Skip to content
Part 45 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

ASMA’U

Bayan tafiyarsu Aunty Hajara, sai gidan ya koma shiru ba kowa, saboda tun da AG ya fita kai su bai dawo ba.

Ta gaji da zama daki ta dawo falo, komai tsab babu bukatar ta gyara.

Saman kujera ta kwanta tana kallo, a haka bacci ya dauke ta.

Cikin baccin ta rika jin bugun kofa, da sauri ta mike hade da daukar mayafinta ta nufi gate.

A muryar bacci ta ce “Waye?”

Daga can wajen Musa ya ce “Ni ne daga gidan Maman Nauwara, ta ce a kawo miki abinci”

Kofar ta bude, hade da karbar kwandon mai dauke da food flask masu kyau “Na gode, ka gaishe ta” ta fada daidai tana tura kofar.

A kan dining ta ajiye basket din hade da wucewa bedroom. Wayarta ta dauka da ke kan side drower, kiran AG ne ku san guda goma sai kuma text message kamar haka “Allah Ya sa ba fushi kika yi ba. Wlh na tsaya yin wani abu mai muhimmanci ne ki yi hak’uri”

Murmushi kawai ta yi hade da yi mishi reply, kafin ta shiga toilet. Alwala ta yi sannan ta fito hade da gabatar da sallahr Azhur.

Bayan ta idar ta nufi wajen abinci da Musa ya kawo, flask din ta shiga budewa daya bayan daya.

Flask na farko kuma babba, fara Kal din shinkafa ce, da ta yi shar. Dayan kuma wake ne, ya dahu luguf, dayan kuma miya ta ji nama sosai. Dayan kuma hadin coslow ne.

A cikin plate ta zuba, sosai abincin ya yi dadi babu karya.

Bayan ta gama kuma wayarta ta dakko ta shiga media,sosai hakan ya mantar da ita jiran AG, Sai da ta ji sallahr la’asar kafin ta tashi ta yi wanka hade da yin alwala.

Bayan ta yi sallah kuma sai ta canja kaya, zuwa lace mai shegen kyau, sosai ta yi kyau, kallo daya kuma za ka yi mata ka tabbatar amarya ce.

Falon ta kara gyarawa hade da kunna turaren wuta, tana tsaka da gyara dining ne ta ji ƙarar bude gate. Ba jimawa kuma motar AG ya shigo

Ba ta dasa abin da yake yi ba har zuwa lokacin da ya shigo, kayan ya aje a tsakiyar falo, kafin ya nufe ta, ta bayanta ya rungomata, kamshinta mai sanyi ya rika ratsa kofofin hancinshi.

Idanunshi ya lumshe yana kara shakar kamshin yayin da yake jin wata irin nutsuwa na shigar shi. Sai ya juyo ta sosai hade da kara rungume ta sosai. A cikin kunnenta ya ce “Alhamdulillah! Burina ya cika” ya kai karshen maganar hade da dauke bakin nashi daga kan kunnenta zuwa kan goshinta ya yi mishi slight kiss.

“I’m very sorry Dear! Wallahi wani abu ne ya tsayar da ni, amma duk hankalina yana kanki”

Ya yi maganar cikin wata irin murya a kasalance.

Hannunta ya rika zuwa kan kujera ta zaman mutum daya ya zauna hade da dora ta saman cinyar, kanta ya kwantar a kan kirjinshi, yayin da take jin gudun numfashi.

“Maman Nauwara ta ce min ta aiko miki da abinci ko?”

Daga yadda take ta daga kanta alamar eh. Har zuwa lokacin idanunta a rufe yake. Yayin da haduwar jikinsu ya saukar mata da kasala.

Ya shiga shafa kanta a hankali, hade da shakar kamshi maya-mayan da kan ke fitarwa.

Sai kuma ya kasa jure hakan, ya daga ta cak zuwa a cikin bedroom saman gado ya kwantar da ita, duk wasu mafarkan da ya dade yana yi game da ita, su ya shiga kokarin mayar dasu gaske.

Ya jima yana jiran wannan ranar, yau kuma da Allah Ya kawo ta, ya kamata ya sauke nauyin da ya jima a kanshi.

