Tafiya ce ta kusan awanni sha'uku tsakanin Jama'a zuwa Nasara, shi ya sa ana kiran sallah magriba suka shiga garin, amma basu isa cikin gidanta ba, Sai ana sallame sallahr isha'i.
Tun daga waje yan kawo amarya ke yaba gida, har zuwa lokacin da suka zaunar da amarya gefen gadonta bakinsu bai yi shiru ba.
Tsarin gidan ba karamin burgesu ya yi ba. Ga shi ita kadai bai hada ta da Maman Nawwara ba.
Ƴan'uwan AG suka shiga hidima da su har zuwa lokacin da suka kwanta baccin huce gajiya.
Lahadi kuma AG ya ce ai. . .