haka ya sa Asad tuntsirewa da dariya tare da fadin “Ikon Allah! Wai ta ya wannan abun ya faru Ahmad, wacece Hafsat? A ina ka san ta? Yaushe kuka hadu?”

“Its long story!” ya fada a gajarce

Kai ya jinjina kafin ya ce “Shi kenan Ango kake, all this long time, daga karshe dai it’s come to and end”

Komai Ahmad bai ce ba, Sai Asad ne ya kuma cewa “Ina son ganin yarinyar nan gaskiya”

“Asad!” cewar Ahmad cikin kosawa da maganganun na shi.

Cikin dariya ya ce “Na kosa mu isa gida in yi wa Hajiya albishir din cewa mun je neman aure mun dawo da baiko.” ya karashe maganar cikin wata dariyar.

Kamar ya yi shiru sai kuma ya ce “Amma wlh kama raina min hankali, kawai ka ja ni zuwa wuri, ba tare da na san komai, Sai da ka ga ba sarki sai Allah za ka ba ni a rubuce, Sai yanzu nake jin haushin kaina da na yi magana da shiru na yi, ka nemawa kanka auran da kanka”

“You have a big problem”

Dariya Asad ya kuma yi, yayin da ya ci ga da tsokanar Ahmad har suka isa gida.

Sai da suka yi sallahr azhur a masallacin kofar gidan, kafin nan suka shiga cikin gidan

Ahmad dai kai tsaye part din shi ya wuce, yayin Asad kuma ya yi part din Hajiya.

Sallamar shi ya sanya ta fitowa sanye da hijabi, hannunta na dama rike da casbaha.

Yadda yake ta murmushi ya sanya Hajiya ma yin murmushi tare da fadin “Da alama tafiyar nan ta yi riba, akwai alamun labari mai dadi a bakinka Asadu”

Sai ya karasa fashewa da dariya hade da kwantawa saman kujerar sosai, yana fadin “Hajiya akwa labari kam, ki nemi wacce ta iya guda a gidan nan, saboda yau dai abun mamaki ya faru, mun je tambayar aure yanzu haka mun dawo da baiko”

Ido Hajiya ta fitar alamun mamaki kafin ta ce “Yi min dalla-dalla”

Ya mike zaune sosai kafin ya ce “Wlh Hajiya ba wasa nake yi ba, an ba Ahmad ƴa”

“Wai wannan Ahmad din?” Hajiya ta yi tambayar hade da nuna Ahmad wanda yake shigowa, yanzu kam babu babbar riga da kuma hular a kanshi, yar cikin shaddar ce kawai da takalmi silifas a kafarshi.

“Shi fa”

Da wani mamakin Hajiya ke bin Ahmad da kallo wanda ya zauna yana aikawa Asad harara.

“A ina aka ba shi yarinyar?”

“A can Makera din”

“Ikon Allah! Wai Asad da gaske, na kasa gasgatawa wlh”

“Wlh Hajiya da gaske nake yi, yanzu haka gobe za mu kai kayan baiko a tsayar da ranar daurin aure”

“Oh Sa’adatu. Allah Ya kawo lokaci kenan. Yar gidan waye a Maƙera din?”

Cikin dariya ya ce “Wlh fa ni ma ban sani ba, da alama shi kanshi angon sai yau ya san mahaifin yarinyar, magana ta zo wurin manya sai kawai aka ce an bamu.”

Saman kujera Hajiya ta zauna, mamaki tab da yanayinta.

Yayin da Asad ke dariyar yadda ta shiga shock.

Ahmad kam dining ya isa, don da gaske yunwa yake ji. Yayin da yake jin shi wani irin sakayau kamar an sauke mishi dutsen Andi daga saman kanshi.

ASMA’U

Yadda a bangaren Ahmad ake ta shirye-shirye kai kayan baiko, tuni bangaren Asma’u kayan nata baikon suka sauka da nauyinsu.

Babu wanda zai kalli kayan nan ya ce wa bazawara aka kawo ma su.

Sosai AG ya yi rawar gani, ya faranta ran Asma’u da kayan baiko na ban mamaki, sosai sai hakan ya sanyata farin ciki. Wata daya kacal aka sanya, a hakan ma AG bai ji dadin hakan ba, so ya yi a sanya sati daya kacal, amma Asma’u ta ƙi, domin sosai tsoron auran take yi, ji take kamar ba ta taɓa yi ba.

Yau ce rana ta farko da AG zai zo wurinta tun bayan da aka tsayar musu da ranar aure.

Ba ta jima ba ta shirya cikin atamfa super wax mai kalar coffee da light brown, dinkin Riga da siket ne wanda ya fito mata da kyakkyawar kirar jikinta.

Farin mayafi ta dora a saman kanta hade shafa turarurruka masu daɗin kamshi.

Wayarta ta dauka ta shiga yi wa kanta hotuna kafin isowar AG din.

Ba ta jima ba kuwa sai ga kiranshi, ba tare da ta daga ba, ta mike zuwa dakin Aunty Hajara ta shaida mata zuwan AG din, sannan ta wuce don bude mishi kofa.

Baki bude take kallon shi, saboda ba ta yi tunanin a mota yake ba, sai ta, wangale mishi babban gate din ya shiga da motar.

<< Abinda Ka Shuka 41Abinda Ka Shuka 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×