Tun Asma’u na yin abun da marmari har ya fara ba ta tsoro, saboda duk after 30mns AG sai ya neme ta, zuwa magriba ba karamin la’asar ta yi ba. Ba ta saba ba. Ahmad ba shi da yawan bukata, zai iya neman ta dare da kuma asuba, shi kenan kawai, a hakan ma ba kullum. Yana ba ta lokaci ta huta, kuma tana jin dadin hakan. Komai na Ahmad a tsare kuma a nutse yake yin shi.

Sai da ya fita sallah ta samu ta dan huta, ana idar da sallahr isha’i kuma ya dawo ya ce ta shirya za su je gidan Maman Nauwara.

A kafa suka taka, saboda gidan babu nisa, duk a kan layi daya ne, tsakaninsu bai fi gida biyar ba.

Suna tafiya suna hira har suka isa

Asma’u ta bude ido sosai tana kallon tsarin gidan wanda ba iri daya ba ne da nata, kuma ba za ta iya kushe na Maman Nauwara ba saboda ya yi kyau, kuma ta tabbata Maman Nawwara ma ba za ta kushe mata nata ba, saboda ita ma natan ya yi kyau.

Falon Maman Nawwara ma ya hadu ga kamshi mai dadi yana tashi, yaranta biyu Ammar da Nawwara zaune saman kujera suna kallo, ganin AG ne ya sanya su tasowa da gudu suka rungume shi. Cikin murnar ganin shi.

Suna a jikinshi suka shiga gaishe da Asma’u, ta amsa hade da neman wuri ta zauna.

Yayin da AG ya kama hannun yaran ya nufi wata kofa, wacce Asma’u take tsammanin ta bedroom ce, saboda ta ji yaran na cewa Ummansu na bedroom, a lokacin da yake tambayarsu tana ina.

Ba jimawa suka fito a tare, Maman Nauwara sanye da doguwar rigar lace coffee da golden mai kyau, dinkin nan ya zauna kamar a jikinta aka dinkashi. Doguwa ce sosai, kuma tana da madaidaicin jiki, hakan ya sa tsawon ya yi mata kyau.

Kai tsaye ba za ace mata baka ko fara ba, tana nan a tsakiya, tana da zubin shiru-shiru, da rashin son hayaniya.

Tun daga nesa ta fadada fara’arta tana fadin “Sannu da zuwa amarya!”

Cikin kunya Asma’u ta yi murmushi, Sai dai ba ta ce komai ba.

Kan three sitter suka zauna, yayin da Asma’u ta gaishe ta, ta amsa cike da fara’a.

“Na ga abinci na gode” cewar Asma’u

“Babu komai. Ai ya ce wai kin ce a maido na dare n ranar ma ba ki cinye ba. Na ce ai ba iri daya ba ne amma ya ajiye idan kin zo kin tafi da shi”

Murmushi Asma’u ta yi kawai ba tare da ta ce komai ba, Sai bayan da suka yi shiru ne AG ya yi sallama, suka amsa kafin ya ce “Laɗifa wannan ita ce Asma’u, kin sha jin sunanta a gidan nan, kuma kin sha ganin hotunanta, a zahiri ne kawai ba ki taba ganinta ba, to yau dai ga ta a gidanki, a karkashin ikon mijinki, a matsayin abokiyar zaman ki, ina fatan za ki taya ni riko, hade da ba ni hakkin kai wajen sauke dukkan wasu nauye-nauye naku.”

Kai Maman Nawwara ta jinjina kafin ta ce” in Sha Allah “

” Madalla! Dukkanku ina sonku wlh, babu wacce zan so in ɓatawa rai don Allah kar ku bar wata kofa da za ta bata mana farin cikinmu”

“In Sha Allah!” suka fada a tare, Sai dai muryar Asma’u ba ta fita sosai ba.

Shi kuma ya dora da “Zan, yi kokarin yin adalci a tsakaninku in Sha Allah, duk wacce na kuskure ma wa ta yi hakuri, ta kuma nusar da ni, ni kuma In Sha Allah zan gyara”

Dukkansu kai suka jinjina alamar suna fahimta.

“Akwai mai magana?”

Duk suka yi shiru, hakan ya sa ya kara maimaita tambayar da ya yi

“Ni dai babu” cewar Maman Nawwara.

“Ni ma haka!” cewar Asma’u

“Oya! Let’s hug each other”

Duk sai suka yi dariya, kafin Maman Nawwara ta Mike tsaye, Asma’u ma sai ta mike ta nufi Maman Nawwara, Suka rungume juna for some seconds, Kafin suka saki juna.

Sai kuma suka shiga hira, wani lokaci Asma’u ta saka baki, wani abu kuma ta yi shiru.

Sai 9pm suka baro gidan zuwa gidan zuwa gida.

*****

HAFSAT

Misalin karfe daya na ranar Juma’a Hafsat ta fito cikin shirin zuwa Dawuri, za ta iya cewa tun da take ba ta taɓa zuwa Dawuri ita kadai ba, Sai dai ko ta dawo ita kadai din, shi ya sa take ta jin tafiyar wani iri.

Danladi kanenta ne ya kira mata mai mashin din da zai kai ta bakin hanya.

Ba jimawa suka dawo tare da mai mashin din, ta kara yin sallama da mutanen gidan sannan ta fita.

Karfe biyu saura tana Dawuri, yanayin yadda aka kara gidan Mama Halima ba karamin burge ta ya yi ba, musamman falon an zuba mishi sabbin kujeru, hatta dakin su Hafsat ba a bar shi a baya ba shi ma ya sha gyara.

Tun da ta isa kuwa su Juwairiyya ke tsokanarta, da Amarya ta sha kamshi, har sai da ta yi kamar za ta yi kuka sannan suka kyale ta.

Sai da suka gama tsokanarta sannan Juwairiyya ta tura ma Ahmad sako kamar yadda ya sanar mata cewa idan Hafsat ta iso, ta sanar mishi “_Ta iso_”

Sai da ya yi murmushi sannan ya ce _”ok my regards to her_”

Ya yi mata reply, a lokacin kuma shi ma yana cikin motar da za ta kawo shi Dawuri, saboda jirgin sha biyu ya hau, ya yi sallahr juma’a a Nasara, ya kuma hawo mota zuwa gida.

Sai da suka yi sallahr la’asar suka tafi wajen kunshi da gyaran kai. Ba kuma su dawo ba sai 7pm

Zuwa lokacin Hafsat ta fara ciwon kanta na al’ada, saboda da zarar an ja mata kai sosai, sai kanta ya fara ciwo.

Shi ya sa abinci kawai ta ci hade da yin sallah ta kwanta.

Duk wasu ayyuka da hirar da su Nabila suka yi da dare ba ta yi ko daya ba.

Asuba kuma aka tashi da shirin daurin aure, zuwa sha biyu an kammala duk wani abinci na daurin aure an adana, yayin da cikin gidan yake cike da mutane, haka ma wajen gidan yake, Malam Ayuba ma ya zo.

Ana fitowa sallahr Azhur ƴan daurin aure suka tafi, ba kuma su dawo ba sai karfe biyar na yamma inda suka dawo dauke da Amarya Maimunatu wacce aka fi sani da Goggo, kuma tsohuwar matar Malam Inusa, Baban Ruma, kuma Yaya ga Alaramma.

Dawowar ƴan daurin aure hade da zugar amarya sai gidan ya kara cika, hayaniya ta kuma yin yawa.

Hafsat dai dama ga ciwon kan jiya, ga kuma yau ta sha hayaniya, Sai kan ya kara yi mata ciwo, yaƙe kawai take yi.

Amma kuma sosai tana cikin nishadi, musamman yadda suka sha kyau, suka zama kamar wasu zara a tsakiyar taurari.

Saboda Mama ba karamin haɗasu ta yi cikin kaya masu kyau da tsada ba.

Dinkuna kala biyar aka yi musu, duk iri daya kuma su da Maman. Lace, shadda, Sai kuma atamfofi guda uku.

Babu wanda zai kalli Hafsat ya ce ba Mama Halima ce ta haife ta ba, saboda kamaninsu musamman  farar fatar.

Gidan bai kaɗaice shiru ba, Sai wajen karfe goma na dare, zuwa lokacin tuni Hafsat ta yi bacci, saboda tun 9pm ta yi baccin, duk wani abu da ya faru bayan wannan lokacin ba ta san shi ba.

Safiyar Lahadi kuma ta shiga shirin komawa gida, su Hafsat kuma sai Monday.

Mama Halima ma dai ta ce mata Tajuddeen ne zai kai ta.

Bangaren Ahmad kuwa bayan ya iso, Juwairiyya ce ke ba shi situation report, kuma shi ma ya je daurin aure, yadda ya ga cikin gidan da kofar gidan ya san ba zai samu damar ganin Hafsat a nutse ba, shi ya sa ma bai neme ta din ba. Amma ya sanarwa da Juwairiyya cewa shi ne zai mayar da ita gida.

Ita kuma Juwairiyya ta sanarwa Mama, Maman kuma ba ta fadawa Hafsat ba, kawai ta ce mata Tajuddeen ne zai mayar da ita.

Shi ya sa kanta tsaye take ta shrinta, yayin da Mama Halima ta hada mata tsaraba kamar yadda dai ta saba.

Karfe hudu ta yi wanka hade da yin sallahr la’asar.

Lace din da ta  suka sanya jiya ta mayar, blue ne mai dauke da fulawoyi pink, dinkin doguwar riga da ya zauna a jikinta sosai.

Sai kuma ya kara haska fatarta da take Fresh ba za ka taba cewa a kauye take kuma gidan Malam Ayuba ba. Ko ina jikinta a cike yake babu alamar rama

Kallo daya za ka yi mata ka fahimci idan ta samu hutu ba karamin budewa za ta yi ba.

Ba ta san dalilin da ya sa Juwairiyya ke ta mata dariya ba, da zarar ta dan tattaɓa wayarta sai ta dago ta kalli Hafsat din ta kwashe da dariya. Ita kuma sai ta ai ka mata da harara.

Arround 4:30pm Juwairiyya ta mike zuwa falon Mama tana fadin “Mama ya iso”

A tare suka fito da Juwairiyyan zuwa dakinsu inda Hafsat da Nabila ke zaune suna kallo, Nabila kuma na nunawa Hafsat yadda ake yin wani game a waya.

Tsaye Mama ta yi bakin kofa idanunta a kan Hafsat ta ce “Kin shirya ko?”

“Eh. Hijab kawai zan sanya, ya dawo ne Ya Tajuddeen din?”cewar Hafsat idanunta a kan Mama

” Eh. Bari su Nabila su fitar miki da kayan. Ke Nabila ku fitar mata da kayan. “

Juwairiyya ce ta dauki ledar da aka haɗawa Hafsat tsaraba, ita kuma Juwairiyya ta ja dan ƙaramin akwatinta zuwa waje. Yayin da Hafsat ke warware pink color hijab ta sanya. Sai fuskar nan ta kara annuri, siririn gashin girarta ya kwanta bakin kikkirin, yayin da fararen idanunta masu kama da an zuba musu Mangyada a ciki suka kara haske, dogon hancin nan nata ya kara tsawo gwanin sha’awa.

“Ma Sha Allah!” cewar Mama, babu, karya Hafsat mai kyau ce, da alama kuma kyan nata shi ne jarinta.

Plat shoe pink ta sanya, daidai lokacin kuma su Juwairiyya suka dawo, Mama kuma ta shiga aikawa da Hafsat addu’ar Allah Ya tsare hanya. Za kuma ta samu lokaci ta zo, saboda tun da Hafsat din ta zo ba su yi wata magana akan auranta ba.

Lokacin da suka bude karamar kofar gate suka fito, sai da ta dan yi turus, saboda motar da ta gani, ta san dai motar Abba(Alh Aminu) ba haka take ba, amma sai ta basar kawai ta ci gaba da tafiya kamar ba komai.

<< Abinda Ka Shuka 44Abinda Ka Shuka 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×